Skip to content

Kankana

Kankana na ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yan itatuwa da ake nomawa a sassa daban-daban na duniya. Ta shahara saboda ɗanɗanonta mai zaƙi, yalwar ruwa da ke cikinta, da kuma sinadaran gina jiki masu amfani ga lafiyar ɗan Adam. Ana cin kankana kai tsaye a matsayin ‘ya’yan itace, sannan ana amfani da ita wajen sarrafa ruwan lemukan sha da wasu kayayyakin abinci. Haka kuma, tana taka muhimmiyar rawa a fannin noma da tattalin arziki, domin noman kankana na samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga ga manoma da ‘yan kasuwa a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya.

Saboda sauƙin nomanta da kuma yawan amfanin da ake samu daga gare ta, kankana ta zama ɗaya daga cikin amfanin gona da ake matuƙar buƙata a kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje. Baya ga amfani da a ita a matsayin abin sha, ana iya amfani da ‘ya’yan da ke cikinta da bawonta ta hanyoyi daban-daban, abin da ke ƙara mata muhimmanci a fannonin abinci, lafiya da masana’antu.

Ma’anar mankana

Kankana ‘ya’yan itace ce mai yalwar ruwa, wadda ke fitowa daga wani tsiro mai yaɗo a ƙasa da ke cikin tsirrai dangin Cucurbitaceae, wato dangin kabewa da kokwamba. Tana da babban ƙwalla a zagaye ko mai ɗan tsawo, mai bawo da kauri wanda yawanci yake da launin kore, yayin da cikinta ke kasancewa ja, ruwan hoda, rawaya ko lemu, gwargwadon nau’in kankanar.

Kankana
Kankana kayan marmari ce da ta shahara a ƙasashe da dama dalilin dandanonta da sinadaran da ke cikinta.

Kashi mafi yawa na kankana ruwa ne, wanda ya kai kusan kashi casa’in cikin ɗari na nauyinta. Hakan ya sa take taimakawa wajen samar da ruwa ga jiki, musamman a lokacin zafi. Haka kuma, tana ɗauke da bitamin, minerals da sinadarai masu hana lalacewar ƙwayoyin halitta, waɗanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar jiki.

Asalin kankana

Masana sun yi imanin cewa asalin kankana ya fito ne daga nahiyar Afirka, musamman yankunan da ke kudancin Afirka, inda har yanzu ake samun nau’o’in kankanar daji. Daga nan ne aka fara nomanta shekaru dubbai da suka gabata kafin ta bazu zuwa arewacin Afirka, Gabas ta Tsakiya da nahiyar Asiya ta hanyar kasuwanci da ƙaura.

A zamanin da, an noma kankana a ƙasar Masar, inda aka gano irinta da ɓawonta a cikin kaburburan sarakuna, abin da ke nuna cewa mutane sun daɗe suna amfani da ita tun kafin ƙarnoni da dama da suka gabata. Daga baya ta bazu zuwa Turai, sannan zuwa nahiyoyin Arewaci da Kudancin Amurka, inda ta zama ɗaya daga cikin muhimman amfanin gonar ‘ya’yan itatuwa.

A yau, ana noman kankana a mafi yawan yankunan duniya masu yanayin matsakaicin zafi. Ƙasashe irin su China, India, Turkiyya, Brazil da Najeriya na daga cikin manyan masu nomanta, kuma ana samar da miliyoyin tan na kankana a kowace shekara domin biyan buƙatun kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

Sunan kankana a kimiyyance

Sunan kankana a kimiyyance shi ne Citrullus lanatus. Tana cikin dangin tsirrai da ake kira Cucurbitaceae, wanda ya haɗa da kabewa, kokwamba, guna da sauran tsirrai masu yaɗo a ƙasa da ke samar da manyan ‘ya’yan itatuwa.

Siffofin kankana

Kankana tsiro ce mai yaɗo a ƙasa, tana da dogayen rassan da kan bazu a faɗin gona.

Ganyen kankana

Ganyenta manya ne, masu launin kore kuma suna da yanka-yanka a gefe da gefe, abin da ke taimaka wa wajen gudanar da aikin samar da abinci ga shukar ta hanyar hasken rana.

Furanni

Furanni kankana ƙanana ne masu launin rawaya. Yawanci tsiron yana samar da furannin maza da mata daban, kuma ƙwari, musamman ƙudan zuma, su ne ke taimakawa wajen ɗaukar ƙwayar fure daga furen namiji zuwa na mace domin a samu wanzuwar ‘ya’ya.

