Petra tsohon birni ne mai cike da tarihi da ke kudancin ƙasar Jordan. Birnin yana cikin wani kwari mai kewaye da tsaunuka na duwatsu masu launin ja da ruwan hoda, dalilin da ya sa ake yi masa laƙabi da Rose City. Petra ya shahara saboda gine-gine da haikalai da aka sassaƙa kai tsaye cikin manyan duwatsu, tare da ingantaccen tsarin tattarawa haɗe da rarraba ruwa da ya ba mutanensa damar rayuwa a yankin hamada. A zamanin da, Petra ita ce babban birnin Masarautar Nabataea, wata ƙabila ta Larabawa da ta yi fice wajen kasuwanci tsakanin yankunan Larabawa, Masar, Siriya da Bahar Rum. Matsayinta a kan manyan hanyoyin kasuwanci ya sa ta bunƙasa sosai tsakanin ƙarni na huɗu kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.) da ƙarni na farko bayan haihuwarsa.
A shekarar 1985, Hukumar UNESCO ta ayyana Petra a matsayin gidan tarihin duniya wato World Heritage Site, saboda muhimmancin tarihinta da al’adunta. Daga baya, a shekarar 2007, aka zaɓe ta cikin Sabbin Abubuwan Al’ajabi Bakwai na Duniya wato New Seven Wonders of the World, abin da ya ƙara ɗaukaka sunanta a idon duniya. A yau, Petra na daga cikin wuraren yawon buɗe ido mafi shahara a Gabas ta Tsakiya, inda miliyoyin baƙi daga sassa daban-daban na duniya ke ziyarta wurin domin ganin kyawawan gine-ginenta da kuma koyon tarihinta.
Asalin sunan Petra
Sunan Petra ya samo asali ne daga kalmar Helenanci, wacce ke nufin dutse ko babban dutse. An ba birnin wannan sunan ne saboda mafi yawan gine-ginensa an sassaka su ne kai tsaye cikin manyan duwatsu masu launin ja da ruwan hoda da ke kewaye da yankin. Sai dai masana tarihi sun yi nuni da cewa mutanen da suka kafa birnin, wato Nabataeans, ba su kira shi da sunan Petra ba. Sunan da suka yi amfani da shi baya tabbatar da shi gaba ɗaya ba, saboda ƙarancin rubuce-rubucen da suka tsira daga zamaninsu.
Wasu tsofaffin rubuce-rubuce da binciken masana sun nuna cewa ana iya danganta Petra da sunan Raqmu ko Rekem, wanda ya bayyana a wasu rubuce-rubucen Nabataea da na tsofaffin tarihi. Duk da haka, har yanzu akwai muhawara tsakanin masana game da ko Raqmu shi ne ainihin sunan Petra ko kuwa wani wuri daban ne da ke kusa da ita. Bayan yankin ya shiga ƙarƙashin tasirin Daular Helenawa da Daular Roma, sunan Petra ya fara karɓuwa sosai a cikin rubuce-rubucen Helenanci da na Romawa. Daga nan ne sunan ya bazu zuwa sauran sassan duniya, har ya zama sunan da aka fi sanin birnin da shi a yau.
Tarihin kafuwar Petra
An yi imanin cewa an kafa Petra tun kafin ƙarni na huɗu kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.), amma ta bunƙasa sosai a matsayin babban birnin Masarautar Nabataea. Kasantuwar ta a kan manyan hanyoyin kasuwanci tsakanin Larabawa, Masar, Siriya da Bahar Rum, Petra ta zama cibiyar kasuwanci mai matuƙar arziki. A shekara ta 106 Miladiyya, Daular Roma ta mamaye Petra tare da haɗa ta a cikin daular ta. Daga baya, sauye-sauyen hanyoyin kasuwanci da kuma girgizar ƙasa sun janyo raguwar martabar birnin, har ya zama kusan babu kowa a cikinsa. A yau, Petra na ɗaya daga cikin wuraren tarihi mafi shahara a duniya.
Yanayin ƙasa da muhalli
Petra tana daga kudancin ƙasar Jordan, a cikin yankin Ma’an, kimanin kilomita 250 daga babban birnin ƙasar, sai dai birnin yana kusa da garin Wadi Musa, wanda shi ne ƙofar shiga wurin tarihi. Har ila yau, Petra tana cikin wani kwari mai kewaye da tsaunukan dutsen sandstone masu launin ja, ruwan hoda da ruwan kasa. Yankin na da kwazazzabai da ƙananan hanyoyi, mafi shahara cikinsu shi ne Siq, wata ƙunƙuntar hanya mai tsawon kusan kilomita 1.2 da ke kai baƙi zuwa cikin birnin.
