Skip to content

Hawaii

Hawaii jiha ce ta hamsin a ƙasar Amurka, wadda ita kaɗai ce daga cikin jihohin Amurka da gabaɗayanta tsibiri ce a cikin Tekun Pacific. Tana da nisa kusan kilomita 3,900 daga gaɓar yammacin Amurka. Jihar Hawaii ta ƙunshi manyan tsibirai guda takwas da ƙananan tsibirai masu yawa, haɗe da duwatsu da rafuka.

Babban birninta shi ne Honolulu, wanda yake a tsibirin Oʻahu, kuma shi ne cibiyar gwamnati. Hawaii ta shahara saboda kyakkyawan rairayin bakin teku, duwatsu masu aman wuta, gandun daji masu yalwar tsirrai, da kuma al’adun al’ummar Hawaiʻi na asali. Haka kuma, tana daga cikin shahararrun wuraren yawon buɗe ido a duniya, inda miliyoyin baƙi ke ziyartar ta a kowace shekara.

Asalin sunan Hawaii

Kalmar Hawaii ta samo asali ne daga harshen al’ummar Hawaiʻi na asali. Masana tarihi da na ilimin harsuna sun gabatar da ra’ayoyi daban-daban kan tushen sunan, amma babu wata hujja guda da aka tabbatar da ita gaba ɗaya.

Ra’ayin da ya fi karɓuwa shi ne cewa sunan Hawaiʻi ya samo asali ne daga Hawaiki ko Sawaiki, Avaiki da Havaiki, wanda tsohon suna ne da al’ummomin Polynesia ke amfani da shi wajen nuni da ƙasar kakanninsu ko asalin da suka fito. A al’adun Polynesia, Hawaiki ba kawai suna ba ne, har ila yau yana da muhimmiyar ma’ana ta tarihi da ta al’ada, domin ana ɗaukarsa a matsayin tushen kakanni da al’ummarsu.

Wani ra’ayi kuma ya ce an samo sunan ne daga Hawaiʻiloa, wanda a tatsuniyoyin gargajiyar Hawaiʻi ake bayyana shi a matsayin wani fitaccen matafiyi a teku da ake dangantawa da gano tsibiran Hawaii. Sai dai masana tarihi sun nuna cewa babu isassun hujjojin tarihi da suka tabbatar da cewa shi ne ya ba tsibiran sunansu.

Sannan a rubutun harshen Hawaiʻi na asali, ana rubuta sunan da Hawaiʻi, inda alamar (ʻ) ke nuna ɗan tsagawar sauti tsakanin haruffa. Wannan alama wani muhimmin ɓangare ne na tsarin rubutun harshen, kuma tana canza yadda ake furta kalmar. Saboda haka, lafazin da ya fi dacewa shi ne Ha-wa-i-i, tare da ɗan tsayawa kaɗan kafin harafin ƙarshe.

Tarihin kafuwar Hawaii

Masana tarihi sun yi imanin cewa mutanen farko da suka zauna a tsibiran Hawaii sun kasance Polynesians, waɗanda suka yi doguwar tafiya ta ruwa a cikin kwale-kwalen gargajiya daga wasu tsibirai na Polynesia. Ana kyautata zaton sun isa Hawaii tsakanin ƙarni na huɗu zuwa na goma sha uku Miladiyya, ko da yake har yanzu akwai muhawara tsakanin masana kan takamaiman lokacin. Bayan sun isa ne suka kafa ƙauyuka, suka bunƙasa noma, kamun kifi, da tsarin shugabanci na gargajiya. Sun kuma gina al’ada mai ƙarfi wadda ta haɗa da addini, waƙoƙi, raye-raye, da tsarin dokoki da ake kira kapu, wanda ke tsara rayuwar al’umma.

