Skip to content

Sakago ya kwace kambun gudun mita 100 daga hannun Usain Bolt

Saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam, wato Humanoid Robot, na daga cikin fasahohin da ke samun gagarumin cigaba a zamanin nan. Ana ƙera su da tsarin jiki mai kama da na ɗan Adam, musamman kai, gangar jiki, hannaye da ƙafafu, domin su iya yin ayyukan da mutane ke yi. Tarihin wannan fasaha ya samo asali ne daga ƙoƙarin masana na ƙirƙirar na’urar da za ta iya motsi, fahimtar muhalli da aiwatar da ayyuka. A farkon wannan fasaha, robots suna yin takamaiman ayyuka ne a cikin yanayin da aka tsara musu. Sai dai cigaban Artificial Intelligence (AI), Computer Vision, Sensors da tsarin sarrafa motsi ya ba su damar yin ayyuka masu rikitarwa.

A yau, manufar ba ta tsaya ga ƙirƙirar robot mai kama da mutum kaɗai ba, ana ƙoƙarin samar da na’urar da za ta iya gani, ji, fahimta, koyo da kuma aiki a duniyar zahiri. Wannan sabon mataki yana da alaƙa da Embodied AI, wato AI da aka haɗa da jikin na’ura domin ta iya mu’amala da zahirin duniya.

A cikin ‘yan shekarun nan, China ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen haɓaka fasahar saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam. Kamfanoni da cibiyoyin bincike na ƙasar suna ƙera robots masu iya yin tafiya, gudu, yin wasanni, ɗaukar kaya da gudanar da ayyuka daban-daban. Ƙasar ta kuma fara amfani da gasanni wajen gwada iyakar ƙarfin waɗannan na’urori. Daga cikin irin waɗannan gasanni akwai World Humanoid Robot Games, wadda ta haɗa robots daga ƙasashe daban-daban domin gwada ƙwarewarsu a wasanni da ayyukan da suka kwaikwayi rayuwa ta zahiri.

Mene ne humanoid robot?

Humanoid Robot saƙago ne da aka tsara da tsarin jiki mai kama da na ɗan Adam, musamman wajen samun gangar jiki, hannaye da ƙafafu domin ya iya yin ayyukan da mutane ke yi. Babban manufarsa ita ce ya iya aiki a wuraren da aka tsara su domin mutane, kamar gidaje, masana’antu da asibitoci. Cigaban AI yana ƙara ba shi damar fahimtar umarni, muhalli da kuma matakin da ya kamata ya ɗauka.

Yadda ya bambanta da sauran robots

Yawancin robots an ƙera su ne domin takamaiman ayyuka, kamar haɗa kayayyaki a masana’anta ko jigilar kaya. Humanoid robot kuwa ana ƙoƙarin ba shi damar yin ayyuka daban-daban a cikin muhallin da ɗan Adam yake amfani da shi. Saboda haka, yana buƙatar haɗin ƙarfi, daidaito, ƙarfin gani, fahimtar muhalli da sarrafa motsi.

Muhimman sassan humanoid robot

Muhimman sassan humanoid robot sun haɗa da jiki da ƙafafu, hannaye da joints, actuators, sensors, kyamara da Computer Vision, processor da AI, da kuma batir.

Actuators suna samar da motsin joints, sensors suna tattara bayanai game da jiki da muhalli, yayin da kyamarori ke taimakawa wajen ganin abin da ke gabansa. Processor da AI suna sarrafa waɗannan bayanai domin robot ya iya yanke shawarar abin da zai yi.

Rawar AI wajen sarrafa saƙago

AI na taimaka wa saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam wajen fahimtar bayanan da yake samu da kuma mayar da su zuwa aiki. Misali, ganin kofi a gaban saƙago kawai bai wadatar ba. Dole ne ya fahimci abin da yake gani, inda yake, yadda zai ɗauke shi ba tare da ya fasa shi ba da kuma inda zai ajiye shi. Wannan shi ne tushen Embodied AI, inda basirar AI ke haɗuwa da jikin saƙago domin ta iya fahimta da aiki a duniyar zahiri.

