Skip to content

Auduga

Auduga ɗaya ce cikin albarkatun gona masu wadatar fiber, wanda hakan ke nuna cewa ta ƙunshi nau’i daban-daban, masu tsayi na zaruruwa. Ana samun auduga daga filaye na dabi’a (natural) na tsirran auduga, waɗanda suke daga jinsin Gossypium. Auduga da farko ta ƙunshi ‘cellulose’, wani abu mai laushi marar narkewa mai mahimmanci ga tsarin shuka, kuma abu ne mai laushi. Shukar auduga tana buƙatar rana mai yawa, dogon lokaci ba tare da sanyi ba, da kuma ruwan sama mai kyau.

Auduga amfanin gona ne na lokacin zafi wanda galibi ana shuka ta a yankuna masu tsayin yanayi masu girma, yawan hasken rana, da matsakaici zuwan yanayin zafi. Yankunan farko da suka fara noman auduga sun haɗa da kudancin Amurka, Sin, Indiya, Pakistan, da Brazil. Noman auduga yana farawa da dasa shukar a cikin filayen gonakin da aka shirya sosai. Yawanci ana shuka tsaba (iri) a cikin layuka kuma ana ware su don ba da damar girma da haɓaka daidai. Da zarar tsiron ya fito, ana shayar da su kuma a ba su taki don haɓaka.

Yayin da shukar auduga suka girma, suna fara samar da gungu na furanni fari ko rawaya. Daga nan sai waɗannan furannin su ba da dama ga ƙwallo auduga, waɗanda su ne tushen shukar auduga. Ana samun gashin auduga a cikin ƙwallon, kuma an kewaye su da wani nau’in bawo mai kariya da ake kira lint.

Ana girbe zaren auduga ta hanyar ɗaukar audugar da hannu ko kuma ta hanyar amfani da injin tsinken auduga, injin da ke cire zaren auduga daga jikin ƙwallon. Bayan girbi, ana tsaftace zaren auduga, a jujjuya su zuwa zaren ko yadi. Auduga shuka ne mai son ruwa, kuma galibi ana feshe ta da magungunan kashe ƙwari da takin zamani. Wannan na iya yin mummunan tasiri ga muhalli da kuma lafiyar manoma. A sakamakon haka, manoman auduga da yawa a yanzu suna amfani da motoci da injina. Wadannan ayyuka na iya taimakawa wajen rage amfani da ruwa, rage abubuwan da ake amfani da su na sinadarai, da inganta lafiyar ƙasa.

Kalmar “auduga” tana nufin wani ɓangaren shukar audugar da ke yin tsiro a cikin ƙwallon, abin da ke tattare da zaren audugar mai laushi. Ana jujjuya auduga cikin zaren da ake sakawa don ƙirƙirar tsumma mai laushi, mai nagarta.

Asalin tushen auduga

Kalmar auduga ta fito daga harshen Larabci “quton.” Farkon samar da auduga ya kasance a Indiya, inda kayan ya samo asali tun ƙarni na biyar BC. Keken kaɗin auduga na farko, wanda shi ne na’urar da ke raba gashin auduga daga tsabarta, an ƙirƙira shi a Indiya a ƙarni na goma sha uku. Keken kaɗin auduga ya sa samar da auduga ya fi sauƙi da sauri, yana taimaka wa fiber ɗin yaɗuwa a matsayin yadin da ake amfani da shi sosai.

A lokacin juyin juya halin masana’antu, tare da ƙirƙirar sabbin fasahohi kamar spanning jenny mai kaɗa auduga, Biritaniya ta zama ɗaya daga cikin manyan masana’antun sarrafa auduga. Duk waɗannan injunan sun ba wa masana’antu damar juyar da auduga da sarrafa ta da ƙara farashi.

Duk da haka, wani ɗan Amurka Eli Whitney ne ya ƙirƙira keken kaɗin auduga mai inji wanda ya haifar da ƙara yawan samar da kayan a Amurka da Turai. Wannan sabon kayan aiki, wanda yake cire tsaba (angurya) daga cikin auduga cikin sauri da inganci ta hanyar amfani da wutar lantarki, ya rage sa’o’in aikin hannu da ake buƙata don samar da damin auduga daga sa’o’i 600 zuwa kawai 12. A lokaci guda, Amurka, musamman ma jihohin Kudancin kasar, sun riƙa samar da auduga mafi inganci, saboda zaruruwan suna da ɗan tsayi kuma sun fi ƙarfi.

Duk da raguwar samar da auduga da ke faruwa lokaci-lokaci sakamakon wasu dalilai, kamar lokacin yaƙin basasa, Amurka har yanzu tana ɗaya daga cikin manyan masu samar da auduga a duniya, tana bayan China da Indiya.

Wuraren da auduga take girma

Auduga tana girma a kusan dukkanin yankuna masu zafi da wurare masu matsakaicin zafi a duniya, ciki har da Amurka, Sin, Indiya, Uzbekistan, Pakistan, Brazil, da Turkiyya. A Amurka, Texas ita ce kan gaba wajen noman auduga, kuma yankin Kudu Plains da ke arewacin jihar shi ne yanki mafi girma da ake noman auduga a duniya.

