Skip to content

Ungozoma

    Aika

    Ungozoma wata mace ce, wadda ta kasance mai sani ko kuma ƙwarariya wurin gudanar da aikin kula da lafiyar uwa da kuma jariri kafin haihuwa, da lokacin haihuwa da kuma bayan haihuwar har zuwa raino da shayarwa. A wasu lokutan har ma da yanayin tarbiya da girman yaro da kuma matakan da ake bi yayin kulawa da shi a kowacee gaɓa ta rayuwarsa.

    114144304 f77a83e2 0fab 4224 b2aa 9edaa58a1f03
    Ungozoma a bakin aiki

    An samu bayanai mabambanta da dama game da ma’anar Ungozoma: Wasu bayanan sun tabbatar da ma’anar Ungozoma a matsayin mace tsohuwa wacce take kula da mai haihuwa. Musamman a lokacin da naƙuda ta kamata. Kuma ita ce a wasu shiyoyin suke kiranta da “ARBIKA”.

    Ungozoma wata mace ce tsohuwa da ta goge matuƙa a fannin tattalin jariri da agazar mai haihuwa.

    A harshan Hausa Ungozoma na nufin “mace tsohuwa”. Wasu kuma suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga “ungo-tsoma “. Dalili shi ne Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya ta faɗo, to sai a ɗaukota, a fito da ita waje ta miƙa wa masu taimaka mata, ta ce da su “ungo-tsoma ” A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne saboda yawan faɗar kalmar “ungo-tsoma “. Sai ta koma ungotsoma. “Ungozoma “

    A taƙaice Ungozoma macece tsohuwa ko babba. Wacce ta yi haife -haife ta goge da matsalolin haihuwa da rainon jariri da biƙi, kana kuma ta san magunguna. Amma fa wajen karɓar haihuwa ba dole sai tsohuwa ba, sai dai ana buƙatarta saboda ƙwarewa , da juriya, da tausayi, da kuma nutsuwa. Domin su ne waɗanda suka ga jiya kuma suka ga yau.

    Rabe-raben ungozoma

    • Ungozomar Gado
    • Ungozomar Sana’a
    • Ungozomar Dangi
    • Ungozomar Masarauta
    • Ungozomar Ɗauki-ajiye

    Ilmin ungozoma

    Ilimi da horarwar ungozoma gaba ɗaya ya shafi ɓangaren mata ne a tsayin rayuwarsu. Wurin mayar da hankali su zama ƙwararru wajen gano hali da kuma yanayin da mai haihuwa take ciki ko kuma mai goyon ciki har zuwa shayarwa. A jiya da yau gaba ɗaya akan wannan tsari ake tafiya.

    Yawanci a wasu ƙasashen, ana kallon Ungozoma a matsayin mai kula da kuma kiwon lafiya. Ana horar da Ungozoma domin a gane bambanci daga fara naƙuda lafiya yanda za su fahimci wasu matsaloli da ka iya tasowa.

    Ungozoma a jiya

    A jiya Ungozoma na karɓar aiyuka da yawa ta fanin da suka shafi duk wata al’ala ta haihuwa zuwa raino da kuma goyon ciki. Idana aka ce amarya ko kuwa uwa na ɗauke da ciki Ungozomar dake wannan unguwa ita ce za ta dinga kula da yanayinta tun daga kan cimarta da kuma yanayin kazarniyarta da abubuwan da ya kamata ta yi har zuwa ranar haihuwarta.

    Tarihin ungozanci

    Tarihin ungozanci ya faro ne daga al’adar gargajiya, inda aka dogara da tsofaffin mata masu ƙwarewa wajen taimakawa masu haihuwa, zuwa lokacin mulkin mallaka inda aka shigo da tsarin kimiyya da matakan kula da tsafta, har zuwa yau da ungozanci ya koma babban fanni na ilimi da kimiyya. Wannan ci gaba ya nuna yadda aikin ya samo asali daga al’ada zuwa matakin da ake ganin shi a matsayin ginshiƙi na kula da lafiyar uwa da jariri a duniya.

    Ungozanci a al’adar Hausawa da sauran al’ummomin Afirka ya daɗe da kasancewa wani muhimmin ginshiƙi na rayuwa. Kafin zuwan tsarin kiwon lafiya na asibiti, mata masu ciki suna dogaro da ungozoma ta gargajiya, wacce ita ce tsohuwa ko mace mai ƙwarewa a cikin al’umma da ta gaji ilimin daga kakanni ko ta koyi ta hanyar yin hidimta wa masu ciki da masu haihuwa. Ungozoma ta gargajiya ita ce mai lura da mace tun daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa lokacin haihuwa, sannan kuma ta ci gaba da lura da lafiyar uwa da jariri bayan haihuwa.

