Sassaƙa wata sana’a ce ta hannu da take da dogon tarihi a rayuwar ɗan’adam, wadda ake nufin fasahar sarrafa wasu nau’o’in kayayyaki masu ƙarfi kamar itace, dutse, ƙarfe, ƙashi da makamantansu, ta hanyar huda su, zanawa ko yankawa domin samar da wani sabon abu mai amfani ko kuma mai ƙawata muhalli. Sana’ar sassaƙa tana daga cikin tsofaffin dabarun fasaha da al’adu da ɗan’adam ya mallaka tun kafin a samu rubutu ko cigaban masana’antu.

Sana’ar sassaƙa aiki ne na hure ice da aiwatar da shi don a mayar da shi wani abin amfani kamar jirgin ruwa da kujera da kyaure da turmi da taɓarya da akushi da sauransu.
A tarihi, sassaƙa ta fara ne dalilin buƙatun rayuwa, inda mutanen farko suka riƙa hudawa ko sassaƙa itatuwa don yin kayan aiki kamar gatari, baka, kibau, turmi, taiki, da kuma kayan ado. A wasu al’adu kuwa, musamman na Afirka da Asiya, sassaƙa ta kai matsayin tallafa wa ayyukan addini da siyasa, saboda ana amfani da ita wajen yin gumaka, tutocin sarauta, da kayan biki na al’ada.

Muhimmancin sassaƙa bai tsaya ga amfanin yau da kullum kaɗai ba. A fannin al’adu da tarihi, sassaƙa ta zama hanya ta adana tarihin al’umma, domin ana sassaƙa alamomi, zane-zane da abubuwa da ke nuna yadda al’umma ta rayu a wani lokaci. Haka kuma, a fannin tattalin arziki, sana’ar ta kasance hanyar samun kuɗin shiga ga mutane da dama, musamman a ƙasashen da yawon buɗe ido ke da tasiri, inda ake sayar da kayayyakin sassaƙa a matsayin kayan tunawa na tarihi.
Bugu da ƙari, a fannin gine-gine da adon muhalli, sassaƙa ta taka rawar gani sosai. Ana amfani da sassaƙaƙƙun ƙofofi, tagogi, ginshiƙai, da kujeru a gidaje da masallatai, musamman a ƙasashen Hausawa da sauran wurare masu al’adu. Wannan ya nuna cewa sassaƙa ba wai sana’a ce kawai, ita ɗin babbar ginshiƙi ce ta rayuwar al’umma tun fil azal.
Asalin sana’ar sassaƙa
Asalin sana’ar sassaƙa ta samo tushe ne tun daga zamanin da mutane ke rayuwa a daji, lokacin da babu wata fasahar zamani. Mutanen farko sun koyi yadda za su yi amfani da abubuwan da ke kewaye da su domin sauƙaƙa rayuwa. Hakan ya haɗa da amfani da itatuwa, dutse, ƙarfe da ƙashi wajen samar da kayayyakin aiki. Mutane sun fara aiwatar da sassaƙa ta hanyar huda itatuwa domin yin kayan amfani na yau da kullum. Misali:

- Kayayyakin aiki: gatari, turmi, taiki, kujeru da kwanukan abinci.
- Kayayyakin farauta da yaƙi: baka, kibau, garkuwa da takubba.
- Kayayyakin amfanin yau da kullum: kamar akushi, abin shaƙa, ƙaho da tambarin gida.
A wasu wurare kuma, sassaƙa ta zama hanyar samar da kayayyakin bauta da ibada. Mutane sun rika yin gumaka daga itace ko dutse, suna ɗaukarsa a matsayin abin bauta ko kuma kariya daga miyagun abubuwa. Wannan ya nuna cewa tun da daɗewa, sassaƙa ta haɗu da al’adu da addinan gargajiya.
Abubuwan da aka fi amfani da su
A tarihi, akwai bambancin kayan da al’umma suka fi amfani da su wajen sassaƙa:
- Itace: shi ne mafi sauƙi, saboda yana da laushi idan aka kwatanta da dutse ko ƙarfe.
- Dutse: ana amfani da shi wajen sassaƙa gumaka, tubalan gini, ko kayan ado.
