Skip to content

Nauyi

Nauyi wani muhimmin batu ne a fannin kimiyyar lissafi wanda ke bayyana ƙarfin jan da ƙasa ke yi wa wani abu. A taƙaice, nauyi shi ne irin ƙarfin da ke jan abu zuwa ƙasa sakamakon tasirin gravity. Duk wani abu mai nauyi, ko ƙanƙanta ko girma, yana fuskantar wannan ƙarfin muddin yana cikin sararin gravity na wata duniya ko wani wata a sararin samaniya. Wannan yana nuna cewa nauyi ba sifa ce ta abu, wata alaka ce tsakanin abin da ƙarfin gravity ke aiki a kansa da kuma wurin da yake.

A rayuwar yau da kullum, mutane da dama kan ɗauki nauyi a matsayin yadda abu yake da sauƙin ɗagawa ko wahalar motsawa. Duk da yake wannan fahimta tana da alaƙa da ma’anar kimiyya, a ilimin physics nauyi yana da ma’ana mafi zurfi, domin ana kallon shi a matsayin ƙarfin da ake iya aunawa da ƙididdigewa ta amfani da ka’idojin kimiyya. Saboda haka, fahimtar nauyi ta fuskar kimiyya yana taimakawa wajen gane yadda abubuwa ke motsi, yadda suke tsayuwa, da yadda suke mu’amala da ƙarfin jan da ƙasa ke yi musu.

Ma’anar nauyi a physics

A ilimin physics, nauyi ana bayyana shi a matsayin ƙarfin da gravity ke yi wa abu mai mass. Wannan ƙarfin yana jawo abu zuwa tsakiyar jikin da ke samar da gravity, kamar yadda doron ƙasa ke jan abubuwa zuwa gare ta. Saboda haka, idan aka ce abu yana da nauyi, ana nufin akwai wani ƙarfin gravity da ke aiki a kansa.

Ana lissafa nauyi ta hanyar ninka mass da ƙarfin gravity, wato:

Weight = Mass × Gravity

Wannan ka’ida tana nuna cewa nauyi yana dogara da abubuwa biyu: yawan mass da kuma ƙarfin gravity. Idan ɗaya daga cikinsu ya canja, to nauyin ma zai canja. Wannan shi ya sa nauyin abu yake bambanta daga duniya zuwa wata ko zuwa wani wuri daban a sararin samaniya.

A ilimin kimiyya, ana auna nauyi da ma’aunin newton (N), domin ana ɗaukar nauyi a matsayin wani nau’i na ƙarfi. Wannan yana nuna cewa nauyi ba yawan abu ba ne face ƙarfin da ke aiki a kan abu.

Muhimmancin nazarin nauyi

Nauyi yana da muhimmanci sosai a fannoni daban-daban na rayuwar ɗan Adam da kuma a fagen binciken kimiyya. A rayuwar yau da kullum, ana amfani da ilimin nauyi wajen auna kayayyaki, tsara gine-gine, ƙididdige nauyin ababen hawa, da kuma tabbatar da daidaito a harkokin kasuwanci. Misali, idan ana sayar da kaya a kasuwa, nauyin kayan yana tabbatar da adalci tsakanin mai saye da mai sayarwa. Haka kuma, a fannin sufuri, sanin nauyin motoci, jiragen ruwa, da jiragen sama yana taimakawa wajen tabbatar da tsaro da ingancin aiki.

A bangaren kimiyya kuwa, nazarin nauyi yana taimakawa wajen fahimtar yadda dokokin motsi ke aiki. Injiniyoyi suna amfani da ilimin nauyi wajen tsara gine-gine da injuna domin su iya ɗaukar nauyin da ake bukata ba tare da haɗari ba. A ilimin sararin samaniya ma, fahimtar nauyi na taimaka wa masana wajen sanin yadda abubuwa ke motsi a sararin samaniya, da yadda ‘yan sama jannati ke rayuwa a wuraren da gravity ya ragu sosai. Saboda haka, ilimin nauyi yana da muhimmanci wajen ci gaban fasaha da kimiyya.

Bambanci tsakanin weight da mass

Duk da cewa mutane da yawa kan rikita tsakanin nauyi (weight) da mass, a kimiyyance abubuwa biyu ne masu ma’ana daban. Mass yana nufin yawan abin da ke cikin wani jiki, wato adadin girman da abu yake da shi. Wannan adadi ba ya canjawa ko da an canja wurin abu daga wannan muhalli zuwa wani. Alal misali, idan mutum yana da mass na kilogram sittin a doron ƙasa, mass ɗinsa zai ci gaba da zama haka ko da ya je duniyar wata.

