Skip to content

eNaira

Kamar tsabar kuɗi ko takardar kuɗi, eNaira mallakin CBN ce. eNaira tana amfani da fasahar blockchain iri ɗaya da kuɗaɗen Bitcoin ko Ethereum, kuɗaɗen eNaira ana adana su a cikin jakar wallet ɗin dijital kuma ana iya amfani da su don biyan kuɗaɗen cinikayya; ana iya canja su ta hanyar dijital ba tare da wahala ba ga kowa a duniya. Sai dai duk da haka akwai bambance-bambance masu mahimmanci. Na farko, eNaira tana da tsauraran sharuɗɗan samun sahalewar babban bankin Najeriya. Na biyu, saɓanin waɗannan kuɗaɗen crypto, eNaira ba wata kadara ce ta kuɗi a kanta ba, nau’i ne na kuɗaɗen dijital na ƙasa kuma tana samun darajarta ne daga naira ta zahiri kawai.

eNaira
Hoto: Business Day

eNaira hanya ce da Najeriya ta ba da damar yin amfani da fasahar blockchain, a tsarin hada-hadar kuɗi ta yau da kullun. Har ila yau, wata hanya ce ta kishiyantar cryptocurrencies, wanda ta zama sananniya a tsakanin al’ummar Najeriya. An yi la’akari da wannan fasaha domin taimakawa hada-hadar kudi a Najeriya, da kuma biyan kuɗaɗe kai tsaye daga gwamnati zuwa ga ‘yan kasa.

eNaira wani nau’in kuɗin dijital ne. Kamar yadda sunan ke nunawa, kuɗi ne waɗanda ke wanzuwa ta hanyar lambobi kawai. Misalin kuɗin dijital shi ne Bitcoin ko Ethereum. Ana amfani da ingantattun dabarun tsaro domin tabbatar aminci yayin hada-hada da sarrafa wadannan kuɗaɗe.

Manyan bankunan ƙasashe da dama suna ƙoƙarin ƙirƙirar nau’ikan kuɗaɗen dijital domin cin moriyar wasu fa’idoji da sukan taso tare da irin su bitcoin da ethereum. Ɗaya daga cikin fa’idojin kuɗin dijital shi ne ƙarancin kuɗaɗen caji yayin aiwatar hada-hada saboda babu masu shiga tsakani.

Misali, lokacin da ake amfani da kuɗin fiat (akasin kudin dijital) kamar naira ko dala, kuɗin na bin hanyoyi da yawa, wanda hakan ke haifar da tsada. Ya danganta da nau’in ciniki, masu shiga tsakani yawanci bankuna ne, tsarin katin cirar kuɗi kamar Visa ko Mastercard. Amma kuɗaɗen dijital, an samar da amintacciyar hanyar hada-hada kai tsaye tsakanin ɓangarori biyu na masu hada-hadar, hakan na rage caji, da rage ɓata lokacin cinikayya.

Babban Bankin Najeriya (CBN) a hukumance ya ƙaddamar da wani nau’in kuɗaɗe na fasahar yanar gizo “eNaira”, Central Bank Digital Currency (CBDC), a ranar 25 ga Oktoba, 2021. Wannan dai shi ne karo na biyu na CBDC da aka buɗe ga jama’a bayan Bahamas.

Dalilin samar da eNaira

A cewar babban bankin na CBN, ana sa ran eNaira za ta haifar da fa’idoji da dama, waɗanda za su iya taimakawa wajen samun cigaba, yayin da eNaira ke ƙara yaɗuwa kuma ana samun goyon bayan ingantaccen tsari. Ana sa ran sabon tsarin kuɗin dijital da babban bankin Najeriya ya ƙirƙiro, wato eNaira, zai ƙara haifar hada-hadar kuɗi da kuma sauƙaƙa hanyoyin fitar da kuɗaɗe, amma akwai bukatar a kula sosai da haɗuran da za a iya aukuwa. Manyan fa’idojin wannan nau’in kuɗaɗe sun haɗa da:

Bunƙasa hada-hadar kuɗaɗe

A yanzu dai ana samar da asusun wallet na eNaira ga masu asusun banki ne kawai, amma ana sa ran a ƙarshe za a faɗaɗa shi zuwa ga duk wanda ke da wayar hannu ko da kuwa ba shi da asusun banki. Yawancin mutane ba su da asusun banki (mutane miliyan 38; daidai kashi 36 cikin 100 na yawan manya), haka nan barin waɗanda ke da wayar hannu su sami damar shiga tsarin eNaira zai ƙara yawan hada-hadar kuɗi da kuma sauƙaƙe aiwatar da hada-hadar musaya kai tsaye da inganci. Ana sa ran matakin zai bai wa kashi 90 na al’ummar ƙasar damar amfani da eNaira.

Kula da kuɗaɗen da aka aika

Najeriya na daga cikin manyan wuraren da ake hada-hadar kuɗaɗe a yankin kudu da hamadar Sahara, inda kuɗaɗen da ake aika wa da su ya kai dalar Amurka biliyan 24 a shekarar 2019. Ana fitar da kuɗaɗen ne ta hanyar kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa (misali Western Union) da kuɗaɗen da suka kai daga kashi 1 zuwa kashi 5 na ciniki. Ana sa ran eNaira za ta rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen hada-hadar kuɗaɗen, wanda hakan zai saukaka wa ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen ƙetare yayin aiko da kuɗaɗe zuwa Najeriya ta hanyar karɓar eNaira daga masu hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa da kuma tura su ga ‘yan’uwansu a Najeriya ta hanyar musayar wallet kyauta.

