Skip to content

Lalle

    Aika

    Lalle na ɗaya daga cikin kayan adon da mata suka fi amfani da shi. Musamman a lokacin bukukuwa ko kuma sha’ani na gyara. Haka kuma yana daga cikin manyan magungunan da al’ada da kuma malam Bahaushe suka gamsu da aikinsa a fannoni da dama.

    51yAcx9sJ L
    Lalle amfanin gona ne da yake fitowa a sassa da dama a arewacin Najeriya da wasu ƙasashen.

    Hausawa suna kiran shi da suna lalle, Turawa kuma suna kiran shi da suna Henna. Yayin da a kimiyance kuma ana kiran shi da suna (lawsonia inermis).

    Wuraren da ya fi fitowa

    Lalle yana da asali a yankunan da ke da yanayin busasshiyar ƙasa da rana mai zafi kamar Asiya ta Kudu, Gabas ta Tsakiya, da Arewacin Afirka. Ana shukashi ne a gidaje da lambuna a yankunan da suke buƙatar yanayin zafi.

    • Arewacin Afirka: Ƙasashe kamar Masar, Sudan, Moroko, da Aljeriya.
    • Gabas ta Tsakiya: Irin su Saudi Arabiya, Yemen, Iran, Iraki, da Siriya.
    • Asiya ta Kudu: Ƙasashe kamar Indiya, Pakistan, da Bangladesh.
    • Sassan Gabashin Afirka: Musamman a Somaliya, Habasha, da Kenya.
    • A Najeriya: Ana shuka lalle a wasu jihohin Arewa inda akwai busasshiyar ƙasa da yanayin zafi, kamar: Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi, da Sokoto.

    A wasu ƙauyuka, mata da yawa sukan shuka lalle a lambun gidajensu don amfanin kansu.

    Yanayin da lalle ya fi buƙata

    • Lalle ya fi son wurare masu bushewa ko ƙarancin ruwa da zafi.
    • Lalle ba ya son ruwa mai yawa ko wuri mai cike da sanyi.
    • Lalle na son ƙasa mai yashi ko yashi mai laushi.

    Siffar bishiyar lalle

    Bishiyar lalle matsakaiciyar shuka ce mai kama da ƙaramar bishiya, masana sun tabbatar da cewa tsayinta ba ya wuce tsayin da ya kai mita 2–6.

    Ganyen lalle

    Bishiyar lalle tana da ƙananan ganye masu siffar dogaye da launi koren-kore mai haske.

    Furranin bishiyar lalle

    Furanninta ƙanana ne da suka ƙunshi launin fari ko ruwan hoda, masu ƙamshi mai daɗi.

    Lokacin da aka fi amfani da lalle

    • Bikin una
    • Bikin aure
    • Bukukuwan sallah
    • Bikin Maulidi

    Yadda sarrafa lalle

    • Ana ɗebo lalle ne ɗanye a gona a kawoshi gida a busar da shi, kuma busar da ake yi masa ta inuwa ake yi masa daga nan sai a sassaɓa shi.
    • A da lokacin iyaye da kakkani dakau ake kaiwa. Amma yanzu da aka samu ci gaba ana kai shi niƙa ne a inji a niƙo sai a kawo shi gida.

    Nau’ikan lalle

    • Busasshen ganyen lalle kafin a niƙa wanda ake kira da sansami.
    • Daddaken lalle shi ne wanda ake dakawa ko niƙawa a kai kasuwa ana siyarwa ko kuma mata a gida suna kasawa suna siyarwa.

    Ƙunshin da ake yi da lalle

    Ƙunshi Dungulmi

    • Ƙunshi Take kwalta
    • Ƙunshi na zane (fulawa)
    • Ƙunshi na salatif

    Sinadaran da ke cikin lalle

    • Lowsone: Shi ne yake taimakawa wurin sarrafa lalle ya bayar da launin ja ko kuma ya yi marun wato kalar duhu.
    • Tennins: Yana taimakawa wurun gyaran gashi ko kuma fata yayin da aka yi amfani da lalle.
    • Coumarins: Yana taimakawa wajen fito da kamshin lalle yayinda aka ƙunsa.
    • Flavonoids: Yana taimakwa wajan hana lallacewar fata ko gashi yayin da aka yi amfani da lalle.
    • Xanthones da Terpenes: Suna taimakawa wurin hana ƙwayoyin cutar fungi yin tasiri.

