Skip to content

Kanumfari

KAanunfari yana daga cikin tsirran da ake amfani da su wajen magungunan gargajiya da kuma amfani a abinci. Haka kuma nau’in tsiro ne da yake da matuƙar ƙamshi a yayin da aka yi amfani da shi a duk inda ya kasance.  Shukar kanunfari tana daga cikin dangin tsirran da ake kira ‘Myrtaceae’, kuma ana samun ta a wurare masu zafi kamar Indiya, Indonesiya, da wasu yankunan Afirka.

Samuwar kanunfari

Kanunfari yana fi fitowa a nau’ikan ƙasar da ke da yanayi mai ɗanɗano da ɗumi. Ana nomansa sosai a yankunan da ke kusa da teku, musamman a ƙasashen Asiya da Afirka.

Ƙasasshen da ya fi fitowa

  • Indonesia: Ita ce ƙasa mafi yawan noman kanunfari a duniya, kuma ana amfani da shi sosai a cikin abinci da kuma sigari (kretek).
  • Madagascar: Wata babbar ƙasa da ke samar da kanunfari mai inganci.
  • Tanzaniya: Yankin Zanzibar na ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake noman kanunfari a Afirka.
  • India: Ana noman sa a jihohi kamar su Kerala, Karnataka, da Tamil Nadu.
  • Sri Lanka: Wata ƙasa da ke shahara wajen noman kanunfari mai inganci.
  • Brazil: Ita ce ƙasar da ke samar da yawancin kanunfari da ake amfani da shi a Amurka.

A Najeriya, ana iya samun kanunfari a kasuwanni, musamman a yankunan Arewa da kuma wuraren da ake safarar kayan ƙamshi daga ƙasashen waje.

Yadda ake shuka kanunfari

  • Ana amfani da sabbin irin (seeds) da ba su bushe ba, domin sun fi yin saurin tsirowa (germination).
  • Ƙasar shukar ta kasance mai kyau, mai danshi, kuma wadda take riƙe ruwa sosai.
  • Ramin da za a zuba irin ya kasance mai zurfi kusan 2-3 cm sannan a rufe da laka kaɗan.
  • Kanunfari yana son a dinga ba shi ruwa akai-akai, amma ba da yawa ba don guje wa ruɓewa.
  • Haka kuma shukar kanunfari tana buƙatar hasken rana da yanayi mai ɗan zafi da kuma ƙasa mai laushi.

Amfanin kanumfari ga lafiya

Masana harkokin lafiya sun bayyana amfanin wannan sinadari na kanunfari a rayuwar ɗan’adam. Misali, ruwan kanunfari na da amfani sosai ga lafiya saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da bunƙasa garkuwar jiki. Kanunfari yana da amfani da yawa ga lafiya da amfanin yau da kullum. Ga wasu daga cikin amfaninsa:

  • Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer. Yana taimakawa lafiyar haƙora da hana kumburin dadashi da fitar da jini.
  • Sannan ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa. Yana maganin jiri da cutar kwalara. Sannan yana taimakawa wajen saisaita sukari a cikin jini da lafiyar hanta saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.
  • Matsalar hanta: Kanunfari na taimakawa wajen gyara hantar da ta samu matsala sakamakon wata guba mai suna ‘thioacetamide’. Musamman, eugenol da ke cikin kanunfari na da matuƙar amfani ga hanta.
  • Ciwon daji: Man kanunfari na iya rage hatsarin kamuwa da ciwon daji. Musamman, sinadarin eugenol yana da iya hana girma da kuma kashe ƙwayoyin ciwon daji, kamar yadda wasu binciken gwaji suka nuna, musamman a cikin cancer ta mama.
  • Maganin ciwon hakori: Ana amfani da man kanunfari ko garinsa domin  rage ciwon haƙori da kuma kumburi.
  • Maganin tari da mura: Yana da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta, wanda ke taimakawa wajen rage tari da mura.
  • Inganta narkewar abinci: Yana taimakawa wajen rage kumburin ciki, ciwon ciki, da kuma yawan gas.
  • Kula da matakin sugar a jini: Yana taimakawa masu ciwon suga wajen daidaita yawan glucose a jini.
  • Inganta lafiyar zuciya: Yana rage yawan cholesterol da hawan jini.
  • Kara kuzari da ƙarfin jiki: Yana taimakawa wajen rage gajiya da kuma ƙarfafa garkuwar jiki.
  • Matsar warin baki: Kanunfari na taimakawa  wurin kawar da matsalar nan ta warin baki.
  • Ana amfani da shi wajen magance matsalolin fata kamar kuraje da ƙaiƙayi. Yana da sinadarai da ke taimakawa wajen tsabtace fata da hana tsufa da wuri.