Mene ne ya faru a Beijing?

Saƙagon China mai suna Tiangong Ultra ya yi gudun mita 100 cikin daƙiƙoƙi 8.86 a gasar World Humanoid Robot Games 2026 da ake gudanarwa a Beijing.

A gasar World Humanoid Robot Games 2026, Tiangong Ultra ya kammala tseren mita 100 cikin daƙiƙoƙi 8.89. Wani saƙagon mai suna Lightning, wanda kamfanin Honor ya ƙera, ya zo kusa da shi a tsawon lokacin daƙiƙoƙi 9.47 seconds. Wannan ya sanya duka robots ɗin biyu cikin lokutan da suka fi tarihin Usain Bolt na daƙiƙoƙi 9.58 sauri. Sai dai wasu robots sun samu matsala bayan sun kai ƙarshen tseren, musamman wajen rage gudu da tsayawa, inda wasu suka faɗi ko suka bugi shingen kariya. Wannan ya nuna cewa iya gudu cikin sauri ba shi kaɗai ne babban ƙalubale ba. Robot yana buƙatar iya sarrafa hanzari, rage gudu da tsayawa cikin aminci.

An gudanar da gasar a Beijing, China, daga ranar 22 zuwa 26 ga Agusta, 2026, a National Speed Skating Oval. Gasar ita ce karo na biyu na World Humanoid Robot Games. An tsara gasar domin haɗa wasanni da gwaje-gwajen da suka kwaikwayi ayyukan rayuwa ta zahiri, domin a fahimci abin da humanoid robots suka riga suka iya yi da kuma inda har yanzu suke fuskantar matsaloli.

Tiangong Ultra ne ya yi wannan nasarar. An danganta cigabansa da Beijing Humanoid Robot Innovation Center. Saƙagon ya riga ya yi fice a shekarar 2025, musamman bayan ya lashe tseren rabin-marathon na humanoid robots. A wannan tseren, ya kammala kusan kilomita 21 cikin awanni 2, mintuna 40 da dakikoki 42. Wannan ya nuna cewa an riga an samu cigaba wajen sarrafa motsin robot na ƙafa biyu a nesa mai tsawo.

Rahotannin da aka danganta da gwajin 2025 sun nuna cewa lokacin mita 100 na robot ɗin ya kasance daƙiƙoƙi 21.50, yayin da a shekarar 2026 ya sauka zuwa daƙiƙoƙi 9.39. Sai dai ya kamata a yi taka-tsantsan wajen kwatanta sakamakon saboda yanayin gwaje-gwajen ba lallai ya kasance iri ɗaya ba.

Sauran saƙago da suka yi fice

Lightning ya yi fice sosai bayan ya kammala mita 100 cikin daƙiƙoƙi 9.47. Rahotanni sun kuma bayyana cewa ya taɓa kammala gudun a daƙiƙoƙi 9.32 a wani gwaji.

Baya ga gudu, gasar ta ƙunshi wasu abubuwa da suka nuna cigaban saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam, ciki har da tsalle da wasanni daban-daban. Wani robot ya kai tsallen tsayi na mita 2.88, yayin da tarihin ɗan Adam a wannan fanni yake a mita 2.45. Wannan ya nuna cewa gasar ba ta mayar da hankali kan gudu kawai ba. Ana amfani da ita wajen gwada iyakar ƙarfin jiki, daidaito, sarrafa motsi da ikon robots na yin ayyukan zahiri.

Adadin robots da ƙasashen da suka halarta

Gasar 2026 ta samu robots 2,056 daga ƙungiyoyi 666 na ƙasashe 16. Wannan ya nuna yadda fannin humanoid robotics yake ƙara samun karɓuwa a duniya. Ƙaruwa irin wannan tana nuna cewa kamfanoni da cibiyoyin bincike suna ƙara saka jari wajen samar da robots da za su iya yin ayyuka a duniyar zahiri.

