Skip to content

Firji

Firji na ɗaya daga cikin muhimman na’urorin lantarki da suka kawo gagarumin sauyi a rayuwar ɗan Adam, musamman a fannin adana abinci da kula da lafiya. Kafin samuwar firji, mutane na fuskantar matsala wajen tsawaita lokacin amfanin abinci, lamarin da ke jawo yawan lalacewa da asara. Samuwar firji ta taimaka matuƙa wajen rage wannan matsala ta hanyar samar da yanayi mai sanyi da ke hana saurin ruɓewar abinci da yawaitar ƙwayoyin cuta. A wannan zamani, firji ya zama muhimmin ɓangare na rayuwar yau da kullum a gidaje, asibitoci, ofisoshi, da wuraren kasuwanci a faɗin duniya.

71hdvlU9OnL. AC UF10001000 QL80
Firji na’ura ce mai matuƙar muhimmanci ga rayuwa da cigaba a fannoni daban-daban.

Ma’anar firji

Firji na’urar lantarki ce da ake amfani da ita wajen sanyayawa da adana abinci da abin sha domin kare su daga lalacewa. Ayyukan firji sun ta’allaka ne kan rage zafin abubuwan da ke cikinsa, ta yadda za a samar da yanayi mai sanyi wanda ke rage saurin ruɓewa da hana bunƙasar ƙwayoyin cuta. Ta wannan hanya, firji yana taimakawa wajen tsawaita lokacin lalacewar abinci, kiyaye ingancinsa, da kuma tabbatar da lafiyar mutane. Saboda irin wannan muhimmanci, firji ya zama ɗaya daga cikin na’urorin lantarki da ba sa rasa muhalli a rayuwar zamani.

Tarihin samuwar firji

Kafin ƙirƙirar firji mai aiki da lantarki, mutane sun dogara ne da hanyoyin adana abinci na gargajiya kamar amfani da ƙanƙara, rijiyoyi, koguna, sanyi na yanayi, ko binne abinci a ƙasa. Waɗannan hanyoyi sun taimaka a wani mataki, amma ba su wadatar wajen adana abinci na dogon lokaci ba.

Asalin tunanin ƙirƙirar firji ya samo asali ne daga binciken kimiyya da aka fara tun a ƙarni na 18. A shekarar 1748, masanin kimiyya ɗan ƙasar Scotland ya yi bayanin farko kan yadda ake iya samar da sanyi ta hanyar tsarin kimiyya na cire zafi daga ruwa. Wannan bincike ne ya zama ginshiƙin fahimtar aikin sanyayawa.

Daga baya, a shekarar 1834, ya ƙirƙiri firji na farko da ke aiki da tsarin amfani da sinadarin sanyayawa. Wannan ƙirƙira ta nuna farkon samuwar firji na zamani. A farkon ƙarni na 20 ne firji ya fara shiga gidajen mutane, musamman a ƙasashen da suka ci gaba da masana’antu. A yau kuwa, firji ya zama gama-gari a duniya, tare da cigaba da inganta fasaharsa domin rage amfani da wutar lantarki da kare muhalli.

Yadda firji yake aiki

Firji yana aiki ne ta hanyar tsarin sanyayawa da ke cire zafi daga cikin na’urar, sannan ya fitar da shi waje. Wannan tsari yana gudana ne a zagaye, kuma yana tabbatar da cewa cikin firji yana kasancewa a yanayi mai sanyi domin adana abinci da abin sha. Firji na aiki bisa haɗakar sassa kamar haka:

Compressor

Compressor shi ne sashin da ke fara aikin sanyayawa a cikin firji. Yana tunkuɗa gas ɗin sanyayawa, yana ƙara masa ƙarfi da zafi, domin ya iya zagayawa cikin tsarin firji gabaɗaya. Wannan tunkuɗawa ce ke ba gas ɗin damar motsawa daga wuri zuwa wuri cikin sauƙi.

Condenser

Condenser shi ne sashin da ke fitar da zafin da gas ɗin sanyayawa ya ɗauko. A nan ne gas ɗin mai zafi ke sakin zafinsa zuwa waje, wanda hakan ke sa ya koma yanayi mai sanyi. Wannan mataki yana da muhimmanci domin ba da damar ci gaba da aikin sanyayawa a cikin firji.

