Sana’a ita ce babbar hanyar dogaro da kai a kowace irin al’umma da ke tinƙahon samar da ci gaba a cikin al’ummarta. Hausawa sun daɗe da samar wa kansu hanyoyin da za su ci gaba a cikin rayuwarsu musamman wajen samar wa kansu abubuwan buƙatun yau da kullum.
Sana’a tana nufin duk wata hanya da mutum zai yi amfani da ita wajen samar wa kansa abubuwan more rayuwa domin biyan wasu buƙatunsa. Wannan ya haɗa da sarrafa wasu abubuwa waɗanda ake amfani da su ko musayar wani abu da wani abu ko saye da sayarwa da dai sauransu. Gano haƙikanin asalin sana’a abu ne mai wuya, sai dai ana hasashen cewar ta samo asali ne daga buƙatocin al’umma a muhallin da suka samu kansu, wannan shi ya haifar da yawaitar sana’o’in, domin kowace al’umma da irin nata buƙata. Haka sana’o’in an kasa su zuwa gida uku a wani ƙaulin kamar na maza da mata da kuma na tarayya.
Ma’anar sana’a
Ita dai kalmar sana’a kalma ce ta Larabci. A Larabce kuwa kalmar na nufin aiki. Daga baya Bahaushe ya ari kalmar tare da ma’anarta daga Larabci. Bayan tafiya ta yi tafiya sai ma’anar kalmar a wurin Bahaushe ta ƙara faɗaɗa har ta ƙunshi duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani abu da za a musanya a tsakanin ɗaiɗaikun al’umma ko rukunin jama’a.
Maigandi (2014:242) ya ce: “Kalmar sana’a kalma ce wadda ake hasashen asalinta daga harshen Larabci ne. Kalmar a harshen Larabci /swana’atu/ ce, sai Bahaushe ya yi mata kwaskwarima don ta dace da yadda yake faɗa. Babban dalili shi ne, a Hausa babu harafin /swa/ sai ya mayar da ita /sinun/. Haka kuma aka shafe harafin /tu/ sai aka Hausance kalmar ta zama sana’a.”

Masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar sana’a. Yahaya da wasu (1987:48) sun bayyana sana’a da cewa: “Hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka don buƙatun yau da kullum.” Don haka, ke nan sana’a wata aba ce wadda mutum ya jiɓanci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harakokin rayuwa.
A ra’ayin Garba (1991:11) cewa ya yi “Sana’a ita ce ginshiƙin rayuwa da tattalin arzikin yau da kullum na Hausawa. Sannan kuma tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da ake gane martabar mutum da ƙasaitarsa da matsayinsa a cikin al’umma. Wannan yana nuna sana’a tamkar wani madubi ne da za a kalla a iya gane matsayin mutum a cikin al’ummar Hausawa.”
Sharifai (1990:11) ra’ayinsa ya karkata ne ga ma’anar sana’a dangane da sana’o’in gado na gargajiya na Bahaushe. Domin cewa ya yi: “sana’a tana nufi wata hanya da mutum yake bi don nema ko samun abinci, abinci yana zuwa ta hanyar kuɗi ko wani abin da rayuwa za ta dogara a kai. Kuma wannan hanya ta zama wadda aka gada ce tun iyaye da kakanni ba wata baƙuwar al’umma ce ta kawo ta ba.”
Fauziya (2013:206) ta hakaito daga Madabo (1979:27) yana cewa, Sana’a daɗaɗɗiyar al’ada ce da ta nuna Hausawa a idon duniya ta kuma bunƙasa ƙasar Hausa ta yadda baƙi suke zaune cikin jin daɗi sakamakon sana’o’i daban-daban. Wannan ya nuna sana’a hanya ce ta ciyar da al’umma na kusa da na nesa, tare da biyan buƙatun yau da kullum a dukkan sha’anoni na rayuwa bisa tsari.
A fahimtar Yahaya, I.Y, da Gusau, S.M. da Yar aduwa, T.M (2001:48) sun tattaro abubuwa masu yawa da suka jiɓanci sana’a. Sun bayyana cewa: “Sana’a wata aba ce wadda mutum ya jiɓanci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Aba ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da sarrafa hanyoyin kimiya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan Adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu.”
A cikin The New Age Encyclopedia (1980:423) an bayyana cewa: sana’a ta ƙunshi duk wani aiki da mutum ke aiwatarwa wanda ya ƙunshi saye da sayarwa domin samun abin buƙata. Haka a ƙamusun Hausa na CNHN (2006:186) an bayyana sana’a ko sana’o’i da cewa: Aikin da mutum yake yi don samun abinci, misali manomi sana’arsa noma, wanzami kuwa sana’arsa aski ne.
