Maldives ƙasa ce mai cike da tsibirai da ke cikin Tekun India, a yankin kudancin Asiya. Tana kudu maso yammacin ƙasashen Sri Lanka da India, kuma tana daga cikin ƙasashe mafi ƙanƙanta a duniya ta fuskar girman ƙasa da yawan jama’a. Maldives ta ƙunshi tarin tsibirai masu yawa, waɗanda suka warwatsu a cikin tekun, kuma suka haɗuwa cikin tsarin da ake kira atolls. Babban birnin ƙasar shi ne Malé, wanda shi ne cibiyar siyasa, tattalin arziki, da rayuwar jama’a.
Ƙasar ta shahara ne a duniya musamman saboda kyakkyawan rairayin bakin teku, ruwa mai tsabta, da kuma wuraren yawon buɗe ido masu jan hankali. Wannan ya sa yawon buɗe ido ya zama babban ginshiƙi na tattalin arzikinta. Baya ga haka, Maldives na ɗaya daga cikin ƙasashen da duniya ke magana kansu game da sauyin yanayi, saboda tana daga cikin ƙasashen da ke cikin haɗarin nutsewa sakamakon hauhawar ruwan teku, domin yawancin ƙasarta na da ƙarancin tsayi sosai daga matakin teku.
Muhalli da yanayin ƙasa
Kamar yadda ya gabata, Maldives tana da tsibirai masu yawa, inda adadinsu ya kai 1,190, waɗanda suke taruwa cikin rukuni-rukuni na atolls guda 26. Atoll wani tsari ne na tsibirai da ke kewaye da ruwa a tsakiya, wanda yawanci ya samo asali daga coral reefs. Wannan tsarin ya sa ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin wuraren da ke da kyawawan halittun ruwa a duniya. Daga cikin waɗannan tsibirai, ƙalilan ne ake zaune a cikinsu, yayin da wasu ake amfani da su don yawon buɗe ido.
Tarihin fafuwar Maldives
Tarihin kafuwar Maldives yana da zurfin gaske wanda ya samo asali tun dubban shekaru da suka gabata, kodayake ba a da cikakken rubutaccen tarihin farko. Masana tarihi da binciken ilimin ƙasa sun nuna cewa mutanen farko da suka zauna a tsibiran Maldives sun fito ne daga yankunan kudancin India da kuma Sri Lanka. Ana danganta su da al’ummomin Dravidian waɗanda suka yi ƙaura ta hanyar teku. Wannan ƙaura ta samo asali ne saboda kasuwanci da neman sabbin wuraren zama.

Rayuwar waɗannan mutanen farko ta ta’allaka ne ga teku. Sun dogara da kamun kifi, amfani da gishirin teku, da kuma cin gajiyar sauran albarkatun ruwa. Haka kuma, tsibiran Maldives sun kasance a tsakiyar hanyoyin kasuwancin teku tsakanin Gabas da Yamma, wanda ya sa suka zama muhimmiyar mahaɗar hulɗar kasuwanci tun da. Wannan mu’amala da sauran al’ummomi ya taimaka wajen shigar al’adu daban-daban da kuma bunƙasar rayuwar zamantakewa.
Shigowar Musulunci
Shigowar Musulunci a Maldives ya kasance muhimmin juyi a tarihin ƙasar. A kusan shekara ta 1153 Miladiyya, an bayyana cewa wani malami ko ɗan kasuwa Musulmi mai suna Abu al-Barakat Yusuf al-Barbari ya taka rawa wajen juyar da sarkin Maldives zuwa addinin Musulunci. Bayan wannan lamari, sarkin ya karɓi Musulunci kuma ya umurci jama’arsa su bi sahu.
Tun daga wannan lokaci, Musulunci ya zama ginshiƙin rayuwar al’ummar Maldives. An fara aiwatar da dokokin Shari’a a harkokin zamantakewa da shari’a, kuma addinin ya shafi dukkan fannoni na rayuwa, ciki har da ilimi, al’adu, da tsarin mulki. Har zuwa yau, Maldives na daga cikin ƙasashen da ke da cikakken rinjaye na Musulmi a duniya, inda addinin Musulunci ke da muhimmin matsayi a kundin tsarin mulki.
