Tarbiyya kalma ce ta Larabci, wadda take ƙunshe da ma’anar koyar da hali na gari da kyautata rayuwar al’umma da shiryar da su zuwa ga halaye da ]abi’u masu kyau da nagarta. Dangane da haka, duk al’ummar da ta kasance haka, za ta zama mai ƙima da kwarjini da ganin mutuncin abokan zama. Kazalika za ta rinƙa ba kowa haƙƙinsa kamar yadda ya dace.
Masana da manazarta sun himmatu wajen fayyace ma’ana da matsayin tarbiyya wajen gina al’umma. Wasu daga cikin masanan sun yi ittafƙin cewa tarbiyya ta ƙunshi renon jikin ɗan’adam da ruhinsa da kyawawan abubuwa masu kamala. Tarbiyya ta haɗa da kyautata hankalin ɗan’adam domin ya sami nagartattar rayuwa da yadda za ta dace da yanayin al’ummarsa, hakan kuma tana kyautata al’adun al’umma su kasance kyawawa tare da inganta su.
Hanyoyin yin tarbiyya
A al’adar Hausawa tarbiyya kan ginu ne a bisa tafarkin magabata. Magabatan nan kuwa sun haɗa da iyaye maza da mata da shugabanni waɗanda suka haɗa da masu unguwanni da hakimmai da kuma sarakuna da sauran shugannin zartarwa na masu mudafun iko. Dangane da haka, wasu daga cikin hanyoyin samar da tarbiyya ga ‘ya’yan Hausawa sun haɗa da:
Hanyar tatsuniya
Tatsuniya ita ce makaranta ta farko wajen raya da kuma inganta tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa. Wannan hanya ce kowa ke tasowa da sanin yadda rayuwa ke gudana, dalili kuwa a cikin tsarin bayar da labaran tatsuniya akan bai wa yara labarai masu ɗauke da darussa daban-daban da ake iya koya domin samun nagartacciyar rayuwa. Galibi masu bayar da tatsuniya tsofaffi ne da suka san hikimomin rayuwar Hausawa a jiya da yau. Daga cikin darussan da yara kan koya su kuma tashi da su a cikin zukatansu sun haɗa da; juriya da kawaici da kauce wa kwaɗayi da son juna da sada zumunci da tsare gaskiya da riƙon amana da sauran nagartattun ɗabi’u da halaye da aka san Hausawa da su.
Hanyar iyaye mata
Hausawa kan ce “Uwa ma ba da Mama” wasu kuma suka ce “ Uwa ma ba ɗa nono” duk dai ya yake karin maganar yake a nan, ana son a nuna muhimmanci iyaye mata ne wajen tabbatar da tarbiyya ‘ya’ya a ƙasar Hausa. Iyaye mata su ne a sahun gaba wajen tarbiyantar da ‘ya’ya tun a matakin shayarwa. Sukan nuna wa yaransu wasu alamu na rashin amincewa da wasu ɗabi’u da halaye da yaransu ke son tashi da su waɗanda suka saɓa wa al’adun Hausawa. Misali idan mace tana goye da yaronta ya roƙi alawa ga wani, a nan za ta Harare shi a wasu lokuta ma har takan haɗa da bugu. Hikimar hakan shi ne ka da yaro ya saba da yin roƙo a cikin rayuwarsa, domin al’adar roƙo abin ƙyama ce cikin zamantakewar Hausawa. A wasu lokuta iyaye mata sukan harari ‘ya’yansu ko su yi musu tsawa idan sun fahimci za su yi wani abin da ba daidai ba. Misali idan yaro zai ci abinci aka ga ya sanya hannun hagu, za a ce masa ya cire ya sanya na dama. Idan ya ƙi fitar da hannun za a iya bugun shi. Haka abin yake ga yanayin zaman cin abinci, dole yaro ya riƙe kwanon cin abinci kuma ya bar yawon surutu, idan aka ƙare cin abincin kuwa yaro ake bar wa ragowar abinci daga ƙarshe. Wannan wata tarbiyya ce da mata suke da alhakin kula da ita a nasu mataki na cikin gida. Idan kuma za a bai wa yaro wani abu, to dole ya sanya hannu biyu wajen karɓar abin nan tare da faɗin na gode. Mata sukan koya wa yara tashi da girmama na gaba ta hanyar gaishe su da karɓa musu kaya idan sun haɗu da su a kan hanya tare da kaya.
Iyaye maza
Babbar tarbiyyar da iyaye maza ke iya bayar wa wajen ‘ya’yansu shi ne tun a mataki na farko su samar masu da sunaye masu kyau ta hanyar tsarkake su daga zargi na rashin tushe, wato su yanka masu dabbar suna. Wannan yana da matuƙar muhimmanci ga Bahaushe domin tan an ne ake sanin tushen mutum mai kyau ne ko marar kyau. Bayan wannan haƙƙin Uba namiji ne ya sanya ‘ya’yansa makarantar koyo addinin musulunci da kuma na bokon zamani, domin yaran su zama na gari a nan gaba. Yin hakan zai sanya ‘ya’yan su zama abin alfahari idan sun zama abin kwarai abin koyi bayan sun girma.
