Skip to content

Kirkirarriyar basira (AI) ta gano sabbin duniyoyi 118 daga bayanan NASA TESS

Exoplanet, ko kuma extrasolar planet, na nufin kowace duniya da ke kewaya wani tauraro da ba rana ba, wato duniyar da take a wajen tsarin falaƙin rana (wato solar system). Tun bayan gano exoplanet ta farko da aka tabbatar da shi a shekarar 1992, binciken irin waɗannan duniyoyi ya zama ɗaya daga cikin muhimman fannoni na ilimin taurari, saboda yana taimakawa masana wajen fahimtar yadda tsarin taurari ke samuwa da kuma yiwuwar samun rayuwa a wasu duniyoyi.

AI RAVEN wani sabon tsarin ƙirƙirarriyar basira (Artificial Intelligence) ne da masana daga jami’ar Warwick suka ƙirƙira domin taimakawa wajen gano sabbin duniyoyi daga ɗimbin bayanan da tauraron bincike na Transiting Exoplanet Survey Satellite (TESS) na hukumar NASA ke tattarawa. Tsarin yana amfani da fasahar machine learning wajen tantance alamomin da ke nuna yiwuwar kasancewar wata duniya tana kewaya wani tauraro, abin da ke sa aikin bincike ya fi sauri da inganci fiye da tsaffin hanyoyi.

A watan Mayun shekarar 2026, wannan bincike ya ja hankalin masana kimiyya a duniya bayan fasahar AI RAVEN ta yi nasarar tantance sabbin duniyoyi 118, ciki har da guda 31 da ba a taɓa tabbatar da su ba, tare da gano alamomi fiye da 2,000 na wasu sabbin duniyoyin da za a ci gaba da bincikensu. Wannan sakamako ya fito ne bayan nazarin miliyoyin bayanan da fasahar TESS ta tattara a tsawon shekaru, abin da ya nuna irin ƙarfin AI wajen gano abubuwan da ɗan Adam kaɗai zai ɗauki lokaci mai tsawo yana nema.

Wannan bincike ya zama ɗaya daga cikin manyan labaran kimiyya na shekarar 2026 saboda ya nuna yadda haɗa fasahar ƙirƙirarriyar basira da binciken sararin samaniya ke sauya hanyoyin gano sabbin duniyoyi. Haka kuma, ya ƙara nuna cewa AI na iya taimaka wa masana wajen hanzarta gano duniyoyin da za su iya kasancewa masu kama da duniya, abin da zai iya buɗe sabon babi a binciken rayuwa a wajen tsarin falaƙin rana.

Mene ne exoplanet?

Exoplanet ko kuma extrasolar planet a Turance, duniya ce da ke kewaya wani tauraro da ba rana ba. Wannan yana nufin cewa exoplanets suna cikin wasu tsarin taurari daban da solar system. Wasu daga cikin waɗannan duniyoyi suna da girma fiye da Jupiter, yayin da wasu kuma suke da kusan girman duniyar earth. Haka kuma, yanayinsu ya bambanta ƙwarai; akwai masu tsananin zafi, masu tsananin sanyi, da kuma waɗanda ake ganin suna iya kasancewa cikin yankin da ruwa zai iya kasancewa a yanayin ruwa.

An fara samun tabbacin gano sabbin duniyoyi a shekarar 1992, lokacin da masana suka gano wasu duniyoyi da ke kewaya wani tauraro mai suna PSR B1257+12. Daga baya, a shekarar 1995, aka gano 51 Pegasi b, wadda ta zama exoplanet ta farko da aka tabbatar tana kewaya tauraro mai kama da rana. Tun daga wannan lokaci, sabbin na’urorin telescopes da tauraron bincike irin su Kepler da TESS sun taimaka wajen gano dubban exoplanets, lamarin da ya canja yadda masana ke fahimtar tsarin samuwar duniyoyi a sararin samaniya.

Binciken sabbin duniyoyi yana da matuƙar muhimmanci ga kimiyya saboda yana ba masana damar fahimtar yadda tsarin taurari ke samuwa da yadda duniyoyi ke bunƙasa. Har ila yau, yana taimakawa wajen gwaje-gwajen ƙa’idojin kimiyyar sararin samaniya da kuma fahimtar ko tsarin falaƙin ranarmu na musamman ne ko kuwa akwai makamantansa masu yawa a faɗin sararin samaniya.

