Gabon ƙasa ce da take a yankin Afrika ta tsakiya, kuma tana a gaɓar Tekun Atlantic a yammacin Afirka. Ƙasar tana a kan layin Equator, wanda ya sanya ta shiga cikin yankin da ake kira tropical rainforest zone, wato yankin dazuzzuka masu zafi da yawan ruwan sama. Gabon tana da iyaka da Equatorial Guinea da Cameroon a arewa, sannan kuma Republic of the Congo a gabas da kudu. Babban birnin ƙasar shi ne Libreville, wanda yake cibiyar siyasa, tattalin arziƙi da gudanarwar ƙasar. Yawan jama’ar Gabon ya haura miliyan biyu da rabi a ƙiyasin shekarar 2026.
Yanayin ƙasar Gabon
Kamar yadda ya gabata, Gabon tana cikin yankin dazuzzukan Equatorial na Afirka ta tsakiya, wanda ya ba ta yanayi mai zafi da yawan ruwan sama, musamman tsakanin watannin Oktoba zuwa Mayu. Wannan yanayi ya taimaka wajen bunƙasar manyan dazuzzuka da halittu iri-iri a ƙasar. A ɓangaren fasalin ƙasa kuwa, Gabon tana da faɗin ƙasa kusan kilomita murabba’i 267,667, sannan ga dazuzzuka masu kauri.

A yammacin ƙasar akwai gaɓar tekun Atlantic da aƙalla tsawonsa zai kai kilomita 885, yayin da tsakiyar ƙasar da gabashinta ke ɗauke da tsaunuka da manyan filaye. Ɗaya daga cikin shahararrun tsaunukan ƙasar shi ne Mont Iboundji. Haka kuma akwai koguna masu yawa kamar Ogooue River, wanda shi ne mafi girma kuma mafi muhimmanci a ƙasar wajen sufuri da tattalin arziƙi.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta Gabon da wasu ƙasashen shi ne yalwar gandun daji. Sama da kashi 75 na ƙasar na rufe ne da rainforest, wanda yake ɗaya daga cikin mafi girman dazuzzuka a Afirka. Waɗannan dazuzzuka suna ɗauke da namun daji masu yawa kamar giwaye, nau’ikan birai, da wasu nau’ikan tsuntsaye da dabbobi masu wuyar samu.
Al’umma da harshe
Al’ummomi
Ƙasar Gabon ta ƙunshi ƙabilu da dama masu mabambantan al’adu da harsuna. Masana sun bayyana cewa, akwai ƙabilu sama da arba’in a ƙasar, kuma mafi yawa suna daga cikin rukunin Bantu peoples. Daga cikin manyan ƙabilun Gabon akwai Fang, waɗanda sune mafi rinjaye a yawan jama’a, sai kuma Punu, Nzebi, Myene da Teke. Kowace ƙabila tana da nata al’adun da tsarin zamantakewa, gami da harshen gargajiya, wanda ake amfani da shi a rayuwar yau da kullum.
Harsuna
Harshen hukuma a Gabon shi ne Faransanci, wanda ya samo asali daga mulkin mallakar Faransa da ƙasar ta taɓa kasancewa a ƙarƙashinsa. Ana amfani da Faransanci a gwamnati, makarantu, kasuwanci da kafafen sadarwa, kuma shi ne harshen da ya haɗa al’ummomin ƙasar masu bambancin ƙabila da harsuna.
Addini da al’adu
Addinai
Kiristanci shi ne addinin da ya fi rinjaye a ƙasar Gabon, musamman roman catholic da protestant churches, waɗanda suka bazu tun lokacin mulkin mallakar Faransa da ayyukan mishan na turawa. Majami’u suna taka muhimmiyar rawa wajen bayar da ilimi, tarbiyya da zamantakewa. Duk da haka, Addini Musulunci yana ɗaukar matsakaicin kaso na mabiya a ƙasar.
Sannan addinan gargajiya sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma, musamman a yankunan karkara. Wasu al’ummomin kuma suna haɗa koyarwar Kiristanci da al’adun gargajiya, musamman wajen bukukuwa, magungunan gargajiya da al’amuran ruhaniya. Ɗaya daga cikin sanannun addinan gargajiya a Gabon shi ne Bwiti, wanda yake haɗa waƙoƙi, rawa da koyarwar ruhaniya. Wannan addini ya shahara musamman a tsakanin wasu ƙabilu kamar Fang da Mitsogo, kuma yana daga cikin addinin da ya fi bayyana asalin al’adun Gabon.
