Trachoma wata cuta ce mai tsanani da ke kama idanu, wadda kuma ta samo asali ne daga ƙwayar cuta mai suna Chlamydia trachomatis. Tana daga cikin manyan cutukan idanu da ke haddasa makanta a faɗin duniya. Sannan cutar na yaɗuwa ne musamman a wuraren da tsaftar muhalli da ruwan sha suka yi ƙaranci, kuma ta fi shafar ƙauyuka da al’ummomin da ke fama da ƙarancin tattalin arziki.
Asalin cutar trachoma
Kalmar “trachoma” ta samo asali ne daga harshen Girkanci, wato tana nufin gajiya ko rauni na sassan ido. Trachoma na daga cikin tsofaffin cututtukan ido da aka fi sani tun a zamanin da. Masana na wancan zamanin sun gano alamominta a cikin tsoffin rubuce-rubucen mutanen Misra, sannan likitocin Girka da Rumawa kamar Galen ma sun bayyana ta. Wannan yana nuna cewa cutar ta daɗe tana damun ɗan’adam tun kafin magungunan zamani su bayyana.
Yadda cutar ke yaɗuwa
Trachoma cuta ce mai saurin yaɗuwa, musamman a cikin al’ummomi masu cunkoson jama’a da kuma rashin tsafta. Daga cikin hanyoyin yaɗuwar ta akwai:
- Ta hanyar hannu ko tufafi: Idan aka taɓa idon mai ɗauke da cutar, sannan kuma aka taɓa na wani idon lafiyayye, toh za’a iya kamuwa da wannan cuta.
- Ta hanyar ƙwari: Musamman ƙudaje da ke hawa a fuskar yara suna ɗaukar ƙazanta daga idon mai cuta su kai ga wani idon na mai lafiya. Wannan ma hanya ce mafi sauƙi da cutar trachoma ke yaɗuwa.
- Ta hanyar ruwa: Ana kamuwa da trachoma ta hanyar amfani da ruwan sha marar tsafta, ko wanke fuska da ruwa ɗaya.
Alamomin cutar trachoma
Cutar trachoma na bayyana ne a matakai daban-daban kamar haka:
- Matakin farko: Idanu zasu yi ja, kumburi, da kuma ƙaiƙayi. Sai zubar hawaye ko ɗigon datti (Kwantsa) a ido.
- Mataki na biyu: Fesowar ƙurajen ciki a fatar ido, kumburin ɓangaren ido na sama (eyelid), da kuma kumburi da ciwon idon da baya jin magani.
- Mataki mai tsanani: Fatar ido tana naɗewa cikin ido (trichiasis), daga nan gashin ido zai riƙa shafar ƙwayar ido tare da haddasa raunuka.
- Matakin Ƙarshe: Shi ne lalacewar idon gaba ɗaya tare da makanta.
Yankunan da cutar ta fi yawa
Trachoma ta fi yawa a ƙasashe masu tasowa na yankin Afirka ta yamma da gabas, inda suka haɗa da Najeriya, Nijar, Chadi, Sudan, Habasha). Sai kuma wasu sassa na Asiya da suka haɗa da (Afghanistan, Nepal, Pakistan), da kuma wasu ƙasashen Larabawa da Latin America.
WHO ta sanya Najeriya cikin manyan ƙasashen da ke da ƙalubale wajen kawar da trachoma saboda yawan jama’a da matsalar tsafta a karkara.
Sannan a ƙididdiga da rahotannin duniya, an tabbatar da sama da mutane miliyan 1.9 a duniya ne ke fama da makantar trachoma. Har ila yau mutane fiye da miliyan 136 a ƙasashe 44 ke cikin haɗarin kamuwa da cutar. A Najeriya, an ruwaito cewa kusan jihohi 16 na Arewa suna fama da matsalar trachoma.
Tasirin cutar trachoma
Yara ƙanana da mata ne suka fi haɗarin kamuwa da ita, saboda sun fi yin hulɗa da ruwa da kuma tsaftar gida. Sannan mutanen da suka makance saboda trachoma kan rasa aikin yi, wannan kuma na rage tattalin arzikin iyali da ƙauyuka, daga ƙarshe kuma matsalar na jawo wariyar jama’a ga masu makanta, musamman a inda aka fahimci ɗaukar ta ake.
Hanyoyin gwaje-gwaje
Likitoci na amfani da hanyoyin bincike tare da tantancewa domin gano cutar kamar haka: binciken ido kai tsaye don gano ƙuraje a fatar ido, gwajin ɗakin gwaje-gwaje (PCR test) don gano Chlamydia trachomatis.
