Skip to content

Tumfafiya

  • Wallafawa:
  • Rukuni: Tsirrai
Aika |

Tumfafiya shuka ce mai matuƙar amfani ga lafiya, wanda aka fi samu a yankunan da ke da zafi gami da ƙasa mai yashi, kamar arewacin Najeriya, Nijar, Chadi, Mali da wasu sassan Asiya. Tumfafiya na daga cikin tsirran da ke da juriya, tana iya rayuwa a cikin hamada, kuma tana da amfani a fannin magungunan gargajiya da kuma fannin kimiyya. Tumfafiya ta samu asali ne daga dangin Apocynaceae, sannan a kimiyyance ana kiranta da Calotropis procera.

whatsapp image 2023 07 22 at 8 11 26 pm
Shukar Tumfafiya

A al’adance, ana ɗaukar tumfafiya a matsayin tsiro mai ƙarfin gaske, saboda farin ruwan da ke cikinta (latex) wanda ke da guba idan ba a sarrafa shi yadda ya dace ba, sai dai kuma, yana da amfani sosai idan an sarrafa shi yadda ya kamata.

Siffofin tsiron tumfafiya

Tumfafiya na iya kaiwa tsayin kimanin mita 1 zuwa mita 4, a wani lokaci ma har takan kai mita biyar. Sannan tsiro ne da rassanta ke yaɗuwa a gefe, har ila yau tsiron na da juriya kuma baya buƙatar ruwa mai yawa.

Ganyenta manya ne masu launin kore mai duhu, suna fitowa a jere bibiyu, sannan suna da kauri da ɗan danƙon da ke hana su bushewa da wuri. Furanninta ƙanana ne masu launin fari da shuni mai laushi, suna fitowa a rukuni-rukuni. Sannan suna da ɗanɗanon da ke jawo ƙudan zuma zuwa kansu. Idan aka yanke tumfafiya, tana fitar da kakkauran farin ruwa mai kama da madara. Wannan ruwan yana ɗauke da sinadaran cardenolides masu ƙarfi. Sannan ruwan zai iya ƙona fata ko haifar da ƙaiƙayi idan ba a kula ba. Amma a gargajiyance, ana amfani da shi don maganin kumburi ko ciwo idan an sarrafa shi yadda ya dace.

‘Ya’yan tumfafiya suna da girma, sannan cike suke da zaren auduga mai laushi da ake kira (fafule), wanda a wasu wuraren ake sarrafa shi don yin matasan kai ko wani abun mai muhimmanci.

Wuraren da tumfafiya ta fi yaɗuwa

Kowace shuka da irin muhallin da ta fi bunƙasa, haka ma tumfafiya tana bunƙasa ne a hamada da ƙasa mai yashi, sannan tana yawan fitowa a gefen hanya, da kuma wuraren da ake zubar da tarkace. Kamar yadda ya gabata, an fi samun ta a Arewacin Najeriya da Nijar, Mali, Chadi, Sudan har ma da ƙasashen Indiya da Saudiyya.

Sinadaran da ke cikin tumfafiya

Binciken masana kimiyya ya nuna cewa tumfafiya na ɗauke da manyan sinadarai masu tasiri a jikin ɗan Adam, da suka haɗa da:

  • Cardiac Glycosides: Sinadaran da ke aiki kan zuciya, suna taimakawa wajen ƙara ƙarfin bugun zuciya, amma suna da haɗari idan aka sha su fiye da kima.
  • Flavonoids: Sinadaran da ke taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki, rage kumburi, da hana tsufa da wuri, saboda suna yaƙi da sinadarai masu gurɓata cells wato antioxidant.
  • Tannins: Sinadaran da ke taimakawa wajen rage zubar jini, ƙara ƙarfin fata, da taimakawa wurin warkar da raunuka. Ana samun su a ganyayyaki da dama, ciki har da tumfafiya.
  • Saponins: Sinadaran da ke fitar da kumfa idan aka gauraya su da ruwa. Suna taimakawa wajen wanke jini, rage kitse a jiki, da ƙara ma garkuwar jiki ƙarfi.
  • Terpenoids: Sinadaran da ke ba tsiro wari ko ƙamshi. A tumfafiya suna taimakawa wajen yaƙar ƙwayoyin cuta, hana kumburi, da taimakawa wajen warkar da cutukan fata. Waɗannan sinadarai ne suka sa tumfafiya ta zama tsiro mai amfani sosai a fannin magungunan gargajiya da kuma kimiyya.

