Skip to content

Bola Tinubu

Bola Ahmed Tinubu na daga cikin fitattun ‘yan siyasa masu tasiri a tarihin Najeriya a wannan zamani. Ya shahara wajen gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya, gina siyasar jam’iyyun adawa, da kuma jagorantar sauye-sauye a Jihar Legas da Najeriya baki ɗaya. A matsayinsa na tsohon gwamnan Jihar Legas kuma shugaban ƙasar Najeriya, Tinubu ya kasance mutum mai tasiri wajen tsara alkiblar siyasar ƙasar tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

An fi saninsa da lakabin “Asiwaju,” ma’ana jagora a harshen Yarabanci, saboda rawar da ya taka wajen haɗa kan ‘yan siyasa, kafa jam’iyyun siyasa da kuma taimakawa wajen fitowar shugabanni daban-daban a Najeriya. Duk da suka da ce-ce-ku-cen da suka taɓa tasowa a kansa, Bola Tinubu ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan jagororin siyasa mafi tasiri a Afirka ta Yamma.

Haihuwarsa

An haifi Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris a shekarar 1952 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya. Bola Ahmed Tinubu, jajirtacce kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a ƙasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya.

FqKKXhZXsAIiozy
Shugaba Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Buhari, lokacin da ya karɓi shahadar lashe zaben 2023.

Iyayensa da iyalinsa

Ba kasafai ake magana a kan mahaifin Bola Tinubu ba, amma mahaifiyarsa sananniya ce, ita ce ma shugabar mata ‘yan kasuwa na birnin Legas da ke zaune a Unguwanr Tinubu, ana kiran ta da sunan Alhaja Mogajiya Habibat mai arzikin gaske.

Asiwaju Bola Tinubu yana da mata daya mai suna Oluremi Tinubu, wadda sanata ce mai wakiltar Jihar Legas ta tsakiya. Ta kasance mai fafutikar kare hakkin jama’a da kuma mai ilimi da ake mutuntawa. Tana kuma gudanar da ayyukan jin kai wadda aka karrama da lambar girmamawa ta kasa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

tinubu wife birthday
Shugaba Tinubu da Maiɗakinsa, a wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Karatunsa

Shugaba Tinubu ya halarci makarantar firamare ta St. John’s da ke Aroloya da makarantar Children’s Home a Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya. Bayan nan sai ya wuce Kwalejin Richard Daley a Chicago da ke kasar Amurka, inda ya samun gurbin yin karatu a Kwalejin. Daga baya ya zarce zuwa Jami’ar jihar Chicago, a Illinois inda ya kammala karatunsa ya kuma fito da Digiri a Harkokin Kasuwanci. Tinubu ya kuma samu kyautar dalibin da ya fi ƙwazo a Jami’ar da kuma shaidar karramawa a ɓangaren Akanta da Hada-Hadar kudi.

Rayuwarsa ta ƙuruciya da asalinsa

Bola Ahmed Tinubu ya taso ne a cikin al’ummar Yarabawa a birnin Legas, inda ya yi rayuwarsa ta ƙuruciya cikin yanayin kasuwanci da mu’amala da jama’a. Mahaifiyarsa, Alhaja Abibatu Mogaji, fitacciyar shugabar mata ‘yan kasuwa ce a Legas, lamarin da ya sa tun yana ƙarami ya saba da harkokin shugabanci, hulɗa da jama’a da kuma dabarun tafiyar da rayuwa.

Unguwar Tinubu da danginsa suka shahara da zama a ciki na daga cikin tsofaffin unguwannin Legas masu muhimmanci a tarihin siyasa da kasuwancin Yarabawa. Wannan muhalli ya taimaka wajen gina tunaninsa da fahimtarsa game da shugabanci da siyasa tun yana matashi. A tsawon rayuwarsa ta ƙuruciya, Tinubu ya kasance mutum mai jajircewa da son neman ilimi. Tun kafin ya tafi ƙasar Amurka domin neman ilimi mai zurfi, ya nuna ƙwazo da hangen nesa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Gwagwarmaya

A lokacin da yake Amurka a shekarar 1975 da taimakon mahaifiyarsa, kasancewar shi mai hazaka, da kuma ke da ƙudirin ganin ya cim ma burinsa, sai ya shiga yin ayyuka da za su kawo masa kuɗi kamar wanke-wanke a gidajen sayar da abinci da aikin gadi da kuma tuka motar-haya domin taimaka masa a ɓangaren karatunsa.

Jajircewar da yake da ita ce ta sa ya shiga jerin ɗalibai masu hazaka a Kwalejin Richard Daley da kuma ta kai har ya kammala karatu a Jami’ar jihar Chicago a 1979 inda ya fito da digiri a fannin Kasuwanci.