Wasanni da gwaje-gwajen da aka gudanar

Gasar ta ƙunshi fannoni daban-daban kamar mita 100, mita 400, mita 1,500, relay, hurdles, long jump, ƙwallon ƙafa, table tennis, weightlifting, tug-of-war, wushu, gymnastics, boxing da dance. Wasu daga cikin wasannin suna gwada ƙarfin jiki da saurin robot, yayin da wasu ke gwada daidaito, sarrafa motsi da ikon yin aiki tare da wasu robots. Saboda haka, gasar ta zama wani dandali na gwada fasahar robots a yanayi mai gasa.

Gwaje-gwajen ayyukan rayuwa ta zahiri

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan gasar 2026 shi ne gwaje-gwajen da suka kwaikwayi ayyukan rayuwa ta zahiri. An gwada robots a yanayi kamar gidaje, otal-otal, masana’antu, wuraren gaggawa, ɗakunan ajiya, shaguna da ofisoshi. Wasu ayyukan sun haɗa da haɗa kayan aiki, jera tubali, buɗe kwalba, ɗaukar ƙananan abubuwa da tweezers da haɗa kebul. Waɗannan ayyuka suna buƙatar fiye da ƙarfi ko sauri. Robot yana buƙatar gani, fahimta, sarrafa hannunsa da kuma gyara kuskure idan wani abu ya samu matsala.

Dalilin da ya sa aka ƙara mayar da hankali kan aiki ba wasa kawai ba

Robot na iya yin gudu ko tsalle cikin sauri, amma hakan kaɗai ba ya tabbatar da cewa zai iya zama mai amfani a masana’anta ko gida. Ayyukan rayuwa ta zahiri suna gwada ko robot zai iya yin abubuwa kamar ɗaukar abu ba tare da ya fasa shi ba, haɗa kebul, amfani da kayan aiki da kuma kammala aiki ba tare da mutum yana sarrafa shi kai tsaye ba.

Wannan ya sa gasar ke matsawa daga tambayar “Shin robot zai iya gudu?” zuwa tambayar “Shin robot zai iya yin aikin da mutum yake yi cikin aminci, daidai kuma da kansa?”

Fasahar da ke tare da Tiangong Ultra

Embodied intelligence

Embodied Intelligence na nufin amfani da fasahar AI tare da jikin na’ura domin ta iya fahimtar muhalli da yin aiki a cikinsa. A wannan tsarin, AI bai tsaya wajen sarrafa bayanai a kwamfuta kawai ba, yana haɗuwa da sensors, kyamara, actuators da sauran sassan robot domin fahimta ta koma aiki na zahiri. Wannan fasaha tana da muhimmanci ga saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam saboda duniyar zahiri tana cike da yanayi masu sauyawa. Saƙago dole ne ya iya gane cikas, daidaita jikinsa, ɗaukar abubuwa da kuma gyara kuskure idan wani abu bai tafi yadda aka tsara ba.

Fahimtar muhalli

Robot yana buƙatar sanin abin da ke kewaye da shi kafin ya iya yin aiki. Wannan shi ne aikin computer vision, wanda ke amfani da kyamara da algorithms wajen nazarin abin da robot yake gani. Tsarin na iya taimaka masa wajen gane mutum, abu, hanya ko cikas. Bayan haka, bayanan da aka samu ana amfani da su wajen tsara motsin robot. A gwaje-gwajen ayyukan rayuwa ta zahiri, wannan fasaha tana da muhimmanci saboda robot ba ya aiki a fili mai sauƙi kawai. Ana gwada shi a wuraren da suka yi kama da gidaje, masana’antu, otal-otal, ofisoshi da sauran wuraren aiki.