Magani da riga-kafi
Ana amfani da tsarin SAFE wanda WHO ta tsara
Tsarin SAFE, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara, wata hanya ce ta kariya da kuma magance cutar trachoma. Ana amfani da tsarin SAFE domin magance matsalolin da ke haddasa yaɗuwar cutar da kuma daƙile illolinta na dogon lokaci, musamman makanta. Kalmar SAFE tana nufin matakai guda huɗu ne, kowannensu na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da trachoma.
-
Surgery
Mataki na farko shi ne Surgery, wato tiyata. Wannan tiyatar na da amfani ne ga mutanen da cutar ta tsananta har ta haifar da abin da ake kira trichiasis, wato lokacin da gashin idon sama ke karkata ciki zuwa ƙwayar ido, yana gogar ido, wanda hakan ke haddasa ciwo, kumburi, da ci gaba da raunana gani har ta kai ga makanta. Yin tiyata domin magance wannan matsala yana hana cigaba da lalacewar ido, kuma yana dawo da nutsuwa da lafiya ga mai fama da wannan matsala.
-
Antibiotics
Mataki na biyu shi ne amfani da antibiotics, wato magungunan kashe ƙwayar cuta. A nan, ana amfani da Azithromycin, wanda ake sha sau ɗaya, ko kuma Tetracycline ointment, wanda ake shafawa a idanu na tsawon kwanaki. Wadannan magunguna na taimakawa wajen kawar da ƙwayar Chlamydia trachomatis daga jikin mutum, domin rage yaɗuwar cutar tsakanin jama’a. Ana raba Azithromycin kyauta a shiyyoyi da cutar ke yaɗuwa, musamman ta hanyar shirin haɗin gwiwa tsakanin WHO da gidauniyoyi kamar Gidauniyar Carter da Gidauniyar Bill da Melinda Gates.
-
Facial cleanliness
Mataki na uku shi ne Facial cleanliness, wato tsaftar fuska. Wannan mataki yana da matukar muhimmanci musamman ga yara, saboda su ne ke fin saurin kamuwa da cutar kuma ke fin yawan yaɗa ta. Yara da ke fama da datti a fuska, musamman majina sukan jawo ƙuda zuwa ga ido, waɗanda ke ɗauke da ƙwayar cutar daga mutum zuwa mutum. Don haka, ana ƙarfafar iyaye da malamai su tabbatar da cewa yara na wanke fuskokinsu akai-akai da ruwa mai tsafta. Wannan yana rage haɗarin kamuwa da trachoma, har ma da wasu cututtuka na ido da baki da hanci.
-
Environmental improvement
Mataki na ƙarshe shi ne Environmental improvement, wato gyarawa da inganta yanayin muhalli. Wannan yana nufin samar da ruwan sha mai tsafta, banɗakuna masu tsabta, da kuma hanyoyi na rage yawaitar ƙudaje. A yankunan da babu waɗannan abubuwan, cututtuka kamar trachoma kan yaɗu cikin sauki. Idan mutane ba su da isasshen ruwa, ba za su iya tsaftace kansu ba. Idan ba a zubar da shara da najasa cikin tsari, ƙudaje da sauran ƙwari sukan yawaita, suna yaɗa cututtuka. Saboda haka, wannan mataki yana tabbatar da cewa mutane suna rayuwa a cikin yanayi mai tsafta wanda ke hana yaɗuwar cututtuka.
A taƙaice dai tsarin SAFE ba wani shiri ne da mutum ɗaya ko ma’aikacin lafiya zai iya aiwatar da shi shi kaɗai ba. Wani tsarin haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, ma’aikatan lafiya, al’umma, da iyaye, domin ceto dubban idanuwa daga makanta ta hanyar tsafta, ilimantarwa, magani, da tsarin rayuwa mai inganci.
Yadda ake aiwatar da tsarin SAFE
A ƙauyuka da dama, inda mutane ke fama da ƙarancin ruwa da tsafta, cutar trachoma na yaɗuwa cikin sauƙi, musamman tsakanin yara. Don haka, amfani da tsarin SAFE yana farawa ne da ilimin jama’a. Ma’aikatan lafiya ko wakilan ƙungiyoyin agaji suna shiga ƙauyuka domin wayar da kai game da cutar, yadda ake kamuwa da ita, da kuma hanyoyin guje mata. Ana amfani da hanyoyin da al’umma ke fahimta, kamar tarukan jama’a, faɗakarwa masallatai da majami’u, ko kasuwanni don isar da saƙo.
A irin wannan mataki, ana ƙarfafar iyaye su kula da tsaftar yara, su dinga wanke fuskokinsu sosai a rana da ruwa mai tsafta. Ana kuma koyar da su illar barin yara suna yawo da datti ko majina a fuska, wanda ke jawo ƙudajen da ke yaɗa cutar.
