Skip to content

Venezuela

Venezuela ƙasa ce da ke arewacin nahiyar Latin America wadda tarihinta ya ƙunshi batutuwan arziki masu yawa, gwagwarmayar siyasa, da sauye-sauyen zamantakewa tun daga zamanin mulkin mallaka har zuwa wannan ƙarni da muke ciki. Daga al’ummomin asali kafin zuwan Turawa, zuwa mamayar Spain, yaƙin neman ‘yanci, da kafuwar tsarin mulki na ƙasa mai zaman kanta, Venezuela ta fuskanci jerin juyin juya hali da sauye-sauye masu tasiri ga makomarta. A ƙarnukan da suka gabata, ganowa da bunƙasar arzikin man fetur ya sauya tsarin tattalin arziki da siyasa, inda ya kawo ci gaba a wasu lokuta tare da ƙalubale masu tsanani a wasu.

Tuta da tambarin ƙasar Venezuela.

Wannan maƙala ta bi diddigin tarihin Venezuela ta hanyar duba manyan lokuta da suka tsara ƙasar, tun daga farkon rayuwa da mulkin mallaka, yaƙin ‘yanci, rikice-rikicen siyasa na ƙarni na 19, tsarin dimokradiyya na ƙarni na 20, har zuwa juyin juya halin Bolivaria da halin da ƙasar ke ciki a ƙarni na 21. Ta wannan tsari, maƙalar na nufin bayyana yadda tarihi, siyasa, da tattalin arziki suka haɗu wajen gina yanayin Venezuela na yau.

Farkon rayuwa a Venezuela

Tun kafin zuwan Turawa, yankin da ake kira Venezuela a yau ya kasance wuri mai yalwar al’adu da tsarin rayuwa na al’ummomin da. Ƙabilu irin su Arawak, Carib, da Chibcha sun kafa ƙauyuka masu tsari, inda suka dogara da noman gargajiya, farauta, kamun ƙifi, da kuma cinikayya tsakaninsu da sauran yankuna. Suna da ilimi kan yanayin ƙasa, koguna, da teku, lamarin da ya taimaka musu wajen samar da abinci da kayayyakin masarufi. Tsarin zamantakewarsu ya dogara da jagorancin gargajiya, girmama al’adu, da kuma rabe-raben aiki a tsakanin al’umma.

Zuwan Christopher Columbus a shekarar 1498 ya kawo babban sauyi ga wannan yanayi. Wannan ziyara ta buɗe ƙofa ga mulkin mallaka daga Turawa Spain, wanda daga bisani ya mamaye yankin gabaɗaya. Spain ta kafa birane, tashoshin jiragen ruwa, da cibiyoyin kasuwanci domin sarrafa albarkatun ƙasa da hanyoyin sufuri. Mulkin mallaka ya zo da sabon tsarin siyasa da addini, inda aka tilasta wa jama’ar koyon harshen Sifaniyanci da addinin Kiristanci, tare da kawar da al’adun asali. A lokaci guda, aka gina tattalin arzikin Turawan mulkin mallaka ta hanyar amfanin gona da albarkatu da ake fitarwa zuwa Turai, musamman coco da sauran albarkatun ƙasa.

Don cim ma hakan, an tilasta aiki mai tsauri ga al’ummomin asalin ƙasar da kuma bayi daga Afirka, waɗanda suka zama ginshiƙan samar da arziki a lokacin. Wannan tsarin ya haifar da tsananin rarrabuwar kawuna, inda Turawan mulkin mallaka suka mallaki iko da dukiya, yayin da yawancin jama’a ke fama da wahala da rashin ‘yanci. Tasirin wannan zamani ya bar dogon tarihi na rashin daidaito wanda ya ci gaba da bayyana a siyasar Venezuela har bayan samun ‘yanci.