Sarrafa motsi da daidaita jiki

Daidaita jiki yana daga cikin manyan ƙalubalen saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam. Saƙago mai ƙafafu biyu yana buƙatar sarrafa wurin da yake a kowane lokaci domin kada ya faɗi. Wannan ya fi rikitarwa yayin gudu, saboda saƙago yana motsawa cikin sauri kuma yana buƙatar daidaita ƙafafunsa da sauran sassan jikinsa cikin ɗan lokaci. Nasarar Tiangong Ultra ta nuna cigaban wannan fasaha, amma matsalar da wasu robots suka fuskanta wajen tsayawa bayan gudu ta kuma nuna cewa gudu da tsayawa matsaloli ne daban-daban.

Ƙafafu, joints da actuators

Ƙafafu su ne ginshiƙin motsin saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam. A jikinsu akwai joints, wato mahaɗar da ke ba sassan jiki damar juyawa ko lanƙwasawa. Actuators kuma su ne na’urorin da ke samar da ƙarfin da ake buƙata domin motsa waɗannan mahaɗun. Za a iya kwatanta aikin actuators da aikin tsoka wajen motsa jikin ɗan Adam. A lokacin gudu, saƙago yana buƙatar haɗa ƙarfi, sauri da daidaito. Ƙarfi kaɗai bai isa ba, domin idan motsin ba shi da daidaito, saƙago na iya rasa daidaitp ko faɗuwa.

Na’urorin ji (sensors)

Sensors suna ba robot bayanai game da jikinsa da kuma muhalli. Suna iya taimakawa wajen sanin matsayi, motsi, saurin juyawa, matsin lamba da tuntuɓar ƙasa. Waɗannan bayanai suna taimaka wa tsarin sarrafawa wajen sanin ko saƙago yana daidaita, ko ƙafarsa ta taka ƙasa yadda ya kamata da kuma yadda zai gyara motsinsa. Saboda haka, saƙago ba ya dogara da kyamara kaɗai. Haɗin bayanai daga sensors daban-daban yana ba shi damar samun cikakkiyar fahimtar yanayinsa.

Batir da tsarin sarrafa makamashi

Saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam yana buƙatar makamashi domin kunna processors, sensors, kyamarori da actuators. Saboda haka, batir yana daga cikin muhimman sassan tsarin. Gudun robot da ɗaga kaya suna buƙatar makamashi mai yawa. Wannan ya sa masu ƙera saƙago ke neman daidaito tsakanin ƙarfin batir, nauyin saƙago da tsawon lokacin da zai iya aiki. Saƙago mai nauyi yana buƙatar ƙarin makamashi wajen motsi, yayin da ƙaramin batir zai iya rage tsawon lokacin aiki. Don haka, ingantaccen tsarin makamashi yana da muhimmanci wajen samar da robot da zai iya aiki na dogon lokaci.

Yadda saƙago ke gudu ba tare da remote control ba

Saƙagon da ke gudu ba tare da remote control ba yana amfani da tsarin sarrafa kansa wajen tattara bayanai daga sensors, nazarin yanayinsa da tsara motsinsa. Tsarin yana karɓar bayanai game da wurin da yake da motsinsa, sannan ya yi amfani da su wajen daidaita ƙafafu da sauran sassan jiki.

Wannan ake kira autonomy, wato ikon na’ura na yin aiki ba tare da mutum yana sarrafa kowane motsi kai tsaye ba. Wannan ikon yana da muhimmanci sosai idan ana son amfani da saƙago mai tsarin jikin ɗan Adam a ayyukan rayuwa ta zahiri.

Nasarar Tiangong a gasar 2025

Tiangong Ultra ya riga ya yi fice kafin gasar 2026. A shekarar 2025, ya lashe tseren rabin-marathon na humanoid robots a Beijing, inda ya kammala kusan kilomita 21 cikin awanni 2, mintuna 40 da dakikoki 42. Wannan nasara ta nuna cewa an riga an samu ci gaba wajen sarrafa tafiya da gudun mutum-mutumi na ƙafa biyu a nesa mai tsawo. Rahotannin da aka samu game da gwajin mita 100 sun nuna lokacin 21.50 seconds a 2025, yayin da a 2026 ya sauka zuwa 9.39 seconds.