Nauyin dutse
Nauyin abubuwa na tallaka bisa ƙarfin gravity da kuma muhalli ko wurin da suka kasance.

Nauyi kuwa yana nufin ƙarfin da gravity ke yi wa wannan mass. Saboda haka, nauyi yana iya canjawa gwargwadon ƙarfin gravity na wurin da abu yake. Misali, nauyin mutum a wata zai ragu idan aka kwatanta da nauyinsa a doron ƙasa, domin ƙarfin gravity na wata ya fi rauni. Wannan yana nuna cewa mass abu ne na dindindin, yayin da nauyi ke sauyawa gwargwadon tasirin gravity.

Wannan bambanci yana da matuƙar muhimmanci a ilimin physics, domin yana taimakawa wajen fahimtar dangantakar abubuwa da ƙarfin jan da ƙasa ke yi musu. Rashin bambancewa tsakanin mass da weight na iya haifar da kuskure wajen ƙididdiga da fahimtar ka’idojin kimiyya.

Nauyi a matsayin ƙarfin gravity

A matsayin ƙarfi, nauyi yana cikin rukuni na ƙarfin da ake kira gravitational force. Wannan ƙarfin yana samuwa ne sakamakon jan da manyan abubuwa kamar duniya ke yi wa abubuwa masu mass. Wannan jan shi ne yake sa abubuwa su faɗo ƙasa idan aka sake su daga sama.

Ƙarfin gravity yana aiki a kan kowane abu mai mass ba tare da la’akari da girman sa ba. Wannan yana nufin ƙaramin dutse da babban dutse duka gravity yana aiki a kansu, kodayake ƙarfin da kowanne yake samu ya bambanta gwargwadon mass ɗinsa. Saboda haka, nauyi shi ne sakamakon haɗuwar mass na abu da ƙarfin gravity na wurin da yake.

Wannan fahimta tana taimakawa wajen bayyana dalilin da ya sa abubuwa ke faɗowa ƙasa da kuma yadda ake ƙididdige ƙarfin da ke aiki a kansu. Haka kuma tana da matuƙar muhimmanci a fannin injiniyanci, sararin samaniya, da sauran fannonin kimiyya.

Dangantakar nauyi da gravity

Nauyi yana da alaƙa kai tsaye da ƙarfin jan da ƙasa ke yi, domin idan babu gravity to babu abin da za a kira nauyi. Idan abu yana cikin wurin da babu tasirin gravity sosai, kamar a sararin samaniya, nauyinsa zai ragu ƙwarai ko ma ya zama kamar babu. Wannan shi ake kira weightlessness, wato yanayin da nauyi ya ragu sosai saboda ƙarancin gravity.

A doron ƙasa, ƙarfin gravity yana da ƙarfi sosai idan aka kwatanta da sauran wurare kamar duniyar wata, shi ya sa nauyin abubuwa a duniya ya fi yawa. Misali, idan mutum yana da nauyin newton 600 a duniya, zai iya samun kusan newton 100 a duniyar wata saboda ƙarfin gravity na wata ya yi ƙasa sosai.

Wannan dangantaka tsakanin nauyi da ƙarfin gravity ita ce ginshiƙin fahimtar yadda abubuwa ke motsi a sararin samaniya da kuma yadda ake tsara ayyukan kimiyya da injiniyanci. Haka kuma tana taimaka wa masana wajen fahimtar yanayin duniyoyi daban-daban da yadda gravity ke tasiri a kansu.

Tarihin fahimtar nauyi

Tun kafin bunƙasar kimiyyar zamani, mutane sun riga sun fara lura da yadda abubuwa ke faɗowa ƙasa da kuma yadda wasu abubuwa suke da nauyi fiye da wasu. Masana falsafa na tsohuwar duniya, musamman na zamanin Girka, sun yi ƙoƙarin bayyana dalilin da ya sa abubuwa ke komawa ƙasa idan aka sake su daga sama. A wancan lokaci, an yi imanin cewa abubuwa masu nauyi suna da wata dabi’a ta komawa zuwa mazauninsu na asali, wato ƙasa. Wannan fahimta ta samo asali ne daga ra’ayoyin masana kamar Aristotle, wanda ya yi bayani cewa abubuwa masu nauyi suna motsawa zuwa ƙasa saboda yanayinsu na halitta.