Zamanin sarauta
Bayan karɓar Musulunci, Maldives ta shiga zamanin sarauta wanda ya ɗauki ƙarnoni da dama. Sarakuna, waɗanda ake kira Sultans, su ne ke jagorantar ƙasar, kuma mulkinsu ya haɗa al’amuran addini da na siyasa. Wannan tsarin ya samar da daidaito da haɗin kai a cikin tsibiran da suka warwatsu a teku.
A wannan lokaci, an gina cibiyoyin gwamnati da na addini, ciki har da masallatai da kotunan shari’a. Haka kuma, sarakunan Maldives sun ci gaba da hulɗa da ƙasashen waje ta hanyar kasuwanci, musamman da yankunan Larabawa, Gabashin Afirka da Kudancin Asiya. Wannan hulɗa ta ƙara bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙarfafa matsayin Maldives na muhimmiyar cibiyar kasuwanci a tekun Indiya.
Zamanin mulkin mallaka
A ƙarni na 19, Maldives ta shiga wani sabon yanayi na siyasa lokacin da ta shiga ƙarƙashin kariyar United Kingdom a shekara ta 1887. Wannan kariya ba ta zama cikakken mulkin mallaka ba ne, amma ta bai wa Birtaniya ikon kula da harkokin waje da tsaro na ƙasar.
Duk da kasancewar sarakuna suna ci gaba da mulki a cikin gida, tasirin Birtaniya ya bayyana a fannoni da dama, ciki har da siyasa da tattalin arziki. Wannan dangantaka ta taimaka wajen kare Maldives daga masu barazanar waje, amma kuma ta takaita ‘yancin ta a wasu fannoni. Wannan yanayi ya ci gaba har zuwa tsakiyar ƙarni na 20 lokacin da ƙasashen duniya suka fara neman ‘yancin kai daga mulkin mallaka.
Samun ‘yancin kai
A shekarar 1965, Maldives ta samu cikakken ‘yancin kai daga Birtaniya bayan dogon lokaci na kasancewa ƙarƙashin kariya. Wannan lamari ya kasance muhimmin mataki a tarihin ƙasar, domin ya ba ta damar tafiyar da kanta ba tare da tsoma bakin ƙasashen waje ba.

Samun ‘yancin kai ya buɗe sabon babi na cigaban siyasa da tattalin arziki. Gwamnatin Maldives ta fara ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma, gina ababen more rayuwa, da kuma bunƙasa tattalin arziki. Haka kuma, ta fara kafa dangantaka da sauran ƙasashe a matsayin cikakkiyar ƙasa mai ‘yanci.
Zama Jamhuriya
Bayan samun ‘yancin kai, a shekarar 1968 Maldives ta sauya daga tsarin sarauta zuwa jamhuriya. Wannan sauyi ya kawo ƙarshen mulkin sarakuna tare da kafa tsarin shugabancin ƙasa wanda shugaban ƙasa ke jagoranta. Shugaban ƙasa shi ne ke da ikon gudanar da harkokin gwamnati da aiwatar da manufofin ƙasa.
Sauyin zuwa jamhuriya ya ba da damar gudanar da zaɓe da kuma shiga tsarin dimokuraɗiyya. Duk da haka, siyasar Maldives ta fuskanci sauye-sauye da dama a cikin shekaru, ciki har da sauyin mulki da ƙoƙarin inganta tsarin dimokuraɗiyya. A lokaci guda, ƙasar ta samu gagarumin cigaba a ɓangaren yawon buɗe ido, wanda ya zama ginshiƙin tattalin arzikinta.