Cigaban saurin robot cikin shekara guda

Bambancin tsakanin 21.50 da 9.39 seconds ya kai 12.11 seconds. Idan aka kwatanta matsakaicin gudun bisa waɗannan lokuta, ya tashi daga kusan 4.65 m/s zuwa 10.65 m/s. Wannan babban sauyi yana nuna ci gaba wajen sarrafa ƙafafu, daidaita jiki da tsarin sarrafa gudu. Sai dai ya kamata a yi taka-tsantsan, saboda yanayin gwajin 2025 da 2026 ba lallai ya kasance iri ɗaya ba. Don haka, bambancin lokacin ba za a ɗauke shi kai tsaye a matsayin cikakken ma’aunin ci gaban fasahar robot ba.

Dalilin wannan gagarumin cigaba

Cigaban ya samo asali ne daga haɗin fasahohi da dama. Ingantaccen tsarin sarrafa motsi yana taimaka wa robot wajen motsa ƙafa ɗaya yayin da yake kiyaye daidaiton jikinsa. Haka kuma, ci gaban actuators da joints yana ba robot damar samar da ƙarfi da sauri. Sensors suna ba shi bayanai game da matsayinsa da hulɗarsa da ƙasa, yayin da AI da software ke taimaka wajen sarrafa waɗannan bayanai. Ƙarin horo da gwaje-gwaje ma suna da muhimmanci, saboda kowanne gwaji yana taimaka wa masu ƙera robots gano matsaloli da inganta tsarin.

Matsalar tsayawa da sarrafa robot bayan gudu

Duk da nasarar gudun mita 100, wasu robots sun samu matsala wajen rage gudu da tsayawa bayan sun kai ƙarshen tseren. Wasu sun faɗi ko suka bugi shingen kariya. Wannan ya nuna cewa samun saurin gudu kaɗai bai isa ba. Robot yana buƙatar iya hanzartawa, rage gudu, tsayawa da dawo da daidaiton jikinsa cikin aminci.

A gasar wannan na iya zama ƙaramin matsala, amma a masana’anta ko gida, faɗuwar robot kusa da mutum na iya haifar da haɗari. Saboda haka, aminci da daidaito za su kasance muhimman ma’aunai na makomar humanoid robotics.

Ayyukan da humanoid robots za su iya yi

Humanoid robots suna da damar yin ayyuka masu yawa saboda an tsara jikinsu ta yadda zai iya mu’amala da wuraren da mutane ke amfani da su. Duk da haka, akwai bambanci tsakanin abin da robot zai iya yi a gwaji da kuma abin da zai iya yi cikin dogaro da kansa a rayuwar yau da kullum.

A masana’antu

A masana’antu, humanoid robots na iya taimakawa wajen ɗaukar kaya, jigilar abubuwa, jera kayayyaki, haɗa wasu sassa da kuma gudanar da ayyukan da ake maimaitawa. Babbar fa’idarsu ita ce ana iya tsara su domin su yi aiki a wuraren da aka riga aka tsara domin mutane, ba tare da an sake gina dukkan tsarin masana’antar ba.

Haka kuma, za a iya amfani da su wajen ayyukan da suke da nauyi ko haɗari ga ma’aikata. Amma kafin amfani da su ya zama ruwan dare, dole ne a tabbatar da amincinsu, juriyarsu da ikon yin aiki na dogon lokaci ba tare da yawan sa hannun mutum ba.

A gidaje

A gida, humanoid robot na iya taimakawa wajen ɗaukar abubuwa, shirya kayayyaki, tsaftace muhalli, taimakawa wajen wasu ayyukan girki da kuma kai abubuwa daga wuri zuwa wani. Sai dai gida ya fi masana’anta rikitarwa. A masana’anta ana iya tsara muhalli sosai, amma gida yana da mutane, yara, dabbobi, kayan daki da abubuwan da suke sauyawa kullum.

