Kabewa wani nau’i kayan lambu ce mai sauƙin narkewa da kuma laushi, wacce aka fi samu a lokacin hunturu. Asalin kabewa ta fito ne daga Arewacin Amurka. A cikin Amurka, kabewa yawanci tana nufin ‘Cucurbita pepo’, wani nau’in lemu na mai laushi da ake samu a lokacin sanyi. A wasu yankuna, irin su Ostiraliya, kabewa na iya nufin kowane nau’in kayan lambu mai laushi kamarta wanda kan samu a yanayin sanyi.

A kimiyyance kabewa ‘ya’yan itace ne, domin tana ɗauke da iri. Wannan ya nuna tana da sinadirai masu kama da kayan lambu fiye da ‘ya’yan itatuwa. Bayan ɗanɗano mai daɗi, kabewa tana da sinadarin gina jiki kuma tana da alaƙa da fa’idojin kiwon lafiya da yawa. Akwai sinadarai masu ban sha’awa guda 9 da ake samu a cikin kabewa.
1. Samar da bitamin A
Kabewa tana da ban sha’awa bayanin martaba na gina jiki. Dafaffiyar kabewa mai nauyin gram 245 ta ƙunshi:
- Calories: 49
- Sinadarin kitse: gram 0.2
- Sinadarin frotin: gram 2
- Sinadarin carbohydrates: gram 12
- Sinadarin fiber: gram 3
- Vitamin A: 245% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Vitamin C: 19% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Potassium: 16% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Copper: 11% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Manganese: 11% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Vitamin B2: 11% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Vitamin E: 10% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
- Iron: 8% na adadin da ake bukata a rana (RDI)
Da kuma karami adadin sinadaran magnesium, phosphorus, zinc, folate da bitamin B da yawa. Bayan tumbatsa da sinadaran bitamin da minerals, kabewa tana ɗan ƙaramin adadin kuzari, saboda tana da kashi 94% na ruwa. Haka kuma, ‘ya’yan kabewa ana iya cin su, suna gina jiki kuma suna da alfanun kiwon lafiya mai yawa.
2. Kabewa na rage damuwa
Sauye-sauyen da jiki ke samu na faruwa dalilin wasu kwayoyin halitta na jiki. Kodayake ba su da ƙarfi sosai, amma suna yin ayyuka masu amfani, kamar lalata ƙwayoyin bakteriya masu cutarwa. Sai dai yawaitar waɗannan abubuwa a jiki na haifar da yanayin damuwa, wanda aka danganta da cututtuka na yau da kullum, ciki har da cututtukan zuciya da ciwon daji.
Kabewa na ɗauke da sinadarin antioxidants, irin su alpha-carotene, beta-carotene da beta-cryptoxanthin. Waɗannan na iya kawar abubuwan da ke haifar da waɗannan cututtuk, tare da hana su lalata ƙwayoyin halitta.
Wani gwajin da nazarin a kan dabbobi sun nuna cewa waɗannan antioxidants suna kare fata daga lalacewa sanadin rana kuma suna rage haɗarin kamuwa da kansa, cututtukan ido da sauran yanayin rashin lafiya.
3. Kabewa na da bitamin masu ba jiki kariya
Kabewa tana cike da abubuwan gina jiki waɗanda za su iya inganta tsarin garkuwar jiki. Na farko, tana da sinadarin beta-carotene, wanda jiki ke sarrafawa zuwa bitamin A. Nazari ya nuna cewa bitamin A na iya ƙarfafa garkuwar jiki kuma yana taimakawa wajen yaƙar cututtuka. Mutanen da ke da rashi bitamin A na iya samun raunin garkuwar jiki
Har ila yau kabewa tana da wadatar bitamin C, wanda ke ƙara samar da ƙwayoyin jinin (white blood), tana taimaka wa ƙwayoyin garkuwar jiki su yi aiki yadda ya kamata kuma tana sa raunuka su warke cikin sauri.
Baya ga bitamin guda biyu da aka ambata a sama, kabewa kuma tana da kyakkyawan sinadarin bitamin E, bronze da folate, duk suna taimaka wa tsarin garkuwar jiki kamar yadda ya kamata.
4. Kabewa na kiyaye ƙarfin gani
A bayyane yake cewa shekaru ko tsufa na ba da gudunmawa wajen raguwar ƙarfin gani. Amma cin abinci mai gina jiki na iya rage haɗarin nakasar gani. Kabewa tana da yawan sinadirai waɗanda aka haɗa su don ƙarfafa idanu yayin da mutum ya tsufa. Misali, sinadarin beta-carotene yana ba samar wa jiki bitamin A din da ake bukata. Bincike ya nuna cewa ƙarancin bitamin A shi ne sanadin makanta.

