Skip to content

Harry Potter

Harry Potter yana cikin jerin littatafai  guda bakwai da marubuciyar Birtaniya J. K. Rowling ta rubuta. Littafin na daga cikin littatafan da suka fi shahara a duniya, musamman a tsakanin yara da matasa. A lokacin da marubuciyar ta rubuta littafi na farko, Harry Potter and the Philosopher’s Stone, sai da ta turawa kamfanonin ta’alifi har guda 12 amma duk suka ƙi karɓar littafin, daga ƙarshe dai kamfanin Bloomsbury suka karɓa suka buga, ya kuma ya fito cikin sa’a tare da samun gagarumar nasara.

Tun daga lokacin da littafi na farko, Harry Potter and the Philosopher’s Stone, ya fita a ranar  26 ga watan Yuni 1997, litattafan suka samu shahara da karɓuwa sosai a wurin masu karatu da manazarta gabaɗaya.

Bangon littafin Harry-Potter, na marubuciya J.K Rowling.

Zuwa watan Fabarairun 2023, an siyar da jimillar kwafi na litattafan guda dubu ɗari shida a duniya. Hakan ya sa littafin ya zama mafi samun ciniki a duniya bakiɗaya. An fassara litattafan zuwa harsuna 85 na duniya.

Bayanin littafin a takaice

Sunan littafi: Harry Potter

Marubuciya: J. K. Rowling

Tsara bango: Thomas Taylor, Cliff Wright, Giles Greenfield & Jason Cockcroft

Ƙasa: Burtaniya

Harshe: Turanci

Maɗaba’a;  Bloomsbury

Kwanan watan ɗab’i: 26 ga Yuni 1997

Sabuntawa: 21 ga Yuli, 2007

Rabe-rabe: Bugun hannu, na sauraro da e-book

Yawan littattafai

Ga jerangiyar litattafan da shekarun da suka fita tare da lambobinsu na ɗab’i:

1. Harry Potter And The Philosopher’s Stone (1997)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-3269-8
  • Paperback: ISBN 0-7475-3270-1

2. Harry Potter And The Chamber of Secrets (1998)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-3848-8
  • Paperback: ISBN 0-7475-3849-6

3. Harry Potter And The Prisoner of Azkaban (1999)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-4215-9
  • Paperback: ISBN 0-7475-4216-7

4. Harry Potter And The Goblet of Fire (2000)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-4624-6
  • Paperback: ISBN 0-7475-4625-4

5. Harry Potter And The Order of the Phoenix (2003)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-5595-8
  • Paperback: ISBN 0-7475-5596-6

6. Harry Potter And The Half-Blood Prince (2005)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-6979-9
  • Paperback: ISBN 0-7475-6980-2

7. Harry Potter And The Deathly Hallows (2007)

  • Hardcover: ISBN 0-7475-9108-8
  • Paperback: ISBN 0-7475-9109-6

Taƙaitaccen bayanin abin da kowane littafi ya ƙunsa

1. Harry potter And The Philosopher’s Stone

 (Sorcerer’s Stone a Amurka): Harry ya gano haƙiƙa bin matsayinsa na matsafi tare da fara zuwa makarantar Hogwarts domin koyon tsafi.

2. Harry Potter And The Chamber of Secrets

Harry tare da abokansa sun gano wani ɓoyayyen babban ɗaki a makarantar Hogwarts mai ɗauke da halittu masu haɗari.

3. Harry Potter And The Prisoner of Azkaban

Harry ya gano cewa wani fursuna mai suna Sirius Black, ya gudo daga magarƙama kuma shi ne ya ci amanar iyayensa har ya ja aka kashe su, yanzu kuma yana so ya kashe Harry.

4. Harry Potter And The Goblet of Fire

Wutar tsafi ta bayyana sunan Harry a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su fafata a gasar makarantun matsafa.

5. Harry Potter And The Order of the Phoenix

Harry ya kafa tawaga mai suna Dumbledore’s Army domin tunkarar baƙaƙen matsafa sakamakon dawowar Voldemort.

6. Harry Potter And The Half-Blood Prince

Harry ya koyi abubuwa masu yawa game da Voldemort da tarihinsa da kuma shi kansa yayin da ya fara girma.