Zaburarwa da yaƙi don neman‘yanci

A farkon karni na 19, yanayin siyasa da tunanin samun ‘yanci daga Turai da Amurka ya fara shiga zukatan ‘yan Venezuela. Ra’ayoyin juyin juya halin Faransa da Amurka sun ƙarfafa tunanin kawar da mulkin mallaka, musamman a tsakanin masu ilimi da ‘yan kasuwa da ke kokawa da haraji da danniya daga ƙasar Spain. Wannan zaburarwa ta haifar da ƙungiyoyin siyasa da tattaunawa kan makomar ƙasa da samun’yancin kai.

A ranar 5 ga Yuli, 1811, Venezuela ta ayyana ‘yancinta daga Spain, lamarin da ya kafa sabuwar gwamnati mai rauni saboda rashin haɗin kai da ƙarancin ƙwarewa a harkokin mulki da tsaro. Wannan ya bai wa Spain damar sake karɓar iko ta hanyar hare-haren soja. Duk da haka, gwagwarmayar ba ta mutu ba. Fitowar Simón Bolívar a matsayin jagora ya ba wa fafutukar sabon salo, inda ya haɗa ƙungiyoyin ‘yan gwagwarmaya tare da amfani da dabarun soja da siyasa wajen yaƙar Spain.

Yaƙe-yaƙe masu tsanani sun gudana a wurare daban-daban, inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi. Nasarar da aka samu a Yaƙin Carabobo a ranar 24 ga Yuni, 1821 ta zama muhimmiyar nasara da ta karya ikon Spain a yankin. Wannan nasara ta buɗe hanyar kafa Babbar Jamhuriyar Colombia, wacce ta haɗa Venezuela da wasu ƙasashe makwabta domin ƙarfafa tsaro da haɗin kai. Duk da haka, bambance-bambancen siyasa da sha’awar ikon kai sun sa Venezuela ta ɓalle a shekarar 1830, ta kafa kanta a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci, kodayake ta fuskantar ƙalubale na gina ƙasa daga tushe.

Rashin kwanciyar hankali da tsara mulki a ƙarni na 19

Bayan samun ‘yanci daga Spain, Venezuela ta shiga wani dogon lokaci na rashin kwanciyar hankali a siyasa. Sabuwar ƙasar ta fuskanci matsalolin gina ƙasa, rashin tsayayyen kundin tsarin mulki, da kuma rikicin ra’ayoyi tsakanin shugabanni kan wane tsari ya fi dacewa da tafiyar da ƙasa. Mulki ya riƙa sauyawa akai-akai ta hanyar juyin mulki da tashe-tashen hankula, inda manyan sojoji da masu ƙarfin siyasa ke fafatawa don mallakar iko. Wannan yanayi ya hana ƙasar samun cigaba mai ɗorewa a fannonin tattalin arziki da zamantakewa.

A tsakiyar ƙarni na 19, rikicin siyasa ya kai ƙololuwa da faruwar March Revolution a shekarar 1858, wacce ta kawo ƙarshen mulkin wasu fitattun shugabannin siyasa tare da rushe tsarin da ke wanzuwa a wancan lokaci. Wannan juyin juya hali ya buɗe ƙofa ga wani mummunan rikici mai tsawo da aka sani da Federal War, wanda ya gudana tsakanin 1859 da 1863. Yaƙin ya raba ƙasa gida biyu tsakanin masu son tsarin tarayya, waɗanda ke neman bai wa jihohi ‘yancin cin gashin kansu, da kuma masu goyon bayan tsarin tsakiya mai ƙarfafa ikon gwamnati. Wannan rikici ya haddasa asarar rayuka masu yawa, lalacewar tattalin arziki, da ƙara rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma, duk da cewa daga ƙarshe an amince da tsarin tarayya a matsayin tsarin mulkin ƙasar.