Ɗaya daga cikin manyan dalilan binciken sabbin duniyoyi shi ne neman duniyoyin da za su iya ba da damar yin rayuwa. Masana suna neman duniyoyin da suke cikin tsarin da ake kira habitable zone, wato yankin da yanayin zafi zai iya ba ruwa damar kasancewa a yanayin ruwa. Kodayake har yanzu ba a tabbatar da yiyuwar rayuwa a kan wata sabuwar duniya ba, cigaban bincike da kuma amfani da AI kamar RAVEN suna ƙara kusantar da masana ga gano amsar tambayar ko ɗan Adam shi kaɗai ne mai rayuwa a sararin samaniya.

Tarihin NASA TESS

Transiting Exoplanet Survey Satellite (TESS) wani tauraron bincike ne da NASA ta ƙaddamar domin gano sabbin duniyoyi a sararin samaniya. An harba TESS zuwa sararin samaniya a ranar 18 ga Afrilu, 2018, tare da manufar binciken taurari mafi kusa da duniyar earth domin gano duniyoyin da ke kewaye da su. Wannan shiri ya gaji aikin Kepler Space Telescope, amma an tsara shi domin ya binciki kusan dukkan sararin samaniya maimakon taƙaita bincike ga wani yanki kaɗai.

Sabbin duniyoyi
Jami’ar Warwick ce ta kirkiro AI RAVEN, ƙirƙirarriyar basirar da ke saukaka gano sabbin duniyoyi cikin hanzari.

Babban dalilin ƙaddamar da TESS shi ne gano duniyoyin da za su iya zama kusa da duniyar earth, domin a sami damar yin ƙarin bincike a kansu ta amfani da manyan na’urorin telescopes na zamani. NASA ta yi imanin cewa gano irin waɗannan duniyoyi zai taimaka wajen fahimtar yadda tsarin taurari ke samuwa, da kuma ƙara yiwuwar gano duniyoyin da za su iya ba da damar rayuwa.

TESS tana gano sabbin duniyoyi ne ta hanyar abin da ake kira transit method. Idan wata duniya ta ratsa gaban tauraronta daga mahangar TESS, hasken tauraron zai ɗan ragu na ɗan lokaci. TESS tana auna waɗannan ƙananan sauye-sauyen haske cikin daidaito sosai. Idan raguwar hasken ta maimaitu a wani tsari na lokaci, masana za su yi hasashen cewa akwai wata duniya da ke kewaya wannan tauraro. Daga nan sai a yi ƙarin bincike domin tabbatar da hakan.

Tun kafin binciken AI RAVEN na shekarar 2026, TESS ta riga ta zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan NASA mafi nasara wajen gano sabbin duniyoyi. Ta gano dubban abubuwa masu ban sha’awa, kuma an tabbatar da daruruwan sabbin duniyoyi ta amfani da bayananta. Waɗannan bayanai ne AI RAVEN ta sake nazari da fasahar machine learning, abin da ya haifar da gano ƙarin sabbin duniyoyi da kuma waɗanda ba a taɓa tabbatar da su ba.

Ma’anar RAVEN

RAVEN kalma ce da aka samo daga RAnking and Validation of ExoplaNets, wato wani tsarin ƙirƙirarriyar basira (Artificial Intelligence, AI) da aka ƙera domin taimakawa wajen ganowa da tantance duniyoyin da ke kewaya wasu taurari a wajen tsarin falaƙin rana. An ƙirƙiri tsarin ne domin rage lokacin da masana ke ɗauka suna binciken dimbin bayanan da na’urorin binciken sararin samaniya ke tattarawa. Maimakon masana su riƙa duba bayanai ɗaya bayan ɗaya, RAVEN na nazartar su cikin sauri tare da nuna waɗanda suka fi yiwuwa su zama sabbin duniyoyi na gaske.

Jami’ar da ta Ƙirƙire RAVEN

Masana daga jami’ar Warwick a Birtaniya ne suka jagoranci ƙirƙirar RAVEN tare da haɗin gwiwar wasu cibiyoyin binciken ilimin taurari. Manufarsu ita ce haɗa ilimin taurari da fasahar AI domin bunƙasa gano sabbin duniyoyi cikin sauri da inganci. Wannan aiki ya nuna yadda haɗin gwiwar masana kimiyya da ƙwararrun AI ke ƙara sauya hanyoyin gudanar da binciken sararin samaniya.