Daga ƙarshe Wushishi (2011:26) yana da ra’ayin cewa: Sana’a hanya ce ta samun aiki na dogaro da kai don tanadar abubuwan biyan buƙatu da neman rufin asiri kan harkokin rayuwa da kuma sarrafa albarkatu ta hanyar kimiya da fasaha da karkatar da su wajen saye da sayarwa da musayar kaya don mallakar abin da ba a iya samar wa kai.
Bisa ga la’akari da waɗannan misalai na ma’anonin sana’a da ke sama, idan aka yi nazarin waɗannan ra’ayoyi na masana za a fahimci cewa, kusan duk bori guda suke yi wa tsafi, domin kuwa kusan duk manufarsu ɗaya dangane da ma’anar sana’a. Bisa ga wannan, ana iya cewa, sana’a wata aba ce da mutum ke aiwatarwa da nufin samun abin masarufi domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum da kariyar mutunci a cikin al’umma. Idan kuwa haka ne, ba shakka sana’a ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma baki ɗaya.
Tarihin samuwar sana’o’in gargajiyar Bahaushe
Masana irin su Garba (1991) da Rimmer da wasu (1948) suna hasashen cewa, buƙatu da wurin rayuwar ɗan Adam su ne ƙashin bayan ginuwar sana’o’insa domin samun sauƙin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum. Don haka, bayan mutum ya samu lafiya, babbar buƙatarsa ta abinci ita ta haifar da sana’ar noma. Haka buƙatar noma ta haifar da samuwar kayan aikin gona wanda daga nan sai ta haifar da sana’ar ƙira da sassaƙa. Haka buƙatar sutura ta haifar da sana’ar saƙa, buƙatar muhalli ta haifar da sana’ar gini. Haka abin ya ci gaba da wanzuwa ta yadda yawan buƙatocin ɗan Adam na ƙaruwa yawan sana’o’insa na ƙaruwa har ya zuwa wannan lokaci a yau. Ta wannan hanya ce aka samu yawaitar sana’o’in gargajiya na Hausawa ta yadda kowa ya ɗauki wata sana’a da ya ga ta fi dacewa da shi domin bayar da tasa gudummawa a cikin al’umma.
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da asalin sana’a. Daga cikinsu akwai Rimmer (1948) da Garba (1991) da Madabo (1970 da 2007) da Umar (1985) da sauransu.
Ga misali Maigandi (2014:245) ya rawaito Alhassan da wasu (1982:32) suna da ra’ayin cewa: kasancewar noma wata daɗaɗɗiyar al’ada ga ɗan Adam saboda abinci, kuma bisa la’akari da karin maganar: Noma na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, ba bu sana’ar da ta riga shi. Wannan ra’ayin na da hasashen cewar sana’ar noma ita ce farko daga cikin sana’o’in Hausawa na gargajiya. A wani ƙaulin, an bayyana cewa, a baya, mutum ya kasance mayawaci ne a cikin daji daga wannan daji zuwa wancan domin neman abinci. A lokacin wannan yawace-yawacen ne yake farauto namun daji da ‘ya’yan itatuwa a matsayin abin masarufi. Wannan hasashen na ganin cewa, sana’ar farauta ita ce sana’ar farko ga ɗan Adam. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da ganin cewa, dabbobi da ‘ya’yan itatuwa da ake amfani da su a matsayin cimaka, ai farautarsu aka yi.
Daga nan aka fara amfani da fatar dabbobi a matsayin muhalli da suturar jiki. Da tafiya ta yi tafiya, har suka sami dabarar samun wuta ta amfani da duwatsu da busasshiyar ciyawa, daga baya sai mutum ya gane amfanin zama wuri ɗaya ya yi noma. Wannan sana’ar ta noma ta haifar da samuwar ƙira domin samar da kayan aikin gona, bayan amfani da itace da duwatsu a matsayin kayan aikin gona kafin samuwar ƙarfe.
Akwai hasashen cewa, sana’ar da ta riga kowace sana’a a duniya ita ce sana’ar sassaƙa, dalili kuwa shi ne, kamar yadda bayani ya gabata cewa, ɗan Adam ya fara farauta domin neman abinci; to ita ko wannan farautar kafin ya yi ta sai da ya tanadi abin yin farautar, watau sarrafa itace a matsayin makamin da zai yi amfani da shi wurin aiwatar da farautar. Idan kuwa haka batun yake, ba shakka sana’ar sassaƙa itace farko ga ɗan Adam. Wannan hasashen zai ƙara ƙarfafuwa idan aka yi waiwaye a kan tarihin annabi Adam (AS) mutum na farko a doron ƙasa wanda tarihi ya tabbatar da cewa, ya yi amfani da sanda wadda yake amfani da ita wajen tafiya kafin bayyanar Ibilis a wajensa.