    Amfanin lalle

    Lalle yana da matuƙar amfani sosai da sasai a wurin kowa ne mutum. Kama daga kan maza har mata da kuma yara ta fannoni da yawa da kuma dama.

    IMG 20250724 WA0012
    Lalle muhimmin kayan kwalliya ne da ado ga mata.

    Amfanin lalle a addini

    Dokta Isa Lawan, wanda aka fi sani da Mai Fada Da Aljanar Sumbuƙa ta Goron Dutse, da ke Kano a arewacin Najeriya, kuma Shugaban Cibiyar ba da Magungunan Musulunci ta Aba Zarril Gifari ya ce, “Ba wai ado da lalle kaɗai ke da falala ba, hatta shuka shi ma a gida ko a gona na korar iskokai daga wuri, da sanya albarka ga sauran shukoki da ke kewaye da shi. Babban aikin lalle na farko shi ne idan mutum ya shafa shi a jikinsa yana ba shi kariya a jikinsa, musamman daga shafar aljanu.”

    Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya Annabi (SAW) ya ce, maza su shafa shi a gemu, domin gashi ne hanyar da shaiɗan ya fi bin jikin ɗan Adam. Ba kuma lalle har sai gashi ya yi jawur ba, a’a sanya shi ko yaya ne a wanke ya wadatar.

    Kariya daga shaiɗanu

    Idan mace tana yawan yin lalle, yana hana shaiɗan raɓar ta, musamman tafin hannu da ƙafa, saboda hannu ya fi saurin ɗaukar cuta, yayin da ƙafa kuma ta fi ɗaukar zafi, shi ya sa idan ka taka garwashi kake jin sa har tsakiyar kanka.

    Haka zalika ana hayaƙi da shi don kore aljanu, kuma ga riba da yake da ita ga manominsa, kuma yana bin ƙofofin jini ya wanke shi tas.

    Yin lalle yana sa farin ciki, saboda yawan baƙin ciki alamar aljanu ce; to idan mace tana yawan yin lalle ba za ta dinga yawan damuwar ba gaira ba dalili ba.

    Sai dai wannan bayani ya ta’alaƙa ne kan lalle na gargajiya ba wai na zamani ba. Duba da cewa na zamani an cakuɗashi da abubuwan da ka iya zama masu illa ma gare shi.

    Lalle a likitance

    Dokta Nuruddin Haladu likita ne a Asibitin Fata na Bela a Jihar Kano, ya kuma ce babu wata illa da a likitance da aka taɓa ganowa lallen gargajiya na da shi har yanzu, sai dai dan abin da ba a rasa ba a ɓangaren na zamani da ake sanyawa sinadarai.

    IMG 20250724 WA0013
    Lalle amfanin gona ne da ke samar da kuɗaɗen shiga ga manoma da gwamnati.

    Illar da za a iya cewa lalle na da shi sai dai ga wasu da bai karɓe su ba, kamar sinadarin Haidrojin da ake sakawa a baƙin lalle, sinadari ne mai karfi, wanda a asibiti wanke gyambo ko wani ciwo ake yi da shi saboda kashe ƙwayoyin cutarsa kafin su yi masa komai.

    To wasu idan bai karɓe su ba yana sanya musu ƙuraje masu ruwa, ko ma ƙaiƙayi na tsawon lokaci da kashe farce ya yi ta raɗaɗi, waɗannan duk ana kiran su ‘allergy’.

    Lalle a fanin kwaliya

    Ana amfani da lalle wurin gudar da kwaliya ta fusakar:

    • Ana niƙa ganyen lalle a yi hodar da ake amfani da ita wurin zanen hannu, ƙafa, ko gashi.
    • Zana lalle a hannu ko kuma ƙafa, al’ada ce daɗɗaɗiya mata musamman a wajen bukukuwan aure da sauran shagulgula.
    • Ana haɗa lalle da zuma da kurkum da lemon tsami domin gyaran fuska a ƙawatata ta yi kyau da ɗaukar hankali.
    • Ana amfani da furanninsa wajen yin turare ko turaren wuta a wasu wurare.
    • Gyaran fata: Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a riƙa wanka da ruwa lallen aƙalla so ɗaya a rana.
    • Fatar fuska: Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika goga fuskar ta ita. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.
    • Ƙurajen fuska: Ga masu fama da ƙurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci pimples ɗin za su ɓace.