    A wancan zamani, kulawa da uwa da jariri ta ta’allaka ne da amfani da hanyoyin gargajiya irin su magungunan ganye, addu’o’i, da wasu al’adu na musamman da ake ɗauka suna kawo sauƙi. Ana ba wa mace shawarwari kan abinci mai lafiya, tsafta, da kuma yin wasu ayyuka na musamman don sauƙaƙa haihuwa. Lokacin haihuwa, ungozoma ta gargajiya ita ce ke karɓar jariri ta hanyar amfani da kayan gargajiya kamar aska ko reza tsinke wajen yanke cibiyar jariri, sannan ta kula da uwa da jariri ta hanyar yi musu wanka, tofe-tofe, da kuma lura da lafiyarsu har sai sun dawo cikin ƙoshin lafiya.

    Ungozoma ta gargajiya tana da matsayi mai girma a cikin al’umma. Ba kawai mai taimakawa wajen haihuwa ba ce, har ma tana kasancewa mai ba da shawara kan sha’anin aure, haihuwa da tarbiyyar yara. A wasu lokuta kuma, ana haɗa aikin ungozanci da addini ta hanyar yin addu’o’i, ruqya, da wasu al’adun gargajiya da ake ɗauka suna ƙara albarka ga uwa da jariri.

    Ungozanci a zamanin Mulkin Mallaka

    Shigowar Turawan mulkin mallaka ya kawo canji sosai ga aikin ungozanci. A ƙarni na 19 da na 20, Turawa suka kafa cibiyoyin kiwon lafiya da asibitoci a manyan birane, sannan daga baya suka buɗe makarantu na koyar da aikin jinya da kuma ungozanci. Wannan mataki ya fara sauya tsarin ungozanci daga gargajiya zuwa tsarin kimiyya.

    A wacnan lokaci, an shigo da sabbin hanyoyi na tsafta da ilimin kimiyya wajen kula da mace mai ciki da jariri. Mata suka fara samun horo a makarantu na musamman don su zama ungozoma na zamani, inda aka mayar da hankali kan tsafta, amfani da kayan aikin lafiya masu tsabta, da kuma hana mace haihuwa a gida ba tare da kulawar likita ko ungozoma mai horo ba.

    Sai dai kuma, mutane da farko ba su gamsu da wannan tsarin ba saboda dogaro da gargajiya. Wasu matan sun fi yarda da tsofaffin ungozoma da suka saba da su, amma daga bisani, sakamakon wayar da kai da kuma nuna illolin rashin tsafta a lokacin haihuwa, mutane suka fara karkata zuwa ga asibitoci da tsarin ungozanci na zamani.

    Ungozanci a zamanance

    A yau ungozanci ya koma wani babban fanni na kimiyya wanda ake koyarwa a matakin diploma, digiri da kuma babbar shaida a jami’o’i. An kafa dokoki da ƙungiyoyi da ke lura da aikin, kamar Nursing and Midwifery Council of Nigeria (NMCN) a Najeriya, wacce ke tabbatar da ingancin horo da aikin ungozoma.

    Ungozoma ta zamani tana amfani da na’urorin bincike kamar ultrasound wajen duban lafiyar jariri da uwa, tana kuma bin tsare-tsaren kiwon lafiya na gwamnati da na ƙasa da ƙasa domin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai. An ƙara wayar da kan al’umma kan muhimmancin zuwa asibiti domin samun kulawar ƙwararru kafin haihuwa, lokacin haihuwa da bayan haihuwa.

    Haka kuma, ƙungiyoyin duniya irin su World Health Organization (WHO) da International Confederation of Midwives (ICM) suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa aikin ungozanci a duniya. A Najeriya, ana gudanar da shirye-shiryen wayar da kai, samar da kayan aiki, da kuma horas da ungozoma don tabbatar da cewa kowace mace mai ciki tana samun ingantacciyar kulawa.

    Muhimman sassan ungozanci


    • Ungozancin ciki (Antenatal Midwifery)


    Wannan shi ne ɓangaren aikin ungozanci da ya shafi kulawa da mace tun daga lokacin da ta ɗauki ciki har zuwa lokacin da za ta haihu. A wannan mataki, ungozoma tana lura da lafiyar mace da jariri, tana yin gwaje-gwaje don tabbatar da cewa babu wata matsala da za ta iya kawo haɗari. Haka kuma, ungozoma tana ba wa mace shawarwari kan abincin da ya dace ta ci, guje wa ayyukan da za su iya cutar da ita ko jaririn, da kuma kula da tsafta. Wannan kulawa tana taimakawa wajen gano matsalolin da za su iya tasowa da wuri kamar ciwon sikari, hawan jini ko rashin abinci mai gina jiki.


    • Ungozancin haihuwa (Intrapartum Midwifery)


    Wannan ɓangare shi ne mafi muhimmanci a aikin ungozoma, domin yana shafar lokacin da mace za ta haifi jariri. A nan, ungozoma tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa mace ta haihu lafiya, ta kula da yadda jariri ke sauka, ta tabbatar da tsafta a wajen haihuwa, kuma ta taimaka wajen rage wahalar da mace ke ji. Idan akwai matsala a lokacin haihuwa, ungozoma mai horo tana da kwarewar gano haɗarin da zai iya barazana ga uwa ko jariri, sannan ta yi matakan gaggawa ko ta kira likita. Wannan bangare na buƙatar haƙuri, ƙwarewa, da saurin yanke shawara.


