Zubar jini a lokacin juna biyu wani yanayi ne da yawanci ke tayar da hankalin mace mai ciki da iyalanta baki ɗaya. A al’ada, mace mai ɗauke da juna biyu ba ta fitar da jini, don haka duk lokacin da hakan ta faru, yana iya zama alamar wata matsala ko kuma rashin matsala, kawai ya danganta da irin yanayin da jinin ya zo. A wasu lokuta, musamman a watannin farko na ciki, zubar jini na iya zama abu na al’ada da ba ya da barazana ga lafiyar mace da jariri. Ta wani ɓangaren yana iya zama gargaɗi na matsalar lafiya ko hatsari ga cikin gaba ɗaya. Saboda haka, yana da matuƙar muhimmanci mace ta samu cikakken bayani kan bambancin zubar jinin da ba ya da matsala da kuma wanda ke iya nuni da matsala mai haɗari.
Zubar jini mai matsala da wanda ba ya da matsala
Kamar yadda ya gabata, zubar jini a lokacin juna biyu yana nufin fitowar jini ga macen da ke da ciki. Wannan yanayi na iya faruwa a farkon makonni na samuwar ciki, ko a tsakiyar ciki, ko kuma a ƙarshen ciki. Yawan jinin da ke fita da kuma yanayin fitowar jinin zai iya bambanta daga mace zuwa mace: wani lokacin zubar jinin kaɗan ne (spotting), wani lokacin kuma yana iya zama mai yawa sosai (heavy bleeding).
A mafi yawan lokuta, zubar jini kaɗan a farkon makonnin ciki ba matsala ba ne, musamman idan babu wasu alamomin rashin lafiya kamar ciwon ciki mai tsanani ko zazzaɓi. Sai dai kuma, zubar jini yana iya zama mai illa musamman idan ya zo da sauran matsaloli kamar jin ciwon mara mai tsanani, zazzaɓi, ko kasala sosai.
Saboda haka, yana da muhimmanci mace mai ciki ta kula da irin wannan yanayi, ta kuma nemi ganin likita idan akwai alamomin da suka fi ƙarfinta, don tabbatar da lafiya da kariyar jariri da kanta.
Haila a lokacin juna biyu. Masana sun sha samun tambaya a kan ko mace mai juna biyu tana yin jinin al’ada? Zance na gaskiya shi ne, Lokacin da mace take ɗauke da ciki, ba za ta ci gaba da fitar da ƙwan haihuwa ba, bare kuma har a zo ga batun jinin al’ada (haila).
Haila tana faruwa ne a lokacin da mace ba ta ɗauke da juna biyu. Don haka, idan mai juna biyu ta samu zubar jini yayin da take ɗauke da juna biyu, toh hakan ba yana nufin jinin al’ada ne ba.
Dalilan zubar jini lokacin juna biyu
Akwai manyan dalilai da ke iya janyo zubar jini yayin da mace ke da ciki. Waɗannan dalilai sun kasu kashi biyu, dalilai marasa haɗari da kuma dalilai masu haɗari.
Dalilai marasa haɗari
Implantation bleeding: A farkon makonni (kwanaki 10 zuwa 14 bayan ɗaukar ciki), ƙwayar ciki tana mannewa a mahaifa. Wannan na iya kawo ɗan zubar jini kaɗan wanda baya da haɗari.
- Canjin hormone (hormonal changes). Wasu lokuta, canjin hormones na cikin jikin mace zai iya janyo zubar jini kaɗan. Kuma akasari ya fi faruwa a first trimester (Watanni ukun farko na samuwar juna biyu)
- Ciwon mahaifa (cervical erosion). Idan mahaifa ta sami canji ko kumburi, hakan na iya sa zubar jini kaɗan.
- Jima’i (sexual intercourse). A lokacin ciki, mahaifa ta fi kauri kuma tana da sauƙin zubar jini bayan saduwa.
Dalilai masu haɗari
Ciki a wajen mahaifa (ectopic pregnancy). Wannan shi ne cikin da ya tsaya a wajen mahaifa, misali a bututun mahaifa (fallopian tube). Wannan yana da haɗari sosai kuma yana buƙatar kulawa ta gaggawa.
