Skip to content

Bhutan

Bhutan ƙasa ce da ke a yankin kudancin Asiya, a cikin tsaunukan Himalaya. Tana tsakanin ƙasashen China a arewa da Indiya ta ɓangaren kudu, gabas da yamma. Bhutan ƙasa ce mai ƙarancin girma idan aka kwatanta da sauran ƙasashen duniya.

Sunan da aka san Bhutan da shi, shi ne “Land of the Thunder Dragon” a hausance shi ne, saboda tsohuwar al’ada da imaninsu na addinin Buddha da ke da tasiri sosai a rayuwar al’ummar. Ƙasar Bhutan ta yi fice a duniya saboda tsarin ta na gross national happiness, wanda ke mayar da hankali ba kawai ga arzikin kuɗi ba, har ma da jin daɗin rayuwa, lafiya, ilimi da kwanciyar hankalin jama’a.

Tarihin kafuwar Bhutan

Bhutan tana da tarihin da ya samo asali tun ƙarni na sha bakwai, lokacin da wani jagoran addinin Buddha mai suna Zhabdrung Ngawang Namgyal ya haɗa yankunan ƙasar wuri guda tare da kafa tsarin mulki mai tushe a addini da jagoranci na gargajiya. Shi ne ake ɗauka a matsayin wanda ya kafa ƙasar Bhutan ta zamani. A tsawon ƙarnoni, Bhutan ta kasance ƙasar da ta keɓe kanta daga ƙasashen duniya, tana dogaro da tsaunukan Himalaya wajen kare kanta daga mamayewa.

A ƙarni na sha takwas da sha tara, ƙasar ta fuskanci rikice-rikice da yaƙe-yaƙe da maƙwabciyarta India, musamman a lokacin da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka fara faɗaɗa iko a yankin kudancin Asiya.

Bhutan coat of arms
Tambarin coat of arms na ƙasar Bhutan.

A farkon ƙarni na ashirin, an kafa sarautar Wangchuck Dynasty a shekarar 1907, wanda ya zama tsarin sarauta na gado har zuwa yau. Wannan ya kawo zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar bayan tsawon lokaci na rarrabuwar iko tsakanin shugabannin addini da na gargajiya.

A tsakiyar ƙarni na ashirin, Bhutan ta fara buɗe ƙofofinta ga duniya a hankali, inta take ƙulla dangantaka da ƙasashen waje, musamman India.

A shekarar 2008, Bhutan ta yi babban sauyi na siyasa inda ta sauya daga tsarin sarauta zuwa dimokuraɗiyya da tsarin majalisa, inda aka fara gudanar da zaɓe na ƙasa. Amma duk da wannan sauyi, sarki har yanzu yana da muhimmiyar rawar takawa, wanda ke nuna alamar haɗin kan ƙasa da ci gaba.

Yanayin ƙasa da muhalli

Kamar yadda ya gabata, Bhutan na cikin yankin kudancin Asiya a cikin tsaunukan Himalaya. Tana da iyaka da ƙasar China daga arewa, yayin da daga kudu, gabas da yamma kuma take makwabtaka da India. Bhutan tana da faɗin ƙasa kusan kilomita 38,394, wanda ya sa ta kasance daga cikin ƙananan ƙasashe a duniya ta fuskar girma. Duk da haka, yanayin ƙasar ya bambanta sosai daga ƙananan kwarurruka a kudu zuwa manyan tsaunukan Himalaya a arewa, inda ake samun dusar ƙanƙara sosai a shekara.

Bhutan flag
Wannan ita ce tutar ƙasar Bhutan.

Yanayin ƙasar Bhutan ya kasu gida uku da suka haɗa da yankin Kudu, wannan yanki yana da zafi da dazuzzuka masu yawa, kuma shi ne inda aka fi samun gonaki da al’umma. Yankin tsakiya wannan yanki yana da tsaunuka da kwarurruka, inda anan yawancin manyan biranen ƙasar suke. Yankin arewa Wannan shi ne mafi sanyi da tsauri, yana da manyan duwatsu masu tsawo da dusar ƙanƙara.

