Zaizayar ƙasa wata alama ce da ke nuna motsawar ƙasa daga wurinta na asali zuwa wani wuri daban. Saboda tasirin wasu muhimman abubuwa da suke samar da hakan, kamar iska, ruwa, ko kuma wasu ayyukan ɗan Adam. Binciken masana ya tabbatar da cewa, an kiyasta rabin ƙasar da ke saman duniya ta ɓace a cikin shekaru 150 da suka wuce sakamakon zaizayar ƙasa.
Zaizayar ƙasa na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar duniya tana shafar abinci, ruwa, da muhalli gabaɗaya. Amma ta hanyar noma, rage sare itatuwa, da sarrafa kiwo yadda ya dace, ana iya dawo da ƙasar da ta lalace tare da kare albarkatun ƙasar baki ɗaya. Ƙasa ita ce ginshiƙin ga rayuwar da take wanzuwa a doron ƙasa.

Ƙasa cike take da ƙwayoyin halittu masu yawa waɗanda ke haifar da tsarin halitta, kuma tana daga cikin mafi muhimmancin albarkatun da ɗan Adam ke dogaro da su a duniya bakiɗaya. Sauye-sauye da dama kan kawo dalilan dake sa ƙasa ta samu zaizayawa wanda hakan kan zama abin da kan hana ƙasa samun cigaba.
Nau’ikan zaizaya
Akwai nau’ikan zaizaya waɗanda suka haɗar da:
Splash erosion
Wannan nau’i na zaizayar ƙasa yana faruwa ne lokacin da digon ruwan sama ke bugun ƙasa da ƙarfi. Buguwar nan tana haifar da watsewar ƙwayoyin ƙasa, inda suke tashi sama ko gefe. Idan ruwan sama ya yi yawa, ƙwayoyin ƙasar da suka watse suna iya yin haɗuwa da ruwa su tafi zuwa wasu wurare, ta haka ƙasa ke rasa ingancinta. Wannan shi ne matakin farko na duk wata zaizayar ƙasa ta ruwa.
Sheet erosion
Sheet erosion na faruwa ne lokacin da ruwa ke wucewa a hankali a saman ƙasa gaba ɗaya, ba tare da ƙirƙirar hanya ko rami ba. Wannan yana haifar da goge ko wanke ƙasa a shimfiɗe, yana rage zurfi da sinadaran ƙasa (nutrients). Ƙasa tana zama mara ƙarfi ga shuka, musamman a wuraren da babu ciyayi.
Rill erosion
A wannan mataki, ruwan sama yana haifar da ƙananan hanyoyi ko ramuka a saman ƙasa yayin da yake gudana. Waɗannan ramukan, da ake kira rills, sukan kasance ƙanana amma suna ƙaruwa da lokaci idan ba a yi gyara ba. A gonaki bayan ruwan sama, ana iya ganin ƙananan rafuffukan ruwa da suka sare ƙasa.
Gully erosion
Gully erosion yana faruwa ne idan waɗancan ƙananan ramuka na rill erosion suka zurfafa suka zama manyan kwaruruka ko ramuka. Wannan nau’i na zaizayar ƙasa yana iya raba ƙasa gida biyu ko lalata gonaki da hanyoyi gaba ɗaya. Rashin tsare ƙasa da ciyayi, yawan ruwan sama, da gangaren ƙasa mai tsanani.
Wind erosion
Wind erosion ita ce lalacewar ƙasa da ake samu sakamakon iska mai ƙarfi da ke tashi da ƙurar ƙasa ta ɗauke ta zuwa wani wuri. Ana samun ta a wuraren da ƙasa ta bushe kuma babu ciyayi ko bishiyoyi da za su riƙe ƙasa. Misali: a hamada ko ƙasashen da ake fama da fari, iska tana iya rufe gonaki da ƙura, tana rage ingancin ƙasa.
River erosion
Zaizayar kogin tana faruwa ne lokacin da ruwan kogin ke yanke gefen kogin ko ƙasan sa yayin da yake gudu. Tsawon lokaci, wannan motsi yana sa kogin ya zurfa, ya faɗa, ko ya canza hanya. Gefen koguna na iya rushewa, bishiyoyi su faɗi, ko hanyoyi su lalace.