Tsarin mulki da siyasar Maldives
A yau, Maldives na da tsarin mulki na jamhuriya mai shugaban ƙasa wanda jama’a ke zaɓa ta hanyar zaɓe kai tsaye. Shugaban ƙasa yana da cikakken iko a ɓangaren zartarwa, inda yake naɗa ministoci da tsara manufofin gwamnati. Tsarin siyasar ƙasar ya haɗa da majalisar dokoki da kotuna masu zaman kansu. Kundin tsarin mulkin ƙasar yana tabbatar da muhimmancin addinin Musulunci a harkokin gwamnati da zamantakewa. Duk da ƙoƙarin inganta dimokuraɗiyya, Maldives na ci gaba da fuskantar ƙalubale kamar rikice-rikicen siyasa da sauye-sauyen mulki. Duk da haka, ƙasar na ƙoƙarin daidaita tsarin mulkinta tare da bunƙasa tattalin arziki, musamman ta hanyar yawon buɗe ido da kuma kula da muhalli.
Tsarin shari’a
Tsarin shari’ar Maldives ya haɗa da dokokin ƙasa na kundin tsarin mulki, da kuma dokokin Musulunci wato shari’a. Addinin Musulunci yana da muhimmiyar rawa sosai a tsarin dokokin ƙasar, kuma kundin tsarin mulki ya tanadi cewar dole ne shugaban ƙasa ya zama Musulmi, har ila yau, duk ɗan ƙasar dole ne ya kasance Musulmi.
Al’umma da harshen Maldives
Al’ummar Maldives na daga cikin ƙananan al’ummomi a duniya ta fuskar yawan jama’a, inda ake ƙiyasta su kusan rabin miliyan. Duk da wannan ƙarancin, akwai ƙarfi da haɗin kai a tsakanin jama’ar, wanda ya samo asali daga tarayyar addini, harshe, da al’adu. Jama’ar ƙasar sun fi zama a warwatse cikin tsibirai masu yawa, amma duk da haka suna da haɗin kai mai ƙarfi ta fuskar asali da ɗabi’u.
Wannan haɗin kai ya samo asali ne daga tarihinsu na zama a matsayin al’umma mai tsari ɗaya, inda babu manyan bambance-bambancen ƙabilanci ko harshe kamar yadda ake samu a wasu ƙasashe. Wannan ya sa aka fi samun daidaito a zamantakewa da fahimtar juna, wanda ke taimaka wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Harshen mutanen Maldives
Babban harshen ƙasar shi ne Dhivehi, wanda shi ne harshen hukuma kuma ginshiƙin sadarwa tsakanin jama’a. Dhivehi harshe ne mai dogon tarihi wanda ya samo asali daga tsoffin harsunan Indo-Aryan na yankin Kudancin Asiya, musamman dangantaka da harshen Sinhala na Sri Lanka. Harshe ne da ke da tsarin rubutunsa na musamman wanda ake kira Thaana, wanda ya bambanta da yawancin rubuce-rubucen yankin.
A lokaci guda kuma, harshen Turanci yana da muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum, musamman a fannoni kamar ilimi, kasuwanci, gwamnati, da yawon buɗe ido. Saboda buɗewar ƙasar ga duniya, yawancin matasa da masu aiki a fannin yawon buɗe ido suna iya Turanci sosai, wanda ke taimaka wa hulɗa da baƙi daga ƙasashe daban-daban.
Rayuwar tsibirai
Yanayin ƙasar na kasancewa tsibirai masu yawa ya yi tasiri sosai a rayuwar jama’a. Mutanen Maldives suna rayuwa ne a cikin ƙananan al’ummomi a tsibirai daban-daban, inda kowanne tsibiri ke da tsarin zamantakewarsa da kuma rayuwar yau da kullum. Rayuwa a tsibirai na buƙatar juriya da dogaro da kai, domin albarkatun ƙasa ba su da yawa. Saboda haka, jama’a sun fi karkata ga ayyukan da suka danganci teku kamar kamun kifi, wanda ya kasance tsohuwar sana’a tun ƙarnoni da suka wuce. Haka kuma, kasuwanci da yawon buɗe ido sun zama muhimman hanyoyin samun kuɗaɗe, musamman a wannan zamani. Wannan tsarin rayuwa ya sa jama’a suke da alaƙa ta kusa da juna, kuma suna taimakon juna a harkokin yau da kullum.
