Skip to content

Shuwaka

Shuwaka, shuka ce da ta yi fice a cikin abinci da maganin gargajiya. A kimiyyance ana kiran ta da vernonia amygdalina, da Turanci kuma ana kiranta da bitter leaf. Tana É—aya daga cikin tsirrai da suka shahara wajen magance cututtuka da yawa. Duk da É—acin da ke tattare da ita, ana amfani da ita wajen sarrafa abinci da kuma kula da lafiya.

A ƙasashe da dama na Afirka ta Yamma da suka haɗa da Nigeria, Niger, Ghana da Cameroon, shuwaka na daga cikin muhimman tsirran da aka daɗe ana saka su a magungunan gargajiya da girke-girke. A Najeriya, musamman tsakanin Hausawa, Yarbawa da Igbo, shuwaka ta zama ɓangare na rayuwar yau da kullum.

Asalin tsiron shuwaka

Shuwaka na daga cikin dangin Asteraceae, sannan tsiro ne da yawanci ke girma a cikin yanayin zafi. Ta samo asali ne daga yankin Sub-Saharan Africa, amma yanzu ta bazu zuwa wasu sassa na duniya saboda amfanin ta ga kiwon lafiya. Ana samun tsiron shuwaka ne a cikin dazuka, gonaki, da ma cikin gidaje a matsayin magani ko kayan abinci.

images 11
Ganyen shuwaka.

Shuwaka tsiro ne mai É—an tsawo, wanda zai iya kaiwa kimanin mita 2 zuwa 5. Tana da manyan ganye masu É—aci, wanda shi ne babbar siffarta da ke bambanta ta da sauran tsirrai. Ganyenta kore ne mai É—an duhu, da shi ne kuma ake amfani wajen dafa abinci da kuma magungunan gargajiya. Tushenta yana da zurfi a cikin Æ™asa, yana kuma iya jure fari da yanayi mai zafi sosai, wannan ne ya sa shuwaka ke girma cikin sauÆ™i a gidajen mutane da gonaki. Furanninta kuma Æ™anana ne masu launin fari ko rawaya. Duk da cewa ba su da amfani kai tsaye wajen magani, amma suna da muhimmanci sosai wajen samar da ‘Æ´aÆ´an tsiron shuwakar.

Sinadaran da ke cikin shuwaka

Ganyen shuwaka ɗauke yake da muhimman sinadarai masu gina jiki da kuma phytochemicals (wato sinadaran dake cikin tsirrai, waɗanda ke ƙara lafiya da ƴaƙar cutuka). Sannan a cikinta a kwai manyan sinadarai masu gina jiki da suka haɗa da:

  • Vitamins: A, C, E, B1, B2, B3.
  • Minerals: Iron, Potassium, Calcium, Magnesium, Zinc.
  • Fiber: Masu taimakawa wajen narkar da abinci. Sannan a cikin shuwaka akwai sinadarin protein
  • Flavonoids: Sinadarai ne da ke aiki a matsayin antioxidants, suna kare Æ™wayoyin halitta daga lalacewa. Sannan suna taimakawa wajen rage kumburi da hawan jini.
  • Saponins: sinadaran da ke rage cholesterol (kitse), sannan suna Æ™arfafa garkuwar jiki da yaÆ™i da cututtuka.
  • Alkaloids: Sinadarai ne da ake amfani da su wurin haÉ—a wasu magunguna saboda Æ™arfinsu. Kuma suna taimakawa wajen magance zazzaÉ“i.
  • Tannins: Sinadari ne da ke da Æ™arfin kashe Æ™wayoyin cuta (antibacterial & antiviral), sannan suna taimakawa wajen kwantar da ciwon ciki, da kuma maganin gudawa.

Amfanin shuwaka a kiwon lafiya

A tsawon tarihi, likitocin gargajiya sun yi amfani da shuwaka wajen magance cututtuka da dama. A wannan zamanin ma binciken kimiyya ya tabbatar da amfaninta a fannin lafiya ga cututtuka irinsu:

  • ZazzaÉ“in malaria: Shuwaka na É—aya daga cikin ganyayyakin da ake amfani da su wajen magance zazzaÉ“in malaria, musamman saboda sesquiterpene lactones (Sinadaran dake a cikin tsirrai, waÉ—anda ake haÉ—a magungunan gargajiya da su.)
  • Rage hawan jini: Ganyen shuwaka na taimakawa wajen sauÆ™aÆ™a hawan jini ta hanyar tsarkake jini, rage kitse da daidaita bugun zuciya.
  • SauÆ™aÆ™a ciwon sugar: Shuwaka na rage yawan glucose a jini, saboda tana É—auke da sinadaran da rage glucose a jini (insulin). Masu nau’in ciwon sugar Type 2 na amfana sosai idan suna cin shuwaka muddin basu zarce Æ™a’ida ba.
  • Tsarkake hanta: A yawanci ana É—aukar shuwaka a matsayin tsiron da ke: kawar da duk wata guba dake taruwa a hanta, tare da taimakawa wajen murmurewar hanta da ta gaji ko ta kamu da ciwo.
  • Kula da narkewar abinci: Ruwan shuwaka na tsaftace hanji, rage kumburin ciki, maganin gudawa da kuma ciwon ciki.
  • Kariya daga kansa: Flavonoids da antioxidants da ke cikin shuwaka suna rage taruwar Æ™wayoyin da ke haddasa cancer, musamman na nono, prostate, da hanji. Amma ba magani ba ne kai tsaye, sai dai tana da rawar takawa wuri bayar da kariya ga cutar Cancer (preventive role).
  • Kula da fata: Ana amfani da ruwan shuwaka wajen warkar da kuraje, rage kaikayi, warkar da rauni, da kuma tsaftace fata.

