Skip to content

Gasar Hikayata ta BBC Hausa

An ƙirƙiro gasar Hikayata ta BBC Hausa a cikin watan Yulin 2016 don ba wa marubuta mata damar baje basirarsu a fagen rubutun ƙagaggun gajerun labarai. Tun bayan ƙirƙiro wannan gasa wanda aka fara karɓan labarai a ranar 1 ga watan Agusta ta shekarar 2016, mata da dama sun samu nasarar samun kyaututtuka, kuma gasar ta kawo sauyi mai yawa a fagen rubutun kagaggun labarai. Ku biyo mu don sanin tarihi, manufofi da nasarorin da gasar ta samu a fannonin adabi da rayuwar al’umma kawo yanzu.

Manufofin ƙirƙiro gasar Hikayata

An ƙirƙiri gasar ne domin ba wa mata damar tofa albarkacin bakinsu da kuma fito da damuwar da take ƙunshe a ransu, ta hanyar rubutu tare da ba su damar da za su janyo hankulan al’umma kan matsalolinsu da kuma samar da mafita a tare da su.

A bayaninsa yayin kaddamar da gasar a shekar 2016, editan Sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, ya bayyana cewa, “A baya mata a nahiyar Afirka sun yi fice wurin bayar da kagaggun labarai da kuma tatsuniya da sauransu”. A nufinsa, lamarin ya sauya a yanzu, musamman a kasar Hausa, tun bayan wanzuwar karatun boko.

A takaice, samar da wannan gasa zai taimaka wurin b awa mata damar furta albarkacin bakinsu, kuma zai bunkasa rubutu a tsakanin mata din; har ila yau, da rage irin giɓin da ke tsakaninsu da maza, wanda rashin daidaito wurin samar da ilimi ya haifar.

Sashen mata da kan iya shiga gasar

Ko wace mace na iya shiga gasar Hikayata. Gasar ba ta bambance matan aure ko kuma ‘yanmata ba, an dai ware jinsin mata kaɗai domin ba su wannan dama. Sai dai kuma a kwai gejin shekaru na shiga ko idan aka haura an wuce ƙa’idar shiga, misali za a iya shiga idan an kai shekaru 18, kuma wacce ta haura shekaru 35 ba za ta iya shiga ba.

Hajiya Bilkisu Funtua a taron Gasar Hikayata ta 2020
Hajiya Bilkisu Funtua, Jagoran Alkalan Gasar Hikayata ta 2020

Gwarazan Hikayata da labaransu daga 2016 zuwa 2024

1. Zakarun shekarar 2016

  • Mataki na ɗaya: Aisha Sabitu (Sansanin Yan Gudun Hijira)
  • Mataki na biyu: Amina Hassan Abdusslam (Sai Yaushe?)
  • Mataki na uku: Amina Gambo Adam Kwaru (In Da Rai)

2. Zakarun shekarar 2017

  • Mataki na ɗaya: Maimuna Idris Sani Beli (Bai Kai Zuci Ba)
  • Mataki na biyu: Bilkisu Sani Makaranta (Zawarcina)
  • Mataki na uku Habiba Abubakar da, Hindatu Sama’ila (Sana’a)

3. Zakarun shekarar 2018

  • Mataki na ɗaya: Safiya Abubakar Jibrin (‘Ya Mace)
  • Mataki na biyu Sakina Lawan: (Sunanmu Ɗaya)
  • Mataki na uku: Bilkisu Muhd Abubakar (Zaina)

4. Zakarun shekarar 2019

  • Mataki na ɗaya: Safiya Ahmad Kaduna (Mairaici)
  • Mataki na biyu: Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo (Ba Ayi Komai Ba)
  • Mataki na uku: Jamila Babayo (A Juri Zuwa Rafi)

5. Zakarun shekarar 2020

  • Mataki na ɗaya Maryam Umar (Rai Da Cuta)
  • Mataki na biyu: Surayya Zakariyya Yahya (Numfashin Siyasata)
  • Mataki na uku: Rufaida Umar Ibrahim (Farar Ƙafa)

