Aduwa na ɗaya daga cikin itatuwan da suka shahara a tsakanin al’ummomin Hausawa da sauran ƙabilu a Afirka. Ana amfani da ita a fannoni daban-daban na rayuwa, musamman wajen magungunan gargajiya. Aduwa ta zama wani muhimmin ɓangare na magungunan gargajiya ga Hausawa. Duk da shigowar magungunan zamani, har yanzu aduwa tana da daraja a tsakanin tsofaffin musamman na da. Sannan tana da matsayi a cikin kasuwancin Hausawa, musamman a yankunan Arewa inda ake siyar da ita da buhu ko a gwangwani.

Sunayen aduwa
Aduwa tana da sunaye mabambanta. Sunan aduwa na kimiyya shi ne, Balanites aegyptiaca Del. A wasu wuraren ana kiranta da suna daban, amma kalmar “aduwa” ta fi shahara a tsakanin Hausawa. Mutanen Habasha na kiran aduwa da Kudkuda, Larabawa na kiran ta da Zachun, Indiya na kiran ta Enguwa yayin da mutanen Swahili kuma na gabashin Afrika ke kiranta Mjunju.
Sassan jikin aduwa
Sassan jikin aduwa su ne ɓangarorin dake jikin bishiyar aduwa waɗanda suke da muhimmanci ta fuskoki da dama. Kowane sashe na jikin aduwa yana da rawar da yake takawa.
Jijiyoyi
Wannan shi ne ɓangaren da ke ƙasanta, shi ne yake riƙe bishiyar a cikin ƙasa, yana kuma shan ruwa da sinadarai daga cikin ƙasa domin ciyar da sauran sassan jikin aduwa.
Rassa
Su ne sassan da suka fantsama daga jijjigen bishiyar (stem). Suna tallafa wa ganye, furanni da kuma ‘ya’ya.
Ganye
Ganyen aduwa yana da siffar mai kauri, kuma yakan fito cikin launin kore mai haske. Hasken rana kan taimaka wurin fitowar ganyen aduwa wato “photosynthesis” domin ingantashi da kuma sinadaren dake tare da shi.
Furanni
Aduwa tanada furanni masu ƙamshi da kyau, kuma suna iya zuwa ɗauke da launuka daban-daban. Sune suke da alhakin haihuwar ‘ya’yan itacen aduwa. Ana niƙa su a haɗa da ruwa ko zuma. Suna ƙunshe da sinadaran carbohydrate, protein, fiber da sinadarai kamar alkaloids da saponins.
‘Ya’ya
Wannan shi ne sashen da ake girba bayan sun nuna domin amfani da su. Ana amfani da su wajen magungunan gargajiya. Ana amfani da su a cikin abinci ko kuma man gyaɗa. Ana fitar da mai daga cikinsu wanda yake da amfani sosai a magani da kuma shafawa.
Iri
Su ne ƙwayoyin haihuwa da ke cikin ‘ya’yan aduwa. Daga cikinsu ake dasa sabbin bishiyoyi, wato su ne tushen ci gaban aduwar da za’a iya shukawa a gaba.
Wuraren da aduwa ke fitowa
Arewa maso Yammacin Najeriya, Katsina, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Borno da kuma Yobe. Ƙasashe kuma akwai, Nijar, Mali, Sudan, Habasha, da kuma Egypt.
Sinadaran jikin aduwa
Aduwa ta ƙunshi sinadarai da dama waɗanda suka haɗa da; Terpenoids, Alkaloids, Flavonoids, Saponins da kuma Tennins,
Abubuwan da ake yi da aduwa
Kwaikwaye
Wani nau’in abin ci ne da aka yi da aduwa ta hanyar amfani da ƙwalonta. Ana fasata ne a ciro ɗan dake cikin ƙwalon a wanke a dafa shi a dinga ɗaurawa ana siyarwa. Ana kiransa da kwaikwaye.
Mai
Idan aka matse ƙwallon aduwa, ana iya samun man girki da ya kai kashi 45 cikin ɗari, wannan mai na ƙwallon aduwa na da matuƙar amfani idan ana dafa abinci da shi. Yana kuma taimakawa wajen magance yawan Cholesterol da ke kawo toshewar hanyoyin jini da Asma da sauran cututtukan da muka ambata a baya.
Amfanin aduwa
Aduwa tana da amfani a wurare da dama, ana amfani da ita sosai, sai dai kuma an fi amfani da ita ta fannin magunguna fiye da komai. Aduwa tana magunguna da dama waɗanda suka haɗar da maganin mura da kuma tari har ma da maganin jiri da hawan jini. Bayan su akwai tarin magungunan da aduwa take yi waɗanda suka haɗar da:
Warkar da gyambo
Ɓangaren masu fama da gyambo ana samun ganyen aduwa dakakke ko kuma a daka shi a ɗanyensa a riƙa wanke gyambon da shi, cikin dan ƙanƙanin lokaci in sha Allahu gyambon zai kame ko ya bushe ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Asma
Ana iya niƙa ƙwallon aduwa a mayar da shi gari sai a riƙa dibar garin kimanin cokali goma ana zubawa a ruwa kimanin cikin kofi guda ana sha da safe har na tsawon kwanaki goma.