Amfanin kanumfari a matsayin abinci

Ana amfani da shi domin ƙara ɗanɗano a abinci kamar shayi, miya, da sauran kayan abinci. Yana da ƙamshi mai daɗi da ke ƙara ingancin kayan haɗi.

Sinadaran da kanumfari ya ƙunsa

Kanunfari na ɗauke da sinadarai masu amfani da yawa. Ga wasu daga cikin manyan sinadaran da ke cikinsa:

  • Eugenol
  • Acetyl eugenol
  • Caryophyllene oxide
  • Vanillin
  • Flavonoids
  • Tannins
  • Bitamin C
  • Bitamin K
  • Fiber
  • Calcium
  • Magnesium
  • Potassium

Matsalolin da kanumfari ke haifarwa

Duk da fa’idodin da kanunfari ke da su, yana da wasu illoli da ya kamata a kula da su, musamman idan aka yi amfani da shi fiye da kima. Ga wasu daga cikin illolin da kanumfari zai iya haifarwa:

Haddasa matsalolin hanta

Sinadarin eugenol da ke cikin kanunfari na iya zama mai amfani ga hanta, amma idan aka sha shi da yawa, yana iya haifar da lalacewar hanta. Shan man kanunfari da yawa na iya zama guba ga hanta, musamman a yara.

Haddasa zubar jini

Eugenol na iya hana daskarewar jini, wanda ke iya haifar da ƙara hatsarin yawan zubar jini, musamman ga mutanen da ke da matsalar daskarewar jini da waɗanda ake shirin yi wa tiyata da waɗanda ke shan magungunan rage daskarewar jini, kamar Aspirin da Warfarin

Kawo matsalolin baki da fata

Shafa man kanunfari a fata na iya haifar da ƙaiƙayi, kumburi, da ciwo ga wasu mutane musamman masu fata mai laushi. Amfani da man kanunfari a kan dasashi da ƙashi na iya haifar da ƙunar baki ko kumburi.

Ta’azzara ciwon sukari

Kanumfari na iya ƙara yawan sikari a jini, wanda hakan na iya shafar mutanen da ke shan magungunan rage sikarin jini, kamar waɗanda ke fama da ciwon suga (diabetes). Idan ana amfani da kanumfari tare da irin waɗannan magunguna, yana iya haifar da saukar sikari da yawa (hypoglycemia), wanda ke da haɗari ga lafiya.

Haddasa bugun jini ga yara

Man kanumfari yana da matuƙar haɗari ga yara, domin ko da kaɗan na iya haifar da bugun jini (seizures), matsalar numfashi, da guba ga hanta. Cin kanunfari da yawa na iya ƙara yawan acid a ciki, wanda zai iya haifar da ciwon ciki, ƙuna a ciki, ko gyambon ciki. Mutanen da ke da ulcer ya kamata su yi taka tsan-tsan wajen amfani da kanunfari.

Hanyoyin kariya

  • Mata masu juna biyu ko masu shayarwa su nemi shawarar likita kafin su sha ko shafa man kanunfari.
  • Kada a ba wa yara ƙanana man kanunfari saboda haɗarin da ke tattare da shi.
  • Mutanen da ke shan magungunan daskarewar jini ko rage sikari a jini su nemi shawarar likita kafin amfani da kanunfari.
  • Idan kana da wata matsala bayan amfani da kanunfari, yana da kyau a tuntuɓi likita nan da nan.

Manazarta

Abdulmumin, U. S. (2021, April 4). Kanumfari na motsa sha’awa ga mata da maza da kuma jinkirta tsufa. BBC News Hausa.

Healthline: Medical information and health advice you can trust. (n.d.). Healthline.

Ishaq, M. (2017, April 26). Magunguna 5 da kanunfari ke yi a jikin dan adam . Legit.ng – Nigeria News.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page