Rabe-raben sana’o’in Hausawa
Sana’o’i sun kasu kashi-kashi gwargwadon buƙatun al’ummar Hausawa, don haka masana sun yi ƙoƙarin karkasa waɗannan sana’o’i zuwa gida-gida gwargwadon fahintarsu. Ga misali Yahaya .I. da Ɗangambo (1986:173) a tasu fahimta sun kasa sana’o’in Hausawa zuwa gida uku. Sana’ar noma da sana’ar sarrafa wani abu domin samun wani abu, misali kamar ƙira da saƙa da sauransu, sai sana’ar jari da ƙwarewa wanda ya shafi gini da kasuwanci da sauransu.
Ana iya ƙarƙasa sana’o’i daki-daki kamar haka:
- Sana’o’in yawaita: Akwai sana’o’in yawaitarwa inda akan fara da abu kaɗan a samu mai yawa. Sana’o’in da ke wannan rukuni sun haɗa da noma na damina da na rani, da kiwo.
- Sana’o’in sayarwa: Akwai sana’o’in sayarwa inda ake samar da wasu abubuwan da suke buƙata su musanya da kuɗi, misali talla, da fatauci da baranda.
- Sana’o’in aiwatarwa: Akwai sana’o’in aiwatarwa inda ake sarrafa wasu abubuwa kamar ma’adinai a mai da su kayan amfani, watau misali sana’ar ƙira da saƙa da sassaƙa da dukanci da rini da jima.
- Sana’o’in biɗa: Akwai kuma sana’o’in biɗa waɗanda sun ƙunshi roƙo da aikatau da ƙwadago irin na jinga da yammaci da safiya.
A hannu ɗaya kuwa, Yahaya (1992:4) duk da yake su ma sun kalli sana’o’in ta fuska uku, amma ga yadda suka raba sana’o’in kamar haka:
Noma, a ƙarƙashinta akwai sana’o’i kamar su ƙira da saƙa da dukanci da sauransu.
- Kasuwanci: Kaso na biyu kuwa kasuwanci, wanda ya ƙunshi fatauci da dillanci da koli da sauransu.
- Dafe-dafe: Kaso na uku kuwa ya ƙunshi dafe-dafe wanda ya ƙunshi soye-soye da gyare-gyare da gashe-gashe.
A ƙarƙashin wannan, wasu masanan sun karkasa sana’o’in ne ta fuskar jinsin masu aiwatar da ita. A bisa wannan tsarin, Fauziyya (2013:208) ta bayyana cewa: Bisa ga ƙa’idojin al’adun Hausawa, ba kowace sana’a kowa yake yi ba, a’a kowace da mai yin ta, waɗansu na mata ne, waɗansu na maza ne, waɗansu kuwa suna yi ne a tare, ma’ana kowane jinsi zai iya gudanar da ita. Bisa ga wannan kason, za a fahimci cewa, sana’o’i rukunin maza sun ƙunshi: ƙira da jima da rini da wanzanci da sassaƙa da dukanci da sauransu. Rukuni na mata kuwa sun ƙunshi kitso da sussuka da dafe-dafe (na wanda aka san matan Hausawa na yi a al’adance) da sauransu, sai na tarayya wanda ya shafi sana’o’i kamar su saƙa da dillanci da aikatau da sauransu.
Al’adun Hausawa sun yi tasiri wajen haifar da wannan kashe-kashen sana’o’in, domin a al’adar Hausawa akwai wasu sana’o’in da ake ganin ba su dace da jinsin mata ba, daga cikinsu akwai farauta da jima da sassaƙa da sauransu. Bisa ga wannan ne Sayinnawal (2015:31) yake da ra’ayin cewa: Wannan na faruwa ne saboda kowace sana’a akwai jinsin mutanen da suka fi dacewa su aiwatar da ita bisa ga kaifin fahintarsu da ƙarfin jikinsu.
Dukkan waɗannan sana’o’i, Hausawa suna gudanar da su ne domin biyan buƙatocinsu na yau da kullum.
Muhimmancin sana’o’in gargajiya
Tushen samun abin rayuwa
Sana’o’in gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen samar wa mutane abin dogaro na yau da kullum. Mutane da dama a ƙauyuka da birane suna samun kuɗin shiga ta hanyar sana’o’i irin su noma, kiwo, ɗinki, saƙa, sassaƙa, gyaran takalmi, da sauran ayyukan hannu. Waɗannan sana’o’i suna taimaka wa mutum ya samu abinci, ya biya buƙatu kamar magani, makaranta da saka jari. Tun kafin zuwan masana’antu, su ne ginshiƙan rayuwar al’umma.