Bhutan ƙasa ce da ba ta da iyaka da ruwa mai faɗi kai tsaye. Hakan ya sa tattalin arzikinta da sufuri ke dogara sosai da hanyoyin ƙasa da kuma makwabtanta, musamman India. Haka kuma, Bhutan tana daga cikin ƙasashen da ke da matuƙar kula da muhalli, inda fiye da kashi saba’in na ƙasar ke cike da dazuzzuka, wanda ke taimakawa wajen kiyaye yanayi da dabbobi.

Al’umma da harshe

Al’ummomi

Bisa ƙiyasin ƙididdigar jama’a na baya-bayan nan, yawan al’ummar ƙasar ya kai kusan mutum miliyan ɗaya zuwa miliyan ɗaya da rabi. Wannan ƙarancin yawan jama’a yana daga cikin dalilan da suka sa Bhutan ke iya mai da hankali sosai kan muhalli, zaman lafiya da ingancin rayuwar al’umma.

Sannan al’ummar Bhutan sun ƙunshi ƙabilu daban-daban, amma manyan rukuni biyu sune: Ngalop su ne mafi rinjaye a arewa da tsakiyar ƙasar, kuma su ne ke da tasiri sosai a siyasa da addini. Sharchop su ne mazauna gabashin ƙasar, kuma suna da tsohuwar al’ada da harshe na musamman.

Haka kuma akwai wasu ƙananan ƙabilu da suka fito daga yankunan kudancin ƙasar, musamman waɗanda ke da alaƙa da al’ummar India, hakan ya sa ake samun bambancin al’adu a yankin.

Harsuna

Harshe na hukuma a Bhutan shi ne Dzongkha, wanda shi ne harshen da ake amfani da shi a gwamnati, makarantu da yawancin harkokin hukuma. Dzongkha yana da alaƙa da tsofaffin harsunan Tibet, kuma yana ɗaya daga cikin alamomin haɗin kan ƙasar.

Baya ga Dzongkha, akwai harsuna da dama da ake magana da su a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Sharchopkha, wanda ake magana da shi a gabashin ƙasar. Lhotshampa, shi kuma a kudancin ƙasar. Duk da wannan bambancin harsuna, gwamnati tana ƙoƙarin ƙarfafa amfani da Dzongkha domin haɗa kan al’umma da kuma ƙarfafa ainihin al’adun ƙasar.

Addini da al’adu

Addinai

Bhutan ƙasa ce da addini da al’adu suka yi matuƙar tasiri a rayuwar al’ummarta, inda mafi yawan ƴan ƙasar suke bin Buddhism, musamman a yankunan arewa da tsakiyar ƙasar, sannan kuma malamai na addini (monks) suna da daraja sosai a wurin al’ummar su. A kudancin ƙasar kuma, akwai ƙananan al’ummomi da ke bin addinin hindi, musamman waɗanda ke da alaƙa da ƙasar India. Sai dai duk da bambancin addini, ƙasar tana ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da jituwa tsakanin mabiyan addinai daban-daban.

Al’adu

Al’adun Bhutan sun dogara sosai da addini da kuma tsohuwar rayuwar Himalayan. Mutane suna yin rayuwa mai sauƙi, kuma suna girmama manya da zaman lafiya. Ɗaya daga cikin shahararrun al’adunsu shi ne tufafin gargajiya, inda maza suke sa Gho, mata suna sa Kira. Waɗannan tufafi suna nuna asalin al’ada, kuma suna da muhimmanci sosai a makarantu da ofisoshin gwamnati.

Ta fannin bukukuwa kuwa, Bhutan tana da bukukuwa da dama da ake kira Tshechu, wanda ake gudanarwa a haikalai daban-daban. A lokacin waɗannan bukukuwa, ana yin rawar gargajiya da waƙoƙin addini, Addu’o’i da tarukan addini. Waɗannan bukukuwa suna ƙarfafa haɗin kan al’umma da kuma tunatar da su koyarwar addinin Buddha.

Ta ɓangaren rayuwar zamani da al’ada kuwa, duk da shigowar zamani, Bhutan tana ƙoƙarin kiyaye al’adunta na gargajiya. Gwamnati tana da tsari na musamman wanda ke tabbatar da ci gaban ƙasa bai lalata al’adu da ruhin al’umma ba. Haka kuma, ana ƙarfafa mutane su ci gaba da amfani da harshe, tufafi da kuma al’adun gargajiya, domin su zama tushen haɗin kan ƙasa.