Sauye-sauye a ƙarni na 20

Shigowar ƙarni na 20 ya kawo sabon salo a siyasar Venezuela, musamman hawan Janar Juan Vicente Gómez mulki a shekarar 1908. Mulkinsa ya kasance mai tsaurin iko, inda ya kafa tsarin da ya takaita ‘yancin siyasa tare da murƙushe adawa. Duk da tsananin danniya, gwamnatin Gómez ta yi amfani wajen ganowa da haɓaka man fetur wanda ya gina tattalin arzikin ƙasar. Samuwar arzikin mai ta sauya Venezuela daga ƙasa mai dogaro da noma zuwa babbar ƙasa mai fitar da man fetur, lamarin da ya ƙarfafa kuɗaɗen gwamnati da tasirinta a duniya.

Sai dai wannan arziki bai wadatar da yawancin al’umma ba. Duk da kuɗaɗen da ke shigowa daga man fetur, rashin daidaito ya ƙaru, inda talakawa ke fama da talauci, ƙarancin ayyukan jin daɗin jama’a, da rashin tsayayyen tsarin walwala. Bayan mutuwar Gómez a 1935, an samu sauye-sauye a hankali, inda aka  buɗe ƙofa ga tattaunawar siyasa da ƙoƙarin gina tsarin dimokradiyya.

A shekarar 1945, wani juyin mulki da haɗin gwiwar sojoji da ‘yan siyasa ya kawo ƙarshen gwamnatin Isaías Medina Angarita. Wannan lamari ya zama muhimmin mataki a tarihin siyasar Venezuela, domin ya haifar da sauye-sauye da suka bai wa jama’a damar shiga harkokin siyasa kai tsaye. An fara shirya zaɓukan dimokuraɗiyya cikin gaskiya, ciki har da zaɓen shugaban ƙasa na farko da aka gudanar bisa ƙuri’ar jama’a. Wannan lokaci ya nuna ƙoƙarin ƙasar na fita daga mulkin danniya zuwa tsarin siyasa mai bai wa jama’a dama, kodayake ƙalubalen da suka biyo baya sun ci gaba da gwada ƙarfin dimokuraɗiyyar Venezuela.

Bunƙasas dimokraɗiyya da ribar mai

Daga shekarar 1958 bayan kifar da mulkin soja, Venezuela ta shiga wani zamani na dimokradiyya mai ɗorewa wanda ya bambanta ta da yawancin ƙasashen Latin America a wancan lokaci. Manyan jam’iyyun siyasa sun cim ma matsaya kan tsarin raba iko da gudanar da zaɓe cikin tsari, abin da ya kawo kwanciyar hankali ƙalilan a siyasa da rage yawan juyin mulki. Wannan yanayi ya bai wa ƙasar damar gina cibiyoyin gwamnati, ƙarfafa majalisar dokoki, da bunƙasa rawar jama’a a harkokin siyasa.

Shigar Venezuela cikin Ƙungiyar Ƙasashen masu arzikin man fetur (OPEC) a 1960 ya ƙara mata ƙarfi a tattalin arzikin duniya. Kuɗaɗen man fetur sun zamo ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar, inda gwamnati ta yi amfani da su wajen gina manyan ayyukan more rayuwa, faɗaɗa ilimi, inganta kiwon lafiya, da tallafa wa shirye-shiryen jin-ƙai. A wannan lokaci, an samu bunƙasar birane da matsakaitan rukunin jama’a, lamarin da ya ƙara tabbatar da matsayin Venezuela a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi wadata a yankin.

nicolas maduro queda solo ultimatum trump
Nicolás Maduro Moros shugaban ƙasar Venezuela, da Amurka ta kama tare da tsarewa a New York.

Sai dai daga ƙarshen shekarun 1970s zuwa 1980s, faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ta fallasa raunin tattalin arzikin da ya dogara kacokan kan man fetur. Gwamnati ta fara fuskantar matsalar ciyo bashi daga waje, hauhawar farashi, da ƙarancin ayyukan yi. Wannan matsin tattalin arziki ya jawo ƙarin rashin jin daɗi a cikin al’umma, wanda ya kai ƙololuwa a 1989. Zanga-zangar jama’a da ta ɓarke sakamakon tsauraran matakan rage kashe kuɗi ta rikiɗe zuwa tashin hankali mai tsanani, inda dubban mutane suka rasa rayukansu, lamarin da ya girgiza tushen tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Zamanin Hugo Chávez da juyin juya halin bolivaria