Yadda AI ɗin ke aiki

RAVEN na aiki ne ta hanyar amfani da fasahar machine learning wajen nazarin sauye-sauyen hasken taurari. Idan wata duniya ta wuce gaban tauraronta, hasken tauraron yana raguwa kaɗan na ɗan lokaci. AI ɗin na nazartar irin waɗannan sauye-sauye tare da kwatanta su da miliyoyin bayanan da aka tattara a baya. Bayan haka,6 yana ba kowace alama maki gwargwadon yiwuwar kasancewarta sabuwar duniya ta gaske, abin da ke taimaka wa masana su mayar da hankali kan bayanan da suka fi muhimmanci.

Bambancin RAVEN da tsaffin hanyoyin

Kafin amfani da RAVEN, masana suna yin nazarin bayanan ne ta sabbin hanyoyin da na zamani ba, inda ake buƙatar lokaci mai tsawo da kuma sa hannun mutane da dama wajen tantance sakamako. Wannan hanya tana iya jawo jinkiri da kuma yiwuwar kuskure saboda yawan bayanan da ake dubawa. RAVEN kuwa tana iya nazarin miliyoyin bayanai cikin ɗan lokaci, tana rage kuskuren da ɗan Adam kan iya yi tare da ƙara yawan duniyoyin da ake iya ganowa. Wannan ya sa ake kallon ta a matsayin wani babban cigaba a amfani da AI wajen binciken sararin samaniya.

Yadda aka gudanar da binciken

Amfani da bayanai daga TESS

Masanan sun gudanar da binciken ne ta hanyar amfani da bayanan da na’urar Transiting Exoplanet Survey Satellite (TESS) ta tattara. TESS tauraron bincike ne na NASA da aka ƙaddamar domin gano duniyoyin da ke kewaya taurari masu kusa da Duniya. Tun bayan fara aikin tauraron, ya tattara ɗimbin bayanai game da miliyoyin taurari a faɗin sararin samaniya.

Nazarin taurari sama da miliyan 2.2

A wannan bincike, RAVEN ya yi nazarin bayanan taurari sama da miliyan 2.2. Wannan adadi ya fi ƙarfin abin da masana za su iya tantancewa cikin ɗan lokaci ta hanyoyin baya. AI ɗin ya binciki canje-canjen haske daga kowanne tauraro domin gano alamun da ke nuna yiwuwar wucewar wata duniya a gabansa.

Amfani da machine learning

Machine learning shi ne ginshiƙin aikin RAVEN. An horar da AI ɗin ta hanyar amfani da bayanan sabbin duniyoyin da aka riga aka tabbatar da su, domin ya koyi bambancewa tsakanin sahihan alamomi da kuma bayanan da ba su da alaƙa da sabbin duniyoyi. Bayan wannan horo, tsarin ya fara nazarin sababbin bayanai tare da ba da hasashen inda ake iya samun sabbin duniyoyi.

Matakan tabbatar da sahihancin sakamako

Bayan RAVEN ya fitar da sakamakonsa, masana ba su amince da shi kai tsaye ba. Sun sake gudanar da ƙarin gwaje-gwaje da nazari ta amfani da wasu hanyoyin kimiyya domin tabbatar da cewa abubuwan da AI ya gano sabbin duniyoyi ne na gaske. Wannan mataki ya taimaka wajen rage yiwuwar kuskure da tabbatar da cewa sakamakon binciken yana da inganci kuma ya dace da ƙa’idojin binciken ilimin taurari.

Sakamakon binciken

Gano sabbin duniyoyi 118

Ɗaya daga cikin manyan nasarorin binciken shi ne gano sabbin duniyoyi guda 118 waɗanda ba a tabbatar da su ba a baya. RAVEN ya gano su ne ta hanyar nazarin bayanan TESS da sauri fiye da yadda ake iya yi ta hanyoyin baya. Wannan ya nuna cewa AI na iya taimakawa wajen hanzarta binciken sararin samaniya.

Sabbin duniyoyi 31

Daga cikin sabbin duniyoyin da aka gano, akwai guda 31 da ba a taɓa tabbatar da samuwarsu ba. Wannan ya ƙara faɗaɗa jerin duniyoyin da aka sani a wajen tsarin falaƙin rana, tare da ba masana sabbin wuraren da za su ci gaba da bincike domin fahimtar yanayinsu da yiwuwar kasancewar rayuwa a cikinsu.