‘Ya’yan kankana

‘Ya’yan kankana suna da girma dabam-dabam gwargwadon nau’inta. Bawonta yana da kauri kuma yawanci kore ne, yana iya kasancewa mai layuka ko tabo masu duhu. Cikinta kuwa yana iya kasancewa ja, ruwan hoda, rawaya ko launin lemu, kuma yana da yalwar ruwa da ɗanɗano mai zaƙi. Wasu nau’o’in suna da tsabar ƙwayoyi baƙaƙe ko ruwan kasa, yayin da wasu aka inganta su ta yadda ba sa samar da ƙwayoyin.

Tsiron kankana

Tsiron kankana yana da tushe ko jijiyar da ke shiga cikin ƙasa domin neman ruwa da sinadaran gina jiki. Wannan tsarin jijiya yana taimaka masa ya jure ɗan ƙarancin ruwa fiye da wasu tsirran lambu, duk da cewa yana buƙatar isasshen ruwa domin samun kyakkyawan girma da yawan amfanin gona.

Nau’o’in kankana

Akwai nau’o’in kankana da dama waɗanda suka bambanta ta fuskar girma, launin ciki, samuwar ƙwayoyin tsaba da kuma ɗandano. Wannan bambancin ya samo asali ne daga zaɓaɓɓun iri da masana suka inganta domin dacewa da yanayi da kuma buƙatun masu amfani.

Mafi shaharar nau’in kankana ita ce mai jan ciki, wadda aka fi samu a kasuwanni kuma take da ɗanɗano mai zaƙi. Haka kuma akwai mai ruwan hoda, wadda take kama da mai jan ciki amma launinta ya fi haske. Wasu nau’o’in kuma suna da ciki mai launin rawaya ko lemu, kuma suna da ɗanɗano da kamanni dabam da na gargajiya.

Ana kuma raba kankana zuwa mai ƙwayoyi da marasa ƙwayoyi a ciki. Mai ƙwayoyi ita ce nau’in da ke samar da ƙwayoyi baƙaƙe ko ruwan kasa a cikinta, yayin da marar tsaba ake samar da ita ta hanyar inganta iri domin ta kasance ba ta samar da ƙwayoyi masu girma ba. Wannan nau’i ya fi samun karɓuwa a wasu ƙasashe saboda sauƙin ci.

Bugu da ƙari, akwai bambanci ta fuskar girma. Wasu nau’o’in suna samar da manyan ‘ya’ya masu nauyin fiye da kilogram goma, yayin da wasu ke samar da ƙanana masu sauƙin ɗauka da adanawa. Haka kuma, ɓawon kankana na iya kasancewa kore mai duhu, kore mai haske ko kuma mai layuka da tabbai masu launi daban-daban.

Yadda ake noman kankana

Noman kankana yana buƙatar ƙasa mai yalwar sinadaran haɓaka tsiro, wadda ke iya zubar da ruwa cikin sauƙi ba tare da ruwa ya tsaya cikinta ba. Tsiron yana bunƙasa sosai a wuraren da ke da yanayi mai zafi da wadataccen hasken rana.

Ana fara noma ne ta hanyar gyara ƙasa da kyau ta kamar tonawa, domin ta yi laushi. Bayan haka sai a shuka iri a ramuka da aka tanada, tare da barin isasshiyar tazara tsakanin tsirrai domin su sami sararin bazuwar rassansu.

Kankana
Kankana nau’in tsiro ce da ke yaɗuwa a ƙasa.

A lokacin girma, ana ba tsiron ruwa akai-akai, musamman idan ana noma shi a lokacin rani. Haka kuma ana amfani da takin gargajiya ko na zamani domin ƙara wadatar sinadaran gina tsiro a cikin ƙasa. Ana kuma cire ciyawa da ke kewaye da tsiron domin rage gasa wajen samun ruwa da sinadaran gina jiki.

Furannin kankana suna buƙatar taimakon ƙwari, musamman ƙudan zuma, wajen yin barbara domin samun wanzuwar ‘ya’ya. Saboda haka, kasancewar ƙwari masu amfani a gonar na ƙara yawan amfanin gona.