Dogaro da kai
Wanda ke da sana’a ba sai ya dogara da wani ba don ya rayu. Sana’o’in gargajiya suna koya wa mutum yadda zai dogara da kansa wajen neman riba da tsira. Wannan yana rage dogaro da aikin gwamnati ko na kamfanoni. Mutum kan iya kafa nasa ƙaramin kasuwanci a gidansa, sannan ya faɗaɗa shi idan ya samu ci gaba. Wannan tsammmani kai yana ƙarfafa jarumta da buwayar zuciya.
Taskance al’adu
Sana’o’in gargajiya suna ɗauke da al’adun gargajiya, tunanin kakanni da dabarun da ake gadarwa. Ayyuka irin su ɗinkin gargajiya, ɓangarorin masaƙa, da abubuwa da ake yi a gargajiyance duk suna nuna hikima da fasahar da ake gadon tsofaffi. Idan aka kiyaye waɗannan sana’o’i, al’adu ba za su gushe ba. Sun zama hanyar adana tarihi ga ƙarnuka masu zuwa.
Bunƙasa tattalin arziki
Sana’o’in gargajiya suna taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki, musamman a ƙananan yankuna. Kayayyakin da ake samarwa kamar tukwane, tabarma, rariya, akushi, kayan sakawa da sauransu duk ana sayar da su a kasuwanni, inda suke kawo kuɗin shiga sosai. Hakan yana samar da kuɗi ga gidaje da kuma taimaka wa tattalin arzikin yankin gabaɗaya. Sau da yawa ana tallata su har zuwa wasu jihohi ko ƙasashe.
Samar da ayyuka
Sana’o’in gargajiya suna ba wa mutane da dama aikin yi. Yawancin matasa idan suka koyi sana’a suna ƙanana, suna da damar kafa tasu sana’ar ko yin aiki tare da iyayen gidansu. Idan matasa na da sana’a, hakan yana rage mugayen ayyuka, zaman banza, da dogaro da iyaye. Sana’a kuma yana iya zama hanyar fita daga talauci.
Inganta fasaha da ƙwarewa
Duk sana’a tana koyar da mutum haƙuri, hikima da ƙwarewa. Masaƙa suna koyar da daidaito da hangen nesa. Masassaƙa suna koyar da dabarun aiki da kayan aiki. Wani lokaci ana amfani da waɗannan ƙwarewa wajen magance matsaloli a rayuwar yau da kullum. Kowane ɗalibi da ya koyi sana’a yana samu ƙwarewar da zai iya amfani da ita har tsawon rayuwarsa.
Sauƙaƙa rayuwar al’umma
Sana’o’in gargajiya suna samar da abubuwan da al’umma ke amfani da su kullum ba tare da dogaro da kayayyakin waje ba. Misali, masunta suna kamo kifi, manoma suna noma abinci, masu tukwane suna samar da tukunya, maƙera suna ƙera wuƙaƙe da kayan aiki. Waɗannan suna rage farashi, sauƙaƙa rayuwa, kuma suna sa abin da ake buƙata ya kasance cikin sauƙin samu.
Haɓaka haɗin kai
Sana’o’in gargajiya galibi ana yin su ne tare da iyalai ko a ƙungiyance. Iyaye suna koyar da yara, ƙananan suna taimaka wa manya, kuma suna haɗuwa a wurare daban-daban don gudanar da ayyuka. Wannan tsarin haɗin kai yana ƙarfafa zumunci, girmama juna da taimakon kai-da-kai tsakanin al’umma. Yana sa mutane su kasance cikin jituwa da fahimtar juna.
Koyar da tarbiyya
Koyon sana’a ba kawai aiki ba ne, hanya ce da ake koyar da tarbiyya. Yaro yana koyon biyayya ga iyayen gidansa, ladabi wajen aiki, tsafta, tsoron Allah da sanin ya kamata. Yana kuma koyon muhimmancin lokaci da kula da kayan aiki. Waɗannan ɗabi’u sukan zama jagora a rayuwarsa, ko da ya girma ya shiga wani fanni daban.
Manazarta
Mustapha, H., Ahmed, M. A., & Shunom, L. I. (2025). Empowering Tradition, Enriching the Future: Reviving Hausa Traditional Hand Embroidery for Nigeria’s Economic Renaissance. Research Journal of Humanities and Cultural.
Kashim, I., Ologunwa, T. P., & Ogunlade, B. A. (2014). Sustainable Hausa Design, Culture and Usability: A Reflection on the Art of Northern Nigeria. Advances in Social Sciences Research Journal, 1(5), 51–64.
Britannica (2025, October 14). Hausa. Encyclopaedia Britannica.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