A ranar 18 ga Janairu, 1778, mai binciken teku ɗan Birtaniya Captain James Cook ya isa tsibiran Hawaii yayin wata tafiyarsa a Tekun Pacific. Shi ne bature na farko da aka tabbatar ya kai ziyara zuwa tsibiran. Zuwansa ne ya buɗe ƙofa ga hulɗa tsakanin Hawaii da Turawa. Daga baya, ƴan kasuwa, mishanoni, da masu neman arziki daga Turai da Amurka suka fara zuwa tsibiran.

A ƙarshen ƙarni na 18, akwai ƙananan masarautu da dama a tsibiran Hawaii. Wani fitaccen jagora mai suna Kamehameha I ya yi yaƙe-yaƙe har ya haɗa mafi yawancin tsibiran ƙarƙashin mulkinsa. A shekara ta 1810, ya kafa Masarautar Hawaii, wadda ta zama ƙasa mai cin gashin kanta kuma ƙasashe da dama a duniya suka amince da ita.

A cikin ƙarni na 19, tattalin arzikin Hawaii ya bunƙasa musamman ta hanyar noman rake da abarba. Hakan ya jawo ƙaruwar ƴan kasuwa daga Amurka da Turai, waɗanda suka fara samun ƙarfi a harkokin siyasa da tattalin arziki. A lokaci guda, mishanoni Kirista sun kafa makarantu da coci-coci, tare da tasirantuwa a tsarin ilimi, addini da rayuwar al’umma.

A shekara ta 1893, wasu ƴan kasuwa da masu shuka rake, tare da goyon bayan wasu jami’an Amurka, suka hambarar da Sarauniya Liliʻuokalani, wadda ita ce sarauniya ta ƙarshe ta masarautar Hawaii. Bayan wannan ne aka kafa gwamnatin riƙo, sannan daga baya aka kafa Jamhuriyar Hawaii.

A ranar 7 ga Yuli, 1898, Amurka ta haɗe Hawaii da ƙasarta. Daga baya kuma, a shekara ta 1900, Hawaii ta zama Territory of Hawaii, wato yanki da Amurka ke gudanarwa amma ba cikakkiyar jiha ba.

A ranar 7 ga Disamba, 1941, sojojin Japan suka kai hari kan sansanin sojojin ruwan Amurka da ke Pearl Harbor a tsibirin Oʻahu. Wannan hari ya jawo Amurka ta shiga yaƙin duniya na biyu. Harin Pearl Harbor kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan tarihi da suka canja akalar siyasar duniya a ƙarni na ashirin.

Bayan shekaru da dama ana tattaunawa kan matsayin Hawaii, an gudanar da ƙuri’ar raba gardama inda mafi yawan mazauna suka amince ta zama jiha. A ranar 21 ga Agusta, 1959, Hawaii ta zama jiha ta 50 a Tarayyar Amurka.

A yau, Hawaii tana ɗaya daga cikin jihohin Amurka mafi shahara saboda kyawawan halittun da ke cikinta, haɗe da al’adunta na musamman, da kuma muhimmiyar rawar da take takawa a yawon buɗe ido, gami da binciken kimiyya, da harkokin tsaron Tekun Pacific.

Yanayin ƙasa da muhalli

Kamar yadda ya gabata, jihar Hawaiʻi tana cikin tekun Pacific ta Arewa, kuma ita ce jiha mafi keɓantuwa daga sauran jihohin Amurka. Tana da nisan kilomita 3,900 daga gaɓar yammacin ƙasar Amurka wato California, yayin da take da nisan kusan kilomita 6,200 daga ƙasar Japan. Wannan ne ya sanya Hawaii ta zama babbar mahaɗa tsakanin Arewacin Amurka, Asiya da Oceania. Hawaii ta ƙunshi tsibirai 137, waɗanda suka haɗa da manyan tsibirai takwas da suka fi shahara gami da yawan jama’a, sai ƙananu tsibirai fiye da ɗari, da duwatsu masu fitowa a cikin teku.