Tsarin mulki

Bhutan tana amfani da tsarin sarauta mai bin tsarin dimokuraɗiyya wato Constitutional Monarchy, inda take ƙasar da ke da sarki, amma kuma tana gudanar da mulki ta hanyar tsarin majalisa da zaɓaɓɓun shugabanni.

Sarkin Bhutan shi ne shugaban ƙasa mai tabbatar da haɗin kan ƙasa. A yanzu, sarauta tana cikin Wangchuck Dynasty, inda Saki ke da ikon kare haɗin kan ƙasa, tabbatar da zaman lafiya tare da bayar da jagoranci a manyan al’amuran ƙasa. Duk da haka, ikon sarki a yau yana iyakancewa ne ta kundin tsarin mulki.

Bhutan tana da Majalisa mai sassa biyu wato National Assembly , wato ƴan majalisa da ake zaɓa ta hanyar zaɓe. Da kuma National Council dake aiki a matsayin majalisar kulawa da shawarwari. Wannan tsarin ne ya ba al’umma damar shiga cikin harkokin mulki.

A tsarin gwamnati, Prime minister shi ne shugaban zartarwa a harkar gwamnati. Shi ne kuma ke jagorantar majalisar ministoci da aiwatar da manufofin ƙasa. Bhutan ta samu kundin tsarin mulkinta na farko a shekarar 2008, wanda ya tabbatar da ƴancin siyasa, tsarin zaɓe na dimokuraɗiyya, raba iko tsakanin sarki da gwamnati, kare haƙƙin jama’a da kuma tsarin gudanar da ƙasa.

Ƙasar tana da rabe-raben gudanarwa zuwa gundumomi (Dzongkhags), inda kowace gunduma ke da shugabanci na gida wanda ke taimakawa wajen gudanar da harkokin yau da kullum.

Tattalin arziki

Bhutan tana da ƙarancin tattalin arziki idan aka kwatanta da manyan ƙasashen duniya, amma duk da haka, tattalin arzikin na da tsari mai ɗorewa wanda ya haɗa da Noma, inda shi ne ginshiƙin rayuwar yawancin al’ummar Bhutan, musamman a yankunan karkara da suke noma shinkafa, masara, alkama da kayan lambu. Haka kuma, kiwon dabbobi kamar shanu da tumaki yana taimakawa wajen samar da madara da nama. Duk da haka, yanayin tsaunuka da ƙasa mai tsauri ya haifar da ƙalubalen noma a wasu yankuna.

Haka kuma, Bhutan tana da arzikin koguna masu ƙarfi daga tsaunukan Himalaya, wanda ya sa hydropower ya zama muhimmin tushen tattalin arziki. Ana samar da wutar lantarki daga ruwa, sannan ana fitar da ita zuwa India, wanda hakan ke kawo wa ƙasar babban kudin shiga.

Sannan yawon shaƙatawa na ɗaya daga cikin hanyoyin samun kuɗin ƙasar, kodayake gwamnati tana inganta shi sosai domin kare muhalli da al’adu. Masu yawon buɗe ido suna zuwa ganin tsaunukan Himalaya, Haikalai (monasteries) da al’adun gargajiya da bukukuwa. Bhutan tana amfani da tsarin (high value, low volume tourism) wato tana karɓar baƙi kaɗan, amma masu biyan kuɗi da yawa domin rage lalacewar muhalli.

Kuɗaɗen ƙasar Bhutan
Wasu daga cikin nau’ikan takardun kuɗin ƙasar Bhutan.

A ɓangaren masana’antu kuwa a Bhutan ba su da yawa. Mafi yawanci masana’antun na sarrafa katako ne da kayan gandun daji, wasu kuma na samar da siminti, wasu kuma Ƙananan masana’antun suna samar da abinci.

Sannan Bhutan tana dogaro sosai da shigo da kaya daga ƙasashen waje, musamman daga India, inda ake shigo da man fetur, abinci da kayayyakin masarufi, Injina da kayan gine-gine. A gefe guda kuma, itama tana fitar da wutar lantarki, katako da wasu kayan noma.