Addini
Addinin Musulunci shi ne ginshiƙin rayuwar al’ummar Maldives. Ƙasar tana bin tafarkin Ahlus-Sunnah, kuma Musulunci shi ne kaɗai addinin da kundin tsarin mulki ya amince da shi ga ‘yan ƙasa. Wannan yana nufin cewa dole ne duk ɗan ƙasar ya kasance Musulmi, kuma wannan doka ta bambanta Maldives da yawancin ƙasashen duniya.
Addini yana taka muhimmiyar rawa a dukkan fannoni na rayuwa, daga tsarin doka zuwa zamantakewa. Ana amfani da shari’ar Musulunci a wasu fannoni na dokoki, musamman waɗanda suka shafi iyali da zamantakewa. Haka kuma, ibada kamar salla, azumi, da sauran ayyukan addini suna da muhimmanci a rayuwar yau da kullum. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da ɗabi’a, ladabi, da mutunci a cikin al’umma.

Addinin Musulunci yana da tasiri mai zurfi a rayuwar mutanen Maldives. Yana taimakawa wajen gina tarbiyya mai kyau, ƙarfafa ladabi da mutunci, da kuma tsara yadda jama’a ke hulɗa da juna. Haka kuma, addini yana ƙarfafa haɗin kai tsakanin jama’a, domin suna da manufa ɗaya da kuma ƙa’idoji iri ɗaya da suke bi. Wannan ya sa al’umma ke kasancewa mai zaman lafiya da haɗin kai, duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a wasu fannoni.
Al’adun Maldives
Al’adun Maldives sun samo asali ne daga haɗuwar al’adu daban-daban, musamman na yankunan India, Sri Lanka, da kuma tasirin Larabawa bayan shigowar Musulunci. Wannan haɗuwar ta haifar da al’adu masu bambanci da ke nuna asalin ƙasar a matsayin mahaɗar hanyoyin kasuwanci na teku. Al’adun sun haɗa da harshe, kiɗa, rawa, da kuma tsarin zamantakewa. Haka kuma, akwai tasirin addini mai ƙarfi a cikin al’adu, wanda ya sa yawancin al’adun suke tafiya daidai da koyarwar Musulunci.
A fannin nishaɗi da al’adu, mutanen Maldives suna da sanannun kaɗe-kaɗe na gargajiya da ake kira Bodu Beru. Wannan salon kiɗa yana amfani da ganguna masu ƙarfi tare da waƙoƙi da rawa, kuma yana taka muhimmiyar rawa a bukukuwa da tarurruka. Wannan kiɗa yana nuna tasirin Afirka da Larabawa, wanda ya samo asali daga hulɗar kasuwanci ta tarihi. Bodu Beru ba kawai nishaɗi ba ne, har ma yana zama hanyar bayyana al’adu da tarihin al’umma
Abinci
Abincin mutanen Maldives ya fi karkata ne ga abincin teku, musamman kifi, wanda shi ne ginshiƙin abinci a ƙasar. Ana haɗa kifin da shinkafa, kwakwa, da kayan marmari don samar da abinci mai gina jiki. Saboda kasancewar ƙasar tsibirai, noma ba ya da yawa, don haka ana shigo da wasu kayan abinci daga ƙasashen waje. Duk da haka, jama’a sun haɓaka hanyoyin girke-girke na musamman da suka dace da albarkatun da suke da su.
Bukukuwa
Bukukuwan addini suna da muhimmanci a rayuwar mutanen Maldives, musamman bukukuwan Musulunci kamar bikin salla ƙarama da babba. A waɗannan lokuta, jama’a suna gudanar da ibada, ziyara, da kuma raba abinci tare da dangi da abokai. Haka kuma, ana gudanar da bukukuwan aure, haihuwa, da sauran al’amuran zamantakewa cikin farinciki da al’adun gargajiya. Waɗannan bukukuwa suna ƙarfafa zumunci da haɗin kai a cikin al’umma.