A asibitoci

A asibitoci, humanoid robots na iya taimakawa wajen jigilar kayayyaki, kai wasu abubuwa tsakanin ɗakuna da gudanar da wasu ayyukan yau da kullum da ba sa buƙatar ƙwarewar likita. Amfani da robots na iya rage wa ma’aikatan asibiti wasu ayyuka masu maimaituwa, musamman waɗanda ba sa buƙatar hulɗar ɗan Adam kai tsaye. Sai dai aiki a kusa da marasa lafiya yana buƙatar matakin tsaro mai girma. Robot dole ne ya iya gane mutane da abubuwan da ke kewaye da shi, ya sarrafa motsinsa yadda ya kamata kuma ya tsaya idan wani abu ya bayyana a gabansa.

A harkokin ceto da gaggawa

Humanoid robots na iya zama masu amfani a wuraren da suke da haɗari ga mutane, kamar gine-ginen da suka rushe, wuraren gobara da wuraren da ke ɗauke da abubuwa masu haɗari. Saboda tsarin jikinsu yana kama da na mutum, ana iya tsara su domin su yi amfani da wasu kayan aiki da mutane ke amfani da su. A irin wannan yanayi, haɗin AI, sensors da sarrafa motsi yana da muhimmanci, domin robot yana buƙatar gano hanya, guje wa cikas da yin aiki a yanayi da ba a tsara shi tun farko ba.

A harkar sufuri da dabaru

A ɗakunan ajiya da cibiyoyin rarraba kaya, humanoid robots na iya taimakawa wajen ɗaukar kayayyaki, jera su, jigilar su da kai su wuraren da ake buƙata. Ana iya haɗa su da tsarin kwamfuta domin su karɓi umarni game da abin da za su ɗauka da inda za su kai shi. Wannan na iya rage wasu ayyuka masu nauyi da maimaituwa da mutane ke yi. Amma har yanzu ana buƙatar tabbatar da cewa robot zai iya yin aikin cikin sauri, daidai da aminci ba tare da yawan sa hannun mutum ba.

A ayyukan da ke da haɗari ga mutane

Ɗaya daga cikin manyan dalilan ci gaba da binciken humanoid robots shi ne amfani da su wajen ayyukan da za su iya jefa mutane cikin haɗari. Misalan irin waɗannan ayyuka sun haɗa da aiki kusa da zafi mai tsanani, sinadarai masu haɗari, wuraren da gine-gine suka rushe da wuraren da bala’i ya faru. A irin wannan yanayi, robot ba wai zai maye gurbin mutum saboda ya fi shi ƙarfi ko sauri ba ne. Babbar manufar ita ce rage haɗarin da ɗan Adam zai fuskanta.

Ƙalubale da matsaloli

Duk da gagarumar nasarar da aka samu, har yanzu akwai manyan ƙalubale kafin humanoid robots su zama masu iya yin ayyuka da yawa cikin dogaro da kansu. Gudun Tiangong Ultra na 9.39 seconds ya nuna ƙarfin jiki da sarrafa motsi, amma ba ya nufin robot ya riga ya iya yin dukkan ayyukan ɗan Adam.

Fahimtar duniyar zahiri

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen Embodied AI shi ne baiwa robot damar fahimtar duniyar zahiri yadda mutum yake yi. Duniya tana sauyawa a kowane lokaci. Mutane suna motsi, abubuwa suna canzawa, haske yana sauyawa kuma wani abu na iya bayyana a wurin da robot bai yi tsammani ba. Robot na iya gane cewa akwai kofi a gabansa, amma dole ne ya san yadda zai ɗauke shi ba tare da ya fasa shi ba, inda zai ajiye shi da abin da zai yi idan wani ya toshe masa hanya. Wannan ya sa fahimtar duniyar zahiri ta fi sarrafa bayanai a duniyar dijital rikitarwa.

Dogaro da ingantaccen bayanan horarwa

AI tana buƙatar bayanai domin koyo. Humanoid robot kuma yana buƙatar bayanai game da tafiya, gudu, ɗaga abubuwa, hulɗa da ƙasa da fahimtar muhalli. Idan bayanan horo ba su da yawa ko ba su wakilci yanayi daban-daban ba, robot na iya kasa yin abin da ake tsammani idan ya fuskanci sabon yanayi.

