Antioxidants rukuni ne na sinadaran da ke kare ƙwayoyin halitta daga lalacewa, wanda wasu ƙwayoyin cuta da ake kira free radicals ke haddasawa. A fannin kimiyyar lafiya da abinci, antioxidants suna daga cikin muhimman sinadaran da ke ba jiki kariya daga cututtuka masu tsanani, kamar cututtukan zuciya, ciwon daji, ciwon sukari, da cututtukan da suka shafi fata.
Asalin kalmar antioxidant
Kalmar antioxidant ta samo asali ne daga kalmar turanci ta oxidation, wadda ke nufin wani tsari na sinadarai da ke faruwa a lokacin da ƙwayar halitta ko wani sinadari ya haɗu da iskar oxygen, ta hanyar da ka iya haifar da lalacewar ƙwayar halittar. Har ila yau, wannan tsari na oxidation na iya samar da wasu ƙwayoyin da ake kira free radicals, waɗanda ke iya cutar da ƙwayoyin halitta. Saboda haka, kalmar antioxidant na nufin sinadari ko ƙwayar da ke hanawa, ko rage lalacewar kwayoyin halitta a lokacin da suka haɗu da oxygen.
Free radicals
Free radicals ƙwayoyin sinadarai ne marasa daidaito, waɗanda ke da electron guda da bai da abokin haɗuwa. Saboda wannan rashin daidaito ne kuma suke kai hari ga sauran ƙwayoyin halitta domin su daidaita kansu. Idan kuma free radicals suka yi yawa a jiki fiye da yadda antioxidants za su iya sarrafawa, ana samun yanayi da ake kira oxidative stress, wanda ke haifar da illoli masu yawa. Har ila yau, idan free radicals suka yi yawa a jiki, suna iya haddasa wasu cututtuka kamar ciwon sukari, da kuma kansa. Sai dai kuma, jiki yana da hanyarsa ta kare kansa daga free radicals ta hanyar samar da antioxidants.
Nau’o’in antioxidants
Antioxidants sun rarrabu zuwa manyan rukunai guda biyu:
Endogenous antioxidants
Waɗannan su ne antioxidants da jiki ke sakarwa da kansa, misalansa sun haɗa da glutathione, superoxide dismutaseda Catalase, amfanin waɗannan sinadarai shi ne, suna taka muhimmiyar rawa wajen kare ƙwayoyin halitta daga lalacewa a matakin farko.
Exogenous antioxidants
Waɗannan su ne antioxidants da ake samu ta dalilin abinci ko supplements, ire-irensa sun haɗa da Vitamin C, Vitamin E, Vitamin A, Flavonoids, Polyphenols da kuma Selenium, dukkanin waɗannan suna samar da antioxidant rukuni na biyu ne ta dalilin abinci.
Supplement antioxidants
Wannan nau’in na antioxidants supplements ana samar da su ne a matsayin ƙarin abinci, yawanci suna zuwa ne a cikin capsule, tablet, ko syrup. Misalinsu akwai Vitamin C tablets, Vitamin E capsules, Beta-carotene, Selenium, Zinc. Amfaninsu shi ne taimakawa waɗanda ba sa samun isasshen antioxidants daga abinci, sannan suna ƙarfafa garkuwar jiki, gami da taimakawa marasa lafiya.
Yadda antioxidants ke aiki ga jiki
Antioxidants suna aiki ne ta hanyoyi daban-daban da suka haɗa da: Bayar da electron ga free radical domin daidaita shi ba tare da haifar da wata illa ba. Sannan duna daƙile sarƙar lalacewar da free radicals ke haddasawa. Kuma suna ƙarfafa enzymes na cikin jiki da ke yaƙi da oxidative stress. Waɗannan amfanin na antioxidants na taimakawa wajen kare lafiyar jiki a matakin ƙwayoyin halitta.
Nau’ukan abinci masu ɗauke da antioxidants
Akwai rabe-raben abincin da suke da antioxidants da suka haɗa da:
- ‘Ya’yan itatuwa: ‘Ya’yan itatuwan da suke ɗauke da antioxidants su ne berries, musamman blueberry da strawberry, lemu, inabi da kuma tufa.
- Kayan lambu: Daga cikin kayan lambu masu ɗauke da antioxidants akwai alayyahu, spinach, carrot, broccoli.
- Abubuwan sha: A cikin abubuwan sha kuma akwai koren shayi da baƙi, sai kuma fresh juice.
- Kayan yaji: Kayan yaji da sinadaran gargajiya masu antioxidants sun haɗa da citta, tafarnuwa, kurkur da kirfa.
- Cocoa da chocolate: Har ila yau cocoa da chocolate na da sinadarin antioxidants, sannan goro, wake da hatsi ma duk suna da shi. Yawanci dai an fi samunsa ga abinci mai launin ja, shuɗi, kore mai duhu.
- Nama da kifi: A wani binciken ma, nama da kifi suna ɗauke da antioxidants, amma ba kamar yadda ake samu a cikin ‘ya’yan itatuwa da kayan lambu ba.
Muhimmancin antioxidants ga lafiya
Antioxidants na da matuƙar muhimmanci ga lafiya ta fannoni daban-daban da suka haɗa da:
- Kariya ga zuciya: Oxidative stress na taka rawa wajen haddasa cututtukan zuciya. Antioxidants kuma suna rage haɗarin taruwar kitse mara kyau, toshewar jijiyoyin jini, da hawan jini.