A tsakiyar shekarun 1990s, gajiya da rashin amincewa da tsohon tsarin siyasa ta ƙaru a tsakanin jama’a. Talauci, rashin daidaito, da zargin cin hanci sun rage martabar manyan jam’iyyun siyasa, yayin da al’umma ke neman sabon shugabanci da sauyi mai ma’ana. A wannan yanayi ne Hugo Chávez, tsohon jami’in soja, ya fito a matsayin wakilin jama’a da fatan kawo sabon salo a tafiyar da ƙasa.

Zaɓen Chávez a 1998 ya nuna juyin juya hali a siyasar Venezuela. Ya gabatar da abin da ya kira Juyin Juya Halin Bolivaria, wanda ya samo asali daga tunanin Simón Bolívar, tare da nufin sake fasalin ƙasa ta fuskar siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa. Manufofinsa sun mayar da hankali kan ƙarfafa ikon gwamnati, ƙwace ko sa ido kan manyan masana’antu, musamman na mai, da kuma rarraba arziki ta hanyar shirye-shiryen jin-ƙai da suka shafi talakawa.

A shekarar 1999, an rubuta sabon kundin tsarin mulki wanda ya sauya tsarin gwamnati, ya faɗaɗa ikon shugaban ƙasa, kuma ya sake fasalin cibiyoyin siyasa. Wannan kundin tsarin mulki ya bai wa Chávez damar aiwatar da manufofinsa cikin gaggawa, tare da ƙarfafa tasirin gwamnatin tarayya a fannoni da dama. Duk da samun goyon baya daga talakawa, manufofin Bolivaria sun jawo muhawara mai zafi daga ‘yan adawa da ƙasashen waje, waɗanda ke ganin tsarin na ƙara tattara iko a hannun shugabanci guda.

Mulkin Nicolás Maduro da rikicin zamani

Bayan mutuwar Hugo Chávez a 2013, Nicolás Maduro ya gaji shugabancin ƙasar a matsayin magajin Bolivaria. Mulkinsa ya zo ne a wani lokaci mai cike da ƙalubale, inda tattalin arzikin Venezuela ke fuskantar faɗuwar farashin mai, raguwar kuɗaɗen shiga, da tarin matsalolin da suka taru tun shekaru baya. Wannan yanayi ya sa gwamnatin Maduro ta fara mulki cikin yanayin matsin lamba daga cikin gida da waje.

A ƙarƙashin mulkinsa, Venezuela ta shiga cikin mummunar matsalar tattalin arziki wadda ta haɗa da matsanancin hauhawar farashi, faduwar darajar kuɗin ƙasa, da ƙarancin abinci da magunguna. Rayuwar talakawa ta tsananta matuƙa, lamarin da ya haifar da ficewar miliyoyin ‘yan ƙasa zuwa ƙasashen makwabta da sauran sassan duniya domin neman mafaka da rayuwa mai sauƙi. Rikicin tattalin arziki ya zama rikicin zamantakewa da na jin-ƙai a lokaci guda.

A fagen siyasa, mulkin Maduro ya fuskanci ƙalubale masu yawa daga jam’iyyun adawa, waɗanda suka zarge shi da murƙushe dimokraɗiyya, yin maguɗi a zaɓe, da amfani da kotuna da hukumomin tsaro wajen tsare ko hana ‘yan adawa. Wannan ya jawo ƙarin rarrabuwar kawuna a cikin al’umma, tare da sukar ƙasashen waje da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Rikicin zamanin Maduro ya zama ɗaya daga cikin mafi tsanani a tarihin Venezuela, ya nuna ƙarshen wani dogon zamani na gwagwarmayar siyasa da tattalin arziki a ƙasar.