Saboda haka, ana buƙatar tattara bayanai daga kyamarori, sensors da motsin jiki, sannan a yi amfani da su wajen inganta yadda AI ke haɗa fahimta da aiki. Gasa kamar World Humanoid Robot Games na iya taimakawa wajen samar da yanayi na gwaji da bayanan da za su taimaka wa masu bincike gano matsalolin robots da inganta su.

Tsaro da aminci

Robot da ke aiki shi kaɗai a fili ba ya fuskantar irin haɗarin robot da ke aiki kusa da mutane. Idan humanoid robot zai yi aiki a gida, asibiti ko masana’anta, dole ne ya iya gane mutum, kayan aiki da cikas. Haka kuma, dole ne ya iya rage gudu ko tsayawa idan wani abu ya bayyana a gabansa. Matsalar da wasu robots suka fuskanta wajen tsayawa bayan gudun mita 100 ta nuna muhimmancin wannan batu.

Batir da makamashi

Humanoid robot yana amfani da makamashi wajen sarrafa actuators, processors, kyamarori da sensors. Idan yana gudu ko ɗaga kaya masu nauyi, amfani da makamashi yana ƙaruwa. Masu ƙera robots suna buƙatar samar da batir mai ƙarfi wanda ba zai ƙara nauyin robot sosai ba. Robot mai nauyi yana buƙatar ƙarin makamashi wajen motsi, yayin da ƙaramin batir zai iya rage tsawon lokacin aiki. Saboda haka, ana buƙatar daidaito tsakanin nauyi, ƙarfi, saurin aiki da tsawon lokacin batir.

Tsadar samarwa

Ƙera humanoid robot yana buƙatar haɗa hardware mai rikitarwa, kamar actuators, sensors, processors da batir, tare da software da tsarin AI. Bugu da ƙari, ana buƙatar bincike da gwaje-gwaje masu yawa kafin a samar da robot mai aminci da inganci. Saboda haka, akwai tambayar tattalin arziki: shin samar da robot da kula da shi zai fi sauƙi da arha fiye da amfani da ma’aikacin ɗan Adam? Amsar wannan tambayar za ta dogara da irin aikin da robot zai yi da kuma farashin samar da shi.

Kammalawa

Nasarar Tiangong Ultra na yin gudun mita 100 cikin dakikoki 9.39 a Beijing ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a fannin humanoid robotics a watan Agusta 2026. Lokacin ya fi tarihin mita 100 na ɗan Adam, wato daƙiƙoƙi 9.58 na Usain Bolt, sauri, amma bai zama sabon tarihin wasannin motsa jiki na ɗan Adam a hukumance ba.

World Humanoid Robot Games 2026 ta kuma nuna cewa fannin fasahar robotics yana matsawa daga gwada robots a wasanni kawai zuwa gwada su a ayyukan da suka yi kama da na rayuwa ta zahiri. Wannan sauyi yana da muhimmanci saboda makomar humanoid robotics ba za ta dogara kawai da tambayar ko robot zai iya gudu ko tsalle ba, sai dai ko zai iya yin aiki cikin aminci, daidai da dogaro da kansa.

Manazarta

Anadolu Agency. (2026, August 22). 2nd World Humanoid Robot Games open in Beijing. Anadolu Agency.

Huang, J., Gao, J., & Yu, Z. (2026). Orchestrating mechanics, perception and control: Enabling embodied intelligence in humanoid robots. Information Processing & Management, 63(1), 104363.

Ibrahim, A., & Chan Ho-Him, C. (2026, August 22). Chinese humanoid robots smash human records in 100m sprint and high jump at Beijing robot games. Associated Press.

Reuters. (2026, August 22). Chinese robots beat Usain Bolt’s 100m world record at Beijing games. Reuters.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×