Skip to content

Gada

Gaɗa nau’in waƙa ce da ake gudanarwa yayin abin da ya shafi biki ko kuma ɗaukar amarya. Sai dai yanzu zamani ya sauya, an samu sauye-sauye da gaɗa ta samu kwaskwarima tare da gatan da ya sa ba a gudanar da gaɗa a yayin ɗaukar amarya sai dai a wuraren kamu wanda ake yi na amarya.

Mama gaɗa suna ne da ake yi wa wata mawakiya inkiya da shi. Wacce ta koma gudanar da waƙoƙin gaɗa da zumar dawo da martabar hashen Hausa, mussamam ma da ta lura da cewar al’adun malam Bahasuhe na neman gushwewa.

Asma’u Sadiƙ , wacce aka fi sani da Baby nice ko Mama gaɗa ta ce a yanzu ta fi maida hankali a waƙoƙin gaɗa ne a wuraren bukukuwa da sauran taruka na matasa maimakon raya al’adu wasu ƙabilun domin tana kishin yarenta da kuma a’adarta ta malam Bahaushe.

Ta ce alal misali irin yadda ake yi a da, kamar zaman dandali da gaɗa, matasa a yanzu sun fi raja’a ne wajen kwaikwayon wasu al’adun mafi yawa na Indiya ko Arabian night hakanne ya sa ta kafa dandalin gaɗa a bukukuwa da ma wasu taruka. Matashiyar ta ce kimanin shekaru biyar kenan da ta sauya sheƙa daga waƙoƙin soyayya da na ‘yan fim zuwa ga waƙoƙin gaɗa, kuma tun daga lokacin da ta fara gaɗa ta samu natsuwa a cewarta ko ba komai ta dawo da martabar harshenta.

A’ina ake yin gaɗa?

Ada ana yin gaɗa ne a dandali ko kuma wuri ɗauko amarya.

Sai dai kuma sauyawar zamani ta sa akasari yanzu am fi yin gaɗa a ranar da ake kamun amarya wanda ake gudanar da wasanni masu ban sha’awa da ƙayatarwa.

Sai dai kuma a yau ana yin gaɗa ne a fili wadata ce ba dandali ba, ana ajiye kayan kiɗa tare da ƙasar wurin da kaya irin waɗanda suka shafi rayuwa da al’adar Bahaushe. Kamar:
1-Kilishi
2-Ƙwarai masu ado (ƙwarya)
3-Adudu
4-Mafitai
5-Tukwanan ƙasa

Su waye suke yin rawar gaɗa

A da ‘yan matan amarya ne kaɗai suke yin rawar gaɗa. Sai dai kuma a yanzu kowa da kowa kan shiga a yi da shi matuƙa yana da sha’awar yin hakan.

Misali:
‘Yan matan amarya. Yara ƙanana da kuma matasa, wasu manyan ma kan shiga domin samar da nishaɗi a tsakanin su. A baya kuma mata ne ke gudanar da gaɗa amma yanzu zamani ya sauya awurin gaɗa har da maza.

Wace irin kwaliya ake yi yayin gaɗa?

Ana yin kwaliya ne irin ta gargajiya, a cika fuska da ɗige-ɗige, baki kuma a cika shi da janbaki. Yayin da za’a saka hoda rabajau.

Waɗanne irin kaya masu gaɗa suke sakawa?

Masu rawar gaɗa suna saka kaya daban-daban, riga daban zani daban, haka ma ɗankwali daban. Wasu kuma kan yi shigar Fulani maza da mata.

Wace irin shiga amarya take yi a wurin gaɗa?
Akasari amarya kan yi shiga irin ta nuna al’adar Bahaushe ko dai kayan baƙin saƙi. Ko kuma ta yi abin da ake kira ciki da alako wato riga da zani da lulluɓin ka duk na atamfa.

Wace irin cima ake ci a wurin rawar gaɗa?

Ana cin abubuwa kala-kala a wurin rawar gaɗa wadanda suka haɗar da:
1-Taura
2-Aduwa
3-Tsamiyar biri
4-Rake
5-Aya
6-Kantu
7-Ƙali-ƙaƙƙau
8-Tsami gaye
9-Tsamiyar biri
10-Magarya
11-Kurna
12-Kwalba da nono

A yanzu da zamani ya sake sauya wa ma takai ta kawo ana gudanar da abubuwa da dama a wurin rawar gaɗa.

Misali:
Yanzu a wurin gaɗa ake kunna wuta wasu daga cikin ‘yan matan amarya suna gefe suna aiwatar da girki irin na gargajiya kowa na zuwa ana layi ana karɓar ɗaya bayan ɗaya.

1-Wasu na suyar awara.

2-Wasu na suyar gyaɗa.

3-Wasu na dahuwar ɗan malele.

4-Wasu wainar fulawa.

Haka za ayi layi kowa yana karɓar, yayin da rukuni na daban suke gefe suna rawa. Ana kuma iya samun wani rukunin maza da mata sun ware suna hira, wasu na ɓarara gyaɗa kamar dai a dandali a ƙauye.

