Ciwon yoyon fitsari yana da alaƙa kai tsaye da ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da mace-macen mata masu juna biyu, wato naƙuda mai tangarda. Ana samun ciwon ne sakamakon doguwar nakuda yayin da da yake yunkurin fitowa, inda kuma mahaifiyar ba ta samun kulawar gaggawa da ta dace a asibiti. Haka nan, sashen al’aurar mace na iya kamuwa da cuta, kuma za ta iya jin zafi yayin saduwar aure.

A kowace shekara a faɗin duniya mata kimanin 50 000 zuwa 100 000 suna fama da ciwon yoyon fitsari. Yoyon fitsari cuta da ke faruwa dalilin buɗewar wata ƙofa tsakanin al’aurar mace da mafitsararta ko duburarta. Matan da ke fama da ciwon yoyon fitsari na fuskantar rashin natsuwa, jin kunya, wariya da matsalolin lafiya. An yi kiyasin cewa sama da mata miliyan 2 ne ke fama da yoyon fitsari ba tare da kulawar magani ba a Asiya da yankin kudu da hamadar Sahara.
Matsalar yoyon fitsari matsala ce da ke addabar mata musamman a kasashen yankin Afrika inda yawancinsu ke kamuwa da cutar bayan haihuwa. Kuma wannan Cutar ta yoyon fitsari takan sa mazajensu kyamatar su har ya kai ga mutuwar aure. Masana harkokin lafiya a Nijeriya sun ce ana samun adadin masu fama da cutar yoyon fitsari a ƙasar sakamakon dalilai da dama ciki har da mummunar fahimtar da ake da ita game da zuwa asibiti a yayin renon ciki. Alƙaluma sun nuna duk shekara ana samun mata kimanin 12,000 zuwa 15,000 wani lokaci har 20,000 ma, da ke kamuwa da cutar yoyon fitsari.
Alamomin yoyon fitsari
Yoyon fitsari ba kasafai yakan yi ciwo ba, amma yana iya haifar da wasu matsalolin da ke buƙatar kulawar likita. Idan aka samu buɗewa tsakanin farji da mafitsara, fitsari zai ci gaba da zubowa daga mafitsarar zuwa cikin farji. Idan haka ta faru, to mace ba za ta iya sarrafa fitsari ba, ba za ta iya riƙe shi ba. Zai riƙa fita ne da zarar ya taru a farjinta. Sauran alamomin yoyon fitsari sun hada da:
- Zazzaɓi
- Ciwon ciki
- Zawo/gudawa
- Rage nauyi
- Tashin zuciya
- Yin amai
Dalilan da ke haifar da yoyon fitsari
A mafi yawan lokuta yoyon fitsari na aukuwa dalilin lalacewar wani nama a al’aurar mace saboda abubuwa kamar:
- Haihuwa
- Tiyatar ciki (sashin mahaifa ko cesarean)
- Ciwon mahaifa, ko kansar hanji
- Magungunan radiation
- Cutukan hanji kamar Crohn’s ko diverticulitis
- Kamuwa da cutar sanyi ko ƙaruwar da mace kan yi lokacin haihu
- Yin rauni, kamar daga hatsarin mota
Gwaje-gwajen yoyon fitsari
Likitan zai yi bincike tare da gwajin ƙashin ƙugu (pelvic) sannan ya yi mace tambayoyi game da tarihin yanayin lafiyarta don gano ko tana da wasu abubuwan haɗari da kan haifar da cutar yoyon fitsari, kamar tiyatar da ba a daɗe da yi ba, ciwon sanyi da sauran su. Bayan haka likitan kan iya ba da umarnin yin wasu gwaje-gwaje suka haɗa da:
Dye test
Likita zai cika mafitsara da sinadarin rini, sai ya umarci mai larurar da ta yi tari. Idan tana da yoyon fitsari, sinadarin rinin zai zubo a cikin farjinta.
Cystoscopy
A wannan gwajin, likita zai yi amfani da wata na’urar siririya mai suna cystoscope don bincika cikin mafitsara da urethra domin gano alamomin lalacewa.
Hoton X-ray
Shi ma wannan hanya ta gwajin cutar yoyon fitsari, gwaji ne na musamman wanda ake yi wa mace allurar sinadarin rini ta mafitsara a cikin fitsar. Yayin hoton X-ray kan nuna ko akwai yoyo tsakanin mafitsari da farjin mace.
Fistulogram
Wannan ma hoton X-ray ne na yoyon fitsari. Zai iya nuna wa likita ko mace na da cutar yoyon fitsari ɗaya ko da yawa ko kuma idan wasu gabobin ƙashin ƙugu matsalar ta shafe su.
Flexible Sigmoidoscopy
Yayin wannan gwaji likita yana duba dubura da na’urar sigmoidoscope (wani siriri, bututu tare da ƙaramar kyamarar a saman shi).
CT urogram
Ana yi wa mace allurar sinadarin rini a cikin jijiya,sai na’urar CT scans ta ɗauki hotunan farji da na fitsari.
Hanyoyin magance cutar yoyon fitsari
Wasu nau’ikan yoyon fitsari na iya warkewa da kansu. Idan cutar yoyon fitsarin ba ta tsananta ba, likita na iya amfani ƙaramin bututu da ake kira catheter a cikin mafitsara don fitar da fitsarin da ya shiga cikin farji kuma ya ba wa sashen da cutar take lokaci ta warke da kanta.

Haka nan likita zai iya amfani da wasu sinadaran gam da aka yi da sinadaran frotin don rufe ko cike ƙofar yoyon fitsari. Har ila yau zai iya ba da magunguna don magance matsalar kamuwa da cutar sanyi a dalilin yoyon fitsari.
Yawancin mutanen da ke da yoyon fitsari suna buƙatar tiyata. Irin nau’in tiyatar da za a yi wa mace ya dogara da nau’in cutar yoyon fitsarin da kuma inda take. Ga yoyon fitsarin farji wanda ke haɗuwa da dubura, likita na iya:
- Yin ɗinki na musamman a wajen da cutar yoyon fitsarin take
- Gutsirar tantanin tsoka daga wani wuri a jiki don rufe ƙofar yoyon fitsarin
- Riɓanya maɗaɗɗiyar tsoka mai lafiya a wajen da cutar take
- Gyara tsokokin dubura idan sun samu matsala
Ƙalubalen cutar yoyon fitsari
Yoyon fitsarin farji na iya zama mai matsala da takura da jin kunya lokacin da ya zubo yakan haifar da wari marar daɗi. Hakazalika yana iya haifar da matsaloli kamar:
- Cututtukan farji ko na hanyar fitsari da ke tafiya da dawowa
- Matsalolin tsafta da kazanta
- Kashi ko tusa wanda ke zubowa ta cikin farji
- Rikicewa ko kumburin fatar kusa da farjin ko dubura
- Kumburowar wani nama mai cutarwa wanda zai iya zama haɗari idan ba a magance shi ba.
Yoyon fitsarin mai dawowa
Matan da ke fama da cutar Crohn, wata cuta ce mai kama sashen hanji, wannan cuta na haifar yiyuwar da babban haɗarin cutukan masu rikitarwa, kamar yoyon fitsari da ke sake dawowa daga baya ko kuma yoyon fitsari wanda ba ya warkewa gabaɗaya.
Manazarta
Mayo Clinic (n .d.). Vaginal fistula – Symptoms and causes. Mayo Clinic.
Cleveland. (2024, May 20). Fistula. Cleveland Clinic.
Musa, I. I. (2022, November 7). Mu leka rayuwar matan aure masu yoyon fitsari. Aminiya.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.