Gano alamomin exoplanets 2,000

Baya ga duniyoyin da aka tabbatar, RAVEN ya kuma gano alamomin sabbin duniyoyi sama da 2,000. Waɗannan duniyoyi ne da ke nuna alamun kasancewa, amma har yanzu suna buƙatar ƙarin bincike da tabbatarwa kafin a saka su cikin jerin duniyoyin da aka tabbatar da su a hukumance.

Nau’o’in duniyoyin da aka gano

Duniyoyin da aka gano sun bambanta sosai. Wasu ƙanana ne masu kama da duniyar earth, yayin da wasu manyan duniyoyi ne masu kama da Jupiter ko Neptune. Haka kuma, akwai duniyoyin da ke kewaya taurari masu zafi sosai, da wasu da ke cikin yankin da yanayinsa zai iya ba da damar kasancewar ruwa, abin da ke ƙara jan hankalin masana wajen ci gaba da bincike kan yiwuwar samun damar rayuwa a wajen duniyar earth.

Muhimmancin wannan bincike

Sauƙaƙa aikin masana

Amfani da RAVEN ya kawo babban sauyi ga ayyukan masana ilimin taurari. A baya, binciken sabbin duniyoyi yana buƙatar masana su shafe lokaci mai tsawo suna nazarin bayanai da hannu domin gano ƙananan sauye-sauyen hasken taurari. Amma da zuwan RAVEN, AI na iya gudanar da wannan aiki cikin sauri tare da ware bayanan da suka fi nuna yiwuwar kasancewar sabbin duniyoyi. Wannan ya ba masana damar mayar da hankali kan zurfafa bincike da tabbatar da sakamakon maimakon ɓata lokaci wajen tantance miliyoyin bayanai.

Saurin bincike

Ɗaya daga cikin manyan fa’idodin RAVEN shi ne rage bata lokacin bincike. Ayyukan da za su iya ɗaukar watanni ko shekaru idan aka yi su ta hanyoyin baya, AI na iya kammala su cikin ɗan lokaci kaɗan. Wannan ya sa ake iya nazarin sabbin bayanai cikin sauri, tare da gano duniyoyi da yawa fiye da yadda ake iya yi a baya.

Gano duniyoyi masu kama da earth

RAVEN ya kuma ƙara damar gano duniyoyin da suke da siffofi masu kama da duniyar earth. Kodayake ba duk duniyoyin da aka gano suke da yanayin rayuwa ba, AI na taimakawa wajen gano waɗanda suke cikin yankin da yanayinsa zai iya ba da damar samuwar ruwa. Irin waɗannan duniyoyi suna da muhimmanci sosai ga binciken yiwuwar rayuwa a wajen duniyar earth.

Gudummawa ga ilimin taurari

Nasarar RAVEN ta nuna yadda fasahar AI ke ƙara taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ilimin taurari. Ta hanyar gano sabbin duniyoyi da kuma taimakawa wajen fahimtar tsarin taurari daban-daban, AI na ba masana damar ƙara fahimtar yadda duniyoyi ke samuwa da kuma yadda tsarin sararin samaniya ke ci gaba da canjawa. Wannan cigaba yana taimakawa wajen faɗaɗa ilimin ɗan Adam game da duniyar da ke kewaye da shi.

Matsayin AI a binciken sararin samaniya

AI a hukumar NASA

A cikin shekarun baya-bayan nan, NASA ta ƙara ƙaimi wajen amfani da fasahar AI ta fuskar gudanar da bincike da sarrafa manyan bayanan da na’urorin bincikenta ke tattarawa. Ana amfani da AI wajen gano sabbin duniyoyi, nazarin hotunan taurari, sa ido kan ayyukan tauraron ɗan Adam, da kuma taimakawa wajen shirya ayyukan binciken sararin samaniya. Wannan ya nuna cewa AI ta zama ɗaya daga cikin muhimman kayan aikin bincike a hukumar.

AI wajen nazarin manyan bayanai

Na’urorin binciken sararin samaniya suna tattara bayanai masu tarin yawa a kowace rana. Saboda girman waɗannan bayanai, yana da wahala masana su tantance su duka cikin lokaci ƙanƙani. AI tana taimakawa wajen tace bayanai, gano muhimman alamomi da kuma ware bayanan da suka fi cancantar ƙarin bincike. Wannan ya rage nauyin aiki a kan masana tare da inganta saurin gano sabbin abubuwa.