- Kariyar ga ciwon daji: Lalacewar DNA sakamakon oxidative stress na iya haddasa sauyin ƙwayoyin halittar da ke haifar da ciwon daji. Antioxidants kuma suna taimakawa wajen rage wannan haɗari ta hanyar kare DNA daga lalacewa.
- Rage tasirin tsufa: Wasu masana suna danganta tsufa da taruwar lalacewar oxidative a jiki. Saboda haka, antioxidants suna taimakawa wajen rage alamomin tsufa, musamman a fata da kwakwalwa.
- Taimaka wa garkuwar jiki: Vitamin C da wasu antioxidants suna ƙarfafa aikin garkuwar jiki wajen yaƙi da ƙwayoyin cuta.
Ƙarin sinadarin antioxidants
Kamar yadda ya gabata, akwai antioxidants na ƙari da ake samar wa ta sigar magani, wanda ya fi kamata da a tuntunɓi likita kafin a fara amfani da su, domin a tashin farko samun antioxidants daga abinci ya fi muhimmanci ga lafiyar jiki. Sannan yawan shan supplements na antioxidants ba tare da ƙa’ida ba na iya zama cutarwa ko jawo lalacewar ƙwayoyin halitta maimakon kare su. Wani binciken ma ya nuna cewa shan antioxidants da yawa a matsayin supplements na iya haddasa mutuwa. Saboda haka masana lafiya suna ba da shawarar da a riƙa samun antioxidants daga abinci na halitta maimakon supplements masu yawa.
Dalilan da ke kawo oxidative atress
Kamar yadda ya gabata, oxidative stress yana faruwa ne idan aka samu rashin daidaito tsakanin free radicals da kuma kariyar jiki antioxidants. Idan free radicals sun yi yawa, suna iya lalata ƙwayoyin jiki. Dalilan da ke kawo shi kuma sun haɗa da:
- Hayaki da gurbatar iska: ta hanyar shan taba sigari ko zama kusa da masu shan taba, sai kuma gurbatacciyar iska.
- Abinci gurɓatacce: abinci mara kyau, da yawan cin abinci mai mai sosai, abinci mai sukari da yawa da abinci na gwangwani
- Damuwa ma na kawo oxidative stress ta yawan tunani da damuwar zuciya.
- Rashin motsa jiki ko yawan motsa jiki fiye da ƙima, shan giya da wasu miyagun ƙwayoyi, wasu cututtukan da kumburi.
- Haske mai ƙarfi, kamar rana mai zafi sosai da X-ray. Sannan akwai wasu magunguna da sinadarai masu guba wato chemicals daga muhalli ko wurin aiki.
A taƙaice Oxidative stress yana faruwa ne idan abubuwan da ke cutar da jiki free radicals sun fi kariyar jiki.
Illolin ƙarancin antioxidants a jiki
Kamar yadda gabata, idan jiki ya rasa isassun antioxidants, Free radicals suna ƙaruwa, wanda ke haifar da Oxidative stress. Wannan na iya jawo matsaloli da dama:
- Yawan kamuwa da cututtuka: Jiki ba zai iya yaƙar ƙwayoyin cuta sosai ba, hakan kuma na iya haifar da ciwon zuciya, ciwon sukari, ciwon daji
- Saurin tsufa: Fata da ƙwayoyin jiki suna lalacewa da wuri, fata ta fara yin laushi da tamoji, gashi na iya fara canza launi da wuri
- Raunin garkuwar jiki: Mutum zai rika yawan kamuwa da mura da sauran cututtuka saboda raunin garkuwar jiki.
- Matsalolin ƙwaƙwalwa: Ƙarancin antioxidants na iya shafar kwakwalwa wanda ka iya jawo mantuwa da wuri, rage basira da mayar da hankali.
- Gajiya da rashin kuzari: Saboda ƙwayoyin jiki suna lalacewa, mutum zai rika jin kasala da ƙarancin ƙarfi.
Alamomin ƙarancin antioxidants ga jiki
Alamomin karancin antioxidants suna tafiya ne da illolinsa, sai dai ƙarin wasu da suka haɗa da:
- Ciwon kai ko rashin nutsuwa: Sau da yawa mutum zai riƙa jin ciwon kai ko damuwa a ƙwaƙwalwarsa.
- Matsalar gani, Ido na iya fara rauni ko ganin haske ya ragu.
- Ciwon tsoka da gaɓoɓi: Jin ciwo a jiki ba tare da dalili mai ƙarfi ba.
- Rashin saurin warkewa: Rauni ko ciwo yana ɗaukar lokaci kafin ya warke.
Antioxidants muhimman sinadarai ne da ke kare jiki daga lalacewar free radicals da oxidative stress ke haifarwa. Ta hanyar cin abinci mai wadatar ‘ya’yan itatuwa, kayan lambu, da hatsi. Antioxidants suna daga cikin manyan ginshiƙan kariyar lafiyar ɗan Adam a matakin ƙwayoyin halitta, kuma ci gaba da bincike a kansu yana ƙara tabbatar da muhimmancin su a fannin kimiyyar lafiya. Antioxidants kuma suna taimakawa wajen ƙara tsawon lokacin da abinci zai iya zama ba tare da lalacewa ba, shi ya sa ake amfani da su a matsayin sinadarin kariya ga abinci.
Manazarta
Professional, C. C. M. (2026, January 7). Oxidative stress. Cleveland Clinic.
BSc, A. A., PhD. (2023, July 12). Antioxidants explained in simple terms. Healthline.
National Library of Medicine. (n.d.). Antioxidants .
LD, M. W. R. (2023, November 8). How can antioxidants benefit our health?
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.