Yanayin Petra na hamada ne, inda ake samun zafi a lokacin bazara da sanyi a lokacin hunturu. Duk da haka, mutanen Nabataea sun ƙirƙiri ingantaccen tsarin tarawa da adana ruwa, wanda ya ba su damar bunƙasa a wannan yanki mai ƙarancin ruwan sama.
Mutanen Nabataea
Nabataea ƙabila ce ta Larabawa da ta kafa Masarautar Nabataea, inda Petra ce babban birninsu. Sun shahara wajen kasuwanci, musamman safarar turare, kayan ƙamshi da sauran kayayyaki tsakanin yankunan Larabawa da Bahar Rum. Mutanen Nabataea sun kasance ƙwararru wajen sassaka gine-gine a cikin duwatsu da kuma ƙirƙirar hanyoyin taraws da adana ruwa a yankin hamada. Hakan ya ba su damar gina birni mai bunƙasa duk da ƙarancin ruwan sama.
Kamar yadda ya gabata, A shekara ta 106 Miladiyya, Daular Roma ta mamaye masarautarsu, amma al’adunsu da fasahar gine-gine sun ci gaba da kasancewa a cikin tarihin Petra.
Muhimman gine-gine da wuraren tarihi
Petra ta shahara da gine-gine da aka sassaka cikin duwatsu. Daga cikin fitattun wuraren tarihi akwai:
- Al-Khazneh: wanda shi ne gini mafi shahara a Petra, da aka sassaƙa a cikin babban dutse.
- The Siq: Ƙunƙuntar hanya mai tsawon kusan kilomita 1.2 da ke zama babbar hanyar shiga Petra.
- Ad Deir: Wani katafaren gini ne da aka sassaka cikin dutse, kuma yana daga cikin manyan abubuwan jan hankalin masu yawon buɗe ido a petra.
- Royal Tombs: Nan kuma tarin manyan kaburbura ne da aka sassaƙa domin sarakuna da manyan mutane.
- Roman Theatre: Gidan wasan kwaikwayo ne da aka sassaka a cikin dutse, wanda zai iya ɗaukar dubban mutane.
Waɗannan manyan gine-gine suna nuna ƙwarewar mutanen Nabataea a fannin gini da fasahar sassaka duwatsu.
Tattalin arziki
Tattalin arziki a Petra ya dogara ne da kasuwanci. Wanda matsayinta a kan manyan hanyoyin kasuwanci ya sa ta zama babbar cibiyar haɗa ƴan kasuwa daga Larabawa, Masar, Siriya da yankin Bahar Rum. Mutanen Nabataea sun yi kasuwancin kayan ƙamshi, turare, lubban wato frankincense, mur, kayan yaji da sauran kayayyaki masu daraja. Hakan ya kawo musu arziki da ci gaba, har Petra ta zama ɗaya daga cikin birane mafi wadata a zamaninta.
Bayan Daular Roma ta mamaye Petra da kuma sauya hanyoyin kasuwanci, tattalin arzikinta ya fara raguwa. Inda A yau kuma, yawon buɗe ido ne ya koma babban ginshiƙin tattalin arzikin yankin.
Addini da al’adu
Mutanen Nabataea sun kasance masu bautar gumaka kafin yankin ya shiga ƙarƙashin daular Roma. Sun gina haikalai domin bautarsu, kuma addininsu ya haɗu da wasu al’adun Larabawa da na Helenawa. Al’adunsu sun fi karkata ga kasuwanci, gine-gine, da fasahar sassaka duwatsu. Bayan yaɗuwar Kiristanci a yankin, an mayar da wasu gine-ginen Petra wuraren ibada. Daga baya kuma, bayan zuwan Musulunci, yankin ya shiga cikin ƙasashen Musulmi.
Sake gano Petra a zamanin yau
Bayan Petra ta shafe ƙarni da dama ba ta da yawan mazauna kuma ba a cika saninta ba a ƙasashen Yamma, an sake gano ta a shekarar 1812. Wani ɗan ƙasar Switzerland mai suna Johann Ludwig Burckhardt ne ya isa wurin, inda ya bayyana tarihinta ga duniya. Tun daga wannan lokaci, masana tarihi da masu binciken kayan tarihi suka fara gudanar da bincike a Petra.