- Ƙarfe: bayan gano yadda ake sarrafa ƙarfe, an fara yin kayan aiki da makamai masu ƙarfi ta hanyar sassaƙa su.
- Ƙashi da ƙaho: wasu al’adu suna amfani da su wajen yin kayan ado da tambarin sarauta.
Matsayin sassaƙa a gargajiyance
A cikin al’ummomin da, masu bin tafarkin gargajiya, sana’ar sassaƙa ba ta tsaya ga kayan amfani ba kaɗai. Ta taka muhimmiyar rawa a fannoni kamar:
- Siyasa: sarakuna da shuwagabanni suna amfani da sassaƙen tutoci, kujerun sarauta, da tambarin mulki don nuna iko da ƙarfi.
- Addini: ana sassaƙa gumaka da abubuwa na ibada.
- Al’adu: ana yin kayan biki da kayan ado na gargajiya daga sassaƙa.
- Adana tarihi: sassaƙa ta kasance wata hanya ta rubutu kafin ƙirƙirar haruffa. Ana sassaƙa alamomi da zane-zane a dutse ko itace domin bayyana labari ko al’ada.
Nau’o’in sassaƙa
Sassaƙa ba sana’a ce guda ɗaya mai iyaka ba, akwai nau’o’i daban-daban bisa ga kayan da ake amfani da su da kuma manufar abin da ake ƙirƙira. Wannan bambanci ya nuna irin faɗin da wannan sana’a ta samu a al’adu da kuma cigaban zamani.

Sassaƙar itace
Wannan shi ne mafi shahara kuma mafi sauƙi, saboda itace yana da laushi idan aka kwatanta da dutse ko ƙarfe. Ana yin kujeru, tebur, turmi, taiki, ƙofofi, tagogi, akushi, abin rufi da sauran kayan amfani. A gargajiya, ana sassaƙa gumaka da tambarin sarauta daga itace. Har ila yau, ana yin kayan ado da kayan yawon buɗe ido daga itace.
Sassaƙar dutse
Dutse na buƙatar ƙarfi da kayan aiki masu nauyi domin sassaƙawa. A tarihi, an yi amfani da shi wajen gina masallatai, gidaje, kaburbura, har ma da gumaka. A ƙasashen Hausawa, ana sassaƙa tubalan dutse don gine-gine masu ɗorewa. A yanzu, ana yin kayan ado da ƙananan siffofi daga dutse a matsayin kayan tarihi.
Sassaƙar ƙarfe
An fara yin wannan sassaƙa ne bayan gano fasahar narkar da ƙarfe a zamanin da. Ana yin makamai (takobi, kibau, garkuwa), kayan aiki (gatari, fatanya, wuƙa), da kayan ado. Ƙarfe yana daɗewa fiye da itace, don haka ya fi dacewa wajen samar da abubuwan da ake so su jure lokaci mai tsawo. A yau, ana amfani da injinan zamani wajen sarrafa ƙarfe zuwa abubuwa masu ban sha’awa.
Bambanci tsakanin sassaƙar gargajiya da ta zamani
- Sassaƙar gargajiya: ana yin ta ne da hannu kawai, ta hanyar amfani da wuƙa, gatari da sauran kayan aiki na gargajiya. Duk abin da aka yi yana ɗaukar lokaci amma yana da alaƙa da al’adu.
- Sassaƙar zamani: ana amfani da injinan lantarki da na’urar kwamfuta (CNC machines, 3D printing, da laser cutting). Wannan yana ba da damar samar da sassaƙa cikin lokaci kaɗan, tare da ingantaccen sakamako.
Muhimmancin sana’ar sassaƙa
Sana’ar sassaƙa ba kawai sana’ar gargajiya ce da ta tsaya kan yin kayan amfani ba, tana da muhimmanci mai faɗi a fannoni daban-daban na rayuwar ɗan’adam. Muhimmancinta ya shafi al’adu, tattalin arziki, addini, da kuma cigaban zamani.
Fannin tattalin arziki
- Sassaƙa hanya ce ta samar da kuɗi da ayyukan yi ga dubban mutane, musamman a ƙauyuka da birane.
- Kayayyakin sassaƙa suna yawo a kasuwanni na cikin gida da na ƙasashen waje a matsayin ababen tarihi da buɗe ido.