Hill erosion
Hill erosion tana faruwa ne a tudai ko duwatsu, inda ruwan sama ke zamewa ƙasa yana ɗauke da ƙwayoyin ƙasa zuwa ƙasan tudu. Rashin ciyayi da sare itatuwa na ƙara yawan wannan matsala. Misali: bayan an sare bishiyoyi a tudu, ana yawan samun ƙasa tana gangarowa ƙasa bayan ruwan sama mai yawa.
Dalilan da ke kawo zaizayar ƙasa
-
Ruwa mai ƙarfi
Hakan na faruwa ne sakammakon zubar ruwa mai ƙarfi daga sama yana dukan ƙasa, a irin wannan yanayi zubar ruwan kan ɗauke ƙasa, musamman a wuraren da babu ciyayi ko itatuwa ko kuma ƙasa mai ƙarfi.
-
Guguwa/iska
Wannan na faruwa ne sakamakon afkuwar iska mai ƙarfi tana ɗaukar ƙura ko kuma laka daga asalin wurin da take zuwa wani waje na daban. Musamman a hamada ko ƙasar da ta bushe.
-
Kiwon dabbobi
Sauya ƙasa daga dazuzzuka zuwa wajan kiwo ga makiyaya ba ya da illa, domin hanya ce ta samarwa dabbobi abinci. Amma daga baya yana jawo zaizaya da asarar ƙasa mai kyau. Idan dabbobi suna da yawa a fili ɗaya, suna cin ganyaye fiye da ƙima, wanda ke cire kariya daga ƙasa, ya sa iska da ruwa su rika fasa ta. Wannan yana hana sabbin tsirrai girma, ruwa baya shiga ƙasa yadda ya kamata, ƙwayoyin ƙasa suna mutuwa, sannan zaizayar ƙasa ta tsananta.
-
Magunguna/sunadarai
Amfani da magungunan kashe ƙwari da takin zamani ya taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, amma amfani da fiye da ƙima yana lalata tsarin ƙasa. Masana sun gano cewa wasu sinadarai suna canza yanayin ƙasa, suna halaka ƙwayoyin da ke da amfani, suna kuma ƙara yawaitar ƙwayoyin cuta masu illa. Wanda rashin ƙwarin sinadaran jikinta kan haifar da zaizayawa cikin ƙanƙanin lokaci.
-
Aiyyukan ɗan Adam
Wannan na faruwa ne sakammakon wasu aiyyuka na ɗan Adam, wanda yake gudanarwa saboda buƙatar kansa ko kuma wani abu na daban. Kamar noman da ba a yi shi cikin tsari da kyautatawa ba, sare itatuwa, ko gini ba tare da yin fundishan mai inganci ba, hakan kan haifar da zaizayar ƙasa. Yin gine-gine akan hanya ba bisa tsari ba, yana haifar da toshewa ruwa hanyar da ya kamata ya bi, daga nan sai ya soma bin duk hanyar da zai bi domin samawa kansa hanya wanda a hankali zai soma zaizaye inda yake bi domin ba nan ce asalin hanyarsa ba.
Illolin zaizayar ƙasa
Zaizayar ƙasa tana da matuƙar illa ga rayuwar al’umma, wala ta fanin inganta muhalli ko kuma samar da kyakkyawar hanya musamman a manyan hanyoyin da suke buƙatar haka. Daga cikin illolinta akwai:
- Rage amfanin gona
- Lalata gonaki da filaye
- Haifar da ambaliya
- Lalata hanyoyi da gine-gine
- Haifar ƙaura ga al’umma saboda lalacewar ƙasar muhalin da suke.
Hanyoyin daƙile zaizayar ƙasa
Daga cikin hanyoyin da za’a kawar da zaizayar ƙasa akwai:
- Dashen itatuwa da kuma ciyayi.
- Gina shinge ko katanga (terraces).
- Yin noma mai tsari da kula da ƙasa yadda ya kamata.
- Rage sare itatuwa.
