Skip to content

Isah Pilot

Isa Sanusi Bayero, wanda aka fi sani da Isa Pilot, ɗan gidan sarauta ne daga birnin Kano, a Arewacin Najeriya. Ɗa ne ga marigayi Sarkin Kano, Sir Muhammadu Sanusi I, wanda ya yi mulki daga 1954 zuwa 1963. Sannan Isah Pilot  kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Ya yi fice a fannonin rayuwa da dama, ciki har da fannin tuƙa jirgin sama, wanda a nan ya samu laƙabin da ya yi shura a bakin jama’a, wato (Isa Pilot.) Amma a zahiri, wannan sunan ya wuce tuƙin jirgi, domin yana wakiltar mutum mai salo, fahimta, wayo, tarihi, da kuma ɗimbin tasiri a wurin jama’a.

FB IMG 1749669787503

Rayuwa da asalinsa

An haifi Isa a cikin gidan sarauta na Bayero, gidan da ke da tarihi mai faɗin gaske. A gidan Bayero, duk numfashi ko motsin da mutum zai yi yana ɗauke da nauyin al’ada, daraja da alhakin da ke kan zuriyar masu sarauta. Isa ya taso ne a cikin irin wannan muhallin da ake horo da tarbiyya ta ɗabi’a da tsarin mulki, tun daga ƙuruciya. Sai dai duk da haka, Isa bai jingina rayuwarsa da gado ko zuriyar da ya fito daga gare ta ba. Ya zaɓi ƙirƙirar kansa bisa sana’a, ilimi, da gini mai ɗorewa.

Ilimi da ƙwarewa

Isa Sanusi Bayero ba kawai ɗan sarauta ba ne, injiniya ne mai cike da ƙwarewa, sannan ƙwararren matuƙin jirgin sama (pilot engineer), wanda ya tuka jiragen gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu. A tarihin aikinsa na pilot, ya taɓa jigilar shugabannin Najeriya sama da guda biyar da suka haɗa da, Ibrahim Babangida, Sani Abacha, Abdissalami Abubakar, Olusegun Obasanjo da Ernest Shonekan. Wannan ne kuma ke nuna amincewa da gwamnati ta yi a kan ƙwarewarsa da kwarjinin aikinsa a wurin al’umma.

Baya ga wannan, Isa ya kafa kamfanoni masu zaman kansu tun kafin zuwan Sarki Sanusi II a karagar mulki. Daga cikin kamfanonin da ya kafa, akwai wanda ya samu amincewa daga babban bankin Najeriya (CBN) a lokacin Gwamna Charles Soludo, domin sarrafa kuɗi ta jirgin sama. Baya ga aikin tuƙi, Isah Pilot yana da jiragen ɗaukar kaya (cargo aircraft) mallakinsa, wanda hakan ke nuna irin nisan da ya kai a fannin kasuwanci da harkokin sufuri.

Rayuwarsa a masarauta

Rayuwar Isa ba ta tsaya a tuƙin jirgi ba. Ya fara aiki a matsayin Principal Private Secretary ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, inda ya yi shekaru yana gudanar da aiki da tsari gami da tsantseni. Isah Sanusi Bayero mutum ne da mafi yawan ƴaƴan marigayi Sarkin Kano Dr.  Ado Bayero suke alfahari da shi,  saboda yadda ya  ƙaunaci mahaifinsu. Duk wata biyayya da ɗan Adam yake yi wa mutum a duniya,  toh Isa Pilot ya yi wa marigayi  Dr. Ado Bayero. Bayan rasuwar Ado Bayero a 2014, ya ci gaba da aiki da Sarki Muhammadu Sanusi II har zuwa shekarar 2017.

A fadar Kano, Isa ya riƙe matsayin chief protocol officer da kuma oracle na fada. Shi ne jagoran duk wata tafiyar sarki, baƙi, da jerin abubuwan da ke da alaƙa da masarautar wannan ne ya sa ake masa kirari da “Isah zancen Sarki, na gaban Sarki.” Bayan sauyin mulki, ya ci gaba da wannan aiki a ƙarƙashin Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Barin muƙami da dalilai

A 2017, an ruwaito cewa an kore shi daga masarauta, amma daga baya Isa ya fito fili ya ƙaryata hakan. A cewar sa, ya bar muƙaminsa ne da kansa, saboda rashin jituwa da salon tafiyar da masarautar a wancan lokaci. Ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda Sarki Sanusi II ya sauya matsayi dangane da neman afuwa a wancan lokaci.

Wannan matsayi da Isah Pilot ya tsaya a kai, ya ƙara masa daraja a idon wasu, wanda suka ɗauki hakan a matsayin tsayin daka da mutunci. Amma kuma hakan ya haifar da suka daga wasu, wanda ke kallon sa a matsayin mai ra’ayin kansa.

Rayuwa bayan masarauta

Bayan barin aiki a fadar masarauta, Isa Pilot ya koma kasuwanci da harkokin sa na sirri. A 2018, an kai masa hari a gidansa da ke Sharada, Kano, amma ya tsira da ransa. Wannan harin ya sake ƙarfafa ra’ayoyin da ke cewa Isa Pilot mutum ne mai faɗa a ji, kuma wanda wasu ke jin tsoro ko ƙiyayya da gaba da shi. A kuma kwanakin nan, Isa ya shahara a kafafen sada zumunta, musamman TikTok da Facebook, inda ake kallon sa cikin kaya na gargajiya, yana wakiltar al’adun Kano da mutuncin masarauta. Wannan salo ya ƙara fito da shi a matsayin wakili na gargajiya da al’adun Arewa, a cikin tsarin zamani.