Petra a matsayin kayan tarihi na UNESCO
A shekarar 1985, Hukumar UNESCO ta ayyana Petra a matsayin gidan Tarihin Duniya wato World Heritage Site, saboda muhimmancin tarihinta, al’adunta da kuma gine-ginen da aka sassaka cikin duwatsu. UNESCO ta bayyana Petra a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren tarihi da al’adun ɗan Adam da ya kamata a kiyaye domin amfanin al’ummomin yanzu da na gaba. Saboda wannan matsayi, ana ci gaba da gudanar da ayyukan kariya da gyaran wurin.
Yawon buɗe ido
Petra na ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido mafi shahara a ƙasar Jordan da ma duniya baki ɗaya. Kowace shekara, dubban baƙi daga ƙasashe daban-daban kan ziyarci wannan tsohon birni domin ganin kyawawan gine-ginen da aka sassaka cikin duwatsu da kuma koyon tarihinsa. Mafi yawan masu yawon buɗe ido suna fara shiga Petra ta hanyar Siq. Bayan fitowa daga Siq, abin na biyu da ke tarbar baƙi shi ne Al-Khazneh. Haka kuma, baƙi kan ziyarci Ad Dei, Royal Tombs, da Roman Theatre, waɗanda duk suna daga cikin fitattun wuraren tarihi na birnin.
Otal-otal, gidajen cin abinci, shagunan kayan gargajiya, masu jagorantar baƙi, da sauran sana’o’i suna samar da ayyukan yi ga dubban mazauna yankin, musamman a garin Wadi Musa, wanda ke kusa da Petra. Baya ga ziyarar rana, ana shirya shirin Petra by Night, inda ake haskaka hanyar Siq da ginin Al-Khazneh da dubban kyandirori. Wannan shiri yana ba baƙi damar ganin Petra cikin wani salo na musamman da ke ƙara fito da kyawun wurin. Saboda muhimmancinta ga tarihin ɗan Adam da kuma yawon buɗe ido, hukumomin Jordan tare da UNESCO suna ci gaba da ɗaukar matakan kare Petra daga lalacewa, tare da tabbatar da cewa baƙi suna ziyarta cikin tsarin da zai kiyaye wannan gado na tarihi.
Muhimmancin Petra a duniya
Petra tana da muhimmanci sosai a duniya saboda tana ɗaya daga cikin manyan shaidun da ke nuna irin ci gaban da tsohuwar Masarautar Nabataea ta samu a fannonin gine-gine, kasuwanci da hanyoyin sarrafa ruwa. Gine-ginen da aka sassaka cikin duwatsu suna nuna irin ƙwarewar da mutanen Nabataea suka mallaka tun fiye da shekaru dubu biyu da suka wuce.
A fannin ilimi da bincike, Petra ta zama muhimmin wuri ga masana tarihi, masu binciken kayan tarihi da ɗalibai daga sassa daban-daban na duniya. Binciken da ake ci gaba da yi a wurin yana ƙara bayyana tarihin tsohuwar fasahar Nabataea.
A takaice, Petra na ɗaya daga cikin manyan wuraren tarihi da suka fi ɗaukar hankali a duniya. Tarihinta, kyawawan gine-ginen da aka sassaka cikin duwatsu, da kuma ƙwarewar mutanen Nabataea sun sa ta zama abin koyi a fannonin gine-gine, kasuwanci da sarrafa ruwa. Duk da dubban shekarun da suka shuɗe tun bayan bunƙasar Petra, har yanzu tana ci gaba da jan hankalin masana tarihi, masu bincike da masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya. Matsayinta a matsayin Gidan Tarihin Duniya na UNESCO da kuma kasancewarta cikin Sabbin Abubuwan Al’ajabi Bakwai na Duniya ya ƙara tabbatar da muhimmancinta ga tarihin ɗan Adam.
A ƙarshe, Petra ba kawai tsohon birni ba ne, har ila yau alama ce ta basira, jajircewa da ci gaban wayewar ɗan Adam. Bayar da kariya ga wannan gado na tarihi da ci gaba da gudanar da bincike a kansa zai tabbatar da cewa al’ummomin yanzu da na gaba za su ci gaba da koyon darussa daga wannan birni mai ban mamaki.
Manazarta
Inside Petra Jordan – Wonders Travel and tourism. (2024, May 5). Wonders Travel and Tourism. .
Wilke, C. (2024, December 17). Who built the ‘lost city’ of Petra—and why did they leave? History.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.