- Ɓari (miscarriage). Idan cikin ya zube kafin ya girma, yana iya janyo zubar jini mai yawa da ciwon ciki.
- Placenta previa (placenta ta rufe bakin mahaifa). Idan placenta ta manne a bakin mahaifa (cervix), hakan na iya kawo zubar jini ba tare da ciwo ba a tsakiyar ciki ko ƙarshen ciki.
- Placental abruption (placenta ta ɓalle daga mahaifa). Wannan yana faruwa idan placenta ta ɓalle daga bangon mahaifa kafin lokacin haihuwa. Zai iya kawo zubar jini mai yawa da ciwon mara mai tsanani.
- Infection: kamuwa da infection a mahaifa ko a gaban mace yana iya janyo zubar jini, musamman idan akwai kumburi ko ciwon infection.
- Multiple babies: Juna biyu mai ɗauke da jariri fiye da ɗaya, shi ma yana kawo zubar jini a lokacin juna biyu.
- Subchorionic hemorrhage: Zubar jinin da yake faruwa idan mabiyiya ta rabu da jikin mahaifa
Duka waɗannan dalilai ne da ke faruwa a farko, tsakiya da watannin ƙarshe na samuwar juna biyu, kuma suna haifar da zubar jini. A shawarce kuma shi ne, mai wannan lalura ta ga likita, domin tabbatar da lafiyarta da ta jaririnta.
Alamomin zubar jini a lokacin juna biyu
Kowace lalura tana da alamomin da ke bayyana samuwarta, tohaka zubar jini a lokacin juna biyu:
- Zubar Jini Kai Tsaye. Wannan shi ne ainihin zubar jinin da ake magana. Yana iya kasancewa ja mai haske ko mai duhu, kuma zai iya kasancewa kaɗan-kaɗan ko kuma mai zuba sosai.
- Ciwon Ciki (Cramping). Yana iya kasancewa kamar ciwon al’ada ko ciwon ciki mai tsanani. A wasu lokuta yana zuwa tare da zubar jinin.
- Rashin Lafiya ko Kasala (Fatigue). Jin kasala ko gajiya sosai fiye da yadda aka saba a juna biyu.
- Bugawar zuciya da sauri (Palpitations). Saboda asarar jini, zuciya na iya bugawa da sauri ko rashin kwanciyar hankali.
- Zazzaɓi (Fever) Idan akwai zazzaɓi, wannan na iya nuna cuta ko wani abu mai tsanani da ke buƙatar kulawa ta gaggawa.
- Sauran alamomi na kumburi ko jin sanyi misali: kumburin kafa, rashin jin daɗin jiki gaba ɗaya.
Haɗarin zubar jini a lokacin juna biyu
- Cutar ciki Ko fetus: Idan zubar jini yana da yawa, yana iya zama alamar matsalar ciki ko barazana ga fetus (Jaririn dake cikin mahaifa bayan makonni takwas da samuwar ciki.
- Barazanar zubewar iki : Zubar jini a farkon ciki (trimester na farko) na iya zama alamar barazanar zubar da ciki.
- Cutar Placenta: A cikin watanni na ƙarshe, zubar jini na iya zama alamar placenta previa (inda placenta ta rufe bakin mahaifa) ko placental abruption (inda placenta ta rabu da mahaifa kafin lokacin haihuwa).
- Infection ko Inflammation: Wani lokaci, infection ko inflammation a mahaifa ko cikin mahaifa na iya jawo zubar jini.
- Matsaloli ga uwa: Idan zubar jini ya yi yawa, zai iya haddasa anemia (rashin jini) ga uwa, wanda ke buƙatar kulawa sosai.
Matakan da ya kamata a ɗauka
Da zaran mace ta tsinci kanta a wannan yanayi, musamman idan zubar jinin ya yi yawa, ko yana tare da zafi mai tsanani, ko kuma tana jin motsin jariri ya ragu, toh ta yi gaugawar ganin likita, domin magance matsalar, tun kafin ta yi tasirin da za a rasa jaririn ko mai juna biyun.