Al’adu
Al’adun Gabon suna nuna haɗin kai tsakanin ƙabilu daban-daban. Haka kuma, sassaƙar itace da yin masks na gargajiya suna daga cikin fitattun fasahohin al’ummar Gabon, musamman wajen al’amuran addini. Yayin da Masks ɗin na gargajiya ke ɗauke da ma’anoni na ruhaniya da al’adu.
A zamanin yau, al’adun mutan Gabon suna ci gaba da sauyawa sakamakon bunƙasar birane, ilimi da sadarwar zamani. Sai dai duk da haka, gwamnati da masana al’adu suna ƙoƙarin kare al’adun gargajiya domin tabbatar da cewa tarihin ƙasar da al’adunta ba su ɓace ba.
Tarihin kafuwar Gabon
Tarihin Gabon ya samo asali tun kafin zuwan Turawa, lokacin da ƙabilun Bantu suka fara ƙaura zuwa yankin daga wasu sassan Afirka ta tsakiya. Waɗannan ƙabilu sun kafa ƙauyuka da tsarin zamantakewa tare da bunƙasa noma, kamun kifi da kasuwanci. Daga cikin ƙabilun da suka fi tasiri a tarihin ƙasar akwai Fang, Myene da Punu kamar yadda ya gabata, waɗanda suka mamaye yankuna daban-daban na Gabon tun ƙarni da dama da suka gabata.

Turawan Portugal ne suka fara isa yankin Gabon a ƙarni na goma sha biyar, inda suka yi hulɗa da mazauna yankin ta hanyar kasuwanci. Sunan “Gabon” an ce ya samo asali ne daga kalmar Portuguese “gabão” wadda take nufin wata irin riga mai hula, saboda yadda gaɓar kogin Komo ta yi kama da siffar wannan riga.
A shekarar 1885, Gabon ta zama ƙarƙashin ikon Faransa a hukumance a matsayin wani ɓangare na French Equatorial Africa. A lokacin mulkin mallaka, Faransa ta bunƙasa harkokin kasuwanci da gudanarwa da albarkatun ƙasar domin amfanin Turawa. Libreville, babban birnin ƙasar, ya zama cibiyar mulkin mallaka da harkokin gwamnati a yankin.
Gabon ta samu ƴancin kai daga Faransa a ranar 17 ga Agusta, 1960. Bayan samun ƴancin kai, Léon M’ba ya zama shugaban ƙasar na farko, sannan daga baya Omar Bongo ya karɓi mulki a shekarar 1967 bayan rasuwar M’ba. Omar Bongo ya yi mulki na tsawon shekaru fiye da arba’in, wanda ya sanya shi ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi daɗewa a mulki.
Tsarin mulkin Gabon
Gabon tana gudanar da mulki ne ƙarƙashin tsarin jamhuriya mai shugaban ƙasa, inda shugaban ƙasa yake zama shugaban ƙasa kuma shugaban gwamnati a lokaci guda. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shugaban ƙasa iko mai yawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati, naɗa manyan jami’ai da kuma kula da tsaron ƙasa. Ana zaɓar shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen kai tsaye daga hannun jama’a.
Kamar wasu ƙasashen, tsarin mulkin Gabon ya ƙunshi ɓangarori uku, ɓangaren zartarwa, majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari’a. Ɓangaren zartarwa yana ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa tare da firaminista da ministoci. Firaminista yana taimakawa shugaban ƙasa wajen gudanar da ayyukan gwamnati da aiwatar da manufofi.
Majalisar dokokin Gabon tana da tsari na gida biyu (bicameral legislature), wato National Assembly da Senate. Wakilan National Assembly ana zaɓensu ne ta hanyar zaɓen jama’a, yayin da sanatoci suke wakiltar yankuna daban-daban na ƙasar. Ayyukan majalisar sun haɗa da kafa dokoki, duba kasafin kuɗi da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati.