A shekararsa ta farko a Jami’ar Chicago, an karrama shi da mukamin malami mai taimakawa wato (tutor) ba turance, domin yana taimakon wasu ‘yan uwansa dalibai da ke ƙananan ajuzuwa. ‘Yan uwansa dalibai da dama sun yaba taimakonsa a ɓangaren karatunsu wanda har ta kai su ga samun sakamako mai kyau.

Shugaba Tinubu yayin da ake rera taken ƙasa Najeriya a wajen wani taro.

A tsawon shekarun da yayi a jami’a, Tinubu ya kasance ɗalibi mafi hazaƙa wanda ya yi ta samun kyautar dalibi mai ƙwazo da kuma shaidar karatu a ɓangaren Akanta da hada-hadar kuɗi, inda kuma ya ƙare digirinsa da sakamako mai daraja ta sama.

A matsayinsa na mai burin abubuwa masu kyau da za su zo, Tinubu ya tsaya tare da yin nasara a takarar shugaban ɗaliban nazarin Akanta da Hada-hadar kudi na jami’ar jihar Chicago a shekararsa ta karshe.

A matsayinsa na mutumin da ba ya manta mafararsa da kuma alakarsa da al’umma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kasance mutumin da ya dauki hidimar al’umma da muhimmanci. Ko da a Mobil, ya jagoranci hidima daban-daban na tara-kudi domin tallafa wa shirye-shiryen ci-gaban al’umma a Jihar Legas.

Ya kuma jagoranci kungiyar Primrose, wata kungiyar siyasa da ke hankoron kawo canji a siyasar Jihar Lagos. Haka nan, Bola Tinubu ya yanke shawarar shiga aikin hidimar al’umma gadan-gadan ta hanyar ajiye babban matsayi da yake da shi a kamfanin Mobil.

300016206 623220599165812 6497458231157540705 n
Shugaba Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a wajen wani taro.

Kasuwanci da ayyukansa

Kafin kammala karatunsa na digiri, Bola Tinubu ya samu aiki da kamfanin harkar akantanci na Arthur Anderson. Daga bisani kamfanin Deloitte Haskins (wanda ake kira da deloitte Haskins and Touche a yanzu) suka dauki hayarsa, bayan nan kuma sai ya yi aiki da GTE Service Corporation, wani babban kamfanin sadarwa a kasar Amurka.

A kamfanin Deloitte Haskins and sells, matashi kuma ƙwararre Bola ya fadada kwarewarsa ta hanyar shiga ayyukan dubawa da gudanarwa na General Motors da yin aiki a Babban Bankin Kasa na Chicago da kamfanin Procter and Gamble da International Harvester da General Electric da sauran kamfanoni na Fortune 500.

Bayan ganin kwarewarsa, kamfanin Deloitte sal da yawa ya kan dauki hayar Bola a matsayin jagoran mambobi da ke sa ido a kamfanin. Bayan dawowarsa Najeriya da kuma samun gogewa a bangaren hada-hadar kudi, Tinubu ya fara aiki da Mobil a matsayin babban mai bincike wanda ta kai har ya zama ma’ajin kamfanin.

Siyasarsa

Bayan komowarsa gida ne kuma ya shiga harkokin siyasa, inda ya shiga kungiyar People Front ta marigayi Janar Shehu Musa Yaradua, kafin daga bisani su rikide zuwa jamiyar SDP, inda kuma a nan ne ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, tare kuma da samun nasara.

Ayyukansa a matsayin sanata

Bayan nasarar da ya samu a zaɓen Sanatan Legas ta Yamma a jam’iyyar SDP, Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa a Majalisar Dattawan Najeriya. A matsayinsa na shugaban kwamitin kula da bankuna, kuɗi da kasafi, ya bayar da gudunmawa wajen tattaunawa da tsara manufofin tattalin arziki da harkokin kuɗi na ƙasa.

Tinubu ya kasance ɗaya daga cikin sanatocin da suka fito fili wajen goyon bayan tsarin dimokuradiyya da kare muradun jama’a a lokacin Jamhuriya ta uku kafin rushewar gwamnati ta hanyar mulkin soja.

Gwagwarmayar NADECO da gudun hijira

Bayan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 wanda aka yi imanin MKO Abiola ne ya lashe, Bola Tinubu ya shiga sahun jagororin gwagwarmayar dawo da dimokuradiyya a Najeriya. Ya kasance cikin waɗanda suka kafa kungiyar National Democratic Coalition (NADECO), wata babbar ƙungiyar adawa da mulkin soja da ta nemi dawo da sakamakon zaɓen da kuma kafa tsarin dimokuradiyya.