Tsargiya
Ana daka ɓawon aduwa har sai ya zama gari, sannan a sanya a cikin ruwan da yara kan yi wanka da shi, misali kamar kududdufi domin kashe ƙwayoin dake haddasa fitsarin jini da sauran wasu ƙwayoyin cututtuka irin su kurkunu da sauran su. Sai dai kuma wannan yana iya kashe kifaye da su dodon kodi dake cikin ruwan ko kududdufin.
Tsutsar ciki
Haka zalika, ana busar da ƙwallon aduwa a daka shi har sai ya zama gari sannan a rika zubawa a kunun gero ana sha lokaci bayan lokaci. Yana maganin tsutsar ciki.
Ƙurajen fata
Ana samun man da aka fitar daga jikin ‘ya’yan aduwa a riƙa shafawa a jiki baki ɗaya, yana maganin ƙurajen jiki sosai, ka zalika yana maganin sanyin ƙashi.
Kumburi
Ana dafa saiwar aduwa a cikin miya a riƙa sha. Tana taimakawa wurin kawar da ciwon ciki.
Cizon sauro
Ana amfani da ganyen aduwa yana maganin cutar cizon sauro sosai.
Garkuwar jiki
Kamar yadda cibiyar tattara bayanai kan hallitu ta duniya (NCBI) ta wallafa a shafinta na intanet, sinadaran flavonoids da phenolics da ke cikin aduwa na ba da kariya daga yaɗuwar ƙwayoyin halitta da ke haddasa cutar kansa. Har ma da ma wasu cututtukan da ƙwayar cutar bacteria ke haddasawa a jikin ɗan’adam tare da kara inganta lafiyar jikin.
Ƙarin kuzari ga maza
Idan namiji yana jiƙa saiwar aduwa yana sha to za ta yi matuƙar ƙara masa kuzari ta ɓangaren mu’amalar sa da iyalin sa.
Maganin aljanu
Ganyen aduwa ya na maganin korar sheɗanu daga jikin ɗan Adam. Ana samo ganyen aduwa haɗe da ƙayoyin dake jikin icen aduwar a busar dashi sai a dake ya zama gari domin yin turaren ƙonawa da shi.
Daidaita bugun zuciya
Mutane da ke fama da yawan bugun zuciya wanda yake sasu zama suna cikin wani yanayi na razana a koda yaushe, ko kuma numfashi yana yi musu wahala sakamakon bugun zuciyar ya yi kaɗan. Shan aduwa hakan nan yana tamakawa wajen daidaita bugun zuciyar.
Matsalolin aduwa
Aduwa na da matuƙar ɗaci wanda idan aka tauna ta da yawa na iya janyo ƙaiƙayi a kan harshe da leɓe.
- Tana haifar da yawan amai.
- Tana haifar da bushewar baki da jin ƙuna a maƙogwaro.
- Tayar da jijiyoyin ciki.
- Haifar da ciwon ciki mai tsanani.
- Haifar da yawan fitsari.
- Janyo gajiya da raunana jiki.
- Shan ta da yawa na sanya jiri.
- Idan aka sha aduwa aka sha wasu magunguna tana iya yin tasirin ƙara ƙarfin maganin ya yi aiki fiye da aikin da zai yi.
- Haifar da karan tsaye ga aikin magani. Ƙarfin aduwa na taka muhimmiyar rawa wurin yin karan tsaye ga aikin wasu magunguna saboda tasirin sinadaranta masu ƙarfi.
Matan da ke da juna biyu na iya fuskantar haɗari idan suka ci aduwa da yawa, saboda:
- Tana ƙarfafa jijiyoyin mahaifa.
- Tana iya tayar da naƙuda kafin lokaci (preterm labor).
- Za ta iya shafar lafiyar jariri idan aka sha ba tare da shawarar likita ba.
Manazarta
Friday, O. A., Mike, E. O., Abraham, G. T., & Joseph, A. O. (2024). Effects of Hydrolysates of Aduwa (Balanites aegyptiaca Del.) Seed on Oxidative Stress in the Livers of Streptozocin-induced Diabetic Rats. Food Supplements and Biomaterials for Health, 4(3).
Ishaq, M. (2019, December 21). Amfani 12 da aduwa ke yi a jikin dan adam. Legit.ng – Nigeria News.
Nasidi, K. (2022, March 7). Amfanin aduwa da muhimmancinta ga jikin dan adam. BBC News Hausa.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 18 August, 2025
An kuma sabunta ta 18 August, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.