Tattalin arzikin Maldives
Tattalin arzikin Maldives ya dogara ne sosai kan albarkatun da take da su, musamman waɗanda suka shafi teku da kuma kyawawan yanayin ƙasar. Duk da ƙarancin albarkatun ƙasa, ta samu cigaba ta hanyoyi na musamman da suka haɗa da:
Yawon buɗe ido
Yawon buɗe ido shi ne babban ginshiƙin tattalin arzikin Maldives. Wanda dubban baƙi daga sassa daban-daban na duniya suke zuwa kowace shekara domin hutu a kan tsibirai masu kyau, yin ninkaya da kallon halittun ruwa da kuma jin daɗin rairayin bakin teku da ruwa mai tsafta. Wannan ɓangaren kuma yana samar da kuɗaɗen shiga mafi yawa ga gwamnati tare da ayyukan yi ga jama’a da dama.
- Kamun kifi: Kamun kifi shi ne na biyu daga cikin tattalin arzikin ƙasar. Kifi, musamman tuna, yana daga cikin manyan abubuwan da ake fitarwa waje kasantuwar yawancin jama’a a tsibirai sun dogara ne da wannan sana’a.
- Shigo da kaya: Saboda ƙarancin albarkatun ƙasa, Maldives tana shigo da yawancin kayan amfani daga ƙasashen waje da suka haɗa da abinci, man fetur, da kuma kayayyakin gini.
Ƙalubale da matsalolin Maldives
Duk da cigaban da Maldives ta samu a fannoni daban-daban, ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale da matsaloli da ke shafar cigabanta na dogon lokaci. Waɗannan matsaloli sun haɗa da na muhalli, tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa, waɗanda ke buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati da kuma haɗin gwiwar ƙasashen duniya.
Barazanar sauyin yanayi
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Maldives ke fuskanta shi ne tasirin sauyin yanayi. Kasancewar ƙasar na daga cikin mafi ƙankanta a tsayin ƙasa a duniya, tana cikin haɗarin nutsewa sakamakon hauhawar ruwan teku. Wannan lamari yana barazana ga rayuwar jama’a, gidaje, da kuma ababen more rayuwa. Bugu da ƙari, sauyin yanayi yana haifar da lalacewar coral reefs, wanda ke da muhimmanci ga kariyar bakin teku da kuma samar da rayuwar halittun ruwa. Idan aka ci gaba da wannan yanayi, zai iya jawo raguwar yawon buɗe ido da kuma kamun kifi, wanda zai yi tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin ƙasar.
Dogaro da fanni ɗaya na tattalin arziki
Tattalin arzikin Maldives ya fi karkata ne ga yawon buɗe ido, wanda ke samar da kaso mai yawa na kuɗaɗen shiga. Duk da amfaninsa, wannan dogaro ya zama barazana idan aka samu matsala a wannan fanni. Misali, rikice-rikicen duniya, annoba, ko matsalolin tsaro na iya rage yawan masu yawon buɗe ido, wanda hakan zai haifar da tangarda ga tattalin arzikin ƙasar. Haka kuma, saboda ƙarancin albarkatun ƙasa, Maldives tana shigo da yawancin kayayyaki daga waje. Wannan ya sa tattalin arzikinta ke fuskantar matsin lamba daga canjin farashin kaya a kasuwannin duniya.
Matsalolin muhalli
Baya ga sauyin yanayi, Maldives na fuskantar matsaloli na muhalli kamar gurɓatar ruwa da taruwar shara, musamman robobi. Saboda ƙarancin ƙasa da kuma yawan masu yawon buɗe ido, sarrafa shara ya zama ƙalubale mai girma. Haka kuma, gine-gine da bunƙasar yawon buɗe ido na iya lalata muhallin halittun ruwa, musamman coral reefs. Wannan yana barazana ga daidaiton tsarin halittu da kuma rayuwar dabbobin ruwa.
