Skip to content

Ciwon Wuya

    Aika

    Ciwon wuya na ɗaya daga cikin matsalolin lafiya da mafi yawan mutane ke fama da shi. Wannan ciwo na iya kasancewa mai sauƙi ko kuma mai tsanani, wanda kuma yake buƙatar kulawar likita. Duk da cewar ciwon wuya bai cika zama cuta mai zaman kanta ba, sai dai ya kan zama alamar wata matsala da ke tattare da ƙashi, tsoka, jijiyoyi ko jijiyoyin jini da ke cikin yankin wuya. Yawan zama a wuri ɗaya, rashin daidaiton zama ko kwanciya, da damuwa suna daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa shi. Sannan wasu cutuka da ke fitowa a cikin maƙoshi na daga cikin dalilan da ke kawo ɗayan nau’in na ciwon wuya, sakamakon ya kasu gida biyu.

    shutterstock 1370070926 scaled 1
    Ciwon wuya nau’i-nau’i ne.

    Ciwon wuya na nufin jin raɗaɗi, takura, ko tauri a yankin wuya, wanda zai iya bazuwa zuwa kai, kafaɗu ko baya. Likitoci kan rarrabe ciwon wuya zuwa:

    • Acute neck pain (na gajeren lokaci): wanda ke ɗaukar kwanaki zuwa makonni kaɗan.
    • Chronic neck pain (ciwon wuya mai tsanani): wanda ya fi makonni 12, kuma yana iya zama alamar wata babbar matsala.

    Nau’ukan ciwon wuya

    1. Ciwon Wuya da ke riƙe jijiya (musculoskeletal neck pain): Wannan shi ne nau’in da mafi yawan mutane ke kira da ciwon wuya. Abubuwan da ke jawo irin wannan ciwon wuyan sun haɗa da:

    • Yanayin zama da kwanciya marar kyau, musamman ga ma’aikatan ofis da ke aiki da kwamfuta.
    • Matsin tsoka: sakamakon ɗaga kaya masu nauyi ko yin aiki fiye da ƙarfi.
    •  Rauni: wanda yake faruwa sakamakon haɗarin mota ko faɗuwa.
    • Matsalolin ƙashi: lalacewar ƙashin wuya saboda tsufa.
    • Ciwukan jijiyoyi: kamar kumburin jijiyar wuya.
    • Cututtuka: kamar ciwon sanƙarau (meningitis), wanda ciwon wuya na daga cikin manyan alamunsa.

    Alamominsa: Daga cikin alamominsa su ne wuya zai riƙe, ta yadda mutum ba ya iya juyawa da sauƙi. Sannan a wani lokaci raɗaɗin na sauka har zuwa kafaɗa ko hannu. Har ila yau a wani lokacin yana zuwa da ciwon kai ko jiri.

    Magungunansa sun haɗa da: Magungunan rage raɗaɗi da kumburi (painkillers, anti-inflammatories), Physiotherapy da motsa jiki na musamman. Idan kuma ya tsananta ana yin allurar corticosteroid ko tiyata idan jijiyar ta matse sosai, sannan Hot compress ko kuma wankan ruwan zafi a hausance, shi ma yana sassauta riƙewar wuya.

    2. Ciwon wuya a cikin maƙoshi (throat-related neck pain): Wannan ne nau’in ciwon wuya na biyu, wanda ba ba riƙewar tsoka ko ƙashi ke haddasa shi ba, sai dai yana faruwa ne a dalilin wasu cututtuka da suka ɓullu a cikin maƙogwaro. Dalilan da suke kawo shi sun haɗa da:

    • Ciwon maƙogwaro (tonsillitis, pharyngitis).
    • Fitowar Ƙurji ko ƙuraje a maƙoshi (throat abscess).
    • Ciwon garkuwar jiki (infection) da ke taruwa a cikin maƙoshi.
    • A wasu lokutan ma, ciwon daji (throat cancer) na haddasa shi.

    Alamominsa: Rashin iya haɗiye yawu ko abinci (painful swallowing), jin kamar abu ya toshe a maƙogwaro, fitowar ƙurji ko kumburi a cikin makogwaro, wani lokaci ana jin wuya yana kumbura gaba ɗaya. Idan ya tsananta, ana yin tiyata don magance matsalar da ta haddasa shi.

    Magungunansa na tafiya ne da kalar cutar da ta haddasa shi, misali:

    • Idan ƙwayoyin cuta ne sila: ana amfani da maganin ƙwayoyin cuta (antibiotics).
    • Idan ƙurji ne: ana yin tiyata domin fitar da shi.
    • Sannan shan ruwan ɗumi da zuma ko gishiri na sa a samu sauƙinsa. Idan ya tsananta a nemi kulawar likitan ENT (Ear, Nose, Throat specialist).