Bangaren shari’a kuwa yana da alhakin tabbatar da adalci da fassara kundin tsarin mulki. Kotun ƙoli da Constitutional Court suna daga cikin manyan kotunan ƙasar. Tsarin shari’ar Gabon ya samo asali ne daga tsarin dokokin Faransa, saboda tasirin mulkin mallaka. Haka kuma, ƙasar tana da tsarin ƙananan hukumomi da yankuna domin sauƙaƙa gudanar da mulki a yankuna daban-daban.
Tattalin arziki
Tattalin arzikin Gabon yana daga cikin mafi ƙarfi a yankin Afirka ta tsakiya, saboda yalwar albarkatun ƙasa da ƙasar take da su. Man fetur shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Gabon, kuma ya kasance babban tushen kuɗaɗen shiga da fitar da kaya zuwa ƙasashen waje tun daga shekarun 1970. Haka kuma, ƙasar tana da manyan albarkatun manganese, uranium da katako, waɗanda suke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa masana’antu da kasuwanci.
Fannin man fetur yana bayar da kaso mai yawa na kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma kuɗaɗen chanji na ƙasashen waje. Manyan kamfanonin mai na ƙasa da na waje suna gudanar da ayyukan haƙar mai musamman a yankunan gaɓar teku. Sai dai masana sun nuna cewa dogaro sosai da man fetur ya sanya tattalin arzikin ƙasar fuskantar matsaloli idan farashin mai ya faɗi a kasuwar duniya. Saboda haka, gwamnati ta fara ƙoƙarin bunƙasa wasu fannoni kamar na noma, yawon buɗe ido da masana’antun sarrafa katako domin rage dogaro da mai kaɗai.
A ɓangaren noma kuwa, duk da cewa ƙasar tana da ƙasa mai kyau da ruwan sama mai yawa, noma bai bunƙasa sosai ba idan aka kwatanta da sauran sassan tattalin arziki. Ana noma kayan abinci kamar rogo, ayaba, koko da kofi musamman a yankunan karkara. Haka kuma kamun kifi yana taimakawa wajen samar da abinci da ayyukan yi ga wasu al’ummomi da ke gaɓar teku.
Gabon tana kuma da yalwar gandun daji, wanda ya sanya fannin katako ya zama muhimmin ɓangare na tattalin arziki. Ana fitar da katako zuwa ƙasashen Turai da Asiya, musamman nau’ikan itatuwa masu tsada. A shekarun baya-bayan nan, gwamnati ta ƙara mayar da hankali kan kare muhalli da amfani da albarkatun gandun daji ta hanya mai ɗorewa.
Muhimmancin Gabon a idon duniya
Gabon tana da muhimmiyar rawar takawa a duniya musamman ta fuskar albarkatun ƙasa, kare muhalli da kuma siyasar yankin Afirka ta tsakiya. Duk da cewa ƙasar ba ta da yawan jama’a sosai, amma tana daga cikin ƙasashen Afirka masu arzikin man fetur da ma’adinai. Fitar da man fetur da manganese zuwa ƙasashen duniya ya sanya Gabon ta zama muhimmiyar abokiyar kasuwanci ga ƙasashe da dama, musamman Faransa, China da Amurka. Haka kuma, tattalin arzikin ƙasar yana taka rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin Central Africa.

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ƙara ma Gabon tasiri a duniya shi ne kare muhalli da gandun daji. Sama da kashi 75 na ƙasar na rufe da rainforest, wanda yake daga cikin mafi girman dazuzzukan Equatorial a duniya. Waɗannan dazuzzuka suna taimakawa wajen rage ɗumamar yanayi ta hanyar shan iskar carbon dioxide daga sararin samaniya. Don haka, masana muhalli suna kallon Gabon a matsayin muhimmiyar ƙasa wajen kare yanayin duniya da kuma halittu masu rai.
A shekarar 2002, gwamnatin Gabon ta kafa manyan national parks guda goma sha uku domin kare namun daji da gandun daji. Wannan mataki ya ƙara jawo hankalin duniya wajen harkokin yawon buɗe ido da kare muhalli. Gabon tana daga cikin ƙasashen Afirka da ake yabawa saboda ƙoƙarin da take yi wajen kiyaye giwaye na daji, gorilla da chimpanzee, waɗanda suke cikin dabbobin da ke fuskantar barazanar ɓacewa.