Sabon tsarin siyasa bayan kame Nicolás Maduro

A farkon shekarar 2026, Venezuela ta tsinci kanta cikin wani mawuyacin hali na siyasa da tattalin arziki, bayan wani muhimmin aiki na ƙasashen waje da ya canja shugabanci a ƙasar. A ranar 3 ga Janairu, 2026, sojojin Amurka sun gudanar da wani babban atisaye wanda ya kai ga kame shugaban ƙasa Nicolás Maduro da matarsa, Cilia Flores, sannan aka tafi da su zuwa New York, Amurka don fuskantar tuhume-tuhume kan laifuka kamar narco-terrorism da fataucin makamai. Wannan lamari ya haifar da sabuwar dangantaka da Venezuela, inda Delcy Rodríguez, tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa, ta zama shugabar wucin gadi bisa umarnin kotun koli da goyon bayan rundunar sojoji, duk da cewa tsarin ƙunshin zaɓe da halaccin tafiyar da iko ya kasance a ƙarƙashin cece-kuce da suka zo daga cikin gida da waje.

Dangantaka da manyan ƙasashe da harkokin mai

Wannan sabon yanayi ya sa Venezuela ke cikin wata sabuwar dangantaka da ƙasashen duniya. A gefen tattalin arziki, an fara samun sauƙaƙe takunkumin Amurka da damar sayar da mai ta wasu hanyoyi bayan dogon lokaci na takunkumi da katange hanyoyin fitar da man fetur. Misali, kamfanin Citgo na Amurka ya sayi man fetur na Venezuelan karo na farko tun 2019, wata muhimmiyar alamar canji a dangantakar tattalin arziki da Amurka da Venezuela, inda aka cim ma yarjejeniya kan sayar da mai wanda zai taimaka wajen samun kuɗaɗe ga kasar.

4164
Shugabar riƙon-ƙwayar Venezuela da aka naɗa bayan kame Moduro.

A lokaci guda, akwai shirin da gwamnatin Amurka ta fito da shi don tattara kuɗaɗen man fetur a asusun gida a Qatar, daga nan a biya kasafin kudin gwamnati na wata da watanni, tare da tabbatar da cewa waɗannan kuɗaɗen sun amfani talakawa maimakon wasu ƙasashe ko kamfanoni na waje. Wannan ya ƙunshi matakan tsara yadda za a yi amfani da kuɗaɗen a harkokin lafiya, abinci, da sauran buƙatun al’umma.

Amma duk da cewa akwai wasu sauye-sauye a fagen tattalin arziki, wasu ƙasashe da ƙungiyoyi suna nuna tsananin damuwa kan tasirin siyasa da dokar ƙasa da ƙasa, inda suka ce irin wannan tsoma bakin ƙasashen waje na iya saɓa wa ka’idojin mulki na ƙasa da ƙasa da yancin ƙasa.

Rikicin siyasa da ƙalubale na cikin gida

A cikin gida, bayan sauye-sauyen shugabanci, an samu sakin wasu ‘yan siyasa, inda gwamnatin wucin gadi ta sanar da saki ɗaruruwan fursunoni ‘yan siyasa a ranakun farko na 2026 a matsayin wani yunƙuri na sassauta matsin lamba da kawo haɗin kai. Sai dai ƙungiyoyi masu kare haƙƙin ɗan Adam sun yi martanin cewa wasu daga cikin waɗannan sakin ba dukkan fursunonin siyasa ba ne, tare da cewa wasu har yanzu suna tsare bisa tuhume-tuhume da ake ganin ba su da hujja mai ƙarfi.

Tasirin tattalin arziki da buƙatu

Duk da ƙoƙarin farfado da fitar da man fetur da kuma sabunta tattalin arziki, Venezuela ta ci gaba da fuskantar matsalolin rashin kuɗaɗen shiga, tashin farashin kaya, da ƙarancin ayyuka ga al’umma. Duk da akwai wasu alamun sauƙi a harkokin samar da kuɗaɗen daga man fetur, masana tattalin arziki suna ganin cewa sake gina amintaccen tsarin tattalin arzikin ƙasar zai kasance aiki mai wahala, saboda dogaro da albarkatun mai na tsawon shekaru da kuma yawan asarar kuɗaɗen shiga a baya.

