Wari, musamman na hammata, ɗaya ne daga cikin matsalolin da suka shafi lafiyar jiki da mu’amalar yau da kullum. Sannan wari na iya hana mutum samun girmamawa, ko sa shi ya zama abin ƙyama a cikin jama’a, don kuwa Hausawa kan ce “Tsafta rigar arziki ce.”
Duk da cewa wari ba cuta ba ne kai tsaye, amma yana iya zama alamar rashin tsafta, wata matsalar lafiya, ko kuma tasirin sinadarai na jikin mutum. A al’adance, mutane kan ɗauki wari a matsayin abu mai sa kunya da rashin daraja, musamman idan mutum bai san kansa ba ko kuma bai yi ƙoƙarin gyarawa ba.
Ma’anar warin hammata
Warin hammata wani yanayi ne da ke faruwa lokacin da gumi ke fita daga jikin mutum ya haɗu da ƙwayoyin cuta (bacteria) da suke a saman fata, wanda hakan ke haifar da wari mai ɗaci marar daɗi. A likitance ana kiran wannan yanayi da Bromhidrosis. Sannan warin hammata ya fi faruwa a lokacin zafi, ko lokacin da aka yi aiki mai cike da gajiya.
Bambancin warin hammata da na sauran jiki
Yanayin warin hammata ya sha bamban da dukkan wari, a taƙaice ma za a ce shi kaɗai ke da irin wannan wari. To ga dalilan da suka kawo haka:
Ƙwayoyin halittar gumi (sweat glands)
Jikin ɗan’adam yana da eccrine glands da apocrine glands, Eccrine glands suna ko’ina a jiki, suna fitar da ruwa mai sanyi da gishiri kawai, wanda ba ya wari sosai. Apocrine glands kuwa suna da yawa a hammata da matsematsin cinya, suna fitar da gumi mai ɗauke da kitse da furotin. Wannan gumin ba shi da wari kai tsaye, sai dai yana zama abinci ga ƙwayoyin bakteriyar da ke rayuwa a jikin fata.
Aikin bakteriya
A hammata akwai yawaitar corynebacterium da wasu nau’in bakteriya masu zuƙar wannan gumi, suna fitar da sinadarai masu wari (volatile fatty acids da sulfur compounds). Wannan sinadarai ne ke sa hammata wari mai ƙarfi fiye da sauran jiki. Don haka, hammata ce cibiyar haɗuwar gumi na musamman, ƙwayoyin sha’awa hormones, bakteriya, wanda hakan yake sa warinta ya fi kowace gaɓa ƙarfi da bambanci.
Dalilan da ke janyo warin hammata
Daga cikin dalilan da ke haifar da warin hammata akwai:
- Rashin tsafta: Idan ya kasance mutum ba ya yin wanka ko wanke hammatarsa sosai, musamman bayan gama aiki ko motsa jiki, gumi yana taruwa, haɗe da ba wa bakteriya damar yawaita.
- Yanayin halitta: Wasu mutanen kuma a halittar jikinsu suna da ƙwayoyin halittar gumi masu yawan fitar da sinadaran (protein da fatty acids) da ke sauƙaƙa haifar da wari.
- Tufafi marasa tsafta: Sanya kaya masu datti, ko kayan da ba su tsotse gumi yadda ya kamata kan sa wari ya tsananta.
- Nau’in abinci: Cin albasa, tafarnuwa, kayan yaji masu ƙarfi da kuma shan giya suna ƙara yawaitar wari.
- Matsalolin lafiya: Akwai cututtuka da dama da kan iya haddasa wari, misali:
- Ciwon sukari: na iya sa numfashi da gumi su riƙa wari.
- Cututtukan hanta ko ƙoda: suna iya canja ƙamshin jiki.
- Hormonal imbalance: musamman a lokacin balaga ko lokacin haila.
Illolin warin hammata
- Illa a cikin zamantakewa: Wari na iya sa mutum ya zama abin gujewa a wajen jama’a, musamman a wuraren taro, aiki ko makaranta.
- Illa ga tunani: Yana iya haifar da rashin ƙwarin gwiwa, kunya, da rashin yarda da kai.
- Illa ga aure ko soyayya: A wasu lokuta wari kan kawo matsala a zamantakewar iyali ko soyayya har a kai ga rabuwa.
- Al’ada: A cikin al’adar Hausawa, mutum mai wari kan zama abin dariya ko habaici a wurin mutane.