Yaushe ake gudanar da gaɗa?

A da ana yin rawar gaɗa ne da dare kuma a dandali amma a yanzu ana gudanar da gaɗa ne da yammaci zuwa dare.

Waɗan ne irin wasanni ake gudanarwa a wurin gaɗa?

Ana gudanar da wasanni kala-kala a wurin gudanar da gaɗa kamar wasannin,
1-Langa
2-‘Yar gala-gala
3-Wasan igiya
4-Wasan kare da sanduna.
5-‘Yar carfke.

Daga cikin ‘yan mata wasu kan riƙe sanduna ko kararre a hannuwansu, wasu kuma ƙwarai wato ƙwarya. Wasu kan ware a gefe da samari, wasu kuma suna ciye-ciye.

Amfanin gaɗa

Kiɗa da waƙa na da matuƙar tasiri a rayuwar Bahaushe. Al’ada ce mai ƙarfi. Wani abu ne da ya shafi rayuwar Bahaushe baki ɗayanta. Kai a bisa gaskiya ma, idan muka leƙa karankataf ɗin al’adun Bahaushe, babu wacce ba kiɗa da waƙa a cikinta in banda mutuwa. Misali, fara daga kan aure, suna, sana’a, bukukuwa, zaman nishaɗi, yaƙi, da sauransu, za mu ga cewa duk ana yi musu kiɗa da waƙa ciki kuma har da malamai. Saboda haka gaɗa akan samu abubuwa kamar:

Nishaɗantarwa

Ƙwarai za a iya samun nishaɗi a cikin gaɗa domin ana gudanar da waƙoƙi, shi kuma kiɗa shi ne ƙashin bayan waƙa. Akan yi waƙa dan a farantawa wanda ake yiwa waƙar ya ji daɗi, ya kuma bayar da kyauta.

Ƙarfafa Guiwa

Daga cikin amfanin gaɗa da akwai ƙarfafa guiwa domin shi Kiɗa yana daga cikin abin da ke ƙara kaimi wurin gudanar da abubuwa da dama. A cikin gaɗa kuwa akwai kiɗa to haka ma gaɗa take taimakawa wurin ƙarfafawa amarya gwiwa zuwa gidan aurenta domin a waƙoƙin da ake gudanarwa a wurin da yawa ana yi mata tuni ne kan wani baƙi na gidan aure da ya rataya a wuyanta. Misali:

Ta zama ta zama ta zama.
Ta zama ɗauko riga
Ta zama ɗauko wando
Ta zama dama furar nan
Ta zama ɗauko buga
To ki sani aure bauta ne babu shi a zamanku na ƙauna.

Da sauran ira-iran waɗannan wanda dole su sakawa mutum kasashin da kuma himma.

Ilimantarwa

Akwai ilimantarwa a cikin gaɗa ta hanyar waƙoƙin gaɗa akan ko yi azanci magana, karin magana, iya sarrafa harshe, a wasu lokutan ma da sanin haƙƙokin zaman aure da kuma rayuwar auren.

Adana Tarihi da Al’adu

Ta hanyar gaɗa ana iya fahimtar yadda al’adun Hausawa suke. Gaɗa tana taka muhimmiyar rawa wurin haifar da nishaɗi tare da ƙarfafa zumunci tsakanin waɗanda suka hallaci bikin. Ta kan kuma kula sabuwar alaƙar zumunta ga wanda suka hallaci gurin da wasu baƙi a wurin gudanar da hidimar.

Waƙoƙin gaɗa

Waƙoƙin gaɗa suna da yawa akwai na da dana yanzu. Misalin waƙoƙin gaɗa na da:

Ga ‘yarku ayiriri ga ‘yar ku mun kawo.
Mu ba mu doke ta ba.
Mu ba mu zageta ba.
Ta ki ci ya ki sha sai ɗan karan kuka.
Kuka kamar ɓaure.

Waƙoƙin gaɗa na yanzu

Ta zama ta zama ta zama.
Ta zama ɗauko riga.
Ta zama ɗauko wando.
Ta zama dama furar nan.
Ta zama ɗauko buta.
To ki sani aure bauta ne babu fushi a zamanku na ƙauna.

Mawaƙan waƙoƙin gaɗa

Akwai mawaƙan gaɗa na da da kuma na yanzu. Za mu iya saka Barmana coge daga ciki saboda mawaƙiyar mata ce da abin da ya shafe su. Ta kuma kan yi waƙoƙin da suka shafi al’adun Bahaushe waɗanda ire-iren su ne ake gudanarwa a wurin gaɗa.

A mawaƙan zamani kuwa a fannin gaɗa za mu iya  • saka,
• Asama’u Saddik
• Naja’atu ta Annabi

Manazarta

Rumbin Ilimin (n.d.). Waƙoƙin Makaɗa

Jarmai, I. (2016, November 16). Ko babu komai na dawo da Martabar harshen Hausa – Inji Asma’u Sadiq mai wakar gaɗa. Voice of America.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×