Skip to content

Twilight Saga

Twilight, jerin littattafan soyayya ne guda huɗu wanda marubuciya Stephenie Meyer ta rubuta. An saki jerin littattafan a tsakanin shekarun 2005 zuwa 2008, littattafan sun bayyana jaruma Isabella Swan, yadda take ƙaunar Edward Cullen. Dukkan jerin littattafan guda huɗun an juya su zuwa fina-finai masu ban mamaki waɗanda Kristen Stewart da Robert Pattinson suka tsara.

Twilight ya shiga hannun miliyoyin masu karatu tun lokacin da aka buga shi a cikin 2005 kuma an sake masa fasalin nau’ikan adabi, don matasa da kuma ƙarfafa wani sabon abu wanda ya sa masu karatu ke son cigaban labarin. Twilight yana daya daga cikin litattafan da aka fi ambata a shekarar 2005 kuma a cikin makonni bayan fitowar littafin ya kasance a cikin jerin littafai biyar da aka fi saya a jadawalin New York Times.

Twilight, na marubuciya Mayer.

Cigaban labarin, wato ‘New Moon’, an sake shi a watan Satumba na 2006 kuma ya shafe makonni 31 a matsayi na ɗaya a kan jerin littafai mafi sayuwa na a dai jadawalin New York Times ɗin. ‘Eclipse’, shi ne littafi na uku a cikin jerin littafan, an fitar da shi a ranar 7 ga Agusta, 2007 kuma an sayar da kwafi 150,000 a ranar farko da aka fara kasuwancinsa. Littafin  kuma ya fito a jerin waɗanda aka fi saya a matsayi na ɗaya, a duk faɗin ƙasar Amurka. Littafi na huɗu kuma na ƙarshe a cikin kundin Twilight Saga, shi ne ‘Breaking Dawn’, an buga shi a ranar 2 ga Agusta, 2008, a bugu na farko an wallafa kwafi miliyan 3.2. Wanda shi ne bugu na farko mafi yawa a tarihin maɗaba’ar. An kuma sayar da kwafi miliyan 1.3 a ranar farko da aka ƙaddamar da kasuwancinsa.

Twilight, a jimlace gabaɗaya littafai huɗun, an sayar da kwafi sama da miliyan 160, an kuma fassara shi zuwa harsuna daban-daban har guda 37, kamar yadda ya zo a shafin Wikipedia.

A watan Nuwambar shekarar 2011, an  sayar da fiye da kwafi miliyan 120 a duk duniya tare da ƙarin fassara zuwa aƙalla harsuna 38 daban-daban na duniya. Littattafan Twilight guda sun shiga tarihin litattafai mafi sayuwa a shekarar 2008, a jadawalin ‘the USA Today Best-Selling Books, kuma sun shafe sama da makonni 235, a jadawalin ‘the New York Times Best Seller list for Children’s Series Books.

A cewar Meyer, jigon Twilight ya zo mata a cikin mafarki a ranar 2 ga Yuni, 2003, game da yarinya da kuma fatalwa wadda take ƙauna amma fatalwar tana kishirwar jininta. Bisa ga wannan mafarki, Meyer ta rubuta daftarin abin da labarin zai ƙunsa, wanda shi ne ya zama babi goma sha uku 13 na littafin.

Ta dauki rubutun daga babi na 13 zuwa ƙarshen littafin, sannan ta ɗauko daga babi na 12 zuwa na farko, a asirce, ba tare da tunanin samun makaranta ba ko kuma niyyar buga shi. Meyer ta yi bincike game da ‘yan asalin ƙabilar Quileute na Amurka, don ta saka al’adunsu a cikin littafin. Abin da ya sa wasu ‘yan kabilar suke ganin hakan kamar cin fuska ne.

Wasu daga cikin muhimman jigogin

Sadaukarwa

Edward ya sadaukar da komai don ya kasance tare da Bella. Ya faru a wurare da yawa, Edward ya yi ƙoƙarin fifita jin daɗin Bella a kan nasa. Ita ma Bella ta ba da kusan komai nata don kasancewa tare da Edward. Tana son Edward ya mayar da ita ta zama ‘yar lelensa domin su kasance tare har ƙarshen rayuwa.

Haɗarin soyayya

Bella da Edward sun faɗa cikin matsananciyar soyayya, Edward na iya zaucewa muddin Bella ta mutu. Ga Bella kuwa, soyayya ta zama jaraba. Ko da lokacin da suka fara samun tangarɗa, Bella ba za ta iya rabuwa da Edward ba.

Jerin littattafan a taƙaice

1. Twilight

Twilight ya samu kyakkyawan aiki. Wasu daga cikin makaranta sun yaba da nagartar littafin tare kuma da siffanta shi a matsayin mai taɓa zuciyar samari. Wasu kuma sun soki shi kuma sun yi tababar cewa labarin ba shi da wata nagartar a zo a gani. Ya kai matsayi biyar a jerin littattafan da aka fi saye a jadawalin New York Times a cikin wata guda da fitowarsa, kuma daga ƙarshe ya dawo matsayi na farko.