Idan aka gano akwai mutane da ke fama da trichiasis (wato lokacin da gashin ido ke gogar idanu saboda lalacewa), ana aika su zuwa cibiyar lafiya mafi kusa ko kuma wasu ƙungiyoyi sukan kawo likitoci zuwa ƙauye don gudanar da tiyata a nan take. Wannan tiyatar tana da sauƙi, kuma yawanci ana yin ta kyauta a ƙarƙashin shirin yaƙi da trachoma. Bayan tiyatar, mutum yana buƙatar hutu na ‘yan kwanaki kafin komawa ayyukansa na yau da kullum.
A bangaren magani, idan aka tabbatar cewa wani kauye ko gari na da matakin yaɗuwar cutar da ya wuce kima, to ana shirya gangamin raba maganin Azithromycin ga kowa da kowa a wannan yankin. Wannan yana rage yaɗuwar ƙwayar cutar daga mutum zuwa mutum. A irin wannan gangami, ana buƙatar haɗin gwiwar masu unguwa, shugabannin al’umma, malamai da malaman addini domin karfafar mutane su karɓi maganin. Wani lokaci, ana amfani da takardar ɗan ƙasa domin tabbatar da kowa ya karɓa.
A matakin muhalli, ƙungiyoyi masu zaman kansu ko hukumomin lafiya na taimakawa wajen gina banɗakuna, haƙa rijiyoyi ko bututun ruwa a ƙauyuka, da kuma koyar da mutane yadda ake amfani da su cikin tsafta. A wasu lokuta, ana koyar da yadda za a gina banɗaki da kayan gida kawai, ba tare da dogaro da taimako daga waje ba. Ana kuma yin aikin gayya domin kawar da shara da hana taruwar ruwa wanda da ke jawo ƙwari, musamman ƙudaje.
A ƙarshe kuma, ma’aikatan lafiya da malamai a makarantu suna taka muhimmiyar rawa wajen lura da sahihancin tsafta da lafiyar yara. Malamai sukan duba fuskokin yara a kowace safiya, su karfafa musu gwiwa su zo makaranta a tsabtace. Haka ma a asibitoci, ana horar da ma’aikatan jinya da ungozoma yadda za su gane alamomin farko na trachoma da yadda za a ɗauki mataki cikin gaggawa.
Misali daga wasu ƙasashe
A wasu ƙasashe kamar Nijar da Habasha (Ethiopia), tsarin SAFE ya taimaka wajen rage adadin mutanen da ke fama da trachoma da kashi fiye da 80%. Wannan ya samu ne saboda an haɗa ilimi da aiki kai tsaye. Wato an shiga ƙauyuka, an yi tiyata, an raba magani, an gina rijiyoyi da banɗakuna, kuma an karfafa tsafta a makarantu da gidaje.
Wannan yana nuna cewa haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomi yana da matuƙar tasiri wajen magance cututtuka irin na trachoma. Tsarin SAFE yana magance cutar tare da inganta rayuwar mutane gabaɗaya. Yana kawo tsafta, lafiya, da kuma ƙarfafa ilimi da fahimta tsakanin jama’a.
Magance trachoma ta hanyar gargajiya
A al’adun Hausawa da sauran al’ummomi da dama na Afirka da wasu sassan Asiya, akwai dogon tarihi na amfani da magungunan gargajiya wajen magance cututtukan ido, ciki har da trachoma. Wannan ya samo asali ne daga rashin isassun cibiyoyin lafiya, rashin magungunan zamani, ko kuma dogaro da al’adar gado da amincewa da hanyoyin da kakanni suka yi amfani da su tun da daɗewa.
A gargajiyance, mutane da dama sun yi amfani da abubuwa kamar:
- Ruwan ganye: Irin su ganyen magarya, zogale, ko tafasa ganyen habbatus sauda. Ana iya tafasa ganyen, a tace ruwan, sannan a bar shi ya huce, sai a shafa ko ɗiga cikin ido domin rage kumburi ko jan ido.
- Gishiri da ruwa: Ana haɗa gishiri da ruwa kaɗan, sai a dinga wanke ido da shi ko shafawa a kusurwar ido. A wasu lokuta ana ɗora auduga da ruwan gishirin a saman ido na ɗan lokaci.
- Ruɓaɓɓen ƙanshi: Wasu na amfani da ƙanshi ko turare da aka niƙa ko aka dafa, a bar hayakin ya shiga ido. A wasu al’adu, ana yawan yin wannan lokacin da ido ya kumbura ko yake zubar da ruwa sosai.
- Hayaki: A wasu lokuta, ana kona wasu nau’in ganyayyaki masu ƙanshi, sai a bar ido a buɗe hayakin ya shiga domin kore cuta.
