Skip to content

Kusufi (Eclipse)

Kusufi (Eclipse)

Idan ana so a fahimci mene ne kusufi, dole ne sai an fara da tsayuwar wata, rana, da earth (duniyar da muke ciki) Saboda su ukun ne suke haɗuwa su samar da eclipse. Ga su kamar hak – wata, rana da kuma earth.

Rana ita ce take bai wa mutane energy waton ƙarfi da kuzari sannan da haske. Rana ita ce wadda ta fi ko wace star (tauraro) girma a solar system ɗin da ake da shi.

Eclipse

Kuma (Solar system ɗin sun haɗa da wata, rana, duniyoyi [planets]). Duka waɗannan taurarin da duniyoyin ba su da haskensu na karan kansu wanda zai sa su ci gashin kansu. Saboda duk wani haske da suke fitarwa daga hasken rana ne.

Misali, idan aka haska silver, za a ga haskenta yana haska can wani waje daban. Saboda haka taurari, wata, da duniyoyi ba su da haskensu na kansu idan babu hasken rana.

Zafin rana kamar yadda masanan suka faɗa ya kai kimanin 6, 000 °C. Girmanta kuma ya linka na earth sau 300, 000. Sannan akwai solar system da ake da shi. Kuma kowace duniya tana kan orbit ɗinta bigire), akwai wasu layukan da aka zana su ne orbit). Amma kuma orbit kawai ƙirƙirar sa aka yi saboda ɗalibai su fahimta, amma babu shi a zahirin gaske.

Abu na gaba da ake so a fahimta a nan shi ne; kowace duniya tana zagaye rana a kan orbit ɗinta. Wannan zagayawar shi ne Rotation. Earth tana kammala rotation ɗin ta cikin awa 24 (sauran duniyoyin sun wuce haka, wasu ba su kai haka ba, kamar mercury da venus).

Duniyoyi tara da ke solar system

Sai dai ita rana ko kaɗan ba ta motsi. Duniyoyi da watanni su ne kawai suke motsi. Rotation ke nan (na ce watanni saboda wata ba ɗaya ba ne amma duniyar wata ɗaya take da shi kuma shi ne wanda muke gani). Wata ba duniya ba ne kuma ba tauraro ba ne, amma satellite ne.

Bayan rotation duniyoyin da watannin suna wani motsin wanda ake kira revolution.

Abin lura, inda wata yake shi ne tsakanin rana da duniya. Amma rana da earth dukansu suna rotating a kan orbit ɗin su. Saboda idan aka duba da kyau za a ga ba saiti ɗaya suke ba. Sannan idan aka kalli yadda wata yake. Ya dace a fahimci position ɗin sa lokacin da yake normal. Wanda za a ga komai a cikin hoton solar eclipse ya faru.

Yayin da duniya da wata suka ci gaba da zagaye rana, akwai lokacin da za a samu wata ya shigo tsakanin rana da duniyar mu. Misali, su zo saiti ɗaya. Lokacin da hakan ya faru, ana samun solar eclipse. Wata ya kare hasken ranar da yake zuwa duniyarmu.

Idan aka duba lokacin da wata ya shigo tsakiyar duniya da rana, hakan yana yin sanadin hasken rana ya ƙi riskar mu.

Ire-iren kusufi

1. Total eclipse

A total eclipse, position ɗin wata yana yin daidai da rana, hakan ya sa watan ya ke rufe hasken rana gaba ɗaya. Kuma hakan yana faruwa duhu zai zo, ya zama kamar dare. Hasken ɗan kaɗan ne yake bayyana a gane solar eclipse ne. Idan aka kalli hoton da kyau za a gani. Inuwar da watan yake samarwa wadda ake kira Umbra, tun da ya rufe hasken ranar ita ce take rufe duniyarmu, kuma mutanen da suke bangaren da ake mu su rana ne kawai za su gane kusufin rana ake a lokacin.

Misali, yanzu a Nigeria idan ana yin rana, America da Philippines zai kasance a wurinsu dare ne, da za a yi kusufin rana, ba za su gane an yi ba.
So, mu ƙaddara a Nigeria kusufin ranar da ake yi total ne, wataƙila Algeria ko south Africa ya zama nasu partial ne. Ya danganta da position ɗin su lokacin da eclipse ɗin ya faru.

2. Partial eclipse

A partial eclipse ɗin kuma wata bai yi saiti daidai da rana ba. Ina nufin wani ɓangare ya rufe na hasken ta amma ba duka ba. So lokacin da hakan ya faru, rana za ta bayyana kamar an ɗan cinye gefenta, idan aka kalli hoton za a gani. Kamar dai yadda ake zana wata.

3. Annular eclipse

Yana faruwa lokacin da wata ya yi nesa sosai da rana. Hakan zai zama hasken da wata ya kare na rana ba duka ba ne. Wannan dalilin zai sa a ga zobe mai sheki ya zagaye wata (ko a ce annulus). Hasken rana ne yake komawa kamar zoben.

Annular solar eclipse

Kusufin rana (Solar eclipse)

Ba abu ne da yake yawan faruwa ba. Wata yana yawan wuce ta sama ko ta ƙasan rana saboda orbit dinsa ya yi kama da na earth. Wannan dalili ne ya sa solar eclipse bai faye faruwa ba.

Rabe-raben kusufin rana.

• Partial solar eclipse
• Annular solar eclipse
• Total solar eclipse.

Kusufin-wata (lunar eclipse)

Yana faruwa idan duniya (earth) ta shigo tsakanin wata da rana. A solar eclipse wata ne yake shigowa, ba kamar kusufin wata ba, shi kusufin rana ana ganin sa a ko wane bangare na duniya idan dare ya yi.

Lunar eclipse

Shi ma kamar kusufin rana, yana da rabe-rabe guda uku:
• Total lunar eclipse
• Partial lunar eclipse
• Penumbral lunar eclipse

Total lunar eclipse: wata gabaɗaya yana cikin inuwar earth. Sunan inuwar Umbra. Wannan zai sa a ga wata ya koma ja. Wannan saboda atmosphere duniyar tamu yana canza launin hasken rana ne.

Partial lunar eclipse: shi kuma wannan lokacin, wani ɗan ɓangare ne na jikin watan kawai ya shiga cikin inuwar ranar. Saboda haka zai dan yi duhu.
Idan kika duba hoton za a ga waje karami ne kawai ya yi duhu.

Penumbral lunar eclipse: shi ne lokacin da watan ya shiga gefen inuwar da duniya take samarwa.

Misali; idan aka ɗauki toch light aka haska mutum da ita da dare, to akwai wata inuwa a gefe mai haske bayan inuwar mutum mai duhu. Inuwa ta gaske, mai duhun kenan, sunan ta umbra. Ta gefen umbra kuma, wadda ba ta kai ta haske ba, sunan ta Penumbra.

Aƙarshe banbamcin kusufin rana da wata kawai shi ne; na rana wata ne yake shigowa tsakiyar duniya da rana. Na wata kuma, duniya ce take shiga tsakiyar wata da rana.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×