Muhimmancin Bhutan a duniya

Bhutan tana da tasiri sosai a duniya ta fuskoki daban-daban na siyasa, muhalli, al’adu da tunanin ci gaban ɗan adam. Babban abinda ya ƙara fito da ƙasar a duniya shine tsarin nan na Gross National Happiness (GNH), wanda ke auna ci gaban ƙasa ba kawai da kuɗi ba, har ma da jin daɗin rayuwar jama’a, lafiyar jiki, ilimi da al’adu, da kuma zaman lafiya da kare muhalli. Wannan ra’ayi ya ja hankalin ƙasashe da masana duniya, domin tsarin ya bambanta da irin nasu.

Ta fuskar kula da muhalli da canjin yanayi kuwa, Bhutan tana daga cikin ƙasashe masu matuƙar kula da muhalli, inda aka santa da ƙasa mai carbon negative, wato tana shan carbon fiye da abin da take fitarwa.

Sannan ƙoƙarin ƙasar na kiyaye dazuzzuka tare da kare nau’ikan dabbobi da tsirrai ya sa ta zama abin koyi a tattaunawar duniya kan canjin yanayi.

Har ila yau, Bhutan tana taka rawa wajen adana al’adun Buddhism na Himalayan, wanda ke da alaƙa da al’adun Tibet da yankin Kudancin Asiya, wannan kuma ya ja hankalin masu bincike da masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya.

Tsarin ƙasar na son ci gaba mai ɗorewa ya ƙara fito da Bhutan a idon duniya, domin tana nuna yadda ƙasa za ta iya ci gaba a hankali ba tare da lalata muhalli ba, sannan zata iya haɗa zamani da al’ada a lokaci guda tare da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai. Wannan ya sa ta zama abin nazari a jami’o’i da cibiyoyin bincike na duniya.

Daga ƙarshe kuma duk da ƙanƙantar ta, Bhutan tana da muhimmiyar alaƙa da makwabtanta musamman India, wanda ke taimaka mata a harkokin tattalin arziki, tsaro da ciniki. Wannan haɗin kai ya sa ta zama babbar mai bada gudunmawa a zaman lafiyar yankin Himalaya.

Matsaloli da ƙalubale

Duk da cewa tana da suna mai kyau a duniya saboda zaman lafiya da tsarin ta na inganta jin daɗi da walwalar jama’a, tana kuma fuskantar wasu manyan matsaloli da ƙalubale da suka haɗa da:

Dogaro da India

Dogaro da ƙasa ɗaya a tattalin arziki, Bhutan tana dogaro sosai da India a harkokin ciniki, shigo da kaya, da kuma sayar da wutar lantarki, Wannan dogaro ya sa tattalin arzikin Bhutan ya kasance mai rauni idan aka samu sauyi a dangantaka ko kasuwanci.

Yawan tsaunuka

Ƙalubalen yanayin ƙasa, kasantuwar Bhutan ƙasa ce mai tsaunuka na Himalayas, sufuri yana da wahala a yankin, saboda tsadar gina hanyoyi, wanda ya ja wasu yankuna suka keɓe kansu daga manyan birane. Wannan kuma yana hana saurin ci gaban tattalin arziki da hidimomin gwamnati.

Ƙarancin masana’antu

Ƙarancin masana’antu da aikin yi, Bhutan ba ta da manyan masana’antu, wanda hakan ke haifar da ƙarancin ayyukan yi ga matasa, dogaro da aikin gwamnati, tare da ƙaura zuwa birane ko ƙasashen waje domin neman aiki.

Tshering Tobgay, firayim ministan Bhutan.
Tshering Tobgay, shi ne firayim ministan ƙasar Bhutan mai ci.

Sauyin yanayi

Sauyin yanayi da muhalli, duk da cewa Bhutan tana da kyakkyawan tsarin kare muhalli, amma tana fuskantar ambaliyar ruwa daga narkewar dusar ƙanƙara da zaizayar ƙasa, sannan ga sauyin yanayi da ke shafar noma da ruwa. Wannan matsala ce mai girma saboda rayuwar jama’a ta dogara ne da noma da yanayi.

Yawan ƙabilu

Kalubalen haɗin kan al’umma, Bhutan tana da ƙabilu da harsuna daban-daban, kuma a wasu lokuta ana samun bambancin ra’ayi tsakanin ƙabilu, tare damatsalolin haɗa al’umma cikin tsarin guda. Gwamnati na ƙoƙarin magance wannan ta hanyar ƙarfafa Dzongkha da manufofin haɗin kai.