Hanyoyin magance warin hammata
- Tsaftar yau da kullum: Yin wanka aƙalla sau ɗaya ko fiye a rana da sabulu mai kawar da ƙwayoyin bakteriya. Sannan goge hammata da kyau bayan wanka haɗe da fesa turare yana rage wari.
- Amfani da kayan tsafta na zamani: Irinsu Deodorant da ke hana wari ta hanyar kashe ƙwayoyin bakteriya. Da kuma Antiperspirant da ke rage fitar gumi.
- Canja tufafi akai-akai: Sanya kaya masu tsotse gumi, irin su cotton, tare da kauce wa tufafin roba ko masu tsuke fata.
- Hanyoyin gargajiya: Ana amfani da ganyen zogale da aka murje a riƙa shafawa. Sannan goga lemun tsami ko ruwan ganyen neem (dogonyaro). Amfani da baking soda ma yana rage wari. Toka da alimun ma na cikin abubuwan da gusar da warin hammata
- Magungunan asibiti: Idan wari ya wuce misali, likita zai iya ba da shawarar magunguna ko tiyata kamar cire ƙwayoyin halittar gumi (Botox injections ko sympathectomy).
- Aske gashin hammata: Aske gashin hammata na cikin abubuwan da ke rage wari, domin gashi na riƙe danshi sosai, don haka idan ya zama ba gashin, to za a samu sauƙin danshin da ke haɗuwa da bakteriya har ya haifar da wari.
Warin hammata a al’adar Hausawa
A al’adun Hausawa, wari ana kallon sa a matsayin rashin tsafta ko sakaci. Inda auren mace ko namiji mai wari na iya zama abu mai wahala saboda jama’a kan ɗauka cewa mutum mai wari ba ya iya gyara gida. Haka kuma, an fi ganin wari a matsayin abin dariya da habaici. Hausawa kan ce:
“Wanda bai yi wanka ba, ya yi kamar wanda bai yi sallah ba.”
“Wari kan kori jama’a, ko da mutum mai daraja ne.”
Warin hammata ba cuta ba ne kai tsaye, sai dai yana ɗauke da nauyin da ya shafi lafiya, zamantakewa da kuma tunanin mutum. Tsafta da ɗabi’ar kiyaye kai su ne ginshiƙai na kawar da shi. Sannan a addinace ma idan mutum na kawar da warin hammata kamar yana cika imaninsa ne, saboda “Tsafta tana daga cikin Imani”, kuma “Allah maɗaukakin Sarki Mai Tsarki ne… Sannan Shi mai kyau ne, kuma yana son mai kyau”. Shi kuma warin hammata ƙazanta ce, don haka cikar kamalar mutum har a addini shi ne ya riƙa kawar da shi.
Wasu dabarun magance warin hammata
- A samu lemun tsami a raba biyu a goga a hammata bayan an yi wanka. Ko kuma a matse ruwan sannan a samu tawul a rika tsomawa, a rinka shafawa a hammata bayan an yi wanka kafin a sanya tufafi. A rika yin haka don magance wannan matsala.
- ‘Rose water’ na taimakawa wajen magance warin hammata. Don haka sai a rika diga ruwan a cikin ruwan wanka, sannan a shafa a hammata bayan an yi wanka.
- A matse ruwan tumatiri sannan a shafa a hammata na tsawon mintuna 15 sannan a shiga wanka. Amma irin wannan zai dan dauki lokaci kamar mako daya kafin a rabu da warin hammata.
- Amfani da alumu “alum “na taimakawa matuka. Sai a tsaoma alum a ruwa, sannan a shafa ruwan a hammata a bari ruwan ya bushe. Yin hakan na magance warin hammata.
- Hodar jarirai na magance warin hammata, domin tana dauke da kamshi sai a rinka shafawa a hammata a kullum bayan an fito daga wanka.
- An san itace ‘sandalwood’ da kamshi sai a samu hodarsa a kwaba da ruwa, sannan a shafa a hammata na tsawon mintuna 20 sai a wanke.
- Man amfuna na taimakawa wajen magance warin hammata. A samu man amfuna a shafa karkashin hammata bayan an fito daga wanka.
Manazarta
Cleveland Clinic. n.d. Body Odor: Causes, Changes, Underlying Diseases & Treatment. Cleveland Clinic.
Healthline. (2023). Smelly armpits: Causes, treatments, prevention, and more. Healthline.
- Medical News Today. 2023. Smelly Armpits: Causes, Treatment, Prevention, and When to Seek Help. Medical News Today
PharmEasy. n.d. Best Home Remedies for Smelly Armpits. PharmEasy.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 2 January, 2018
An kuma sabunta ta 24 August, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.