Evaporator

Evaporator shi ne sashin da ke ɗaukar zafi daga cikin firji. Lokacin da gas ɗin sanyayawa ya shiga wannan sashi, yana faɗaɗa, yana ɗaukar zafi daga iska da abubuwan da ke ciki. Wannan ne ke haifar da sanyaya abinci da abin sha da ake ajiyewa a cikin firji.

Thermostat

Thermostat na’ura ce da ke lura da yanayin zafin da ke cikin firji. Ita ce ke daidaita lokacin da firji zai yi aiki ko ya tsaya, gwargwadon zafin da aka saita. Idan zafin ya yi yawa, thermostat zai kunna tsarin sanyayawa, idan kuma ya yi ƙasa da kima, zai dakatar da shi. Wannan yana taimakawa wajen adana wutar lantarki da tabbatar da ingantaccen aiki.

Nau’ikan firji

Fridge

Firji na’ura ce da ake amfani da ita wajen sanyaya abinci da abin sha a yanayin sanyi mara tsanani. Yawanci zafin da firji ke samarwa yana tsakanin matsakaicin sanyi da ɗan ƙasa da haka, wanda hakan ke dacewa da adana abinci na yau da kullum kamar kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, madara, abincin da aka dafa, da abin sha. Babban aikin firji shi ne rage saurin ruɓewar abinci ta hanyar hana bunƙasar ƙwayoyin cuta, ba tare da daskarar da abincin gabaɗaya ba. Saboda haka, firji ya fi dacewa da abincin da ake buƙatar amfani da shi cikin ɗan gajeren lokaci. Ana samun firji a kusan kowane gida, ofis, da wurin kasuwanci, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen kula da lafiyar abinci da rage asara.

refrigerator condenser
Condenser nan ɓangaren da ke samar da gas a cikin firji.

Freezer

Freezer na’ura ce da ake amfani da ita wajen daskarar da abinci gabaɗaya ta hanyar rage zafi zuwa matakin ƙasa sosai. Wannan yanayin sanyi mai tsanani yana hana kusan dukkan ayyukan ƙwayoyin cuta, wanda hakan ke ba da damar adana abinci na dogon lokaci, kamar nama, kifi, kaji, da sauran abinci masu saurin lalacewa. Freezer ta fi firji ƙarfi wajen sanyaya abinci, kuma ana amfani da ita musamman idan ana son adana abinci na makonni ko watanni. Saboda irin wannan aiki, freezer tana da muhimmanci a gidaje masu yawan amfani da abinci, shagunan sayar da nama da kifi, asibitoci, da manyan wuraren kasuwanci.

Firjin mai aiki da makamashin solar

Firjin solar na’urar sanyaya abinci ce da ke aiki ta hanyar amfani da wutar lantarkin da hasken rana ke samarwa. Ana haɗa shi da solar panel da baturi, inda panel ke tattara hasken rana ya mayar da shi makamashin lantarki, sannan a ajiye wutar domin amfani da ita ko da lokacin da rana ba ta haskawa. Wannan nau’in firji yana da matuƙar amfani a yankunan da ba sa samun wutar lantarki akai-akai, musamman a ƙauyuka da wuraren da ke nesa da layin wuta.

Solar firji yana taimakawa wajen adana abinci, abin sha, da magunguna cikin sanyi na tsawon lokaci ba tare da dogaro da wutar lantarki ba. Yana da muhimmanci sosai a asibitoci da cibiyoyin lafiya wajen adana allurai da magungunan da ke buƙatar sanyi. Duk da cewa farashinsa yana iya yin tsada, solar firji na rage kashe kuɗin wuta, yana kare muhalli, kuma yana ba da mafita mai ɗorewa ga matsalar adana abinci a wuraren da wuta ke da wahalar samu.

Fa’idodin firji

Firji na ɗaya daga cikin kayan lantarki da ya zama dole a kowane gida saboda yana tsawaita lokacin lalacewar abinci, rage ɓarna, da sauƙaƙa rayuwa. Yana ba da damar ajiya cikin tsari, yana sauƙaƙa samun abinci a kowane lokaci, kuma yawancin firjunan zamani suna da tsarin ajiyar wuta mai rage amfani da lantarki. Ga wasu daga cikin manyan fa’idodinsa:

Tsawaita lokacin lalacewar abinci

Firji yana kiyaye abinci da abin sha cikin yanayi mai sanyi da kwanciyar hankali, wanda ke hana saurin lalacewa. Abinci kamar madara, nono, man shanu, kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, abin sha, da sauran abubuwa suna kasancewa cikin inganci fiye da yanayin ɗaki na yau da kullum, wanda ke ba da damar amfani da su na tsawon lokaci ba tare da lalacewa ba.

