Littafin Malam Zalimu rubutacen wasan kwaikwayo ne wanda yake ɗauke da labari mai cike da darussa na rayuwa, inda aka nuna halayyar wani malami mai suna Malam Zalimu, wanda yake amfani da matsayinsa na malami ya shiga rigar addini ya fake da guzuma yana harbin karsana domin cimma mummunar manufarsa.
Da wannan dama yake amfani yana zaluntar waɗanda suke ƙasa da shi. An bayyana yadda yake amfani da darajar da jama’a suke bashi tamkar hanyar ci da buguzum domin turasasa mabiyansa su yi masa biyayya tare da tsoratarwa.
Labarin ya jawo hankalin masu karatu akan illar zalunci, da yadda zalunci ke janyo bala’i ga mai aikata shi da kuma al’umma baki ɗaya.
A gefe guda kuma, littafin ya nuna yadda waɗanda aka zalunta suke ƙoƙari su tsira, tare da nuna muhimmancin adalci, gaskiya, da tsoron Allah.
Muhimmin jigo
Muhimmin jigo a labarin shi ne zalunci da kuma cikin amana. Labarin ya nuna yadda Malam Zalimu ya yi amfani da matsayinsa na malami wajen cutar da jama’a. Wanda ya kasance babban abin kaico. Domin ko Addini ya gargaɗi masu riƙe da muƙami ko ilimi da kada su ci amanar waɗanda suke jagoranta. Bayan zalunci kuma akwai,
- Bin malamai
- Tsananin kishi
- Rashin ilmi
Su ma wasu matakai ne da suka taka rawa sosai a tafiyar babban jigon labarin.
Ƙananun jigo
Duk da cewa littafin ya mallaki manyan jigogi masu armashi da kuma tsuma zuciyar mai karatu. Amma kuma hakan bai hana shi mallakar ƙananun jigogi ba. Waɗanda suka kasance sun taimaka wa tafiyar manyan har labarin ya cimma manufar da yake son cimmawa. Ƙananun jigogin da suke cikin labarin sun haɗar da:
- Rashin haƙuri
- Rashin girmama miji
- Tasirin zugar ƙawaye
- Yaudara
- Ha’inci da kuma
- Handama da babakere
Bayanin littafin a taƙaice
- Marubuci: Ado Ahmad Gidan Dabino.
- Shekarar wallafa: 2009
- Shafukan bugun farko: 73
- An sabunta bugu a shekarun: 2010, 2011, 2012, 2013, 2014, 2015, 2016, 2017, 2018, 2019, 2020, 2021, 2022, 2023.
- Adadin shafukan sabon bugu: 60
- Lambar ISBN: 978-2149-41-5
- Kamfanin ɗab’i: Gidan Dabino Publishers, Suit IC, 123 Mangwarori Street by City Ice, Sabon Titi Sani Mainagge, Kano-Najeriya.
Tarihin mawallafin a takaice
Ado Ahmad Gidan Dabino, ɗaya ne daga cikin fitattun marubutan Hausa. Waɗanda suka ga jiya suka ga yau kuma ake damawa da su har yanzu. An haife shi a shekarar 1964 a Kano, Najeriya.
Ado Ahmad Gidan Dabino ya taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa adabin Hausa da kuma fito da jigogin da suka shafi soyayya, aure, da kuma al’adun Hausawa.
- Baya ga rubutu, mawallafi ne kuma jarumi a masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood).
- Shi ne tsohon shugubar ƙungiyar marubuta ta ƙasa ANA reshen jihar Kano.
- Shi ne tsohon shugaban haɗɗaɗiyar ƙungiyar masana’antar shirya fina-finai ta MOPPAN.
- Shi ne shugaban kamfanin Gidan Dabino Publishers, kamfanin da ke wallafa littattafan Hausa.
Ra’ayoyin masu karatu
-
Hafsat Mai hula
”Na karanta Malam Zalimu, na fahimci littafin na ƙunshe da yadda malamai suke gudanar da mugunta a tsakaninsu ta hanyar malunta tare da nuna fin ƙarfi akan waɗanda suke ƙasa da su. Na kuma fahimci yadda ake gudanar da rayuwar kishi tare da rashin ilmi wajan gudanar da shi har ta kai an kaucewa ubangiji domin azabtar da kishi. Daga cikin abin da na koya a littafin Malam Zalimu akwai: Illar zalunci ga wanda ake jagoranta. Illar ha’inci da kuma yaudara tare da tasirin rashin ilmi da kuma illar bin malamai.”
-
Gaziyya
“Na ɗauki darasi daga littafin Malam Zalimu: Wannan littafin na Malam Zalimu yana nuna mana zalunci babu kyau, kuma idan kana yinsa za ka samu daidai da kai. A koyaushe mutum ya riƙe Allah shi kaɗai ba waninsa ba, saboda ko misali idan aka ɗauka akan shi Malam Zalimu da Laminde da kishiyarta za mu ga ita da ta dogara ga Allah ai ta zauna lafiya saɓanin Saude da ta ƙare Talatarta a Laraba a ɗakin malam Zalimu. Ba don malam Nafi’u ba da ta ƙarar da gishirinta a dahuwar ƙaho.”
-
Aisar
“Ban taɓa karanta littafin wasan kwaikwayon da aka gudanar da tsantsar zalunci kamar wannan littafi na Malam Zalimu ba, marubucin ya yi ƙoƙari matuƙa da gaske ya kuma samar da mafitar da ta dace a ƙarshen labarin domin Hausawa sun ce ƙarshen alawa ƙasa. Kuma ramin ƙarya kurrare ne. Haka kuma duk abin da ka shuka shi za ka girba. Wani abu mai armashi shi ne yadda aka nuna ƙarfin tasirin addu’a a lokacin da aljanin da Saude ta sa Malam Zalimu ya turawa Laminde ya gaza yin tasiri saboda tana ibada. Allah Ya sakawa marubucin da alheri.”
Manazarta
Adam, R. (n.d.). Ado Ahmad Gidan Dabino MON. Tashar Hausa.
Dabino, A. a. G. (n.d.). Taskar gidan Dabino. Gidan Dabino
WorldCat.org. (n.d.) Malam Zalimu: Wasan Kwaikwayo. WorldCat.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 14 September, 2025
An kuma sabunta ta 14 September, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.