Zinare wani muhimmin sinadari ne daga sinadaran ƙasa. Yana daga cikin ƙarafa masu matuƙar daraja wanda ake amfani da shi a fannoni da dama na rayuwa, tun daga kayan ado har zuwa masana’antu. Zinare wani irin ƙarfe ne mai matuƙar daraja, wanda ya shahara a tarihi da zamantakewa a matsayin alamar arziƙi, iko da kwarjini. Idan aka dubi batun zinare a ma’aunin hikima da rubutun ilimi (musamman ta fuskar nazari da kimiyya), akwai wasu manyan sassa guda uku da za a iya karkasa bayanin ciki domin sauƙin fahimta.

Zinare a mahangar tarihi
Zinare tun zamanin da ana darajanta shi ba kawai saboda ƙimarsa ba, har da matsayin da yake da shi a zuƙatan mutane. Masana falsafa da malamai sun tattauna kan wannan sinadari.
Zinare ke wakiltar kyautatawa da ɗaukaka. Misali, a falsafar Plato da Aristotelian, zinare yana nuni da “nagarta” mai tsarki, kamar yadda zinariya ke da tsabta da ɗaukar hankali. A rubuce-rubucen addinai da tarihin falsafa, ana kwatanta mutum mai ƙima da zinariya. Hakan na nuni da cewa darajar mutum ba ana aunata da abu ba ne kawai, har da nagarta da cancantar abin.
Zinare a mahangar kimiya
Daga mahangar kimiyya, zinare na ɗaya daga cikin ƙarafa mafi tsabta da juriya, wanda ke da siffofi da ke da ma’ana mai zurfi. Zinare yana da lamba Au a tsarin jadawalin sinadarai. Ba ya ruɓewa ko lalacewa, wanda ke sa ya zama abin amfani a fannoni kamar na lantarki, likitanci da na’urori masu ƙayatarwa.
Zinare ta fuskar tattalin arziƙi
A duniya, kuɗin zinare (gold standard) shi ne ginshiƙin darajar kuɗi kafin a ƙirƙiri tsarin kuɗin zamani. Wannan yana nuna yadda ƙimar zinare ta taka rawa a tsarin adalci da daidaito na kasuwanci.
Zinare a mahangar hujjoji
A rubutun ilimi mai gamsarwa, ya zama wajibi a kawo hujjoji da suke da ma’ana daga mahangogi daban-daban:
- Hujja daga tarihi: Kamar yadda aka samu a Masar da Babilon, zinare yana daga cikin abubuwan farko da ɗan Adam ya ko yi amfani da su don ajiya da musayar kaya.
- Hujja daga kimiyya: Saboda siffofinsa masu nagarta, zinare yana daga cikin sinadarai da ba sa shiga mu’amala da sauƙi. Wannan yana ba shi matsayi da daraja wanda ba ya ƙarewa cikin ƙanƙanin lokaci, shi ya sa har zuwa yanzu ake damawa da shi ta kowa ce fuska.
- Hujja daga falsafa: A cikin nazarin mahangar rayuwa, zinariya na nuni da ƙarshe ko matakin ƙarshe na kamala – kamar yadda a harshen Larabci ake cewa: “Zinariya ta haƙiƙa ba ta canzawa da lokaci.”
Siffofi da yanayin zinare
Zinare yana da yanayi mai ban sha’awa, kalarsa kalar ruwan ɗora wa ce mai cizawa wato ta turu, shi ya sa har ake yi mata laƙabi da kalar zinariya. Yana da ɗaukar ido sosoi, kafin a narka shi yana da nauyi, amma idan akaa sarrafashi zuwa wasu abubuwa bai cika yin nauyi ba sai dan idan agogo ne.
Yadda ake samun zinare
Zinare na samuwa ta hanyoyi daban-daban da suka haɗa da tsarin halitta da na fasaha. Ga cikakken bayani a ƙididdigance. Zinare yana samuwa ne a cikin ƙasa ta hanyar wasu tsare-tsaren halittar duniya kamar:
- Fashewar duwatsu (volcanic activity): Yayin da magudanun ƙarƙashin ƙasa ke tashi da zafi, sinadaran zinare sukan tafi tare da ruwan zafi zuwa saman ƙasa.
- Cikin duwatsu: Bayan sanyayawa, zinare yakan bayyana a cikin duwatsu ko a cikin kogunan dutse.
- Guguwar ruwa da iska: Zinare kan wuce daga tuddai zuwa koguna, inda zai tara a ƙasan koguna ko guraren da ruwa ke taruwa.
Hanyoyin samun zinare
Masana kimiyya sukan yi amfani da fasahar zamani don gano inda ake iya samun zinare:
- Nazarin dutse da ruwa (Geological Survey): Ana binciken sinadarai a ƙasa da ruwa don gano zinare.