Wata hanyar gina tarbiyya ga Hausawa ita ce hanyar da za a sanya yara makarantu domin su sauya tunaninsu zuwa ga zama masu amfani ga kansu da kuma al’umma gabaɗaya. A tsarin bayar da ilmin addinin musulunci da boko, ana gina mutum ne ga sanin Allah da haƙoƙin zamantakewar mutane. Wannan ne ya sa ake iya rarrabe wanda ya je makaranta (mai ilmi) wanda bai je makaranta ba (maras ilmi). Dalili kuwa shi ne mai ilmi ne al’umma kan amfana da shit a fuskoki da dama, yayin da maras ilmi kan zama abin ƙyama a cikin jama’a. Wannan ya nuna irin tarbiyyar da ya samu ba mai kyau ba ce.
Hanyar Maƙwabta
Ma}wabtaka ita ce kusantar da mutum yake yi da wani ta gida ko wurin zama ko wurin aiki. Takan haifar da zaman tare da kula da juna. Asali ma a zamantakewar Hausawa maƙwabta kan taimaka wajen gyarawa da kuma inganta tarbiyyar yara musamman a jiya, ba yanzu da zamunanci da aron al’adun baƙi ya yi tasiri a kanmu ba. A zamantakewar Hausawa, maƙwabci kan yi iya ƙoƙarinsa na ganin ya inganta tarbiyyar ‘ya’yan maƙwabtansa ta hanyar tsawata su idan sun yi abin da bai dace ba ko ma ya hkunta su idan sun yi wani babban laifin da ya saɓa wa al’ada. Wannan matakin kuwa yakan taimaka wajen gina tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa musamman a lokutan da suka gabata.
Hanyar shugabanni
Wani kaso na waɗanda gina tarbiyya ya ta’allaka kuwa su ne shugabannin al’umma. Waɗannan su ne mutanen da suke da alhakin kula da rayuwar mutane da dukiyoyinsu wajen samar masu da tsaro ingantacce. Yin sakaci ga ayyukan shugabanni yakan kawo barazana ga tarbiyyar matasa a duk inda suke, rashin ginanniyar tarbiyya ga matasa kuwa sakamakonsa taɓarɓarewar tsaro da zama lafiya da kuma samun cigaba mai ɗorewa.
Don haka, a ƙasar Hausa inda aka fito sarakuna da hakimai da masu unguwanni sukan yi aiki kafaɗa da kafaɗa wajen ganin sun inganta tarbiyyar matasa a kowane mataki. Yin hakan kuwa ya haifar da samun zama lafiya da lumana a faɗin ƙasar maimakon abin da yake faruwa a yau.
Sauran al’umma
Al’umma na nufin ɗaukacin mutanen da suke zaune a wuri ɗaya kuma suke da al’adu da ɗabi’u iri ɗaya. A ra’ayin masana ilmin zaman Jama’a kuwa (sociologist) ganin suke al’umma a matsayin ƙabila mai asali da harshe ɗaya da ra’ayin zaman duniya (falsafa) ɗaya da kamanni kusan iri ɗaya da kuma al’adun gargajiya iri ɗaya. Dangane da haka za a iya ɗaukar al’umma a matsayin taron mutane ko jama’a da suke zaune cikin aminci da fahimtar juna wanda hakan kan faru ne a dalilin nasabar jini ko auratayya da kume zamantakewar garuruwa da sana’o’i. A nan ana son a nuna cewa bayar da tarbiyya ga yara da matasa aiki ne na jama’a baki ɗaya. Don haka, ake son al’umma su himmatu wajen kula da wannan al’amari mai muhimmancin gaske. Yin saku-saku da sha’anin tarbiyya ne ke haddasa ayyukan rashin kunya da imani a faɗin ƙasar nan.
Matsayin tarbiyya
Sha’anin tarbiyya abu ne da yake da muhimmancin gaske a kowace nahiya da al’ada. Dangane da haka lamarin tarbiyya wajen gina kowace al’umma abu ne da ke da babban matsayi. Tarbiyya tana da matsayi wajen samar ilmin matasan kowace al’umma, samar da ilmin nan kuwa wani mataki ne na samar da al’ummar da za ta iya riƙe kanta ta hanyar dogaro ga kai da rashin yawaitar ayyukan ta’adanci da rashin aiki ke haifarwa. Wannan ne ya sa tun gabanin Hausawa su haɗu da baƙin al’ummu (kamar Larabawa da Turawa da sauran ƙabilun cikin ƙasa) suke riƙe da sana’o’insu na gargajiya masu kore masu zaman banza da rashin aikin yi. Mutane sun ginu a bisa tafarkin koyon sana’o’i da dogaro da kai, wanda tarbiyyar Hausawa ta tanadar a cikin al’adunsu na zamantakewa.
Manazarta
Abdullahi, S. U . (1985) Gasikiya Dokin ƙarfe. Kano. Mainasar Printing Press.
Abraham R.C (1946) The Dictionary of hausa Language. London, Hodder and Stoughton.
Awobuluyi, O. (1976): The New National policy on Education in Linguistic Perspective. University of Ilorin Press.
CNHN (1981). Rayuwar Hausawa. Lagos. Thomos Nilson Nigeria Limited.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.