Sauƙaƙa rayuwa

Firji yana sauƙaƙa rayuwar yau da kullum ta hanyar ba ka damar samun abinci a kowane lokaci ba tare da buƙatar fita saye kullum ba. Zai iya adana manyan abubuwan abinci, wanda ke rage yawan sayayya kullum. Duk lokacin da ake buƙata, za a iya samun kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, abin sha mai sanyi, da ƙanƙara cikin sauƙi.

Rage ɓarnar abinci

Adana abinci a cikin firji yana taimakawa wajen kauce wa zubar da abinci. Ta hanyar kiyaye abinci daidai, za a rage yiwuwar zubar da kayan abinci da suka lalace ko suka tsufa. Haka nan yana taimakawa wajen shirya abincin gida yadda ya kamata, yana rage ɓarna kuma yana tabbatar da amincin abinci na dogon lokaci.

Zaɓin wajen ajiya mai tsari

Firjunan zamani suna ba da hanyoyi masu kyau na tsara abinci. Yawanci suna da shelves da sassa daban-daban don daidaita zafi bisa bukatar abubuwan ajiya, wanda ke sauƙaƙa adana kayan abinci cikin aminci. Wasu nau’ikan suna da na’urorin bayar da ruwa da kankara, tare da sassa daban-daban don abubuwa daban-daban.

Rage amfani da wuta

Firjunan zamani suna da tsarin rage amfani da wutar lantarki, wanda ke rage yawan kuɗin lantarki. Idan aka kwatanta da tsofaffin firji, na’urorin zamani suna amfani da fasaha mai inganci wacce ke rage yawan lantarki da ake amfani da shi. Wannan yana rage tasirin muhalli da kuma yawan kuɗin wutar gida da ake biya.

Matsalolin firji

Duk da amfanin firji, yana da wasu illoli da ya kamata a sani. Firji yana zuƙar wutar lantarki, yana buƙatar kulawa da gyara akai-akai, cin wuri a gida, kuma tsarin samar da shi da amfani da sinadarin sanyayawa na iya shafar muhalli idan ba a kula ba. Ga wasu manyan matsalolinsa:

Inside of refrigerator showing inner workings of compressor and coils scaled e1640014855420
Compressor ita ce na’urar da ke ƙunshe da gas ɗin da ke taimakawa wajen samar da sanyi.

Zuƙar wutar lantarki

Wasu firjunan na iya amfani da wuta mai yawa, musamman tsofaffin nau’ikan ko waɗanda ba a rage yawan amfani da lantarki. Wannan na haifar da karin kudin wuta a gida kuma yana ƙara yawan amfani da lantarki.

Buƙatar gyara da kulawa

Firji yana buƙatar tsafta da kulawa akai-akai don tabbatar da aiki yadda ya kamata. Wannan ya haɗa da tsaftace coils na condenser, ƙofofi, na’urar matsawa, da sassa daban-daban. Wasu lokuta, defrosting na bukatar a yi shi don hana ƙanƙara taruwa, kuma wasu sassa na iya buƙatar gyara mai tsada idan sun lalace.

Cinye wuri

Firji na ɗaya daga cikin manyan kayan lantarki, don haka yana buƙatar isasshen wuri a cikin gida. Samun wuri a gidaje ƙanana ko ɗakunan haya na iya zama ƙalubale, musamman idan girman firji ya yi yawa.

Tasirin muhalli

Firji na iya yin tasiri ga muhalli a lokacin amfani da sharar da ake samu daga masana’antu da kuma yayin amfani a gida. Sinadarin sanyayawa (refrigerant) da ake amfani da shi a firji na iya cutar da muhalli idan ba a zubar da shi yadda ya kamata ba, kuma zafin da condenser ke fitarwa yana ƙara matsalolin gurɓata muhalli.

Manazarta

Brain, M., & Elliott, S. (2023, August 18). How refrigerators work. HowStuffWorks. .

Nawaz, A. (2025, December 23). Advantages and Disadvantages of a refrigerator: A guide. fridgeacguide.com. .

Refrigeration equipment risk assessment. (n.d.). Croner-i.

Jim & Daves Appliance. (n.d.).  4 Dangers of living with a broken fridge  Jim & Daves Appliance.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×