Yadda ake sarrafa auduga

  • Samar da auduga wani tsari ne da ke da hannu sosai, tun daga dasa ’ya’yan auduga zuwa tsinƙar amfanin gonar auduga zuwa sarrafa ta a cikin keken kaɗin nata.
  • Yayin da aka tsinki auduga da hannu a farkon zamanin da, a yau, yawancin samar da auduga yana farawa da na’urar tsinkar auduga (wanda ke tsigo shuka gabaɗaya) ko ƙwallon audugar daga jikin shukar.
  • Bayan an ɗebo audugar, sai a baje ta a ajiye a cikin sarari kafin a aika da ita zuwa keken kaɗi.
  • A wajen keken kaɗin, ana goge buhunan zuba audugar kafin a zuba don raba kayan da datti, iri, da sauran su.
  • Bayan audugar ta ratsa cikin keken kaɗi kuma ta rabu gabaɗaya daga tsabar, ana matsa danyar audugar a adana ta, a shirya ta don jigilar zuwa masana’antu inda za a ci gaba da sarrafa ta zuwa wani abin.
  • Ana saka audugar da aka ware daga tsabar cikin inji, wanda zai ƙara tsaftace kayan kuma ya samar da gajerun zaruruwa zuwa dogaye don yin saƙa.

Nau’ikan auduga

Akwai nau’ikan auduga guda hudu, kowacce tana da tata siffar.

Audugar Pima

Ana la’akari da ita a matsayin mafi kyawun nau’in auduga a duniya, gashin auduga nau’in Pima suna da laushi kuma suna da tsawo. Audugar ta fito ne daga Kudancin Amurka. Ana buƙatar kayan audugar Pima sosai, saboda tana da juriya ga dusashewa, yagewa, da murƙushewa.

Audugar Masar

Auduga Masar tana kama da auduga Pima. Su biyun ma suna cikin ajin kimiyya iri ɗaya, wato daga dangin ‘gossypium barbadense’ suke. Suna da siffofin juriya iri ɗaya, sai dai ita wannan ana shuka ta ne a cikin kwarin Kogin Nilu a ƙasar Masar.

Audugar Upland

Auduga na sama yana da gajerun zaruruwa kuma tana da kusan kashi 90% na yawan audugar da ake samarwa a duniya. Tushenta ya fito kuma yana girma a Amurka ta tsakiya, Mexico, Caribbean, da kudancin Florida.

Audugar organic

Wannan nau’in auduga ita ce kowace  auduga da ake nomawa ba tare da amfani da sinadarai ba kuma daga tsirrai waɗanda ba a haɗa su ta hanyar kwayoyin halitta ba.

Siffofin auduga

Auduga na da wasu keɓantattun siffofi na musamman waɗanda suka mayar da ita mafi soyuwa kuma shahararriya a masana’antun sarrafa tufafi. Daga cikin waɗannan siffofi akwai:

  • Laushi: Shukar auduga tana da laushi, kuma wannan laushin yana haifar da zare mai santsi.
  • Juriya: Tsarin salon shukar auduga yana da ƙarfi, yana samar yadi mai ƙarfi da juriyar lalacewa.
  • Shaƙar iska: Yadudduka na auduga suna da ƙima sosai saboda akwai sarari da yawa tsakanin zaren auduga.
  • Riƙe rini sosai: Saboda yanayin da yake sha, auduga yana ɗaukar rini cikin sauƙi kuma ana iya yin shi da launuka iri-iri.
  • Fitar numfashi: Tsarin zare ko yadin auduga ya sa ya fi fitar da numfashi fiye da yadukan roba.
  • No static clin: Auduga ba ta da makamashin lantarki, don haka a wannan ba batun da ya shafi auduga ba ne.

Amfani auduga

Auduga tana da amfani da yawa, a cikin nau’ikan masana’antu daban-daban. Wasu daga cikin gama-garin alfanun auduga sun haɗa da:

Saƙa yadudduka

Ana amfani da auduga don yin nau’ikan yadudduka da ake sakawa, ciki har da zannuwa, denim, damask, flannel, da sauran su.

Samar da tufafi

Auduga wani abu ne da masana’antun sarrafa kayan sawa da saƙa ke amfani da ita a sakamakon yawan samar da ita. Tana da taushi da karko, da kuma fitar iska. Ana yawan amfani da auduga don samar T-shirts, wandunan jeans, riguna, da sauran su.

Zanen gado da tawul

Kasancewar auduga tana da laushi sosai kuma tana ɗaukar nauyi, don haka tana da muhimmanci ga masana’antun sarrafa kayan shimfiɗa kamar zannuwan gado da tawul ɗin da ake buƙata don tsane danshi.

‘Yan kamfai

Sakamakon dalilai da aka bayyana a sama na ƙimar auduga, tana sanya tufafi kowane iri su masu dacewa.

Adon gida

Haka nan ana amfani da auduga a ko’ina cikin gida don kayan kwalliya, labulaye, dardumai, matasan kai da sauran su.

Man auduga

Shukar auduga wata shuka ce da ake samar da zaren auduga, kuma ana amfani da ‘ya’yan (angurya) wajen samar da man auduga, wanda ake amfani da shi wajen samar da kayan shafawa, sabulu, kyandir da sauran su.

Takardu

Ana amfani da auduga don yin samfuran takarda masu inganci kamar su takardun banki, kuɗi, da takarda mai kyau.

Takalma

Ana amfani da su don yin sawun takalmi na ciki.

Marufi

Ana amfani da zaren auduga don yin kayan tattarawa kamar jakunkuna, buhu, da kayan naɗewa.

Manazarta

The Story of Cotton- History of cotton. (n.d.).

Weigmann, & H, H. (2025, May 27). Cotton | Description, fiber, History, production, uses, botanical name, & Facts. Encyclopedia Britannica. .

Learn. (n.d)  What is Cotton. Genetic Utah

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×