6. Zakarun shekarar 2021

  • Mataki na ɗaya Aisha Musa Dalil (Haƙkina)
  • Mataki na biyu Aisha Hamisu Maraɗi (Butulci)
  • Mataki na uku Zulaihat Alhassan (Ramat)

7. Zakarun shekarar 2022

  • Mataki na ɗaya: Amira Souly Maraɗi (Garar Biki)
  • Mataki na biyu: Hassana Labaran (Haihuwar Guzuma)
  • Mataki na uku: Maryam Muhd (Al’ummata)

8. Zakarun shekarar 2023

  • Mataki na ɗaya: Aisha Adamu Hussaini (Rina A Kaba)
  • Mataki na biyu:Aisha Abdullahi Yabo (Baƙin Kishi)
  • Mataki na uku: Aisha Abdullahi Jos (Tuwon Ƙasa)

9. Zakarun shekarar 2024

  • Mataki na ɗaya: Hajara Ahmad Hussain (Amon ‘Yanci)
  • Mataki na biyu: Amrah Auwal Mashi (Kura A Rumbu)
  • Mataki na uku: Zainab Chibaɗo (Tsale Ɗaya)
Aisha Muhammad Sabitu, gwarzuwar gasar Hikayata ta farko a shekarar 2016
Aisha Muhammad Sabitu, gwarzuwar gasar Hikayata ta farko a shekarar 2016

Jigogin laraban da suka yi nasara daga 2016 zuwa 2024

Shekarar 2016

1 – Gudun hijira

2 – Lalata yara da ba su ƙwayoyi

3 – Rashin ilimi

Shekarar 2017

1 – Fatalwa da ƙawance da kuma kishi

2 – Zawarci

3 – Sana’a

Shekarar 2018

1 – Jinkirin aure

2 – Fariya da kyawu

3 – Ɓatan miji/Soyayya/Alƙawari

Shekarar 2019

1 – Maraici

2 – Haihuwar ‘ya’ya mata

3 – Fyaɗe

Shekarar 2020

1 – Korona

2 – Siyasar mace

3 – Farar ƙafar

Shekarar 2021

1 – Fyaɗe

2 – Garkuwa da mutane

3 – Fyaɗe

Shekarar 2022

1 – Garar biki

2 – Burin auren mai kuɗi

3 – Siyasar mace

Shekarar 2023

1 – Maganin mata

2 – Kishi

3 – Auren miji ɗan son banza

Shekarar 2024

1 – Zanga-Zanga.

2 – Cin amanar aure da garkuwa da mutane.

3 – Garkuwa da Mutane.

Kammalawa

Babu shakka duk da irin kalubalen da ba za a rasa ba, gasar Hikayata ta haifar da cigaba ta fuskoki daban-daban kama daga bunƙasa adabi ta hanyar samar da ingantattun labarai waɗanda suka haska ɓoyayyun matsalolin mata da matasa, zuwa inganta rayuwar gwarazan ta hanyar samun ayyukan yi da ci gaba da karatunsu. Wasu sun samu guraben karo karatu a jami’o’i, wasu sun samu ayyukan yi a cikin ma’aikatun gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu, yayin da wasu suka mallaki jari suka kafa sana’o’i daban-daban.

Ku karanta cikakken tsokacin masana game da gasar Hikayata ta BBC Hausa.

Manazarta

BBC News Hausa. (2016, July 26). Gasar Hikayata ta mata zalla. BBC Hausa

Fagge, K. Y. (2020, July 6). Gasar rubutattun gajerun labaran Hausa ta Arch. Ahmad Musa Dangiwa

Ismail, H. S. (2025, March 17). Tarihi da tasirin gasar Hikayata ta BBC Hausa. Bakandamiya Hikaya

Malumfashi, B.Y. (2019, May 31). Tsokaci da sharhi game da Hikayar Mata. Aminiya

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page