Ƙalubalen siyasa
A fannin siyasa, Maldives ta sha fuskantar rikice-rikice da sauye-sauyen mulki. Duk da kasancewarta jamhuriya mai bin tsarin dimokuraɗiyya, ana samun rashin jituwa tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma sauye-sauyen shugabanci da ke haifar da rashin daidaito.Wannan yanayi na iya rage yawan zuba jari daga waje da kuma jinkirta aiwatar da muhimman manufofi na cigaba. Haka kuma, yana iya shafar yadda duniya ke kallon ƙasar a matsayin abokiyar hulɗa mai aminci.
Matsalolin rarrabuwar jama’a
Kasancewar jama’ar Maldives suna zaune a tsibirai da suka warwatsu, yana kawo ƙalubale wajen samar da ayyukan gwamnati kamar ilimi, lafiya, da sufuri. Isar da waɗannan ayyuka zuwa dukkan tsibirai na buƙatar kuɗi da tsari mai kyau. Haka kuma, wasu ƙananan tsibirai na fama da ƙarancin ababen more rayuwa, wanda ke haifar da bambanci tsakanin rayuwar jama’a a manyan tsibirai da ƙananan tsibirai.
Matsalolin samar da ruwa da abinci
Maldives na fama da ƙarancin ruwa mai tsafta, domin yawancin ruwan da ake samu daga ruwan sama ne ko kuma a tace ruwan teku. Wannan yana buƙatar fasaha da kuɗi mai yawa. A ɓangaren abinci, ƙasar na dogaro sosai da shigo da kayan abinci daga waje. Duk wata tangarda a harkokin sufuri ko kasuwanci na duniya na iya haifar da ƙarancin abinci ko tashin farashi, wanda hakan zai shafi rayuwar jama’a.
Matsalolin tsaro da garkuwa da ƙasa
Saboda kasancewarta ƙasar mai tsibirai da yawa a warwatse, Maldives na fuskantar ƙalubale wajen kula da tsaro da iyakokinta na teku. Wannan yana buƙatar haɗin gwiwa da sauran ƙasashe domin tabbatar da tsaro, musamman daga barazanar safarar miyagun ƙwayoyi ko sauran laifuffuka na teku.
Muhimmancin Maldives a duniya
Duk da cewa Maldives ƙasa ce mai ƙarancin girma da ƙarancin yawan jama’a, tana da matsayi mai muhimmanci a idon duniya ta fannoni da dama. Wannan muhimmanci ya samo asali ne daga yanayinta na musamman a matsayin ƙasa mai tsibirai a tsakiyar Tekun Indiya, wanda hakan ya ba ta damar taka rawa a fannoni kamar tattalin arziki, muhalli, da hulɗar ƙasashen duniya.

A fannin yawon buɗe ido, Maldives ta zama ɗaya daga cikin fitattun wurare da ake ziyarta a duniya. Kyakkyawan rairayin bakin teku mai farin yashi, ruwa mai haske, da tsibirai masu zaman kansu sun sa ta zama abin jan hankali ga masu yawon shakatawa daga sassa daban-daban na duniya. Wannan ya sa ƙasar ta zama wata muhimmiyar cibiyar yawon buɗe ido, inda manyan otal-otal da wuraren hutu ke samar da ayyukan yi da kuma kuɗaɗen shiga ga gwamnati. Saboda haka, yawon buɗe ido ya zama ginshiƙin tattalin arzikinta, wanda ya taimaka wajen bunƙasa sunanta a matakin duniya.
Rawar da take takawa a sauyin yanayi
Maldives ta zama wata muhimmiyar murya a duniya wajen batun sauyin yanayi, musamman saboda raunin da take da shi ga tasirin wannan matsala. Kasancewar ƙasar na daga cikin ƙasashen da ke da ƙasa mafi ƙanƙanta a tsayi a duniya, tana fuskantar barazanar nutsewa sakamakon hauhawar ruwan teku, wanda ke da alaƙa da sauyin yanayi.