    • Ungozancin bayan haihuwa (Postnatal Midwifery)


    Bayan mace ta haihu, akwai buƙatar kulawa sosai domin lafiyarta da ta jaririnta su tabbata cikin ƙoshin lafiya. A wannan mataki, ungozoma tana taimaka wa mace wajen dawo da ƙarfinta, tana lura da jinin da yake fita daga jikinta, tana kuma kula da riga-kafin kamuwa da cututtuka. Ungozoma tana ba wa uwa shawarwari kan shayar da jariri nono, tsafta, da kuma yadda za ta kula da kanta da jaririnta. Haka kuma, tana bincika jariri domin gano matsaloli da wuri kamar ƙarancin nauyi, matsalolin numfashi ko cututtuka.


    • Ungozancin lafiyar iyali (Family Health Midwifery)


    Aikin ungozanci bai tsaya ga lokacin ciki da haihuwa kawai ba, yana kuma da alaka da lafiyar iyali gabaɗaya. A wannan ɓangare, ungozoma tana ba da shawarwari kan tsare-tsaren haihuwa, wato yadda iyali za su tsara yawan ’ya’yansu domin samun ingantacciyar lafiya da rayuwa mai ma’ana. Haka kuma, tana wayar da kan mata da maza game da muhimmancin yin riga-kafi, kula tsafta a cikin gida, da kuma yadda za a kula da lafiyar yara. Wannan ɓangare na ungozanci yana da muhimmanci musamman a ƙasashe masu yawan jama’a da kuma matsalolin tattalin arziki.

    Amfani da dabaru wurin kula da lafiyar abin da ke ciki. Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa da makamantarsu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani ɗan ƙaramin ƙoƙo wajan gyara shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauƙi.

    Wani muhimmin aikin shi ne: Ungozoma za ta yi ta kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai ɗaci, da kuma bata magungunan rage zaƙi, da kuma samun ƙarin ƙarfin jiki. Kamar su,

    • Bubukuwa
    • Saiwar kalumbo
    • Gadon-macijiFarin zoɓo
    • Sassaƙen mangawaro

    Gudummawar ungozoma

    A al’adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci ƙwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Ƙauye ko Gari ko Unguwa Inda jama’a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Rijiya ko Rafi don buƙatar rayuwa.

    Saboda muhimmancin Ungozoma a al’umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa,

    “Ungozoma kin fi mai ɗa son ɗa “.

    Haka har cikin karin magana an ambaci Ungozoma, misali :

    “Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu “. Da kuma,

    “Ai ba a ƙare haihuwa ba an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu”.

    Ire-iren wannan kan sake fito da martabar Ungozoma da kuma amfaninta a rayuwar al’umma tun daga kan jiya da kuma yau.

    Ungozoma wani jigo ce a rayuwar kowa ce al’umma domin suna taka muhimmiyar rawa wurin kula da lafiya. Suna iya shiga cikin kasada wajen matsaloli kamar su;

    • Katsewar haihuwa
    • Haihuwar Tagwaye
    • Jinkirin faɗowar mabiyiya wato mahaifa wurin haihuwa.

    Ƙasashe da dama da suka samu cigaba suna ware kuɗaɗen domin horar da mata su zama Ungozomomi, daga darajar matan da dama sun daɗe suna karɓar haihuwa a gargajiyance.

    A wani bincike da shafin Aminiya ya gabatar ya tabbatar da cewa, samun yawaitar Ungozoma ya rage mace-macen mata yayin haihuwa.

    Matsalolin ungozoma

    Wasu daga cikin Ungozoma suna da matsala, musamman waɗanda suke karambanin karɓar haihuwa a gida. Hakan kan haifar da matsala ga uwa ko kuma jaririn da ta haifa idan aka samu akasi. Matsalolin sun haɗar da;

    • Yin aikin da ya fi ƙarfinsu: Matsalolin da suka ƙunshi ciki da haihuwa wanda suka gagari ilimin Ungozoma yayin da haihuwa ta yi gaddama maimakon su miƙa su ga babban likita sai su yi ta naci wurin gwada ƙoƙarinsu.
    • Hantara ko kuma kyarar masu haihuwa: Da yawa wasu daga cikin Ungozoma na kyarar masu haihuwa. Wanda mai haihuwa abin da ta fu buƙata shi ne kulawa da lalashi da kuma ƙarfafa guiwa.
    • Saurin fushi: Ana samun hakan musamman a ƙananun asibitocin da suka haɗa yaran da suka karanci abin kuma suke da ƙarancin shekaru, wanda hakan kan kawo saɓanin mai haihuwa da mai karɓa.

    Manazarta

    Mustapha, O. (2016, April 15). Samar Da Kwararrun Ungozomomi Ya Rage Mace-mace Mata. Aminiya.

    L, A. (2020, December 8). Matsayin ungozoma wajen haihuwa. Madres Hoy.

    Rarah, J. S. (n.d.). UNGUZOMA (MIDWIVES).

    Tarihin Wallafa Maƙalar

    An kuma sabunta ta 21 September, 2025

    Sharuɗɗan Editoci

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×