Twilight shi ne littafi na farko a jerin Littafai guda huɗu da marubuciya Stephenie Mayer ta rubuta.

2. New Moon

New Moon, labari ne mai ban sha’awa da ya fita a 2006. Kashi na biyu a cikin jerin Twilight Saga, littafin ya ci gaba da labarin Bella Swan da dangantakarta da Edward Cullen, lokacin da ta shiga babbar sakandare. Lokacin da Edward ya bar Bella bayan ɗan’uwansa ya kai mata hari, ta kasance cikin ɓacin rai da baƙin ciki na tsawon watanni har sai da Jacob Black ya zama babban amininta. Duk da haka, rayuwarta ta sake juyawa lokacin da yanayin Jacob ya bayyana.

New Moon shi ne littafi na biyu da marubuciyar ta rubuta wanda ya kasance cigaban na farko ne.

3. Eclipse

Eclipse shi ne labari na uku a cikin jerin Twilight Saga na Stephenie Meyer. Ya ci gaba da kawo labarin Bella Swan da soyayyar Edward Cullen. Littafin ya bayyano sasantawar Bella tsakaninta da soyayyar Edward da kuma abokantakarta da Jacob Black.

Eclipse shi ne littafi na uku a jerin kundin Twilight Saga.

4. Breaking Down

Breaking Dawn, shi ne labari na huɗu wanda ya fita a 2008 a cikin jerin Twilight Saga. An raba shi kashi uku, kashi na farko da na uku an rubuta su ne ta fuskar Bella Swan, kashi na biyu kuma an rubuta shi ta fuskar Jacob Black. Littafin ya bi diddigin abubuwan da suka faru a littafin da ya gabata, wato Eclipse, yayin da Bella da Edward Cullen suka yi aure, suka bar Jacob da raɗaɗi.

Breaking Down, shi ne littafi na huɗu kuma na ƙarshe a jerin kundin Twilight Saga na marubuciya Mayer.

Ra’ayoyin wasu makaranta littattafan

Wasu daga cikin mutanen da suka karanta littattafan sun tofa albarkacin bakinsu, a kafar Goodreads kamar haka:

Sarah

“Dole ta sa na nemi wannan littafi saboda duk abin da ake yayatawa na ji sun shafi bangarorin da na fi so. Kuma mutane da yawa sun ba ni shawarar na karanta shi. Ni babbar mai son labaran soyayya ce da kuma jarumtaka da abin tsoro, don haka lokacin da na fara jin labarin littafin, na yi matuƙar farinciki da son karanta shi domin ya haɗa abubuwan da na fi so. Amma, na yi nadamar sayansa da tilasta wa kaina in gama karanta shi, ina jin haushi idan ina karanta littafi ya zo ƙarshe. Ina ɗaya daga cikin mutanen da suke son abubuwan da suka shahara, Twilight ya shahara, don haka ina son shi kwarai.”

Shannon

“Wannan littafi, a gare ni, kamar alawar cakuleti ce: mai dadi. Bari in faɗi a sarari cewa, ni mai sha’awar soyayya ne, musamman ma mai tsanani, mai sha’awa, mai ban tausayi. Ba na karanta littattafan soyayya, domin a gare ni ba su da kwarjini. Littafin Meyer yana da ƙarin wani abu da nake buƙata.”

Khanh

“Ku kira ni mahaukaci, amma Twilight bai yi muni ba. To, idan ma yana da muni amma bai yi tsanani ba. Abubuwan da suka biyo baya sun kasance masu ban tsoro, amma littafin farko ba shi ne mafi munin abin da na taɓa karantawa ba. Na karanta mafi muni a baya. Zan karanta mafi muni a nan gaba. Na karanta littattafan da so a ce takarda ce don in liƙe ta a jikin ɗaki na riƙa kallo yayin da nake fushi.”

Kai Spellmeier

“Duk da yake ina son wannan littafi, sau ɗaya a lokaci guda kuma har yanzu ina da tabo mai sauƙi a dalilinsa. Ina kuma so in gane cewa labarin soyayya a tsakiyarsa mai ɗaci ne, kuma yana ƙara yin muni a gaba. Meyer ta sha zargi a wajena sakamakon yin amfani da al’adun Quileute, haka ma na ji haushi game da wariyar launin fatar da ta nuna lokacin da ta hana daraktan fim din farko saka duk wanda ba fari ba.”