Shugabannin ƙasar sun yi amfani da wannan yanayi wajen jan hankalin duniya kan muhimmancin ɗaukar matakai na gaggawa. Musamman, tsohon shugaban ƙasar Mohamed Nasheed ya yi fice wajen wayar da kan duniya, har ma ya gudanar da wani taron majalisar ministoci a ƙarƙashin ruwa domin nuna irin haɗarin da ƙasar ke fuskanta. Wannan ya sa Maldives ta zama wata alama ta ƙasashen da ke cikin haɗarin sauyin yanayi, kuma ta taka rawa wajen ƙarfafa tattaunawa a matakin duniya kan kare muhalli.
Hulɗa da ƙasashen duniya
A fannin hulɗar ƙasashen duniya, Maldives na taka rawa mai muhimmanci duk da ƙarancin ƙarfinta. Tana da dangantaka da ƙasashe da dama a fannonin kasuwanci, taimakon cigaba, da kuma kare muhalli. Haka kuma, ƙasar tana cikin manyan ƙungiyoyin duniya kamar Majalisar Dinkin Duniya, inda take da damar bayyana ra’ayoyinta da kuma kare muradanta a matakin ƙasa da ƙasa.
Bugu da ƙari, Maldives tana cikin ƙungiyoyin yankin Asiya waɗanda ke taimaka mata wajen haɓaka tattalin arziki da tsaro. Ta hanyar wannan hulɗa, ƙasar na samun tallafi da haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, musamman wajen bunƙasa ababen more rayuwa da kare muhalli.
Muhimmancin albarkatun ruwa
Saboda kasancewarta ƙasa mai yalwar teku, Maldives na da muhimmanci a fannin albarkatun ruwa, musamman kamun kifi. Kifi yana daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma samar da abinci ga jama’a. Haka kuma, ana fitar da kifaye zuwa ƙasashen waje, wanda ke ƙara wa tattalin arzikin ƙasar ƙarfi.

Bugu da ƙari, ruwan tekun Maldives na ɗauke da dimbin halittu na ruwa iri-iri, waɗanda ke da muhimmanci ga tsarin halittu na duniya. Wannan ya sa ƙasar ke da rawar da za ta taka wajen kare muhalli da albarkatun teku, musamman a lokacin da duniya ke fuskantar barazanar lalacewar muhalli.
Jerin shugabannin Maldives daga 1968-2026
- Ibrahim Nasir (1968 – 1978): Shi ne shugaban ƙasa na farko bayan an rushe tsarin sarauta, ya taka rawar gani wajen samun ƴancin kai a 1965 kafin zama shugaban ƙasa.
- Maumoon Abdul Gayoom (1978 – 2008): Ya yi mulki na tsawon shekaru 30. Ya kuma bunƙasa yawon buɗe ido da tattalin arziki, sai dai an yi suka kan tsawon lokacin da mulkinsa ya ɗauka na rashin cikakken tsarin dimokuraɗiyya.
- Mohamed Nasheed (2008 – 2012): Shi ne shugaban farko da aka zaɓa ta hanyar cikakken zaɓe na dimokuraɗiyya, ya shahara wajen magana kan gurɓacewar yanayi, ya kuma sauka daga mulki bayan rikicin siyasa.
- Mohamed Waheed Hassan (2012 – 2013): Ya karɓi mulki bayan murabus ɗin Mohamed Nasheed, inda ya kammala wa’adin gwamnatin.
- Abdullah Yameen (2013 – 2018): Ya mayar da hankali kan ci gaban ababen more rayuwa, sai dai an soke kan tsauraran matakan siyasa.
- Ibrahim Mohamed Solih (2018 – 2023): Shi ne shugaban da ya inganta dangantaka tsakanin Maldives da ƙasashen duniya, sannan kuma ya ƙarfafa dimokuraɗiyya
- Mohamed Muizzu (2023 – zuwa yanzu): Shi ne shugaban ƙasa mai mulki a halin yanzu, ya zo da sababbin manufofi a siyasa da tattalin arziki.
Manazarta
Heger, M., Atas, E., & Forsch, S. (2025, May 22). Thriving in a Warming World: How Maldives can Adapt to Climate Change. World Bank.
Center for South Asian and Middle Eastern Studies. (n.d.) Maldives | Center for South Asian and Middle Eastern Studies | Illinois.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.