Duk da cewa wannan tsohuwar fahimta ta taimaka wajen gina tunanin farko game da nauyi, ba ta dogara da cikakken binciken gwaji ko lissafi ba. An fi karkata ne ga tunanin falsafa maimakon hujjojin kimiyya. Saboda haka, fahimtar nauyi a wancan lokaci ba ta kai matsayin da za ta iya bayyana ainihin dangantakar da ke tsakanin abu da ƙarfin jan da ƙasa ke yi masa ba.

Da zuwan masana kimiyya na ƙarni na goma sha shida da na goma sha bakwai, an fara yin gwaje-gwaje da lura ta hanyar da ta fi inganci. Wannan ya haifar da sauyi daga tsohuwar fahimta ta falsafa zuwa fahimtar kimiyya mai tushe a kan gwaji da lissafi. Wannan canji shi ne ya kafa harsashin fahimtar nauyi kamar yadda aka sani a yau.

Gudunmawar Isaac Newton

Babban sauyi a tarihin fahimtar nauyi ya zo ne ta hannun Isaac Newton, wanda ya bayyana yadda nauyi yake da alaƙa da ƙa’idar gravity. Newton ya fahimci cewa ƙarfin da ke jawo abu ya faɗo ƙasa shi ne irin wannan ƙarfin da ke riƙe wata da sauran duniyoyi a cikin tsarin sararin samaniya. Wannan tunani ya zama muhimmin mataki wajen haɗa abin da ke faruwa a doron ƙasa da abin da ke faruwa a sararin samaniya a ƙarƙashin doka guda.

Newton ya bayyana cewa duk wani abu mai ɗauke da mass yana jan wani abu mai mass da wani ƙarfi da ake kira gravity. Wannan ƙarfi shi ne yake haifar da nauyi idan abu yana kusa da doron ƙasa ko wasu duniyoyin. Ta wannan fahimta, Newton ya nuna cewa nauyi ba kawai wani yanayi na abu ba ne, face sakamakon wani ƙarfi ne da ke aiki a kansa.

Gudunmawar Newton ta sauya yadda duniya ke kallon nauyi, domin ya samar da bayani mai tushe na lissafi da gwaji wanda ya wuce tsoffin ra’ayoyi na falsafa. Wannan ya zama ginshiƙi ga ilimin mechanics da sauran sassan kimiyyar lissafi. Har yau, fahimtar nauyi da gravity tana ci gaba da dogaro da tubalin da Newton ya kafa.

Tasirin ƙa’idar gravity

Ƙa’idar gravity ta Newton ta yi matuƙar tasiri wajen bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha. Ta hanyar wannan ƙa’ida, masana sun samu damar fahimtar yadda abubuwa ke motsi a doron ƙasa da kuma yadda taurari da duniyoyi ke zagayawa a sararin samaniya. Wannan ya ba da damar yin hasashe mai inganci game da motsin abubuwa da kuma tsara lissafe-lissafen da suka shafi nauyi da motsi.

A fannin injiniya, ƙa’idar gravity ta taimaka wajen tsara gine-gine, injuna, da hanyoyin sufuri ta yadda za su iya jure nauyin da ake ɗora musu. A fannin sararin samaniya kuwa, dokar gravity ta zama ginshiƙi wajen ƙididdige yadda jiragen sama da tauraron dan Adam za su tashi da kuma yadda za su zagaya a sararin samaniya.

Tsarin lissafin nauyi

A ilimin physics, ana lissafa nauyi ta hanyar amfani da wata muhimmiyar ka’ida da ke bayyana alaƙar da ke tsakanin mass na abu da kuma ƙarfin gravity da ke aiki a kansa. Wannan ka’ida tana nuna cewa nauyi yana ƙaruwa idan mass ya ƙaru ko kuma idan ƙarfin gravity ya fi ƙarfi. Haka kuma, idan ƙarfin gravity ya ragu, nauyi ma zai ragu ko da mass bai canja ba.

Wannan tsarin lissafi ya ba da damar auna nauyi daidai ta hanyar amfani da ƙididdiga maimakon zato. Hakan yana da matuƙar muhimmanci a fannoni kamar injiniyanci, kimiyyar sararin samaniya, da ilimin motsi, inda ake buƙatar sanin ainihin nauyin abu domin tsara aiki yadda ya dace.