Tasirin maganin gargajiya
Kodayake waɗannan hanyoyin gargajiya suna taimakawa wajen rage zafi, kumburi ko ɗan ƙaiƙayi. Sai dai ba duk lokacin ne suke da tasirin tsaye akan cutar da ta haifar da matsalar ba. A wasu lokuta, suna rage alamomi na ɗan lokaci, amma ba su hana cutar dawowa ba. Haka kuma, idan ba a kula ba, wasu daga cikin hanyoyin gargajiyar na iya:
- Haifar da ƙarin kumburi.
- Jawo haɗarin kamuwa da wata cuta ta daban.
- Haifar da lahani a ido idan an yi amfani da abubuwa masu ƙarfi ko datti.
Shirin WHO na kawar da trachoma (GET 2020)
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ƙaddamar da wani babban shiri mai suna GET 2020, ma’ana Global Elimination of Trachoma by the year 2020, wanda manufarsa ita ce a kawar da trachoma a matsayin wata babbar matsalar lafiyar jama’a a duniya. Wannan shiri ya samo asali ne daga yadda cutar ke yaɗuwa a ƙasashe masu ƙarancin samun ruwa da tsafta, da kuma yadda take haddasa makanta ga miliyoyin mutane, musamman mata da yara a karkara.
Tun da farko an ƙuduri niyyar kawar da cutar kafin shekara ta 2020, sai dai wasu ƙalubale, kamar rashin wadataccen ruwan sha, tsaro, da kuma ƙarancin ma’aikatan lafiya a wasu yankuna, sun sa aka tsawaita burin zuwa shekara ta 2030. Har yanzu ana ci gaba da aiki tuƙuru a ƙarƙashin wannan tsari.
Ƙasashen da suka kai ga nasara
A sakamakon wannan shiri da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu, wasu ƙasashe sun riga sun cika sharuɗɗan kawar da trachoma kamar yadda WHO ta tanada. Daga cikin waɗannan ƙasashe akwai:
- Morocco: Ta zama ƙasar farko da WHO ta tabbatar da cewa ta kawar da trachoma a shekarar 2016.
- Ghana: Ta samu wannan nasara a shekarar 2018.
- Saudi Arabia: Ta bayyana cewa ta kawar da trachoma a hukumance a shekarar 2019.
Waɗannan ƙasashe sun yi hakan ne ta hanyar aiwatar da tsarin SAFE da haɗin kai tsakanin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Ƙoƙarin da ake yi a Najeriya
Najeriya na daga cikin ƙasashen da cutar trachoma ke yaɗuwa a sassa da dama, musamman a arewacin ƙasar. Sai dai kuma, an ɗauki matakai masu kyau domin magance wannan cuta. Gwamnati tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi da dama na gudanar da ayyuka a fannonin lafiya da tsafta. Wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke taka rawa sosai sun haɗa da:
- The Carter Center: Wata ƙungiya ce da ke aiki da niyyar kawar da cututtuka masu haddasa makanta. A Najeriya, suna aiki a jihohi kamar Nasarawa da Plateau, inda suke bayar da magunguna kyauta da kuma horar da ma’aikatan lafiya.
- Sightsavers: Su ma suna tallafa wa shirin kawar da trachoma a jihohi da dama ta hanyar bayar da magunguna (Azithromycin), aikin tiyatar ido kyauta ga masu fama da trichiasis, da kuma ilimantar da jama’a kan tsafta da hanyoyin kariya.
- CBM (Christian Blind Mission): Wata ƙungiya ce da ke taimaka wa masu fama da nakasa, musamman masu matsalolin ido. Suna bayar da horo, kayan aikin tiyata, da tallafi ga cibiyoyin lafiya da ke kula da trachoma.
A ƙoƙarin da ake yi, ana raba magunguna kyauta a tsakanin al’umma, ta hanyar haɗin gwiwa da shuwagabannin gargajiya, malaman addini, da malaman makaranta. Wannan hanya tana taimakawa wajen karɓuwar shirin a tsakanin jama’a. Ana kuma koyar da mutane muhimmancin tsaftar fuska, amfani da banɗakuna, da wanke fuska da hannu akai-akai.
Manazarta
American Academy of Ophthalmology. (2024, November 14). What is Trachoma? American Academy of Ophthalmology.
Solomon, A. W., Burton, M. J., Gower, E. W., Harding-Esch, E. M., Oldenburg, C. E., Taylor, H. R., & Traoré, L. (2022). Trachoma. Nature Reviews Disease Primers, 8(1).
Mayo Clinic (n.d). Trachoma – Symptoms and causes. Mayo Clinic. .
World Health Organization: WHO. (2025, July 18). Trachoma. World Health Organization.
Tarihin Wallafa Maƙalar
An wallafa maƙalar 28 September, 2025
An kuma sabunta ta 28 September, 2025
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.