Rage bayanan sirri

Najeriya tana da faffaɗan tattalin arzikin tare da hada-hadar kasuwanci da ayyukan yi, daidai da rabin GDP da kashi 80 na ayyukan yi. eNaira wani asusun ajiya ne, kuma dukkan hada-hadar da aka yi bisa ƙa’ida ana iya gano su gabaɗaya, saɓanin hada-hadar kadarorin crypto na coins. Da zarar eNaira ta yaɗu kuma ta shiga cikin tattalin arziƙi, za ta iya fayyace sahihancin biyan kuɗi na yau da kullun da ƙarfafa kuɗaɗen shiga. Kasuwanci na yau da kullun na iya fa’idantuwa idan karɓar eNaira ta haɓaka ta amfani ta hanyar hada-hadar kuɗi.

Matakan rage haɗari

Hukumomin Najeriya suna ɗaukar matakan shawo kan haɗuran da ake fuskanta a fagen hada-hadar kuɗaɗe. Tura kuɗi daga banki zuwa jakar eNaira wallet ya dogara da hada-hadar yau da kullun da ka’idojin amfani domin rage haɗarin da sauran cibiyoyin kuɗi. Haɗarin hada-hadar kuɗi, kamar waɗanda ke tasowa daga amfani da eNaira don satar kuɗi, ana rage su ta hanyar amfani da tsarin tabbatar da sahihanci da kuma amfani da ƙarin tsauraran matakan kulawa ga masu amfani da tsarin da ba a tantance su ba. Misali, a yanzu mutanen da ke da lambar tantancewa ta banki (BVN) ne kawai za su iya buɗe wallet, amma nan gaba za a faɗaɗa tsarin da za a yi wa mutanen da ke da layin waya (SIM).

Enaira0
Hoto: National Star

Sai dai masu amfani da layin waya za su kasance ƙarƙashin ƙa’idoji da tsauraran sharuɗɗan da kuma iyakance adadin kuɗin da za su yi amfani da su. Duk da haka, masu amfani da jakar kuɗin waɗanda suka cika mafi girman ƙa’idojin ba za su riƙe fiye da Naira miliyan 5 kowace jakar eNaira ba. Don magance haɗarin damfara ta yanar gizo, ana sa ran gudanar da binciken tsaro na fasahar IT akai-akai.

Gudummawar bankin duniya IMF

Babban bankin duniya na taimakawa ta fuskar fasaha da shawarwarin inganta manufofi. Sashen Kuɗi da Kasuwannin Jari na IMF ya shiga cikin tsarin samar da eNaira, haɗi da shirya bita. Manufar IMF 2021 Mataki na IV, ta jaddada buƙatar sa ido kan kasada da tasirin kuɗaɗen da ke da alaƙa da kuɗin dijital na babban bankin. IMF a shirye yake ya yi aiki tare da hukumomi kan nazarin bayanai, raba abubuwan eNaira tare da wasu ƙasashe, da kuma tattauna hanyoyin sauya tsarin manhajar eNaira gabaɗaya.

Matsayin bankuna

Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ne ke da alhakin raba kuɗin eNaira. Suna yin hakan ta hanyar ƙirƙirar ƙarin ayyukan biyan kuɗi na eNaira, ta haka ne za su ƙirƙiro tsarin yanayin biyan kuɗi.

Yadda ake amfani da eNaira

Domin amfani da tsarin eNaira, ana buƙatar sauke manhajar eNaira Speed ​​Wallet a kan wayoyin hannu. Akwai nau’ikan manhajar eNaira wallet iri biyu kamar haka:

  • eNaira Speed ​​Wallet (Combo)
  • eNaira Speed ​​​​App Lite

Abubuwan buƙata don buɗe asusun eNaira

Idan za a buɗe asusun eNaira, ana buƙatar lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), lambar waya, da lambar tabbatarwa ta banki (BVN). Sai dai ba duk matakan asusun eNaira ba ne ke buƙatar duk waɗannan hanyoyin tantancewa.

Nau’ikan asusun eNaira

Tiers Bukatun Adadin kuɗi

Tier 1 NIN da lambar waya ₦20,000

Tier 2 BVN da lambar waya ₦ 200,000

Tier 3 BVN, lambar waya, da takardar bill. ₦500,000

Fa’idojin amfani da asusun eNaira

  • Tura kuɗaɗe kyauta
  • Saukaka hada-hada cikin sauri
  • Saurin mallaka ga mutanen da ba su da asusun banki

Matsalolin amfani da eNaira

  • Sirri: Ba kamar sauran blockchains ba kamar Bitcoin waɗanda za a iya amfani da su ba tare da suna ba, eNaira na buƙatar ka’idojin tantancewar KYC.

Manazarta

Abiodun, B. (2023, July 28). Everything about the eNaira. Techpoint Africa.

Salami, I. (n.d.). Nigeria’s digital currency: what the eNaira is for and why it’s not perfect. The Conversation.

SemiColonWeb. (n.d.). ENAIRA | Central Bank of Nigeria.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page