Magarya bishiya ce da ake samu a wurare da dama a nahiyar Afirka, musamman a yankunan da ke da zafi kamar su Arewacin Najeriya. Sunanta na kimiyya shi ne Faidherbia albida, kuma ana kiranta da Acacia albida a wasu wurare. A Hausa kuma, akan kiranta da sunan magarya. Ana kuma kiranta da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciya ce da aka tabbatar tana da albarkar daɗewa a doron ƙasa.
Kuma tana ƙunshe da magunguna masu matuƙar mahimmanci ga jikin ɗan Adam kuma ta na da ƙarfin kashe ƙwayoyin cuta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Ana samun magarya a ko’ina a sassan duniya. Magarya ba kawai iya itaciya ba ce, bishiya ce dake ɗauke da ‘ya’ya masu matuƙar amfani. Suna ɗauke da sinadarin magunguna a tattare da su. Tare da ɗanɗano mai daɗi, wanda mutane kan yi amfani da ita bayan an busar da ita ta hanyoyi da dama. Haka nan, bayan ‘ya’yan itaciyar ana amfani da ganyen domin magunganu daban-daban.
Wuraren da magarya take fitowa
Magarya tana iya fitowa a wurare da yawa, kuma mabambanta. Wasu lokutan shukata ake yi wasu lokutan kuma da kanta take fitowa sakammakon abubuwa kamar haka,
- Ka dai an sha an zubar
- Ko ruwa ya jawo ‘ya’yan zuwa wurin,
- Ko kuma ubangiji ya nufa ta fito.
Sai dai kuma tana fitowa a nahiyar Afirka, musamman a yankunan Sahara da Sahel (kamar Najeriya, Nijar, Mali, Chadi, Burkina Faso, Senegal da sauransu). A Najeriya, tana yawan fitowa a jihohin Arewa kamar Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Yobe. Ana samun ta a cikin dausayi, filayen noma, da makiyaya saboda tana jure fari da ƙura.
Yanayin magarya
Magarya Itaciya ce mai tsawo sosai an yi ƙiyasi kan cewa tana iya kaiwa tsayin (mita 15 zuwa 25). Tana da ganye mai launin kore mai haske, kuma suna faɗuwa lokacin damina (saɓanin sauran bishiyoyi). ‘Ya’yanta sun kasance a zagaye (ring-shaped) kamar zobba, a wasu sassan kana kiransu zoben magarya.
Sinadaran magarya
Magarya na ɗauke da sinadarai irin su,
- Tannins
- Flavounoids
- Iron
- Protein
- Calcium
- Potassium
- Soponnins
Tana kuma ɗauke da sinadarin “antioxidant” kuma ta na iya taimakawa wajen magance damuwa da rashin barci, ta na kuma taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi.
Har ila yau, ‘ya’yan itaciyar ta ƙunshi nau’in alkaloids, da saponin, da kuma triterpenoid. Dukkan sinadaran uku su na taimakawa wajen tsaftace jini. Kyakkyawan tsaftataccen jini alama ce da ke nuna cewa duk mahimman gaɓoɓi sun sami isashshen jini mai wadatar iskar oxygen. Wannan ya na sanya ƙara samun kuzari da ingantacciyar lafiya.
Akwai nau’in bitamin C a cikin magarya, wadda ya ke fitar da fata mara kyau da kuma bayar da kariya ga fatar domin lafiyayya ta samu gurbin zama. Wane bincike ya kuma nuna cewar, magarya za ta iya zama babban tushen sinadarin “calcium da phosphorous,” wadda ke taimakawa wajen kula da ƙarkon ƙashin jikin ɗan adam. Musamman ga tsofaffi ko mutanen da ke da raunin ƙashi.
Sassan magarya da amfaninsu
Ganyen magarya
- Ƙarin jini
- Rage zazzaɓi
- Maganin mura da tari
- Wanke ciki da kuma
- Maganin sanyi na mata.
Ɓawon magarya
- Maganin ciwon ciki
- Gyambon ciki
- Ciwon haƙori da haƙarƙari.
‘Ya’yanta magarya
- Ƙarin ƙarfi da kuzari
- Maganin zazzaɓi
- Gyaran fata (idan an shafa ga ƙaiƙayi ko ƙuraje).
Itacen magarya
- Gina gida da buɗaɗɗen ɗaki
- Itacen girki.