- Kasuwancin kayan sassaƙa na taimakawa wajen rage zaman kashe wando da kuma ƙara kuɗaɗen shiga na ƙasa.
Fannin addini da al’adu
- A gargajiya, sassaƙa yana da alaƙa da ibada da bautar gargajiya, inda ake sassaƙa gumaka da tambarin addinai.
- A al’ummar Hausawa da sauran ƙabilu, suna yin kujerun sarauta, sandar iko, tambarin ƙabilu, da sauran kayan mulki daga sana’ar sassaƙa.
- Haka kuma, tana da alaƙa da bukukuwa da shagulgulan al’adu, inda ake sarrafa kayan ado, kayan rawa, da sauran kayayyaki na biki.
Fannin ado da gine-gine
- Sassaƙa tana da rawar gani wajen ƙawata gine-gine, musamman ƙofofi, tagogi, ginshiƙai, da kayan ɗaki.
- Masallatai, majami’u, da gidaje masu tarihi suna da kyawawan ƙofofi da ɓangarori da aka yi da kayan sassaƙa.
- A gine-gine na zamani, ana amfani da sassaƙa wajen ƙirƙirar kujeru, tebura, bangon gida, da kayan ƙawata ofisoshi.
Fannin tarihi da adana al’adu
- Sassaƙa wata hanya ce ta adana tarihi. Ana sassaƙa alamomi da zane-zane a dutse ko itace don nuna labarin al’umma.
- Abubuwan tarihi da aka gano a wuraren binciken kimiya sun nuna cewa sassaƙa ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin da al’umma ta wuce.
- Hakan ya sa sassaƙa ke zama ginshiƙi wajen kare al’adun gargajiya daga gushewa.
Cigaban zamani da fasaha
- A wannan zamani ana amfani da sana’ar sassaƙa wajen ƙirƙirar zane-zanen zamani, kayan ado na kasuwanci, da sauransu.
- An haɗa sassaƙa da fasahar kwamfuta (CNC machines da 3D printing) domin samar da kayan aiki na zamani cikin inganci.
- Wannan ya nuna duk da cewa sassaƙa tsohuwar sana’a ce, amma tana taka rawar gani a ci gaban zamani.
Kalubalen sana’ar sassaƙa
Ƙarancin kayan aiki na zamani
Yawancin masu sana’ar sassaƙa, musamman a ƙauyuka, suna amfani da kayan gargajiya irin su wuƙa, gatari. Wannan yana sa aikin ya ɗauki lokaci mai tsawo, kuma sakamakon ba ya yin gogayya da na masana’antu. Rashin samun injinan zamani kamar CNC machines, injin hudawa, da grinders ya janyo masu sana’ar suna kasa samar da kayayyaki masu yawa da inganci, abin da yake rage darajar kayansu a kasuwa.
Rashin tallafi daga gwamnati
A mafi yawan lokuta, gwamnati ba ta bayar da isasshen tallafi ga sana’ar sassaƙa. Rashin samun rancen kuɗi, horo, da cibiyoyin koyarwa ya sanya matasa da yawa ba sa ganin sana’ar a matsayin abin dogaro. A sakamakon haka, yawanci sassaƙa ta zama sana’ar dattawa, ba tare da sabbin matasa suna shigowa cikin sana’ar ba, wanda hakan na iya kawo barazana ga ɗorewar ta a nan gaba.
Tasirin fasahar zamani
Fasahohin zamani irin su 3D printing da kayan masana’antu ya rage kasuwa ga kayayyakin da aka yi da hannu. Mutane da dama suna fifita kayan da aka ƙera a masana’antu saboda suna da rahusa, suna kuma da sauƙin samu. Wannan ya sa sana’ar sassaƙa ta gargajiya ta fara rasa ƙima, tare da barazanar ɓacewa idan ba a ɗauki matakan farfaɗo da ita ba.
Ƙarancin ciniki da tallatawa
Kodayake masu sassaƙa na samar da kayayyaki masu kyau da inganci, rashin hanyoyin tallatawa ya hana su samun gagarumar riba. Ba a haɗa sana’ar sosai da yawon buɗe ido ba, wanda ya kamata ya zama babbar hanyar samun kasuwa. Rashin haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da ƙasa ya sa kayayyakin sassaƙa na cikin gida ba sa shiga kasuwannin waje yadda ya kamata.