    Lalle a matsayin magani

    Lalle yana taimakawa wajen warkar da wasu cututtukan fata da rigakafin wasu ƙwayoyin cuta.

    • Amosanin kai: Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle domin maganin amosarin gashi. Ana yin hakan ne ta hanyar kwaɓa lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosarin kai.
    • Ana dafashi a ba mace mai jego ra shiga domin ƙawar da cuttuka, musamman idan aka haɗa shi da ganyen magarya.
    • Lalle yana da ni’imar sanyaya jiki idan aka shafa a tafin ƙafa ko tafin hannu.
    • Gyambon yatsa: Masu gyambon yatsa (ɗankankare) na amfani da lalle wajen neman sauki. Akan kwaɓa shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsar don neman waraka ko busar da shi.
    • Dattin ciki: Shan ruwan lalle na wanke dattin dake ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa aka tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.
    • Ciwon ƙafa: Yin lalle na rage ciwon ƙafa. A kwaɓa lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka na rage raɗaɗi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.

    Lalle a al’ada

    • Ana amfani da lalle wurin yin bikin kamun amarya a wasu sassan har da ma da ango wanda ake kira da wankan lalle.
    • Ana ƙunsa wa yaron da aka haifa kalle a al’adar malam Bahaushe daga zarar an haife shi da sunan kariya daga masu kambun baka.

    Lalle a matsayin sana’a

    Lalle ya takaimaka matuƙa wurin samar da kasuwanci tsakanin mata da maza. Sana’ar lalle sana’a ce mai kyau da inganci da kuma riba. Masu yin sana’ar sun tabbatar da yadda suke samun rufin asiri da ita ta fuskoki da yawa.

    Masu yin sana’ar lalle

    Kowane jinsi yana yin sana’ar lalle maza fa mata. Duba da yadda bayanai suka nuna waɗanda suke shigowa daga waje domin sayen sa maza ne, musamman daga ƙasashen Sanigal, da Equatorial Guinea, har ma da Central Afirka.

    Maza

    Maza suna siyar da lalle sansami wato wanda ba a daka ba, wasu kuma suna siyar da wanda aka daka ɗin domin gudanar da kasuwanci. Har ma suna saffararsu zuwa garuruwa.

    Mata

    Mata kuma suna siyar da shi dakakkensa suna kuma siyar da kwaɓɓaɓe ga masu amfani da shi ta sigar yin ado wato ƙunshi.

    Lalle a matsayin alama

    • Ana yin lalle matsayin malama a al’adar malam Bahaushe.
    • Mafi akasari matan aure sun fi yin lalle a amma ‘yan mata da yara ma ana yi musu lokacin bukukkuwa ko wani abu.

    Matsalolin lalle

    Lalle yana da matsaloli da dama ta wasu fuskokin.

    Janyo hankali

    Lalle yana janyo hankalin maza akan mace yayin da yi shi ta kuma bayyana shi a idon duniya. Shi ya sa sau tari matan aure suke sanya safa idan suka yi shi.

    Zargi

    Sau tari idan mace ta yi lalle irin na al’adun baya wanda ake kira da dungulmi, mutane kan zargi cewa ta yi ne saboda namen wani abu.

    Lalata ƙafa

    Lalle yana lallata ƙafar mata sosai, musamman yanzu da yawanci ake amfani da fetur wajan ƙwaɓinsa mata kan koka kan yadda yake sanya musu kaushi da faso. Haka kuma ko da babu fetur yawan yin lalle akai akai yana sa ƙafa ta yi kaushi ta yi faso.

    Manazarta

    Dokaji, R. S. (2022, August 26). Ko na samu aiki ba zan bar sana’ar lalle ba. Aminiya.

    Mustapha, O. (2018, May 26). Amfanin lalle a fatar jiki. Aminiya.

    Tijjani, B. (2022, December 30). Amfanin lalle wajen gyaran fata. Leadership Hausa.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 25 July, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×