7. Harry Potter And The Deathly Hallows

Harry, Ron, da Hermione sun ɗauki niyyar yin wata tafiya mai hatsarin gaske domin samun lagun Voldemort domin samun nasara.

Karɓuwa

Labarin Harry Potter ya samu karɓuwa sosai a duniya. Karɓuwarsa da shahararsa ya sa aka fassara shi zuwa harsuna 85. Faruwar hakan ya sa marubuciya J. K. Rowling ta zamo marubuciyar da aka fi fassara litattafanta a duniya. Daga cikin harsunan da aka fassara litattafan akwai Koriyanci, Armaniyanci Yukraniyanci, Larabci, Hindi, Urdanci, Bengaliyanci, Walshanci Bulgariyanci Afirkanci, Latbiyanci da dai sauransu.  Gaba ɗaya litattafan guda bakwai an siyar da kwafinsu sama da guda miliyan ɗari shida. Sannan wannan gagarumar nasara ta sa marubuciyar littafin da zama marubuciya ta farko da ta taɓa zama biloniya a duniya.

J. K Rowling, marubuciya, ‘yar ƙasar Birtaniya.

Litattafan Harry Potter sun samu karɓuwa a wajen yara da matasa fiye da kowane irin littafi, hakan ya sa littafin ya zamo sananne a sama da ƙasashe 200, kuma dukkan litattafan sun samu nasara a harkar kasuwancinsu. A bisa wannan karɓuwa da suka yi ne ma har ta kai ga an juya labaran zuwa fim, inda aka ɗauki labarin kowane littafi a matsayin fim ɗaya, face Harry Potter And The Deathly Hollows wanda aka raba shi gida biyu, kuma duka fina-finan sun samu karɓuwa sosai, jimillar kudin da fina-finan suka kawo a harkar kasuwancinsu ya kai dala biliyan bakwai da ɗigo bakwai. Bayan shekaru kuma sai kamfanin HBO suka sanar da cewa za su shirya wani sabon shiri mai dogon zango a kan labarin Harry Potter. Akwai kuma wasannin wayoyin hannu da na kwamfuta da aka ƙirƙiro duk saboda karɓuwar Harry Potter.

Yabawa

Masana da kuma masu sharhi sun yaba wa littafin sosai, musamman ta fannin abubuwa kamar haka:

  • Fikirar marubuciyar wurin iya ƙirƙiro duniya guda mai faɗi irin haka.
  • Taurarin labari masu shiga rai waɗanda mai karatu ke iya alaƙantuwa da su.
  • Taɓo abubuwa masu muhimmanci irin su abota, soyayya tare da nuna bambanci tsakanin adalci da zalunci.
  •  Salon rubutu, barkwanci da kuma iya bayyana lokutan annashuwa da kuma na baƙinciki.
  • Tsara labari mai ma’ana tare da jan hankalin mai karatu wanda ke cike da abubuwan mamaki.

Kyautuka da lambobin yabo

Marubuciya J. K. Rowling ta samu lambobin yabo masu tarin yawa a sakamakon labarin Harry Potter. Daga cikin lambobin yabon da ta samu a kwai: National Book Award, Hugo Award, da kuma Order of the British Empire award.

Litattafan Harry Potter sun samu lambobin yabo masu yawan gaske tun bayan fitowarsu, ga wasu daga ciki:

  • Platinum Award daga Whitaker Gold
  • Whitbread children’s book of the year award (1999)
  • WHSmith book of the year (2006)
  • Hugo Award for Best Novel 2001, Harry Potter and the Goblet of Fire

Baya ga waɗannan kamfanonin jaridu da mujallu, da laburare tare da sauran kafofin yaɗa labarai da na ilimi da dama sun karrama litattafan Harry Potter da lambobin yabo tare da rubuta muƙalolin yabo a kan wannan littafi.

Babbar nasarar da littafin ya samu fiye da kowane shi ne farfaɗo da son karatu a tsakanin yara da matasa, tare da samun mabiya masu ɗumbin yawa

Manazarta

Harry Potter (n.d.).  Official Harry Potter Encyclopedia.

Wikipedia contributors. (2024, August 20). Harry Potter.

Wiki, C. T. H. P. (n.d.). Harry Potter (book series). Harry Potter Wiki.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×