ExoMiner da sauran AI na NASA

Kafin RAVEN, NASA ta riga ta ƙirƙiri wasu tsarin AI kamar ExoMiner, wanda aka yi amfani da ita wajen tabbatar da samuwar sabbin duniyoyi ta amfani da bayanan da Kepler Space Telescope ta tattara. ExoMiner ya taimaka wajen tabbatar da dubban exoplanets cikin sauri da daidaito. Haka kuma, NASA na ci gaba da bunƙasa wasu sabbin tsarin AI domin amfani da su a ayyukan binciken duniyar Wata, Mars da sauran sassan sararin samaniya.

Makomar AI a binciken sararin samaniya

Masana suna ganin cewa rawar AI za ta ƙara faɗaɗa a nan gaba. Ana sa ran za a yi amfani da AI wajen sarrafa motocin binciken sararin samaniya masu zaman kansu, gano sabbin taurari da duniyoyi, nazarin bayanan da za a tattara daga duniyar Mars, da kuma taimakawa wajen yanke shawara a lokacin manyan ayyukan binciken sararin samaniya. AI za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ginshiƙan cigaban ilimin sararin samaniya.

Kalubale da gazawar AI

Yiwuwar samun kuskure

Duk da irin cigaban da AI ta samu, ba ta da cikakkiyar kariya daga kuskure. A wasu lokuta tana iya ɗaukar wasu sauye-sauyen haske a matsayin alamar sabbin duniyoyi alhali ba haka ba ne. Haka kuma, tana iya gaza gano wasu duniyoyi idan bayanan da aka tattara ba su da inganci ko kuma suna da hayaniya.

Tabbatarwar masana

Saboda yiwuwar samun kuskure, sakamakon da AI ke bayarwa ba ya zama tabbaci na ƙarshe. Masana ilimin taurari dole ne su sake gudanar da ƙarin bincike da gwaje-gwaje ta amfani da wasu hanyoyin kimiyya domin tabbatar da cewa sabbin duniyoyin da AI ta gano na gaske ne. Wannan ya sa AI ke aiki a matsayin mataimaki, ba mai yanke hukunci na ƙarshe ba.

Matsalolin bayanai

Ingancin aikin AI yana dogara ne da ingancin bayanan da aka ba ta. Idan bayanan sun kasance marasa inganci, ba cikakku ba, ko kuma suna ɗauke da kura-kurai, hakan na iya shafar sahihancin sakamakon da AI za ta bayar. Saboda haka, tattara bayanai masu inganci yana da muhimmanci wajen samun ingantaccen bincike.

Tasirin binciken ga kimiyya

Binciken sabbin duniyoyi ya ƙara faɗaɗa fahimtar masana game da yadda tsarin taurari ke samuwa da kuma yadda suke bunƙasa a cikin sararin samaniya. Kafin gano dubban duniyoyi, masana sun fi dogara da tsarin hasken rana na duniyar earth wajen fahimtar samuwar taurari. Amma binciken da aka gudanar ta amfani da bayanan NASA TESS da kuma dabarun ƙirƙirarriya basirar (AI) ya nuna cewa tsarin taurari na iya samuwa ta hanyoyi daban-daban, kuma akwai duniyoyi masu siffofi da yanayi iri-iri fiye da yadda aka taɓa zato. Wannan ya ƙara bunƙasa ilimin taurari tare da taimaka wa masana wajen inganta ka’idojin da suka shafi samuwar tsarin taurari.

Wani muhimmin tasirin wannan bincike shi ne ƙara kusantar masana ga amsa tambayar da ta daɗe tana jan hankali, wato ko akwai rayuwa a wasu duniyoyi ban da duniyar earth. Duk da cewa ba a tabbatar da samuwar rayuwa a wata sabuwar duniya ba, gano duniyoyi masu kama da duniyar earth ko kuma waɗanda suke cikin yankin da ruwa zai iya kasancewa a matsayin ruwa ya ƙarfafa fatan cewa wata rana za a iya gano alamomin rayuwa a wajen tsarin falaƙin ranarmu. Wannan ne ya sa binciken sabbin duniyoyi ya zama ɗaya daga cikin manyan manufofin ilimin taurari na wannan zamani.