Baƙin al’adu

Ƙalubalen zamani da al’ada, shigowar zamani da fasahar sadarwa na kawo sauyin dabi’un matasa, raguwar wasu al’adun gargajiya, da kuma tasirantuwa da al’adun waje, duk da Bhutan na ƙoƙarin daidaitawa tsakanin ci gaban zamani da kiyaye al’ada.

Jerin shugabannin Bhutan tun daga farko

Tun bayan kafuwar masarautar Bhutan ta zamani a shekarar 1907, ƙasar ta kasance ƙarƙashin sarakuna daga gidan sarautar Wangchuck. Ga jerinsu:

  • Ugyen Wangchuck (1907–1926): Shi ne sarkin Bhutan na farko. Ya haɗa yankuna daban-daban na ƙasar tare da kafa masarautar Bhutan ta zamani.
  • Jigme Wangchuck (1926–1952): Ya gaji mahaifinsa, kuma ya ci gaba da kiyaye zaman lafiya da ‘yancin kai na ƙasar.
  • Jigme Dorji Wangchuck (1952–1972): Ana kiransa “Mahaifin Bhutan ta Zamani” saboda gyare-gyaren da ya aiwatar a fannin siyasa, ilimi, da tattalin arziki. Ya kafa majalisar dokoki tare da fara buɗe Bhutan ga duniya.
  • Jigme Singye Wangchuck (1972–2006): Ya shahara wajen ƙirƙirar manufar Gross National Happiness (GNH), wato auna ci gaban ƙasa ta hanyar jin daɗin jama’a ba kawai ta fuskar tattalin arziki ba. A zamaninsa ne aka fara shirye-shiryen dimokiradiyya.
  • Jigme Khesar Namgyel Wangchuck (2006–zuwa yanzu): Shi ne sarkin Bhutan na yanzu. Ya ci gaba da ƙarfafa tsarin dimokiradiyya, ilimi, da ci gaban tattalin arziki, tare da kiyaye al’adun gargajiya na ƙasar.

Sauyin tsarin shugabanci

Bhutan ta kasance cikakkiyar masarauta tun daga shekarar 1907 har zuwa farkon ƙarni na 21. A shekarar 2008, ƙasar ta kafa sabon kundin tsarin mulki wanda ya mayar da ita masarauta mai bin tsarin dimokiradiyya (constitutional monarchy). Tun daga wannan lokaci, sarki yana ci gaba da kasancewa shugaban ƙasa, yayin da Firayim Minista da majalisar dokoki suke gudanar da harkokin gwamnati na yau da kullum.

  • Jigme Thinley (2008–2013): Shi ne Firayim Minista na farko da aka zaɓa bayan Bhutan ta rungumi tsarin dimokiradiyya a shekarar 2008. Ya jagoranci gwamnatin farko ta dimokiradiyya, tare da mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki, kare muhalli, da ci gaba da manufar Gross National Happiness (GNH), wato auna ci gaban ƙasa ta hanyar jin daɗin jama’a.
  • Tshering Tobgay (2013–2018): Ya hau mulki bayan zaɓen shekarar 2013. A lokacin mulkinsa ya fi mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziki, rage matsalar rashin aikin yi, da inganta harkokin ilimi da lafiya. Haka kuma ya yi ƙoƙari wajen ƙara buɗe Bhutan ga masu yawon buɗe ido da masu zuba jari.
  • Lotay Tshering (2018–2024): Kafin ya shiga siyasa, fitaccen likita ne a Bhutan. Ya yi mulki a wani lokaci da aka fuskanci annobar COVID-19, inda gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen kare lafiyar jama’a da kuma farfaɗo da tattalin arziki bayan annobar.
  • Tshering Tobgay (2024–zuwa yanzu): Ya sake komawa kan mulki bayan jam’iyyarsa ta yi nasara a zaɓen shekarar 2024. A halin yanzu yana ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki, jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje, da ƙara inganta harkokin yawon buɗe ido da ayyukan yi ga matasa.

Manazarta

Bhutan (11/03). (n.d.). U.S. Department of State.

Research Starters | EBSCO Research. (n.d.) Bhutan | Geography and Cartography

 

 

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×