A halin yanzu, yawan mutanen Venezuela yana kusan kaiws 28.5 miliyan, tare da ƙaruwar al’ummomi ƙanana saboda ficewar mutane zuwa ƙasashen waje a baya, wanda ke ƙara wa gwamnati nauyi wajen samar da ayyukan jin daɗin jama’a da kuma farfado da tattalin arziki.

Jerin shugabannin Venezuela

1. José Antonio Páez (1830–1835): Shi ne shugaban farko bayan Venezuela ta ɓalle daga Gran Colombia. Ya taka rawa wajen kafa jamhuriya da tsarin mulkin ƙasa.

2. José María Vargas (1835–1836): Likita ne kuma farar hula na farko da ya zama shugaban ƙasa. Mulkinsa ya fuskanci juyin mulki, lamarin da ya sa ya sauka da wuri.

3. Carlos Soublette (1837–1839): Shugaba mai ƙoƙarin samar da kwanciyar hankali bayan rikice-rikicen farko na jamhuriya.

4. Julián Castro (1858–1859): Mulkinsa ya zo ne bayan March Revolution. Ya gaza shawo kan rikicin siyasa da ya haifar da Federal War.

5. Juan Crisóstomo Falcón (1863–1868): Jagoran masu ra’ayin tarayya bayan Federal War. Ya kafa tsarin tarayya amma mulkinsa ya kasance mai rauni.

6. Antonio Guzmán Blanco (1870–1888): Shugaba mai tasiri sosai. Ya aiwatar da sauye-sauyen zamani a ilimi, gine-gine, da tsarin gwamnati.

7. Joaquín Crespo (1892–1898): Shugaba daga fannin soja. Mulkinsa ya kasance cike da rikicin siyasa da juyin mulki.

8. Cipriano Castro (1899–1908): Ya hau mulki ta hanyar juyin juya hali. Mulkinsa ya nuna ƙarfin soja da rikici da ƙasashen waje.

9. Juan Vicente Gómez (1908–1935): Shugaba mai kama-karya na dogon lokaci. Ya kafa tsarin tsakiya mai ƙarfi kuma ya fara bunƙasa samuwar man fetur.

10. Eleazar López Contreras (1935–1941): Ya rage tsaurin mulkin kama-karya bayan Gómez. Ya fara buɗe ƙofa ga dimokuraɗiyya a hankali.

11. Isaías Medina Angarita (1941–1945): Ya ƙara faɗaɗa ‘yancin siyasa da jam’iyyun siyasa kafin juyin mulkin 1945.

12. Rómulo Betancourt (1945–1948): Jagoran dimokradiyya ne. Mulkinsa ya kawo zaɓe na gaskiya kafin sojoji su kifar da gwamnatin.

13. Marcos Pérez Jiménez (1952–1958): Shugaban soja ne mai kama-karya. Ya yi manyan ayyukan more rayuwa amma ya tauye ‘yanci.

14. Wolfgang Larrazábal (1958–1959): Shugaban rikon ƙwarya bayan kifar da mulkin soja. Ya jagoranci dawowar dimokraɗiyya.

15. Rómulo Betancourt (1959–1964): Ya kafa tsarin dimokradiyya mai ɗorewa. Ya tsaya tsayin daka kan juyin mulkin soja.

16. Raúl Leoni (1964–1969): Ya ci gaba da tsarin dimokraɗiyya tare da fuskantar ƙungiyoyin ‘yan tawaye.

17. Rafael Caldera (1969–1974): Ya yi sulhu da ‘yan tawayen siyasa. Mulkinsa ya kawo sassaucin siyasa.

18. Carlos Andrés Pérez (1974–1979): Mulkinsa ya ci gajiyar arzikin man fetur. Ya faɗaɗa ayyukan gwamnati sosai.

19. Jaime Lusinchi (1979–1984): Mulkinsa ya fuskanci matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashi.

20. Carlos Andrés Pérez (1989–1993): Karo na biyu mai cike da rikici. Manufofinsa sun haifar da Caracazo da kuma tsige shi.