- Rage gine-gine ba bisa ƙa’ida ba.
- Samar da hanyoyin magunan ruwa.
Amfanin zaizayar ƙasa
A kodayaushe ana kallon zaizayar ƙasa a matsayin matsala mai lalata muhalli, amma a wasu lokuta tana da fa’ida idan ta kasance cikin iyaka. Don haka tana da amfani a fannoni daban-daban kamar noma, yanayin ƙasa da kuma tattalin arziki. Ga wasu daga cikin amfaninta:
-
Ƙara ingancin ƙasa a wasu wurare
Lokacin da ruwa ko iska suka ɗauko ƙasa daga wani wuri zuwa wani, sau da yawa tana taruwa a ƙananan wurare inda ake samun ƙasar da ta fi kyau domin yin noma. Wannan yana taimaka wa manoma wajen noman kayan marmari da sauran amfanin gona.
-
Haɓaka ma’adinai a ƙasa
Zaizayar ƙasa na iya kawo ƙasa daga ƙasan ƙasa zuwa sama, inda take ƙara sabbin sinadarai (minerals) da ke taimakawa girman tsiro da ƙara yawan amfanin gona.
-
Ƙirƙirar sabbin siffofin ƙasa
A wasu lokuta, zaizayar ƙasa na haifar da kwaruruka, koguna da fadamu, waɗanda ke amfani wajen ajiyar ruwa, noma, ko kuma yawon buɗe ido. Wannan na iya taimaka wa tattalin arziƙin yankuna.
-
Taimakawa wajen nazarin tarihin ƙasa
Masana kimiyya na amfani da bayanan zaizayar ƙasa wajen nazarin tsarin ƙasa, gano tsoffin ma’adinai da fahimtar yadda ƙasa ta sauya tsarinta tsawon lokaci.
-
Ƙara amfani da albarkatun ruwa
Zaizayar ƙasa na taimaka wajen samar da wuraren da ruwa ke taruwa kamar tafkuna ko fadamu, wanda ke taimakawa wajen kiwo da noman rani.
-
Tasirin zaizayar ƙasa
Tasirin zaizayar ƙasa ba ya tsaya ga rasa ƙasar ba ne kawai. Hakan yana haifar da gurɓatar ruwa da taruwar laka a cikin koguna da rafuka, wanda ke sa hanyoyin ruwa su toshe, sannan kifi da sauran halittu su ragu. Ƙasashen da suka lalace kuma suna rasa ikon riƙe ruwa, wanda ke ƙara haɗarin ambaliya.
Lafiyar ƙasa muhimmin abu ne ga manoma da duk al’ummar duniya, domin rayuwarsu tana dogaro da kyakkyawan tsarin noma wanda yake farawa da ƙasan da ke ƙarƙashin ƙasa.
Lokacin da gonaki suka maye gurbin tsirrai, ƙasar sama tana bayyana kuma tana bushewa. Yawan da kuma nau’in ƙwayoyin halitta da ke sa ƙasa ta kasance mai ƙarfi suna raguwa. Abubuwan gina jiki suna salwanta yayin da ruwan sama ke wanke su. Ƙasa tana iya tashi da iska ko kuma ruwa ya wanke ta.
Idan babu ganyaye ko tsirrai da ke rufe ƙasa, ruwa yana iya kwashe ƙasa zuwa cikin koguna. Tsirran da ake nomawa bayan sare itatuw kamar kofi, auduga, waken soya da alkama ba sa iya riƙe ƙasa. Yayin da ƙasa ke rasa ƙimar ta, manoma suna matsawa gaba don sake sare wasu dazuzzuka, abin da ke ci gaba da jawo asarar ƙasa.
Manazarta
Admin. (2024, June 24). Soil erosion. BYJUS.
Usman, S., Amana, S. M., & Jayeoba, J. O. (2025). Evaluation of surface soil quality and land suitability for agricultural soils affected by soil erosion. Discover Soil., 2(1).
Tarihin Wallafa Maƙalar
An wallafa maƙalar 17 October, 2025
An kuma sabunta ta 17 October, 2025
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.