A ɓangaren siyasa kuwa, Gabon tana taka rawa a ƙungiyoyin yankin Afirka kamar Economic Community of Central African States (ECCAS) da African Union (AU). Tsawon shekaru, ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun kwanciyar hankali a yankin Afirka ta tsakiya idan aka kwatanta da wasu maƙwabtan ƙasashe. Wannan ya ba ta damar kasancewa muhimmiyar ƙasa wajen tattaunawar siyasa, zaman lafiya da haɗin kan yankin.
Matsaloli da ƙalubale
Duk da yalwar albarkatun ƙasa da tattalin arzikin da Gabon take da shi, ƙasar tana fuskantar matsaloli da ƙalubale da dama a ɓangarori daban-daban. Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen ƙasar shi ne dogaro sosai da man fetur wajen tattalin arziki. Tun shekaru da dama, mafi yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati suna fitowa ne daga harkar mai. Wannan ya sanya tattalin arzikin Gabon ya ke fuskantar matsala idan farashin mai ya faɗi a kasuwar duniya. Masana tattalin arziki suna ganin cewa rashin bunƙasa sauran fannoni kamar noma da masana’antu ya ƙara tsananta wannan matsala.
Wata babbar matsala kuma ita ce rashin daidaiton rabon arziki tsakanin jama’a. Duk da cewa Gabon tana daga cikin ƙasashen Afirka masu matsakaicin yawan kuɗin shiga ga kowane mutum, har yanzu akwai talauci da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa da mazauna karkara. Manyan birane kamar Libreville suna samun ci gaba fiye da wasu yankuna, wanda ke haifar da bambanci a rayuwa da samun ayyukan yi.
A ɓangaren siyasa kuwa, Gabon ta sha fuskantar zarge-zargen rashin cikakken dimokuraɗiyya da yawaitar ikon shugabanni na dogon lokaci. Mulkin Omar Bongo da na ɗansa Ali Bongo Ondimba sun jawo muhawara daga cikin gida da kuma ƙasashen waje dangane da sahihancin zaɓe da tsarin siyasa. A wasu lokuta, an samu zanga-zanga da tashin hankali bayan zaɓe sakamakon rashin gamsuwa daga ɓangarorin adawa.

Haka kuma, duk da ƙoƙarin kare muhalli, sare dazuzzuka da matsin lamba daga ayyukan hakar ma’adinai suna ci gaba da zama barazana ga gandun daji da namun dajin ƙasar. Masana muhalli suna nuna damuwa kan bunƙasar tattalin arziki ba tare da tsari mai ɗorewa ba na iya haifar da lalacewar muhalli a nan gaba. Saboda haka, Gabon tana ƙoƙarin haɗa ci gaban tattalin arziki da kuma kare albarkatun muhalli domin tabbatar da dorewar cigaba.
Jerin sunayen shugabannin Gabon
Tun bayan samun ƴancin kai daga Faransa a shekarar 1960, Gabon ta samu shugabanni masu zuwa a matsayin shugabannin ƙasa:
- Léon M’ba (1960 – 1967): Shi ne shugaban ƙasar na farko bayan ƴancin kai. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsarin mulkin farko na Gabon kafin rasuwarsa a 1967.
- Omar Bongo Ondimba (1967 – 2009): Ya hau mulki bayan rasuwar Léon M’ba, kuma ya yi mulki na fiye da shekaru 40. A zamaninsa, Gabon ta kasance ƙarƙashin tsarin jam’iyya guda na dogon lokaci kafin sauye-sauyen siyasa.
- Ali Bongo Ondimba (2009 – 2023): Ya gaji mulki daga mahaifinsa Omar Bongo. A lokacinsa an samu ƙarin tattaunawa kan dimokuraɗiyya da zaɓe, tare da ci gaba da amfani da arzikin man fetur a tattalin arziki.
- Brice Clotaire Oligui Nguema (2023 – zuwa yanzu): Ya zama shugaban riƙon ƙwarya bayan juyin mulkin soji da aka yi a shekarar 2023, wanda ya kawo ƙarshen mulkin Ali Bongo a wancan lokaci.
Manazarta
History World. (n.d.). HISTORY OF GABON | HistoryWorld.
Papisco. (2021, March 11). Culture, languages & religions | Discover Afrika.
Historyrep. (2025, January 22). Complete list of Gabon presidents from 1960 till date. History Rep.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.








