Wizard’s First Rule, littafi ne wanda Terry Goodkind ya rubuta, shi ne littafi na farko a cikin jerin littafan da aka fitar a Tor Fantasy, a cikin kundin nan na almara mai taken The Sword of Truth. An buga littafin a shekara ta 1994. Ya kuma shiga kasuwa a cikin watan Satumba, 1995. An kuma sake fitar da littafin tare da sabunta zanen bangon, wanda Keith Parkinson ya yi a ranar 23 ga Yuni, 2001.
Bugu da ƙari, littafin an sanya shi cikin jerin shirye-shiryen drama na zango-zango wanda ake aiwatarwa a talabijin, da ake kira Legend of the Seeker, wanda aka fara a ranar 1 ga Nuwamba, shekara ta 2008, kuma ya gudana har tsawon zango biyu, inda ya ƙare a watan Mayu, 2010.
Kundin da littafin Wizard’s First Rule ya faɗa a ciki, an sayar da kwafi miliyan 25 a duk faɗin duniya kuma an fassara shi zuwa fiye da harsuna 20.
Bayanin littafin a taƙaice
– Mawallafi: Terry Goodkind
– Karantawa a audio: Sam Tsoutsouvas
– Tsara bango: Keith Parkinson da Doug Beekman
– Harshe: Ingilishi
– Kundi: The Sword Of The Truth
– Maɗaba’a: Tor Books
– Kwanan watan ɗab’i: 15 ga Agusta, 1994
– Sabuntawa: 23 ga Yuni, 2001
– Wajen wallafa: Amurka
– Adadin shafuka: 836
– Lamabr littafi ta ƙasa da ƙasa (ISBN): (0-312-85705-5)
Ra’ayoyin makaranta littafin
Ga ra’ayoyin wasu daga cikin makaranta littafin, a wata manhajar wallafa littafai ta yanar gizo mai suna ‘subreddit’ inda a can ɗimbin mutane kan yi dafifi wajen karanta littafin. Ga kaɗan daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu;
• Willow Greentree
“Wannan littafi, da duk littattafan da ke biye suna ɗaya daga cikin mafi kyawun jerin littattafan da na taɓa karantawa.”
• KristinnK
“Duk da ƙiyayyar da nake yi wa wannan shafi na ‘subreddit’, daga ƙarshe na ba da kai bori ya hau ta hanyar yanke shawarar ba wa ‘Wizard’s First Rule’, na Terry Goodkind dama. Kuma ina farincikin sanar da cewa ina son littafin sosai kuma ina ba da shawara ga kowane mai karatu musamman ma masu son ‘classic fantasy’. Na ga cewa littafin yana da tsari mai kyau fiye da yawancin littattafan fantasy. Har ila yau, labari ne da tabbas za a iya karanta shi a yayin da ake cikin kaɗaici.”
• Gibberish5
“Na ji daɗin wannan Littafin, a lokacin da na karanta shi ina makarantar sakandare, amma na ci gaba da nazarin shi har sai da na buga littafin da jama’a ba su yi tsammani ba.”
• None Of Your Business
“OMG, na gano cewa ɗaya daga cikin marubutan da na fi so ya mutu! Wannan mummunan abu ne kuma mai ban tausayi. Na haɗu da Terry a shekara ta 1996, kuma na yi magana mai kyau da shi. Ya kasance mai karamci kuma babban mutum! Ko a yanzu, bayan shekaru da yawa na tuna da shi sarai. Na ba wa ‘yata wannan littafin wanda ya fi ta girma. Tana girmama kowane ɗayan littattafansa kuma ta mallake su duka. Tun daga lokacin da na haɗu da shi, har yanzu ban sake karanta ko ɗaya daga cikin littattafansa ba. Na gode sosai, Terry, domin ka sanya tunaninmu ya farka. Ka nishadantar kuma ka zaburar da mutane da yawa da littafanka masu motsa tunani.”
Yadda Bangon littafin yake
Zanen bangon da Keith Parkinson ya yi don bugu na farko, yana kwatanta Richard da Kahlan a wurin da aka yi muhawara da takamaiman bayani. An ba da shawarar cewa daidaita yanayin wurin da Richard da Kahlan suka hadu, Parkinson ya kwatanta abin da ya faru a gefen wani ruwa maimakon a kan hanyar tudu don kwatanta mahimmancin lokacin.
An kuma yi hasashen cewa wurin shi ne mafarkin Richard na daukar Kahlan don ganin duk wasu wurare na musamman da ya gano a cikin dazuzzukan Hartland.
Abin da ke cikin zanen Parkinson an yi shi da wayo. Matsayinsa a bangon littafin ya sa magudanar ruwa ta kai rabin layin, yayin da kan Richard shi ne tsakiyar cikakken zanen.
Kyautuka
Littafin ya samu nasara cin kyauta a shekara ta 1995, wato a gasar Locus Poll Award – Best First Novel – Inda ya zo a mataki na bakwai 7.
Game da mawallafin
Mawallafin littafin wato Terry Lee Goodkind, an haife shi a ranar 11 ga watan Janairun shekarar 1948. Ya rasu a watan Satumba 17, 2020. Marubuci Ba’amurke ne. Sananne ne a fagen rubutun almara da mamaki da labarai masu ban tsoro.
Manazarta
AudioFile Magazine. (n.d.) WIZARDS FIRST RULE by Terry Goodkind Read by Sam Tsoutsouvas Audiobook Review. AudioFile Magazine.
Wiki, C. T. S. O. T. (n.d.). Wizard’s first rule. Sword of Truth Wiki.
Wikipedia contributors. (2024b, July 18). Terry Goodkind. Wikipedia.