Dangantakarsa da masarauta

Isa Sanusi Bayero:

  • Ɗa ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I
  • Ɗa ne ga ɗan Sarkin Kano Dr. Ado Bayero
  • Ɗan gidan Sarkin Kano Ibrahim Dabo
  • Ƙani ne ga Galadiman Kano Abbas Sunusi
  • Ƙani ne ga Wamban Kano Sunusi Lamido Ado Bayero
  • Kawun Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
  • Kuma babban mai bada shawara ne ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero

Wannan zuriyar da tsatson masarauta na nuna matsayin Isa ba kawai a Kano ba, har ma a tarihin Najeriya gaba ɗaya.

Kirari da salo

Isa Pilot ba kawai suna ba ne, kalma ce da ke ɗauke da cikakken labarin mutum mai cike da salo da tasiri. Ga wasu daga cikin kirarinsa:

  • Isan Ɗan Maryamu
  • Wazirin Sarkin Aljani
  • Zanga-zanga Uban Sunusi na II
  • Mai masaukin Sarkin Aljanu
  • Baƙar Fura dakan Iblisai
  • Isa rabi mutum, rabi aljan
  • Ka tuƙa mota a ƙasa, ka tuƙa jirgi a sama
  • Zanga-zanga jikan Dabo
  • Mai Sarki, Zancen Sarki, Na Gaban Sarki
  • Suna kiwon Akuya, kai Zaki kake kiwatawa.

Rabi mutum rabi aljan

Rabi mutum, rabi aljan kirari ne na musamman da mutane ke ma Isa Sanusi Bayero, wannan kirari kuma ya jefa ayar tambaya a zukatan al’umma, har wasu suke gani kamar yana da alaƙa da aljannu. Sai dai a kyakkyawar fahimta, wannan nan kirari na Rabi Mutum, Rabi Aljan da ake masa, kirari ne mai ɗauke da zurfin ma’ana. Ana kallon Isa Pilot a matsayin mutum da ya haɗa tsari biyu: mutum mai kamala, wayo da tarbiyya, da kuma mutum mai zafi, dabara da ɓoyayyen salo.

Me ya sa ake kiransa rabi mutum, rabi aljan?

A kyakkyawan hasashe na manyan dalilan da suka sa ake masa wannan kirari na Rabi mutum, Rabi Aljan sun haɗa da:

  • Rayuwa tsakanin zamani da gargajiya. Shi mutum ne mai rawani da rigar sarauta, amma kuma mai tuƙin jirgi haɗe da fasahar zamani.
  • Lafazi da hikima: Yana magana da lafazi mai nauyi da hikima. Inda wasu ke fahimtar sa, wasu kuma ba sa fahimta, hakan ne ya ƙara masa daraja sosai a idon jama’a.
  • Dabara da ra’ayi: Yana tsayawa kan ra’ayinsa, ko da ya sha bamban da ra’ayin kowa. Wannan ne ke sa wasu su girmama shi, musamman masu goyon bayan Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero. A ɗayan bangaren wasu kuma suka zarge shi.
  • Mutum ne Mai Iri biyu: Wani lokacin ana jin shi cikin tausayi da salo, wani lokacin kuma cikin ƙarfi da zafi. Wannan ke sa mutane su ɗauke shi a matsayin mutum da ba kowa ke gane kansa ba, har wasu kan yi masa kirari da “Da mutum yayi karo da Isah Pilot, gwara ya yi karo da goshin jirgi.”

Tasiri da gudunmawa

Isa Pilot yana daga cikin jiga-jigan da suka tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin masarauta a lokacin sauyin mulki da rikice-rikice a masarautar Kano, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya da gaskiya da ɗa’a,  ko da hakan zai sa su rasa matsayi.

A shekarar 2023, ya sake bayyana a faifai a matsayin mutum mai kishin dan Adam, lokacin da Amnesty International ta naɗa shi Country Director a Najeriya. Wannan babban matsayi ya sake ƙara tabbatar da cewa Isa Pilot ba kawai ɗan sarauta ba ne, mutum ne da duniya ke ganinsa da daraja.

Isa Sanusi Bayero Ɗan Sarki ne, Malami ne, sannan Batijjane ne. Isah Pilot ba kawai mutum ba ne; labari ne mai rai da rai, wanda ke bayyana yadda mutum zai iya tafiya da zurfinsa, ya gina kansa bisa nagarta, ƙwazo, da son ci gaba. Mutum ne da ya riƙe tarihi a hannu guda, ya rungumi zamani da ɗayan hannun, kuma ya shiga zukatan mutane da salon da ba a saba gani ba.

Rayuwarsa ta faro daga fadar Kano zuwa cikin jirgi, daga masarauta zuwa kafafen sada zumunta, daga kirari zuwa juyayi.  Isa Pilot ya kafa wata gagarumar alama da za ta ci gaba da kasancewa a zukatan mutane. Kirarin “Rabi mutum, Rabi Iblis”  yana bayyana cikakken Isa, wato mutum wanda babu  kamarsa a masarautar Kano.

Manazarta

Emir Sanusi’s ex-private secretary, Isa Pilot, reveals why he dumped monarch — Daily Nigerian”

“Nigeria: Amnesty Int’l appoints Isa Sanusi as Country Director – Amnesty International Nigeria” .

Emir Sanusi sacks own private secretary – Daily Trust”

Emir Sanusi uncle attended Edo cross-over Church Service, not Kano Emir’s Son – Fact Check – SolaceBase”

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×