    A taƙaice babancinsu shi ne, ciwon wuya na tsoka ko kuma jijiya: yana hana juyawa, da kuma raɗaɗin da ka iya sauka zuwa hannu. Ciwon wuya na maƙogwaro kuma yana hana haɗiye yawu ko abinci, sannan yana ɗauke da raɗaɗi na cikin maƙoshi, wani lokaci ƙurji ko kumburi na bayyana.

    Illolin da ciwon wuya ke haifarwa

    Ciwon wuya ba ƙaramar cuta ce da za a yi sakaci a kanta ba, domin tana rikiɗewa daga ƙaramin ciwo, zuwa babban ciwon da ka iya haddasa babbar illa ga lafiya, wanda daga cikin illolin sakaci da shi sun haɗa da:

    • Ciwon zai zama na dindindin.
    • Matsalolin jijiyoyi da ka iya haifar da naƙasa.
    • Rashin iya motsi ko haɗiya.
    • Matsalar numfashi idan ciwon na cikin makogwaro.

    Hanyoyin kariya

    A ɓangaren kariya ma ciwon wuya na da nashi, wanda idan aka kiyaye za iya kauce ma kamuwa da shi, idan kuma har an kamu, zai iya zuwa da matukar sauƙi. Kaɗan daga cikin hanyoyin kariyarsa akwai:

    • Yin zama da kwanciya cikin daidaito.
    • Kaucewa ɗaukar kaya masu nauyi da kafaɗa ɗaya.
    • Yawan motsa jiki na yau da kullum.
    • Yin amfani da matashin kai mai kyau.
    • Shan ruwa mai yawa da kiyaye tsafta don rage cututtuka na makogwaro.

    Shin ana ɗaukar ciwon wuya

    E, ciwon wuya ya kasu gida biyu, akwai wanda ake ɗauka, akwai wanda ba a ɗauka, amma ga rabe-raben su kamar haka:

    Ciwon wuyan da ake ɗauka (Infectious causes)

    Wannan ciwo yana faruwa ne saboda ƙwayoyin cuta kamar bacteria ko virus. Yana iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ta iska, ruwa ko cudanya. Misalan irin wannan ciwon wuya sun haɗa da: Tonsillitis (ƙurajen makogwaro) wanda yake kawo ciwon wuya, wahalar haɗiya, zazzaɓi. Haka kuma akwai Strep throat wanda cutar bacteria ce mai tsanani wadda take buƙatar maganin riga-kafi. Akwai kuma Mumps (ƙanƙara) wadda take haddasa kumburin wuya da ciwo yayin tauna, tana kuma yaɗuwa ta iska ko ruwa. Mafi tsanani daga ciki akwai Meningitis (ƙumburin kwakwalwa) wadda take haddasa ciwon wuya da ba a iya lanƙwasawa, zazzabi, kai ciwo da kasala, kuma yana buƙatar kulawar gaggawa a asibiti. Alamomin da ke nuna ciwon wuya da ake ɗauka sun haɗa da zazzabi, kumburi, tari, atishawa da kuma matsalar haɗiye.

    Ciwon wuyan da ba a ɗauka (Non-infectious causes)

    Irin wannan ciwon ba shi da alaƙa da ƙwayoyin cuta, ba ya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, kuma mutum guda ne kawai zai iya fama da shi. Misalan wannan ciwon sun haɗa da Muscle strain, wanda yake faruwa idan aka yi barci da wuya a karkace ko kuma a zauna a guri ɗaya na dogon lokaci. Haka kuma akwai Ciwon cervical spine ko disc problem wanda yake da alaƙa da matsala a ƙashin wuya. Wani lokaci kuma damuwa na iya haddasa tsamin tsoka a wuya. Idan ciwon wuya ya biyo bayan waɗannan dalilai, ba a samun zazzabi, kumburi ko wahalar haɗiya.

    Yadda ake bambance su

    Idan ciwon wuya yana tare da zazzabi, kumburi, tari, atishawa ko wahalar haɗiya, ana ɗaukar shi a matsayin ciwon da ake iya ɗauka. Idan kuma babu waɗannan alamomin, sai dai tsamin wuya bayan bacci ko zama tsawon lokaci ko matsalar jijiya da ƙashi, to wannan ciwon ba a ɗauka ba.

    Manazarta

    Eske, J. (2025, May 29). Sore throat and neck pain: What is the link?

    Healthdirect Australia. (n.d.). Neck pain. Treatments, Causes and Related Symptoms | Healthdirect.

    Neck pain – Symptoms and causes. (n.d.). Mayo Clinic.

    Professional, C. C. M. (2025, September 11). Neck pain. Cleveland Clinic.

    Tarihin Wallafa Maƙalar

    An kuma sabunta ta 24 September, 2025

    Sharuɗɗan Editoci

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×