Jimillar faɗin ƙasar Hawaii kuma ya kai kusan murabba’in kilomita 28,311, wanda ya haɗa da ƙasa da kuma wani ɓangare na ruwa da ke cikin iyakarta. Duk da cewa ƙasarta ba ta da faɗi idan aka kwatanta da wasu jihohin Amurka, sai dai tana da iyakar teku mai faɗi sosai.

Masana ilimin ƙasa, sun tabbatar da cewa, tsibiran Hawaii sun samo asali ne daga aman wutar ƙasa da ya daɗe yana faruwa a ƙarƙashin tekun Pacific. Yayin da farantin tekun Pacific (Pacific Plate) ke motsawa a hankali a saman wani wuri mai zafi da ake kira hotspot, sabbin tsaunuka masu aman wuta sun ci gaba da samuwa. Wannan ne ya haifar da jerin tsibirai da duwatsu masu aman wuta da suka yi layi daga kudu maso gabas zuwa arewa maso yamma.

A tsarin yankuna na Amurka, Hawaii ba ta da iyaka ta ƙasa da wata jiha ko wata ƙasa, domin ruwa ne ya kewaye ta gaba ɗaya. Wannan ne ya bambanta ta da duk sauran jihohin Amurka.

Manyan tsibiran da ke Hawaii

Kamar yadda ya gabata, jihar Hawaii tana da tsibiran da yawansu ya kai 137, a cikinsu ne kuma aka samu manya guda takwas, da suka haɗa da:

Hawaiʻi (Big Island)

Wannan shi ne tsibiri mafi girma a cikin jihar Hawaii, ku san ma a shine mafi girman tsibiri a kaf ƙasar Amurka. Saboda girmansa, ana kiransa Big Island domin bambance shi da sunan jihar baki ɗaya. Tsibirin na ɗauke da manyan tsaunuka masu aman wuta, ciki har da Mauna Loa, Mauna Kea, Kīlauea, Hualālai, da Kohala. A nan ne kuma ake samun gandun dajin Hawaii Volcanoes National Park.

Maui

Maui shine tsibiri na biyu mafi girma a Hawaii. Ya shahara da kyawawan rairayin bakin teku, hanyoyin tafiye-tafiye masu ban sha’awa, da kuma dutsen Haleakalā, wanda yake ɗaya daga cikin manyan tsaunuka masu aman wuta na jihar. Kuma yawon buɗe ido shi ne babban ginshiƙin tattalin arzikin Maui.

Oʻahu

Oʻahu shi ne tsibirin da ya fi yawan jama’a a Hawaii. A kansa ne babban birnin jihar Honolulu yake, da kuma mafi yawan cibiyoyin gwamnati da sassan kasuwanci. Har ila yau, a Oʻahu ne sanannen bakin teku na Waikīkī yake, da kuma tashar sojojin ruwa ta Pearl Harbor, wadda ta shahara a tarihin Yaƙin duniya na biyu.

Kaua’i

Kauaʻi shi ne tsibiri mafi tsufa daga cikin manyan tsibiran jihar. Saboda yalwar gandun daji, koguna da korayen kwaruruka, ana yi masa laƙabi da Garden Isle, wato tsibirin lambuna. Tsibirin na da kyawawan wuraren yawon buɗe ido da suka haɗa da Na Pali Coast da Waimea Canyon.

Molokaʻi

Molokaʻi ya fi shahara ne wajen adana al’adun gargajiyar mutanen Hawaiʻi. Tsibirin bashi da yawan gine-ginen zamani kamar sauran manyan tsibirai, abin da ya sa har yanzu ake ganin salon rayuwar gargajiya a wasu sassan tsibirin.

Lānaʻi

Lānaʻi ya kasance cibiyar noman abarba a ƙarni na 20, inda har aka taɓa kiran tsibirin da Pineapple Island. A yau, ya fi karkata ga yawon buɗe ido da manyan otal-otal masu cike da kayan alatu.