Amfanin tumfafiya a magungunan gargajiya

  • Maganin ciwon kai da kumburi: Ana amfani da farin ruwan tumfafiya ta hanyar shafawa don rage zafin ciwon kai ko kumburi, amma a ƙarƙashin kulawar ƙwararre. Sannan a ƙa’ida ba’a shan wannan farin ruwa, saboda gubar da ke cikinsa.
  • Maganin ƙurajen fata da ciwo: Ana daddaka ganyen tumfafiya a shafa a kan ƙuraje ko ciwo don neman waraka.
  • Maganin toshewar mafitsara: A wasu wurare ana dafa ganyen tumfafiya a haɗa da zuma mai kyau don rage toshewar mafitsara. Amma ba a haɗa irin wannan maganin kai tsaye, har sai an samu shawara daga wurin ƙwararrun masana a fannin magungunan gargajiya da kuma kimiyya.
  • Sannan a al’adun wasu mutanen, suna ƙona ganye ko itacen tumfafiya, tare da fesa tokar don korar ƙwari ko neman tsari na al’ada.

Hanyoyin sarrafa tumfafiya

  • Wasu masana’antun suna sarrafa audugar da ke cikin ‘ya’yan tumfafiya don yin matasan kai, ko ƙwallo. Kuma a wasu ƙasashen ana sarrafa ta wajen samar da fiber mai kama da auduga.
  • Tace ruwa da tsabtace muhalli: Saponins ɗin da ke cikin tumfafiya suna da amfani wajen tace gurɓataccen ruwa ko rage ƙazanta a kimiyyar muhalli.
  • Magungunan kimiyya: Masana kimiyya suna bincike kan amfani da cardiac glycosides da flavonoids daga tumfafiya wajen ƙirƙirar magunguna na ciwon zuciya, cututtukan fata, kumburi da sauransu

Me ya sa ake danganta tumfafiya da aljannu?

A al’adar Hausawa, ana danganta wasu tsirrai da aljannu saboda tsofaffin al’adu ko tsoro, ko kuma halayen da aka fahimta game da tsiron a karan kansa. Tumfafiya, na daga cikin tsirran da aka fi alaƙantawa da iskoki bisa ga manyan dalilai kamar haka:

  • Siffarta mai ban tsoro

Tumfafiya tana da manyan ganye masu kauri. A lokacin dare, Inuwarta tana yin duhu sosai, har wasu na cewa inuwar kan yi siffar mutum a cikin dare. Wannan yanayin na daga cikin abin da ke haifar wa mutane tsoron shukar tumfafiya, musamman a yankunan da mutane basu cika wucewa ba.

  • Muhallin da take fitowa

Sannan kaɗaicewar shukar, don yawanci ana samunta a gefen rafuka, ko a bakin ƙauyuka, ko kuma wuraren masu ƙarancin jama’a. Hausawa na ganin irin wannan wuri na iya zama mazaunin halittu, musamman masu cutarwa saboda shirun da muhallin yake da shi, har wani lokaci ma ana ba da shawarar kar a yanke ta da daddare, saboda tsoron kada a ɓata wa wani aljani gida.

Sannan darajar da hausawa da wasu ƙabilu suka ba tumfafiya ya sa suna dasa ta a bakin ƙofa don tsare gida daga mugun abu. Amma duka wannan hasashe ne da kuma imani irin na mutanen da. Amma kuma martabar tsiron cikin tsafi da magungunan margajiya ya ƙara haifar da ra’ayin cewar tana da alaƙa da iskoki, domin kuwa mafi yawancin masu ba da magungunan gargajiya suna amfani da ita a wurin ƙullawa ko kuma kwance sihiri.

A muhimmin bayani na kimiyya kuwa tumfafiya ba ta da wata alaƙa da aljannu ko halittu masu cutarwa, ita ɗin tsiro ne  wanda ke da ingantattun sinadaran magani kamar flavonoids, tannins, saponins da sauransu. Don haka danganta tumfafiya da aljannu al’ada ce ta mutane kawai, ba gaskiyar kimiyya ba.

Illolin tumfafiya

Duk da amfanin tumfafiya, ta wani ɓangaren kuma tana ɗauke da sinadaran da ke da ƙarfi sosai, don haka, farin ruwan jikinta na iya ƙona fata ko sa ƙaiƙayi idan aka shafa ba bisa ƙa’ida ba. Sannan shan ruwan tumfafiya na iya haifar da illa mai tsanani da suka haɗa da bugun zuciya, amai, tashin zuciya.

Bai kamata mata masu ciki su yi amfani da ita ba, domin tana iya kawo matsala ga jaririn da suke ɗauke da shi.

Sannan yara ma bai kamata su taɓa ruwan ko cirar tumfafiya ta ba tare da kulawa ba. Har ila yau, a kiyaye ɗiga ruwan a ido, baki da kunne.

Manazarta

Calotropis procera – Useful Tropical Plants. (n.d.).

Calotropis procera. (n.d.). Fact Sheet Fusion V2.

Calotropis (Calotropis procera) | Feedipedia. (n.d.).

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×