A wani bincike na bincike guda 22, masana kimiyya sun gano cewa mutanen da suka fi shan sinadarin ‘beta-carotene’ suna da ƙarancin hadarin kamuwa da cutukan ido. Kabewa tana ƙunshe da adadi mai yawa na bitamin C da E, waɗanda ke aiki a matsayin antioxidants kuma suna iya daƙile ƙwayoyin bakteriya masu cutarwa lalata ƙwayoyin halittar ido.
5. Kabewa na rage ƙiba da nauyi
Kabewa tana cikin nau’ikan abinci masu yawan sinadaran gina jiki. Wannan na nuna cewa tana da ƙarancin sinadarin calorie (sinadarin kuzari) duk da cewa tana ƙunshe da sinadaran abinci masu yawa.
A taƙaice, kabewa abinci ce mai taimakawa wajen rage nauyi saboda za ku iya cin ta da yawa fiye da sauran sinadaran carbohydrates, irin su shinkafa da dankali. Amma dai duk da haka idan an ci tana samar da ɗan ƙaramin adadin kuzari. Bugu da ƙari, kabewa tushe ne fiber mai kyau, wanda zai iya taimakawa wajen rage yawan sha’awar abinci.
6. Kabewa na daƙile cutar kansa
Kwayoyin ciwon daji suna haifar da ƙwayoyin bakteriya masu taimaka musu su haɓaka cikin sauri. Kabewa tana wadatar ‘carotenoids’, waɗanda su ne sinadarai waɗanda za su iya aiki a matsayin antioxidants. Wannan na ba su damar yaƙar ƙwayoyin bakteriya masu cutarwa, hakan zai taimaka wajen samun kariya daga wasu cututtukan daji. Bincike ya nuna cewa mutanen da ke da yawan ‘alpha-carotene’ da ‘beta-carotene’, suna da ƙarancin haɗarin kamuwa da ciwon daji na ciki.
Hakazalika, yawancin binciken ɗan’adam sun gano cewa mutanen da ke yawan amfani da ‘carotenoids’ suna da ƙarancin haɗarin kamuwa da kansar makogwaro, pancreas, nono da sauran cututtukan daji.
7. Kabewa na inganta lafiyar zuciya
Kabewa na dauke da sinadirai iri-iri waɗanda suke inganta lafiyar zuciya. Tana da yawan sinadarin potassium, bitamin C da fiber, waɗanda aka danganta da fa’idojin inganta zuciya. Binciken ya bayyana cewa mutanen da abinci mai yawan potassium suna da ƙarancin hawan jini da kuma rage haɗarin bugun jini. Waɗannan cutuka ne guda biyu masu haɗari ga zuciya.
8. Kabewa na inganta lafiyar fata
Kabewa tana cike da abubuwan gina jiki waɗanda ke da amfani ga fata. Tana da wadatar ‘carotenoids’ kamar beta-carotene, wanda jiki yake juyawa zuwa bitamin A. A zahiri, kabewa mai nauyin gram 245 dafaffiya tana samar da kashi 245% na sinadarin bitamin A. Nazarin ya nuna cewa sinadarin ‘carotenoids’ na iya aiki a matsayin garkuwa daga hasken rana. Da zarar an yi amfani da wannan sinadarin, ana jigilar shi zuwa gaɓoɓin jiki daban-daban ciki har da fata. Yana taimakawa wajen kare ƙwayoyin halittar fata daga lalacewa dalilin hasken ultraviolet (UV) mai cutarwa.
Bugu da kari, kabewa tana da sinadarin bitamin C, wanda ke da muhimmanci ga lafiyar fata. Jiki yana buƙatar wannan bitamin don samar da wani nau’in furotin da ke ƙarfafa fatar jiki.
9. Kabewa na ƙara ɗanɗanon abinci
Kabewa tana da daɗi kuma mai sauƙin sarrafawa a cikin tsarin abinci. Daɗaɗinta ya sa ta zama mahadi wajen sarrafa wasu nau’ikan abinci. Ana amfani da ita sosai a girke-girke miyar taushe da sauran su. Kabewa tana da ɓawo mai tauri, don haka tana buƙatar a fere shi kafin a yi amfani da ita.
Matsololin cin kabewa
Kabewa tana da muhimmanci sosai kuma tana ƙara lafiya ga jiki sosai. Amma duk da haka, wasu mutane na iya fuskantar rashin lafiyar bayan cin kabewa.
Haka nan kuma kabewa na iya haifar da yawan yin fitsari, wanda ke nuna cewa cin kabewa da yawa na iya janyo yawaitar fitsari marar misali. Wannan tasirin na iya cutar da mutanen da ke shan wasu magunguna kamar lithium.
Manazarta
Rd, K. J. M. (2023, May 19). Pumpkin: Nutrition, benefits and how to eat. Healthline.
WebMD (n.d). PUMPKIN: Overview, uses, side effects, precautions, interactions, dosing and reviews. WebMD.
WebMD (2024, April 22). Health benefits of pumpkin. WebMD.