Ɓacewar al’adun gargajiya
Wasu daga cikin kayayyakin sassaƙa na gargajiya suna da alaƙa da addini da bukukuwan gargajiya. Amma tasirin addinai na zamani da canjin al’adu sun sa gumaka, tambarin sarautu, da wasu kayan al’ada suka daina sayuwa. Idan haka ta ci gaba, sana’ar sassaƙa za ta rasa asalin darajarta ta al’ada, ta koma kawai abin kallo a cikin gidajen tarihi.
Matsalolin muhalli
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen sassaƙar itace shi ne sare itatuwa ba tare da shuka sababbi ba. Wannan yana janyo asarar gandun daji, rushewar muhalli, da kuma ƙara tsadar kayayyakin da aka sarrafa daga itace a kasuwa. Idan ba a samar da tsari na kiyayewa da shuka sabbin itatuwa ba, sana’ar sassaƙa da ta dogara da itace za ta iya shiga mummunar matsala nan gaba.

Hanyoyin inganta sana’ar sassaƙa
Horarwa da matasa
Ɗaya daga cikin hanyoyin inganta sana’ar sassaƙa shi ne horar da matasa domin su gaji wannan sana’a mai daraja. Idan aka buɗe cibiyoyin koyarwa na musamman, za a iya haɗa dabarun gargajiya da na zamani domin su samar da ƙwarewa ta musamman. Wannan zai sa sana’ar ta ci gaba, ba tare da ta tsaya ga dattawa kaɗai ba.
Amfani da kayan aiki na zamani
Samar da injina da kayan aikin zamani kamar CNC machines, grinders da na’urorin laser zai sauƙaƙa ayyukan masu sassaƙa, ya rage musu wahala, tare da tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa sun dace da kasuwannin duniya. Wannan zai ba da damar yin gogayya da kayayyakin masana’antu.
Tallafa wa masana’antun gida
Tallafin gwamnati da ƙungiyoyi na musamman ga masu sassaƙa zai ƙara musu ƙarfin gwiwa. Idan aka samar da rance da cibiyoyin haɗin gwiwa, masu sana’ar za su iya yin aiki a ƙungiyance, wanda hakan zai ƙara samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando a cikin al’umma.
Haɗa sana’ar da yawon buɗe ido
Sassaƙa na iya bunƙasa idan aka haɗa ta da harkar yawon buɗe ido. Ana iya shirya baje koli a wuraren shakatawa, gidajen tarihi da bukukuwa na al’adu, inda baƙi za su sayi kayayyakin da aka sassaƙa. Wannan zai ƙara darajar sana’ar tare da kawo ƙarin kuɗaɗen shiga ga al’umma.
Ƙarfafa bincike da nazari
Ana buƙatar gudanar da bincike a kan hanyoyin da za su tabbatar da ɗorewar sana’ar ba tare da lalata muhalli ba. Sake shuka itatuwa bayan sarewa ko amfani da kayayyaki madadin itace kamar ƙarfe da filastik a wasu fannoni zai taimaka wajen kare muhalli tare da bunƙasa sana’ar.
Amfani da fasahar sadarwa
Masu sassaƙa za su iya amfani da intanet da kafofin sada zumunta wajen tallata kayansu. Wannan zai faɗaɗa kasuwancin daga cikin gida zuwa ƙasashen waje, ya kuma buɗe ƙarin dama ga bunƙasar sana’ar.
Manazarta
Adepegba, K., & Abati, O. I. (2017). Yoruba woodcarving: New characteristics, new uses. Journal of Humanities and Cultural Studies, 2(1), 341-356.
Ambursa, S. S. (2015). “Sana’a Sa’a: Nazari a kan Sana’ar Sassaƙa a Garin Birnin Kebbi.” Sakkwato: Kundin Digiri na Farko, Sashen Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Odeniyi, A. A. O. (2025). Training and practice of carving at LAUTECH Art School: Trainees’ feedback. Srawung: Journal of Social Sciences and Humanities, 4(3).
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 12 September, 2025
An kuma sabunta ta 12 September, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.