Ta hanyar wannan ka’ida, masana sun fahimci cewa nauyi ba wani adadi ne na dindindin ba, domin yana canjawa gwargwadon ƙarfin gravity. Wannan shi ne dalilin da ya sa nauyin abu a duniyar wata ya bambanta da nauyinsa a doron ƙasa.

Ka’idar lissafin nauyi ita ce:

Weight = Mass × Gravity

Wannan yana nufin cewa nauyi yana samuwa ne ta hanyar ninka mass na abu da ƙarfin gravity na wurin da abu yake. Idan mass ya yi yawa, nauyi zai ƙaru. Haka kuma idan gravity ya fi ƙarfi, nauyin ma zai fi yawa. Misali, idan abu yana da mass na kilogram 10, kuma ƙarfin gravity na wurin shi ne mita 9.8 a cikin sakan biyu, to nauyin abin zai zama newton 98. Wannan misalin yana nuna yadda nauyi ke dogara kai tsaye da mass da gravity. Wannan ka’ida tana da matuƙar amfani domin tana bayyana a sarari cewa nauyi sakamakon karfin gravity ne, ba wai adadin abu ba.

Bayanin W, m, da g

A cikin ka’idar Weight = Mass × Gravity, kowanne harafi yana da ma’anarsa ta musamman.

  • Harafin W yana nufin (weight) nauyi, wato ƙarfin gravity da ke aiki a kan abu. Ana auna shi da naúrar newton.
  • Harafin m yana nufin mass, wato yawan abin da ke cikin abu. Ana auna mass da kilogram, kuma yawanci ba ya canjawa ko da an canja wurin abu daga wannan wuri zuwa wani.
  • Harafin g yana nufin ƙarfin jan da ƙasa ke yi a kan kowanne kilogram na abu. A doron ƙasa, wannan adadi yawanci yana kusan 9.8 m/s². Wannan shi ne adadin da ke sa nauyi ya kasance daban a wurare daban-daban.

Ma’aunin auna nauyi

Newton a matsayin SI Unit

A ilimin kimiyya, ana auna nauyi da naúrar newton (N), wadda ita ce SI unit na gravity. Tun da nauyi wani nau’i ne na ƙarfi, ya zama dole a auna shi da naúrar ƙarfi maimakon ta mass. Newton guda ɗaya yana wakiltar ƙarfin da ake buƙata domin bai wa abu mai ɗauke da mass kilogram ɗaya saurin motsi na mita ɗaya a cikin sakan biyu.

Nauyi a duniyar wata
Nauyin mutum a duniya na bambata matuƙa idan aka kwatanta da nauyinsa a duniyar wata sakamakon ƙarfin gravity.

Amfani da newton a matsayin ma’aunin nauyi yana taimaka wa masana wajen bambancewa tsakanin mass da weight. Yayin da mass ake aunawa da kilogram, nauyi kuwa ana aunawa da newton saboda yana wakiltar ƙarfin gravity. Wannan tsarin ma’auni yana da matuƙar muhimmanci a kimiyya domin yana tabbatar da daidaito da sauƙin fahimtar sakamakon gwaji da ƙididdiga.

Dangantakar newton da kilogram

Akwai dangantaka kai tsaye tsakanin newton da kilogram ta hanyar gravity. Idan abu yana da mass na kilogram ɗaya a doron ƙasa, nauyinsa zai kusan zama 9.8 newtons. Wannan yana nuna cewa kilogram na mass guda ɗaya yana samar da nauyi na kusan newton 9.8 a ƙarƙashin gravity na duniya.

Saboda haka, idan aka san mass na abu, za a iya lissafa nauyinsa ta hanyar ninka kilogram ɗin da 9.8. Wannan alaƙa tana taimaka wa masu nazarin physics wajen sauya mass zuwa nauyi cikin sauƙi. Wannan dangantaka kuma tana nuna cewa kilogram da newton ba abu guda ba ne; kilogram na nufin mass, yayin da newton ke nufin nauyi ko force.