Rage nauyi: Shuwaka na rage nauyi saboda É—acinta da kuma ikon ta na rage cholesterol, shuwaka na tallafa wa masu neman rage nauyi ta hanyar: kara narkewar abinci, hana yawaitar kitse.

Amfanin shuwaka a girke-girke

Duk da ɗacin ta, shuwaka na daga cikin muhimman ganyayyakin da ake amfani da su a cikin girki a Afirka. Ana amfani da ita wajen yin miyar shuwaka, wanda ya shahara a wajen mutanen Igbo da Hausawa, ta hanyar wanketa sosai har sai ɗacin ya lafa, yawanci ana haɗa shuwaka da man gyada, kifi, wake, ko nama, domin ƙara mata armashi a baki.

Amfanin shuwaka a tsohuwar al’ada

  • A wasu al’adu, shuwaka na da amfani sosai fiye da abinci ko magani. Wasu yankunan suna amfani da ita wurin tsarkake jiki da É—aki. Wasu kuma na shafa ganyen shuwaka a gida don tsarkake muhalli, ko hana Æ™wari.
  • Sannan a can baya ana saka shuwaka a cikin kayan haihuwa. Mata masu juna biyu ko masu haihuwa ana ba su ruwan shuwaka domin sauÆ™aÆ™a zafin ciki da kuma tsarkake mahaifa bayan haihuwa. Masu wasannin gargajiya da masu noma suna shan shuwaka don Æ™ara Æ™arfi da da inganta lafiyar numfashi.

Illolin da ke tattare shuwaka

Duk da yawan amfanin shuwaka take da su, toh kuma tana da illolin da ka iya afkuwa idan ba a yi amfani da ita yadda ya kamata ba. Daga cikin illolinta a kwai:

  • ÆŠacinta: kamar yadda kowa ya sani shuwaka na da É—aci, kuma cin kowane nau’i na É—aci ba bisa Æ™a’ida na iya haddasa ciwon anta, ciwon ciki, amai, tare da Æ™ananan matsalolin narkewar abinci.
  • Zubewar ciki: KaÉ—an daga cikin Illolinta ga mai ciki shi ne za ta iya haifar da zubewar ciki, inda wasu sinadaran da ke cikin shuwaka kamar sesquiterpene lactones na iya sa mahaifa ta yi Æ™arfi ko motsi fiye da Æ™ima, wanda zai iya zama haÉ—ari ga jariri, musamman a farkon watanni 1 zuwa3
  • Sannan yawan amfani da shuwaka ga mai juna biyu zai iya rage yawan sinadarin folic acid a jiki. Folic acid kuma yana da matuÆ™ar muhimmanci ga cigaban kwakwalwar jariri.
  • Ta wani bangaren ma shan ruwan shuwaka na iya sauya daidaiton hormones. Hakan kuma na iya haifar da matsaloli a cigaban ciki, ko kuma tsawon lokaci kafin daukar ciki.
  • Wasu matan masu ciki kuma, shan ruwan dafaffiyar shuwaka na iya kawo musu zafin ciki ko tashin zuciya.
  • Haka kuma masu shan maganin diabetes ko hypertension su kula domin shuwaka ma na da irin nata tasirin wurin dakushe kaifin wasu magungunan.

Manazarta

G, O., & G, L. (2013). Heavy Metal Content in Bitter Leaf (Vernonia amygdalina) Grown Along Heavy Traffic Routes in Port Harcourt. InTech eBooks.

Iwalokun, B., Efedede, B., Alabi-Sofunde, J., Oduala, T., Magbagbeola, O., & Akinwande, A. (2006). Hepatoprotective and Antioxidant Activities ofVernonia amygdalinaon Acetaminophen-Induced Hepatic Damage in Mice. Journal of Medicinal Food, 9(4), 524–530.

Degu, S., Meresa, A., Animaw, Z., Jegnie, M., Asfaw, A., & Tegegn, G. (2024). Vernonia amygdalina: a comprehensive review of the nutritional makeup, traditional medicinal use, and pharmacology of isolated phytochemicals and compounds. Frontiers in Natural Products, 3

SharuÉ—É—an Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×