- Hotunan tauraron ɗan’adam (Satellite Imaging): Ana amfani da fasahar tauraron ɗan’adam wajen gano sassan duniya masu arziƙin zinare.
- Gobarar wuta (Drilling): Ana haƙo ramuka domin ɗaukar samfurin ƙasa domin gwaji a kan ko akwai zinare.
Haƙar zinare (maining)
Bayan an tabbatar da akwai zinare, sai a fara aikin haƙar shi:
Hakar saman ƙasa
A wannan hanya, ana fasa ƙasa a buɗe tare da tonowa da manyan injuna don a fidda zinare daga duwatsu. Ana amfani da wannan hanya idan zinare na kusa da saman ƙasa.
Hakar ƙarƙashin ƙasa
Idan zinare yana da zurfi a ƙasa, sai a gina ramukan dogaye domin shiga ciki da ɗaukar shi. Wannan hanya na da haɗari amma ta fi dacewa da manyan adadin zinare.
Zinaren cikin koguna
Wannan hanya ce inda zinare ke taruwa a koguna ko bakin rafi. Ana ɗiban ƙasa daga ƙasan kogi, a wanke shi a tafki ko kwano, sannan zinare zai ragu a ƙasa saboda nauyinsa.
Ƙassashen da ake samun zinare
A duniya China, ita ce ƙasa ta farko a duniya da wajen haƙo zinare ya fi yawaita a can. Sai kuma sauran ƙasashen duniya kamar haka:
- Rasha
- Australiya
- Amurka da Afirka ta Kudu su ne suka fi haƙo zinare.
- A Afirka, Ghana na daga kan gaba.
- A Najeriya: Akwai zinare a jihohi irinsu Zamfara, Kebbi, Kaduna, Niger, Osun,Taraba, sai Kogi da Katsina su ma suna da wuraren haƙar zinare.
Abubuwan da ake yi da zinare
Akwai abubuwa da dama da ake yi da zinare musamman ta fuskar kayan ado na mata,
- Sarƙoki
- Ɗankunnaye
- Warwaro
- Zobe
- Haƙorin mata na kwaliya
Amfanin zinare
Zinare yana da amfani a fannoni da dama wanda suka haɗar da:
- Kayan ado: Saboda ƙyalli da juriya, ana ƙera kayan ado da shi, kasantuwarsa abu mai jan hankali da ɗaukar ido.
- Tattalin arziƙi: Yana matsayin kadara mai daraja kuma ana amfani da shi wajen saka jari da kare kuɗi daga hauhawar farashi.
- Fasahar zamani: Ana amfani da shi a wayoyin salula, kwamfuta, da na’urorin likitanci saboda yana da ƙarfin watsa lantarki kuma baya lalacewa.
- Likitanci: Ana amfani da shi wajen cusa haƙori da wasu nau’in magunguna.
Matsalolin zinare
Duk da amfaninsa, zinare na da wasu manyan matsaloli, tun daga kan yin ado da shi ko zuba hannun jari ko kuma hanyar samuwarsa:
- Lalata muhalli: Haƙar zinare kan jawo rugujewar gandun daji da gurbatar ruwa sakamakon amfani da cyanide da mercury.
- Cin zarafin ma’aikata: A wasu ƙasashe, yara da mata na aiki cikin haɗari da rashin kariya sakammakon aikin haƙar zinare.
- Rikice-rikice: Wuraren da ake aikin haƙar zinare akan fuskanci rashin nutsuwa ta hanyar janyo rikici da tashe-tashen hankula, musamman a yankunan da doka ba ta da ƙarfi.
- Matan da suke amfani da shi wurin kwaliya, suna kasancewa cikin ɗar-ɗar sakammakon saka shi kan iya sanyawa a farmake su. Haka kuma suna kasancewa cikin rashin nutsuwa idan suka saka, sakammakon tsoron kada ya faɗi su yi asara.
- Da dama masu saka shi matsayin hannun jari na fuskantar barazanar asara, musamman yayin da farashin dala ya yi ƙasa.
- Ƙarfafa cin hanci da rashawa ta fuskar gwamnati da kuma tsakanin masu cinikayyar shi.
Manazarta
Musa, A. & Abdullahi, M. (2021). An Overview of Gold Mining in Northern Nigeria. Journal of Mining and Geosciences, 57(3), 22–34.
Nigeria Geological Survey Agency (NGSA, 2020). Gold Deposits in Nigeria – A Technical Report.
United Nations Environment Programme (UNEP, 2019). Environmental and Health Impacts of Gold Mining.
World Gold Council (2024). Gold Demand Trends Report.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.