Amfanin magarya ga lafiya
- Ciwon daji (cancer): Idan ana dafa garin magarya ana sha da zuma yana kashe ƙwayar cutar daji koda a cikin jini ne idan kuma ya yi miki sai arinka dafa garin magaryar da ruwan khal ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbaɗa garin magaryar.
- Tana ƙara ƙarfin yaƙar cutarfata kamar su tautau, makero, Karzuwa da sauransu
- Ana kwaɓata a zuma arinka sha ana shafawa a wurin da abin ya shafa.
- Shan garinta da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon Jiki.
- Tana magance ulcer idan ana shan ta da madara ko zuma.
- Tana taimakawa lafiyar hanta. Tare da daidaita nauyin mutum.
- Tana tsayar da zaw cikin ƙanƙanin lokaci idan aka sha garinta da ruwa ko koko.
- Tana taimakawa miƙar da ƙasusuwa musamman ga mai karaya.
- Tana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki da ruwan ganyanta wanda aka tafasa. Suna kuma shan garinta da madara.
- Magarya tana warware sihiri kamar yadda malaman sunna suka bayyana. Idan aka jiƙa garin a ruwa tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alƙur’ani mai girma.
- Bugu da ƙari, magarya na da amfani ga tsarin juyawar ƙwaƙwalwa. A al’adance wasu mata kan yi amfani da magarya domin rage juyayi da damuwa.
- Magarya na taimakawa wajen rage ƙiba, kuma ta na zama rigakafi ga kamuwa ga wasu ƙananan cututtuka.
- Magarya tana da matuƙar amfani wajen kiwon shanu, raguna da awaki, suna cin ganyenta da ‘ya’yanta, musamman a lokacin fari.
- Ana dafa ganyen magarya a sha kamar shayi don rage ciwon makogoro da kumburin tonsil.
- Ana amfani da garin ganyen magarya ana wanke gashi da shi domin ya ƙara ƙarfi, ya hana karyewa, kuma ya sa gashi ya yi laushi da sheƙi.
- Shan ruwan dafaffen ganyen magarya yana taimakawa wajen narkewar abinci da kuma kawar da matsalolin ciki kamar kumburi da cushewa.
- Ana niƙa ganyen magarya sabo sannan a shafa a kan raunuka, yana taimakawa wajen saurin kafe su da hana ƙwayoyin cuta shiga.
- Ana shafa ganyen magarya da aka niƙa da ruwa a fuska domin kawar da kuraje da sa fatar fuska ta yi laushi.
Matsalolin magarya
Zawo da ciwon ciki: Cin ‘ya’yan magarya da yawa a lokaci guda yana iya haifar da matsalolin ciki, kamar gudawa, ciwon ciki ko tashin zuciya.
- Ƙarancin jini: Duk da cewa magarya na da amfani, ya kamata a ci daidai gwargwado. Yawan ci ba tare da haɗata da wasu nau’o’in abinci masu gina jiki ba zai iya haifar da ƙarancin bitamin da ma’adanai.
- Allergy: Wasu mutane na iya samun rashin jin daɗi ko rashin lafiyar jiki (allergic) kamar ƙaiƙayi ko ƙumburi bayan cin magarya.
- Ƙurajen fuska: Cin ‘ya’yan magarya da yawa, musamman waɗanda ba su nuna sosai ba, yana iya haifar da fitowar ƙuraje a fuska saboda yawan sikari da sinadarai masu zafi a cikinsu.
- Matsalar mama: Magarya na da ƙarfi, wasu matan da ke shayarwa na iya jin ciwon nono ko cushewarsa idan suka ci ‘ya’yanta da yawa.
- Ƙwayar magarya da ba a tauna da kyau ba, ko kuma yawan cin su a lokaci guda, yana iya haifar da toshewar hanji, musamman a yara.
Manazarta
Anwar, S. (2023, December 30). Amfanin Ganyen Magarya Ga Lafiyar Dan’adam. Leadership Hausa.
National Research Council. (2008). Lost crops of Africa: Volume III: Fruits. Washington, DC: The National Academies Press.
Tsoho, A. B., Bello, M. A., & Muhammad, M. I. (2020). Ethnomedicinal and phytochemical importance of Faidherbia albida in Northern Nigeria. Journal of Medicinal Plants Research, 14(2), 45–51.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.