Bayanin littafan a taƙaice

Marubuciya: Stephenie Meyer Morgan

Kundi: Twilight Saga

Matsayin labarin: Ƙirƙirarre

Maɗaba’a: Little, Brown and Company

Kwanan watan ɗab’i:

  • Twilight – 1 ga Oktoba, 2005
  • New Moon –  Satumba 2006
  • Eclipse – 7 ga Agusta, 2007
  • Breaking Down – 2 ga Agusta, 2008

Adadin shafuka:

  • Twilight – 498
  • New Moon – 629
  • Eclipse – 563
  • Breaking Down – 756

Tsara bango:

  • Gail Doobinin (design)
  • John Grant (photograph)

Lambar ISBN:

  • Twilight –              978-0-316-16017-9
  • New Moon –         978-0-316-16020-9
  • Eclipse –               0-316-16019-9
  • Breaking Down – 0-316-06792-X

Kyautukan da labarin ya samu

  • Georgia Peach Book Award (2007)
  • Buxtehuder Bulle (2006)
  • Kentucky Bluegrass Award for 9-12 (2007)
  • Prijs van de Kinder- en Jeugdjury Vlaanderen (2008)
  • Books I Loved Best Yearly (BILBY) Awards for Older Readers (2009)
  • West Australian Young Readers’ Book Award (WAYRBA) for Older Readers (2008)
  • Garden State Book Award for Fiction (Grades 9-12) (2008)
  • South Carolina Book Award for Young Adult Book Award (2008)
  • Grand Canyon Reader Award for Teen Book (2008)
  • Maryland Black-Eyed Susan Book Award for High School (2008)
  • Golden Sower Award for Young Adult (2009)
  • Nevada Young Readers’ Award for Young Adult Category (2007)
  • The Flume: New Hampshire Teen Reader’s Choice Award (2007)
  • Pennsylvania Young Readers’ Choice Award for Young Adult (2009)
  • Rhode Island Teen Book Award (2007)
  • Evergreen Teen Book Award (2008)
  • Michigan Library Association Thumbs Up! Award Nominee (2006)
  • Teen Read Award Nominee for Best All-Time-Fave (2010)
  • Deutscher Jugendliteraturpreis Nominee for Preis der Jugendjury (2007)
  • Iowa High School Book Award (2008)
  • Eliot Rosewater Indiana High School Book Award (2008)
  • Lincoln Award (2008)
  • Literaturpreis der Jury der jungen Leser for Cover (2007)
  • Prix Et-lisez-moi (2008)
  • Gateway Readers Award (2008)

Taurarin cikin labarin

• Edward Cullen
• Jacob Black
• Laurent
• Renee
• Bella Swan
• Billy Black
• Esme Cullen
• Alice Cullen
• Jasper Hale
• Carlisle Cullen
• Emmett Cullen
• Rosalie Hale
• Charlie Swan
• Mike Newton
• Jessica Stanley
• Angela Weber
• Tyler Crowley

Taƙaitaccen tarihin marubuciyar

Stephenie Meyer, an haife ta a watan Disamba 24, 1973. Marubuciya ‘yar ƙasa Amurka ce, ta yi fice da sanannen kundin littafanta mai suna ‘Twilight Saga,’ jerin litattafai ne guda huɗu masu jigon soyayya mafi akasari ga matasa.

Stephanie Mayer Morgan, marubuciya ‘yar ƙasa Amurka.

Meyer, wacce ta tashi a Phoenix, Arizona, ta sami tallafin karatu na ƙasa da ƙasa kuma ta halarci Jami’ar Brigham Young, inda ta kammala karatun digiri a shekarar (1997) a fannin adabin Ingilishi. Ta yi aure a shekara ta 1994, tana da ‘ya’yanta maza uku, kamar yadda ta bayyana a tarihin rayuwarta, a shafinta na yanar gizo.

Meyer ta shiga Ƙungiyar American Night Writers Association (ANWA) don da haɗuwa da marubuta mata na LDS. Ta kammala rubuta littafin cikin wata uku. Sai ‘yar’uwarta ta karanta littafin ta ga cewa ya yi daɗi kuma ya yi ma’ana. A ƙarshe ta ba wa Meyer shawara da ta aika da littafin ga hukumomin adabi don a duba mata.

Ita ce marubuciya mafi samun cinikin lattafai ta shekarar 2008 da 2009 a cikin Amurka, ta sayar da littattafai sama da miliyan 29 a cikin shekarar 2008 da kuma miliyan 26.5 a cikin shekarar 2009. Ta sami lambar yabo ta ‘2009 Children’s Book of the Year’ daga British Book Awards a kan littafi ‘Breaking Dawn’, wanda ya kasance na ƙarshe a jerin littattafan kundin Twilight.

Manazarta

Bio | Stephenie Meyer. (n.d.).

Twilight (The Twilight Saga, #1). (n.d.). Goodreads.

Wikipedia contributors. (2024, September 16). Twilight (novel series). Wikipedia.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×