Lokacin girbi yakan zo bayan kimanin kwanaki saba’in zuwa ɗari da yin shuka, gwargwadon nau’in iri da yanayin da aka noma shi. Ana gane kankanar da ta nuna ta hanyar sauyin launin ɓangaren da ke kwance a ƙasa, bushewar ganyen da ke kusa da ‘ya’yan, da kuma sautin da take bayarwa idan aka ɗan buga bawonta.

Amfanin kankana

Kankana na da amfani mai yawa ga rayuwar ɗan Adam. Mafi girman amfaninta shi ne kasancewarta abinci mai wadatar ruwa da sinadaran gina jiki, wanda ke taimakawa wajen ƙosar da ƙishirwa da kuma samar wa jiki wasu muhimman abubuwan da yake buƙata.

Ana ci ko shan kankana kai tsaye a matsayin ‘ya’yan itace, sannan ana sarrafa ta zuwa ruwan lemo da sauran nau’o’in abinci. A wasu ƙasashe, ana amfani da ita wajen yin haɗa lemuka da sauran kayayyakin masana’antar sarrafa abinci.

Ƙwayoyin cikin kankana ma suna da amfani. Ana busar da su a ci a wasu al’ummomi, ko kuma a matse su domin samar da mai. Haka kuma suna ɗauke da sinadaran gina jiki da suka haɗa da furotin, kitse masu amfani da wasu minerals.

Ɓawon kankana ma ba a watsar da shi gabaɗaya. A wasu wurare ana amfani da shi wajen ciyar da dabbobi, yin takin gargajiya ko kuma sarrafa wasu nau’o’in abinci bayan an dafa shi.

A fannin tattalin arziki kuwa, noman kankana na samar da ayyukan yi ga manoma, masu safara, masu sayarwa da masana’antun sarrafa kayan abinci. Hakan yana taimakawa wajen ƙara kuɗaɗen shiga da bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu nomawa.

Amfanin ƙwayoyin kankana

Ƙwayoyin kankana na da amfani ga lafiyar ɗan Adam, domin suna ɗauke da sinadaran gina jiki masu muhimmanci. Sun ƙunshi furotin, kitse masu amfani (unsaturated fats), da minerals irin su magnesium, phosphorus, potassium, baƙin ƙarfe (iron), zinc da jan ƙarfe (copper). Haka kuma suna ɗauke da wasu bitamin na rukunin B, waɗanda ke taimakawa wajen samar da kuzari da gudanar da ayyukan jiki.

A wasu ƙasashe, musamman a nahiyoyin Asiya da Afirka, ana busar da ƙwayoyin kankana a ci kai tsaye ko a gasa su a matsayin abin ci. Haka kuma, ana matse su domin samar da mai da ake amfani da shi wajen girki ko a wasu masana’antu. Saboda yalwar sinadaran gina jiki da ke cikinsu, ƙwayoyin kankana na taimakawa wajen gina ƙwayoyin halitta, ƙarfafa tsoka, tallafa wa lafiyar zuciya da jijiyoyin jini, da kuma inganta aikin garkuwar jiki idan aka ci su cikin daidaito a matsayin wani ɓangare na ingantaccen tsarin abinci.

Sinadaran da ke cikin kankana

Ruwa

Kankana na ɗauke da ruwa mai yawa, wanda ya kai sama da kashi casa’in cikin ɗari na nauyinta. Wannan ya sa take taimakawa wajen samar wa jiki isasshen ruwa, musamman a lokacin zafi.

Bitamin A da C

Baya ga ruwa, kankana na ƙunshe da bitamin C, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki da kuma kare ƙwayoyin halitta daga lalacewa. Haka kuma tana ɗauke da bitamin A, wanda ke da muhimmanci ga lafiyar ido, fata da tsarin garkuwar jiki.

Minerals

Har ila yau, kankana na ƙunshe da minerals kamar potassium da magnesium, waɗanda ke taimakawa wajen daidaita aikin tsokoki, jijiyoyi da bugun zuciya. Tana kuma samar da ƙaramin adadin phosphorus da wasu sinadaran da jiki ke buƙata.

lycopene da citrulline

Wani muhimmin sinadari da ke cikin kankana shi ne lycopene, wani sinadarin carotenoid mai ba ta jan launi. Lycopene na daga cikin sinadarai masu kare ƙwayoyin halitta daga lalacewar da sinadarai masu cutarwa ke haifarwa. Haka kuma, kankana na ɗauke da citrulline, wani sinadarin amino acid da ke taka rawa wajen inganta zagayawar jini da wasu ayyukan jiki.