Sannan duk wani yanayi na zubar jini, yana da kyau a sanar da likita domin a tantance dalili da hanyoyin magani.
Matakan kariyar zubar jini a lokacin juna biyu
Yana da kyau kowace mace mai juna biyu ta san matakan da suka kamata ta bi wurin kare kanta daga zubar jini:
- Cin abinci mai gina jiki: Yin amfani da abinci mai wadatar sinadaran folic acid, iron, da sauran abinci masu gina jiki don ƙarfafa jikin uwa da lafiyar jariri.
- Kiyaye lafiya: Yin rigakafin cututtuka (kamar malaria ko infection) da kuma guje wa abubuwan da za su iya kawo illa.
- Kiyaye lafiya yayin ɗaukar nauyi: Guji yin aiki mai nauyi ko motsa jiki mai tsanani wanda zai iya kawo matsala.
- Zama cikin kulawar likita: Yin ziyara akai-akai a asibiti don duba lafiyar jariri da uwa (Antenatal Care).
- Guje wa shan miyagun ƙwayoyi: Haka zalika, guje wa shan sigari, giya ko wasu ƙwayoyi masu illa.
Hanyoyin magance zubar jini a lokacin juna biyu
Hanzarta zuwa asibiti: Idan mace ta fara jin alamar zubar jini (ko ta fara zubar jini), abu mafi mahimmanci shi ne zuwa asibiti ko wurin kiwon lafiya don likita ya duba ta.
Hutu da kwanciya: Likita zai iya bada shawarar hutu (bed rest) idan akwai alamun hatsari.
Shan magunguna: Likita zai iya bada magunguna don rage ciwon ciki ko tabbatar da lafiyar mahaifa.
Kula da infection: Idan akwai wani infection da zai iya kawo matsala, za a iya bada magani don magance shi.
Kamar yadda ya gabata, zubar jini a lokacin juna biyu lamari ne mai hatsarin gaske, musamman idan ya kasance jinin mai yawa ne. Idan kuma kuma ya kasance kaɗan, kuma a watannin farko na samuwar ciki bai cika zama matsala ba, kawai abin da ya fi shi ne da mace mai juna biyu ta ga jini komin ƙanƙantarsa ta tuntuɓi likita, domin shi kaɗai ne zai faɗa mata jinin mai haɗari ne, ko marar haɗari.
Sannan ba sai jinin ya zo ba sannan mace zata je asibiti, alama kaɗai idan ta bayyana, kamar zubar jini kai tsaye, Ciwon ciki ko cramping, jin kasala ko rashin lafiya, bugawar zuciya da sauri, zazzaɓi, da sauran alamomi kamar kumburi, duk suna iya bayyana tare da zubar jini. Toh da zaran ta ji waɗannan alamomi ta yi gaugawar ganin likita.
Matakan kariya kuwa sun haɗa da cin abinci mai gina jiki, kiyaye lafiya da gujewa cututtuka, gujewa ɗaukar nauyi mai yawa, zuwa awon ciki don kulawar likita (antenatal care), da kuma gujewa shan miyagun ƙwayoyi. Idan zubar jini ya fara, mafi muhimmanci shi ne ganin likita da wuri, hutu da kwanciya (bed rest), amfani da magunguna masu taimakawa, da kula da infection idan akwai.
A ƙarshe, wannan bayanin yana tabbatar da cewa kowane irin zubar jini a lokacin juna biyu yana da kyau mace ta ɗauke shi da muhimmanci. Duk da cewa wasu nau’ukan zubar jini ba su da haɗari, wasu na iya zama alamar matsala mai tsanani. Saboda haka, neman shawarar likita na da matuƙar muhimmanci don tabbatar da lafiya ta uwa da jariri, da kuma magance duk wata matsala da ka iya tasowa a lokacin juna biyu.
Manazarta
ACOG. (n.d.). Bleeding during pregnancy. ACOG.
March of Dimes. (n.d.). Bleeding and spotting from the vagina during pregnancy. March of Dimes.
Professional, C. C. M. (2025, June 9). Bleeding during pregnancy. Cleveland Clinic.
Website, N. (2024, November 14). Vaginal bleeding in pregnancy. nhs.uk.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.