Saboda matsin lamba da barazanar rayuwa daga gwamnatin soja, Tinubu ya tsere daga Najeriya zuwa ƙasashen waje inda ya ci gaba da fafutukar neman dawo da mulkin farar hula. A lokacin gudun hijirar, ya yi aiki tare da sauran fitattun ‘yan gwagwarmaya wajen wayar da kan ƙasashen duniya game da halin da Najeriya ke ciki ƙarƙashin mulkin soja.

Kalubale da rikice-rikice a mulkinsa na Lagos

A lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya fuskanci ƙalubale da dama, musamman rikicinsa da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin shugaba Olusegun Obasanjo.

Rikicin ya fi ƙamari ne bayan gwamnatin Legas ta ƙirƙiro sababbin ƙananan hukumomi 37 domin ƙara kusantar gwamnati ga jama’a. Wannan mataki ya jawo saɓani tsakaninsa da gwamnatin tarayya, wanda ya kai ga dakatar da kuɗaɗen gwamnatin tarayya da ake bai wa jihar. Duk da haka, gwamnatin Tinubu ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ta hanyar ƙarfafa tsarin tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, wanda daga baya ya zama abin koyi ga sauran jihohin Najeriya.

All Progressive Congress APC leader Bola Tinubu 2023
Shugaba Tinubu a wajen yaƙin neman zaben 2023.

Farin jininsa ya karu ne a siyasar Najeriya wajen sunan da ya yi wajen marawa ‘yan Arewa baya a siyasa, tun daga marigayi Janar Shehu Musa ‘Yaradua, zuwa Atiku Abubakar da Nuhu Ribado sai kuma Shugaban Muhammadu Buhari a karkashin jamiyar APC mai Mulki a yanzu.

Matsayinsa na gwamnan Legas

A yayin da sojoji suka kada gangan siyasa a 1998, Bola Tinubu ya dawo gida, ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyar AD ko Alliance for Democracy, inda ya mulki jihar Legas tsawon shekaru takwas. A wannan lokaci ne dai Tinubu ya kafa abin da ake ganin jam’iyar siyasa da magoya baya da dama da suka zame masa jari a tafiyar siyasarsa ta neman shugabancin Najeriya a wannan lokaci. Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara 8.

Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.

Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da bangaren aikin gwamnati.

Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma’aikatu irinsu ma’aikatar gidaje da ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.

A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.

Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al’ummarta.

Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al’umma.

Asiwaju Tinubu, ta hanyar kirkire-kirkire da sabbin tsare-tsare ya cire Jihar Lagos daga samun kudaden shiga na shekara-shekara na Naira biliyan 14.64 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 60.31 a shekarar 2006. Ya zuwa watan Maris din 2007, jihar ta samu kudin haraji a wata da ya kai naira biliyan 8.2.

Ƙoƙarinsa wurin kafa APC

A zaɓen 2015, Asiwaju ya zama babban mai goyon bayan hadewar jam’iyyarsa da wasu jam’iyyun adawa biyu – Jam’iyyar CPC da kuma Jam’iyar ANPP domin kawo karshen mulkin Jam’iyar PDP.

Jam’iyyun guda uku sun hade daga baya inda suka samar da jam’iyar All Progressive Congress (APC). Duba da rawa da ya taka wajen kafa jam’iyyar, an bai wa Tinubu mukamin jagoran jam’iyyar na kasa. A nan ma, ya sadaukar da burinsa na siyasa, domin karfafa jam’iyyar da ba ta fifiko a kasa baki daya.

A 2015, jam’iyyar ta APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2015, wanda karon farko da jam’iyyar adawa ta kada shugaba mai mulki a Najeriya. Tinubu ya taimaka wa Jam’iyyar ta APC wajen samun nasara.

A yau, APCn ita ke mulkin Najeriya bayan samun nasarar zaɓen shugaban kasa. Jam’iyar na kuma da mafi rinjayen mambobi a majalisar tarayyar kasar guda biyu da kuma gwamnoni a jihohi 22 na kasar.

Manazarta

BBC News Hausa. (2023, March 1). Bola Ahmed Tinubu: Tarihin zaɓaɓɓen Shugaban NajeriyaBBC News Hausa.

Voa. (2023, January 17). 2023: Tarihin Dan Takarar Shugaban Kasa, Bola Tinubu (APC). Voice of America.

McKenna, A. (2024, August 13). Bola Tinubu | Biography, Wife, Chicago, & Facts. Encyclopedia Britannica.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×