Calories

Duk da kasancewarta mai ɗanɗano, kankana ba ta da yawan sinadarin kuzari (calories), abin da ya sa take cikin ‘ya’yan itatuwan da ake ba da shawarar a haɗa su cikin ingantaccen tsarin abinci.

Cututtuka da ƙwari masu addabar kankana

Kamar sauran amfanin gona, kankana na iya kamuwa da cututtuka da hare-haren ƙwari, waɗanda kan rage yawan amfanin gona da ingancinsa idan ba a ɗauki matakan kariya ba.

Cututtuka

Daga cikin cututtukan da suka fi addabar kankana akwai powdery mildew, downy mildew, fusarium wilt, anthracnose da kuma cututtukan ƙwayoyin cuta kamar Watermelon Mosaic Virus. Waɗannan cututtuka kan haifar da bushewar ganye, lalacewar rassan tsiro, ruɓewar ‘ya’ya ko kuma rage girman amfanin gona.

Ƙwari

Haka kuma, akwai ƙwari da dama da ke lalata kankana, ciki har da aphids, whiteflies, thrips, fruit flies da kuma wasu nau’o’in ƙwari masu cin ganye. Wasu daga cikin waɗannan ƙwari ba wai kawai suna cin tsiro ba ne, har ma suna yaɗa ƙwayoyin cuta daga tsiro zuwa wani.

Domin rage waɗannan matsaloli, ana amfani da iri masu jure cututtuka, ana iya sauya tsarin shuka, ana cire tsirran da suka kamu da cuta daga gona, sannan a yi amfani da hanyoyin sarrafa ƙwari da cututtuka cikin hikima, ciki har da amfani da magungunan da suka dace idan ya zama dole.

Girbi da adanawa

Ana girbe kankana ne idan ta nuna. A lokacin girbi, ana yanke kankanar da wuƙa mai kaifi ko almakashi tare da barin ɗan guntun kara a jikinta. Yin haka yana rage yiwuwar samun rauni a jikin ‘ya’yan, wanda kan sa ta fara lalacewa cikin sauri.

Lemon kankana
Ana markaɗa kankana a haɗa ta wani sinadarin don yin lemo mai daɗin dandano.

Bayan girbi, ana ware kankanar da ta lalace daga mai kyau. Ana adana lafiyayyun ‘ya’yan a wuri mai sanyi, busasshe kuma mai iska. Ya kamata a guji jefa su ko tara su ta hanyar da za ta haddasa matsananciyar matsuwa, domin hakan kan sa bawonta ya fashe ko ya ji rauni.

Idan an yanka kankana, ya kamata a rufe ɓangaren da aka yanka sannan a adana ta a cikin firiji domin kare ta daga gurɓata da kuma tsawaita lokacin da za ta kasance cikin inganci.

Muhimmancin kankana ga tattalin arziki

Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki a ƙasashe da dama. Nomanta na samar da ayyukan yi ga dubban mutane, tun daga masu samar da iri, manoma, masu jigilar kaya, masu sayar da amfanin gona har zuwa masana’antun sarrafa kayan abinci.

A Najeriya da wasu ƙasashen Afirka, kankana na daga cikin amfanin gonar da ke samar wa manoma kuɗaɗen shiga, musamman a lokacin da buƙatarta ke ƙaruwa a kasuwanni. Kasuwancinta na taimakawa wajen haɓaka harkokin sufuri, ajiya da cinikayyar kayan gona tsakanin yankuna.

Har ila yau, kankana na samar da albarkatun ƙasa ga masana’antun da ke sarrafa ruwan ‘ya’yan itatuwa, abinci da sauran kayayyakin da ake samu daga ƙwayoyinta da bawonta. Wannan yana ƙara mata muhimmanci wajen samar da ƙarin darajar amfanin gona, wanda ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki da rage asarar amfanin gona bayan girbi.

Saboda yawan buƙatar kankana a kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, bunƙasa nomanta na iya ƙara yawan fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje, samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasa da kuma ƙarfafa cigaban ɓangaren noma.

Manazarta

Athavale, M. (2026, May 20). 13 Health Benefits of Watermelon and Recipes. PharmEasy Blog.

LD, M. W. R. (2025, February 19). What are the health benefits of watermelon? Medical News Today.

Maccido, A. (2025, July 28). Watermelon: Health benefits of watermelon. BBC News Pidgin.

 

 

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×