Har ila yau, sakamakon binciken ya taimaka wajen tsara shirye-shiryen bincike na gaba. Masana suna amfani da bayanan da AI ta gano domin zaɓar sabbin duniyoyi mafi dacewa da za a sake bincikawa ta amfani da manyan na’urorin hangen nesa. Wannan yana rage ɓata lokaci da kuɗi, domin maimakon binciken dubban taurari gabaɗaya, ana mayar da hankali kan waɗanda ake ganin suna da mafi girman yiwuwar kasancewa masu muhimmanci.

Binciken ya kuma ƙara tasiri ga ayyukan NASA da sauran hukumomin sararin samaniya kamar ESA da JAXA. Yanzu ana ƙara saka hannun jari wajen haɓaka sabbin na’urorin bincike, tattara bayanai masu inganci, da kuma amfani da AI wajen nazarin miliyoyin bayanan da ake samu daga sararin samaniya. Wannan haɗin gwiwa tsakanin kimiyyar taurari da fasahar AI ya buɗe kofar sabon zamani na binciken sararin samaniya.

Makomar binciken sabbin duniyoyi

Makomar binciken sabbin duniyoyi tana da alaƙa sosai da ƙirƙirar sabbin na’urorin hangen nesa masu ƙarfi. A cikin shekaru masu zuwa, masana suna sa ran amfani da telescopes masu inganci fiye da waɗanda ake da su yanzu, waɗanda za su iya gano ƙananan duniyoyi masu kama da duniyar earth tare da nazarin yanayinsu cikin cikakken bayani. Waɗannan na’urori za su ba masana damar gano ko akwai ruwa, iskar oxygen, methane ko wasu sinadarai da za su iya nuna yiwuwar samun rayuwa.

Haka kuma, haɗa AI da manyan na’urorin telescopes zai ƙara saurin bincike fiye da kowane lokaci. AI za ta ci gaba da nazarin miliyoyin bayanai cikin ɗan lokaci kaɗan, tana gano abubuwan da idanun ɗan Adam ko tsaffin hanyoyi ba za su iya ganowa ba. Wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen gano sabbin duniyoyi da kuma fahimtar siffofinsu cikin sauri da inganci.

Masana suna kuma sa ran cewa bincike na gaba zai kai ga gano dubban sabbin duniyoyi, ciki har da waɗanda suke da girma da yanayi masu kama da duniyar earth. Haka kuma, ana fatan za a sami damar nazarin iskar da ke kewaye da waɗannan duniyoyi domin gano alamomin da za su iya nuna kasancewar rayuwa. Idan hakan ya tabbata, zai zama ɗaya daga cikin manyan nasarorin kimiyya a tarihin ɗan Adam.

A nan gaba, binciken exoplanets na iya sauya yadda mutane ke kallon matsayin duniyar earth a cikin sararin samaniya. Idan aka gano wata duniya da ke ɗauke da alamomin rayuwa, hakan zai canja fahimtar bil’adama game da rayuwa da kuma matsayinmu a wannan babbar duniya ta sararin samaniya. Saboda haka, binciken sabbin duniyoyi ba kawai neman sabbin duniyoyi ba ne, har ila yau hanya ce ta neman amsa wasu daga cikin manyan tambayoyin da suka daɗe suna damun ɗan Adam.

Kammalawa

A taƙaice, amfani da fasahar  ƙirƙirarriyar basira wajen nazarin bayanan NASA TESS ya nuna yadda AI ke sauya hanyar gudanar da binciken ilimin taurari. Gano sabbin exoplanets ya ƙara faɗaɗa fahimtar masana game da samuwar tsarin taurari tare da ƙarfafa bincike kan yiwuwar rayuwa a wajen duniyar earth. Wannan cigaba ya nuna cewa haɗin gwiwar AI da manyan na’urorin bincike zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gano sabbin duniyoyi da warware manyan sirrika na sararin samaniya. A nan gaba, ana sa ran wannan fanni zai samar da sabbin bayanai da za su sauya fahimtar ɗan Adam game da duniya da kuma matsayin rayuwa a faɗin sararin samaniya.

Manazarta

NASA. (2018, April 18). Transiting Exoplanet Survey Satellite (TESS). 

NASA Exoplanet Exploration Program. (n.d.). Discovering exoplanets.

ScienceDaily. (2025, December 18). Artificial intelligence helps astronomers discover more than 100 hidden exoplanets.

University of Warwick. (2025, December 18). RAVEN artificial intelligence identifies more than 100 previously hidden exoplanets.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×