21. Rafael Caldera (1994–1999): Ya sake dawowa mulkia karo na biyu. Ya fuskanci matsalar tattalin arziki da rashin amincewa da tsohon tsarin siyasa.

22. Hugo Chávez (1999–2013): Ya kafa Juyin Juya Hali na Bolivaria. Ya sauya tsarin siyasa, ya ƙarfafa ikon gwamnati, kuma ya shahara a duniya.

23. Nicolás Maduro (2013–2026): Magajin Chávez. Mulkinsa ya kasance cikin tsananin rikici na tattalin arziki, siyasa, da cece-ku-ce a duniya.

Albarkatun ƙasar Venezuela

1. Man Fetur: Man fetur shi ne mafi girma kuma mafi muhimmanci a tattalin arzikin Venezuela, wanda ke samar da kusan 95% na kuɗaɗen shiga daga fitar da shi. Kasar na daga cikin manyan masu fitar da man fetur a duniya, musamman mai nau’in heavy crude da ke daga filayen Zulia da Orinoco Belt.

2. Iskar Gas: Venezuela na da manyan ma’ajiyun iskar gas, kusan 5–6% na ajiyar duniya. Ana amfani da shi wajen samar da wutar lantarki a cikin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje, musamman zuwa Amurka da Caribbean.

3. Zinare: Zinare ya kasance babban albarkatu mai mahimmanci, kodayake yana da kaso ƙasa da 1% na tattalin arzikin ƙasar da ake fitarwa. Ana hakowa a yankunan Guayana da Bolívar, inda ake amfani da shi wajen tallafawa ajiyar kudin ƙasa.

4. Karafa (Iron Ore da Copper): Venezuela na da karafa da dama, musamman iron ore da copper, wanda ke ba da gudunmawa ga masana’antu da kuma fitarwa. Iron ore yana da kimanin 0.5–1% na tattalin arzikin ƙasar da ake fitarwa, yayin da copper ke ɗaukar kaso kaɗan.

5. Bauxite: Bauxite na da mahimmanci wajen samar da aluminium. Venezuela na ɗaya daga cikin ƙasashen Latin America da ke da tarin sinadarin bauxite, sai dai kason da ake fitarwa ƙasa da 1% ne.

6. Lu’u-lu’u: Kasar na da arzikin lu’u-lu’u (diamonds) a yankin Guayana, wanda yake da ƙima amma kason da ake bi fitarwa bai wuce 0.1–0.2% ba.

7. Albarkatun ruwa: Ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen samar da wutar lantarki ta hanyar hydroelectric power, musamman a dam ɗin Guri da Caruachi, wanda ke ba da kusan 70% na wutar lantarki a ƙasar.

8. Dazuzzuka: Dazuzzukan Venezuela suna da arzikin itatuwa, namun daji, da kayan noma. Ana amfani da su wajen samar da kayan gini, itacen mai amfani, da kuma halittu.

9. Filayen noma: Filayen noma sun haɗa da shukoki kayan abinci, kamar masara, shinkafa, da wake. Duk da haka, kason da ke shiga cikin tattalin arzikin ƙasar daga noma bai da yawa sosai, saboda dogaro da man fetur.

10. Albarkatun reku: Venezuela na da teku mai faɗin arziki a yankin Caribbean, wanda ke samar da kifi da albarkatun ruwa. Haka nan akwai damar haɓaka man fetur da iskar gas a karkashin ruwa, wanda zai iya ƙara kaso mai yawa a tattalin arziki nan gaba.

Manazarta

BBC News. (2024a, September 9). Venezuela country profile. BBC News

Britannica Editors (January 4, 2026) History of Venezuela. Britannica

Reach a village ministries. (n.d.). Venezuela.  Reach a village ministries

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×