Skip to content

Uwar Gulma

Uwar Gulma wani shahararren littafin Hausa ne, wanda ya ƙunshi wasan kwaikwaiyo rubutacce. Littafin ya shahara a matakan ilimi daban-daban, kama daga kan makarantun firamare har zuwa matakin sakandire har ma manyan makarantun kwalejoji musamman a Arewacin Najeriya. Littafin ya shafi abin da ya danganci zamantakewa ta rayuwar gidan malam Bahaushe ta yau da kullum ta fuskar bayyana wasu lamura da suke gudana a rayuwar zamantakewa.

Littafin wasan kwaikwayon Uwar Gulma, wanda marubuci Muhammad Sada ya rubuta.

Littafin ya samun karɓuwa sosai da sosai, domin sai da ya kasance babu makarantun da ba a karanta shi daga makarantun gwamnati har masu zaman-kansu a matakin koyarwa. Kuma akwai ma’abota bincike da dama da suka yi rubutu a game da littafin tare da fito da abubuwan da suka shafi littafin masu muhimmanci.

Muhimman jigon labarin

Babban jigon littafin Uwar Gulma jigo ne da ya shafi zamantakewa, sai dai kuma akwai wasu muhimman jigogin da suka kasance a cikinsa waɗanda suka taka rawa wurin ƙayatar da labarin ta fuskoki mabambanta. Wanda aka yi amfani da hikima da kuma zalaƙa wurin tabbatar da shiryuwarsu a kan tsari. Muhimman jigoginn sun haɗar da:

  • Gulma
  • Rashin haƙuri
  • Dillanci
  • Shaye-Shaye
  • Cin hanci

Ƙananun jigo a labarin

Duk da cewa littafin Uwar Gulma ya mallaki manyan jigogi masu armashi da kuma tsuma zuciyar mai karatu. Amma kuma hakan bai hana shi mallakar ƙananun jigogi ba. Waɗanda suka kasance sun taimaka wa tafiyar manyan har labarin ya cim ma manufar da yake son cimmawa. Ƙananun jigogin da suke cikin labarin sun haɗar da:

  • Munafurci
  • Rashin martaba miji
  • Rashin kawaici
  • Rashin kunya
  • Rashin ɓoye sirrin gidan aure
  • Rashin bincike
  • Karuwanci

Bayanin littafin a taƙaice

Marubuci: Muhammad Sada

Shekarar wallafa: 1968

Adadin shafuka: 13 a bugun farko

Sabuntawa: 1971, 1974, 1975, 1980, 1984, 2004, 2007 da 2010.

Lambar ISBN: 978-978-169-159-1.

Ra’ayoyin masu karatu

Akwai ra’ayoyin mabambanta da dama waɗanda suka yi batutuwa a kan littafin Uwar Gulma. Ra’ayoyin sun haɗar da:

Hajara Ahmad Maidoya

“Na ji ma ban karanta littafin da ya zauna a kaina ba sama da littafin Uwar Gulma. Domin abu ne da aka karanta tun ana zangon yarinta har zuwa girma. Tun ana karanta mana har muka soma karantawa da kanmu. Gaskiyar magana littafin yana cikin littafan da suke nishaɗantar da ni, domin akwai darrusan ƙaruwa cikinsa uwa-uba kuma akwai abubuwan da suke haska mana yadda zamantakewarmu ya kamata ta kasance da kuma yadda ya kamata iyaye su kula da gidan auren ‘ya’yansu.”

Kamal Muhammad Lawan

“Littafin Uwar Gulma littafi ne da ya jima yana ba ni nishaɗi, tun muna yara ake karanta mana shi, tun muna saurara kawai domin daɗin labari har ta kai mun soma fahimtar ai ba labari ake ba mu ba darasin rayuwa ake koya mana. Shi ne littafin da na fara karantawa da kaina a tsaye gaban allo cikin ‘yan uwan ɗalibai kuma na koyi abubuwa da dama cikin litrafin Uwar Gulma.”

Sumayya Tijjani Nasir

“Idan ka ɗauke littafin Magana Jari ce da kuma su Ruwan Bagaja, to babu littafin da ya samu karɓuwar da littafin Uwar Gulma ya samu a wajena. Domin yara da yawa suna ɗokin a karanta musu shi, littafin ya fito da darusan rayuwa da dama. Sannan wani abu mai armashi duk da littafin na cike da ɓarna wadda ta danganci irin su shaye-shaye da gidan karuwai da kuma almundahana wurin gudanar Shari’a uwa uba kuma gulma da kitimurmura irin ta mata. Amma marubucin ya yi amfani da hikima ya tsara labarin tare da fito da komai ba tare da yin amfani da batsa ba. Wanda hakan ya sake tabbatar da cewa marubucin ya san kansa ya kuma san abin da ya kamata. Ba zan mance lokacin da muke yara ba har murna muke malamin darasin Hausa ya shigo saboda a karanta mana Uwar Gulma. Har wata waƙa muke yi wai ita: Halima Hayyatu Uwargulma.”

Taƙaitaccen tarihin marubucin

Marubucin littafin shi ne Alhaji Alhaji Muhammed Sada, ya kasance marubuci kuma masanin harshen Hausa. Marubucin haifaffen garin Katsina ne a ƙaramar hukumar Kankiya. Duk da kasancewar littafin ya kasance rubutu na farko da ya wallafa, har zuwa wannan lokaci babu wani takamaiman bayani kan cewar marubucin ya rubuta wani labari bayan shi amma hakan ba ya hana a saka shi cikin lissafin marubuta na gaba-gaba musamman idan ana bayar da labarin marubutan da suka gabata da kuma litattafansu.

Manazarta

Alhaji Muhammad Sada – Wikipedia. (n.d.). Muhammad Sada

Uwar Gulma. (n.d.). Uwar Gulma Google Books.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×