Nauyi a duniya

A doron ƙasa, gravity yana da ƙarfi mai kusan 9.8 m/s², wanda ke nufin cewa kowanne kilogram na mass yana fuskantar nauyi na kusan 9.8 newtons. Wannan shi ne dalilin da ya sa abubuwa ke da wani takamaiman nauyi a duniya. Misali, idan abu yana da mass na kilogram goma, nauyinsa a duniya zai kusan zama newton casa’in da takwas. Wannan ƙima tana taimaka wa masana wajen yin ƙididdigar nauyi daidai a ayyukan yau da kullum da na kimiyya.

Nauyi a duniyar wata

A duniyar wata, ƙarfin gravity ya fi rauni sosai idan aka kwatanta da na duniya. Yana kusan kashi ɗaya cikin shida na gravity na duniya. Wannan yana nufin cewa abin da yake da nauyi mai yawa a duniya zai yi sauƙi sosai idan aka kai shi duniyar wata. Misali, idan mutum yana da nauyin newton 600 a duniya, a wata nauyinsa zai ragu zuwa kusan newton 100. Wannan canjin yana faruwa ne saboda gravity na wata ya yi ƙasa sosai, ba wai saboda mass ɗin mutum ya canja ba.

Nauyi a sauran duniyoyi

A sauran duniyoyi, nauyi yana canjawa gwargwadon girman gravity na kowace duniya. A duniyoyi masu girman gaske kamar Jupiter, gravity ya fi na duniya ƙarfi, saboda haka nauyin abu zai ƙaru idan yana can. A wasu duniyoyi masu ƙarancin gravity kuma, nauyi zai ragu. Wannan yana nuna cewa nauyi ba wata sifa ce ta dindindin ba, domin yana dogara da muhallin da abu yake ciki. Abin da bai canjawa shi ne mass, amma nauyi yana sauyawa da gravity.

Na’urorin auna nauyi

Spring balance

Spring balance wata na’ura ce da ake amfani da ita wajen auna nauyi ta hanyar amfani da faɗaɗawar spring. Wannan kayan aiki yana aiki ne bisa ka’idar cewa idan aka ɗora abu a kan spring, spring ɗin zai miƙe gwargwadon nauyin abin. Adadin miƙewar spring ɗin shi ne ake amfani da shi wajen tantance nauyin. Wannan kayan aiki yana auna nauyi kai tsaye a cikin newton, saboda yana auna ƙarfin da gravity ke yi wa abu. Saboda haka, spring balance yana da amfani sosai a gwaje-gwajen physics domin yana ba da damar auna nauyi kai tsaye.

Beam balance

Beam balance wani kayan awo ne da ke aiki ta hanyar kwatanta mass na abubuwa biyu. Yana da sanda mai daidaito a tsakiya, inda ake ɗora abu a gefe ɗaya sannan a sanya ma’auni a ɗaya gefen har sai an samu daidaito. Wannan kayan aiki ba ya auna nauyi kai tsaye, sai dai yana auna mass. Duk da haka, ana amfani da shi a matsayin kayan auna nauyi a rayuwar yau da kullum saboda alaƙar da ke tsakanin mass da nauyi. Beam balance yana da matuƙar amfani saboda yana ba da sahihin sakamako ba tare da dogaro da spring ba. Wannan ya sa ake amfani da shi a ɗakunan gwaje-gwaje da wuraren da ake buƙatar daidaitaccen awon mass.

Electronic scale

Electronic scale na’ura ce ta zamani da ke amfani da makamashin lantarki wajen auna nauyi ko mass. Yana aiki ne ta hanyar gano matsin da abu ya yi a kan wani sashi na na’urar, sannan ya juya wannan bayanin zuwa adadin da ake iya karantawa a fuskar na’urar. Wannan nau’in kayan awo yana da sauri kuma yana ba da daidaitaccen sakamako cikin sauƙi. Saboda haka, ana amfani da shi sosai a bangaren kasuwanci, asibitoci, ɗakunan gwaje-gwaje, da masana’antu. Babban amfanin electronic scale shi ne sauƙin amfani da kuma daidaiton sakamakonsa. Haka kuma, yana iya auna ƙananan abubuwa daidai fiye da wasu tsoffin kayan auna.

Manazarta

HyperPhysics. (n.d.). Mass, weight, and gravity. Georgia State University.

NASA. (2023). Gravity and orbits. National Aeronautics and Space Administration.

OpenStax. (2022). University physics volume 1. Rice University.

Physics Classroom. (n.d.). Newton’s laws and weight. The Physics Classroom.

Britannica, T. Editors of Encyclopaedia. (2024). Weight (physics). Encyclopedia Britannica.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×