Niʻihau

Niʻihau tsibiri ne mai zaman kansa wadda iyali ɗaya suka mallaka tun shekara ta 1864. Ba a yarda wasu mutanen su shiga tsibirin ba sai da izini na musamman. Saboda wannan ya sa harshen Hawaiʻi da wasu al’adun gargajiya ci gaba da kasancewa a cikinsa fiye da sauran tsibirai.

Kahoʻolawe

Kahoʻolawe shi ne mafi ƙarancin manyan tsibirai takwas. Tsibirin ba shi da mazauna na dindindin saboda ƙarancin ruwan sha da kuma lalacewar da ya fuskanta lokacin da sojojin Amurka suka yi amfani da shi wajen gwajin makamai. A yau ana ci gaba da aikin gyaran muhalli da kuma dawo da martabar al’adun tsibirin.

Yanayi jihar Hawaii

Yanayin jihar Hawaiʻi yana daga cikin mafi daɗi kuma mafi daidaito a duniya. Saboda matsayinta a tsakiyar Tekun Pacific da kuma kasancewarta a yankin da ke kusa da Tropic of Cancer, inda jihar ba ta fuskantar tsananin sanyi ko matsanancin zafi kamar yadda ake samu a wasu sassan duniya.

Lokutan shekara a Hawaii

A Hawaii ba a samun yanayi huɗu irin bazara, rani, kaka da hunturu kamar yadda ake samu a yawancin jihohin Amurka. Maimakon haka, ana raba shekarar zuwa manyan lokuta biyu:

Lokacin zafi

Wannan lokaci yana farawa ne daga Mayu zuwa Oktoba. Yanayi kan kasance mai ɗan zafi tare da ƙarancin ruwan sama a mafi yawan yankunan tsibiran. Wannan shi ne lokacin da yawancin masu yawon buɗe ido ke ziyartar Hawaii.

Lokacin sanyi da damina

Wannan lokaci ya kan fara daga Nuwamba zuwa Afrilu. A wannan lokacin ana samun ƙarin ruwan sama, musamman a arewa da gabashin tsibirai. Amma duk da haka, yanayin sanyi ba ya kai matakin da ake samun dusar ƙanƙara a bakin teku.

Tasirin Trade Winds

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke sa yanayin Hawaii ya kasance mai daɗi shi ne iskokin da ake kira Trade Winds. Waɗannan iskoki suna kaɗawa daga gabas zuwa yamma, suna sanyaya yanayi tare da rage zafin rana da yawan danshi. Saboda tasirin waɗannan iskoki, gefen da iska ke bugawa yakan fi samun ruwan sama da ciyayi masu yawa, yayin da gefen da iska ba ta bugawa sosai yakan kasance a bushe.

Bambancin yanayi

Duk da ƙarancin faɗin jihar, Hawaii tana da bambancin yanayi sosai. Wasu yankuna suna samun ruwan sama mai yawa a duk shekara, yayin da wasu suke da yanayi mai kama da hamada.

Misali, Dutsen Waiʻaleʻale a tsibirin Kauaʻi yana daga cikin wuraren da suka fi samun ruwan sama a duniya, yayin da wasu yankuna na tsibirin Hawaiʻi Big Island ke samun ƙarancin ruwan sama.

Dusar ƙanƙara

Ko da yake Hawaii jiha ce mai yanayin zafi, akan samun dusar ƙanƙara a lokacin hunturu a kan kololuwar manyan tsaunuka kamar Mauna Kea da Mauna Loa. Wannan yana faruwa ne saboda tsayinsu mai yawa, wanda ya haura mita dubu hudu.

Guguwar teku

A wasu lokuta, Hawaii na fuskantar guguwar teku wato tropical cyclones ko hurricanes, musamman tsakanin watan Yuni da Nuwamba. Sai dai guguwar da ke kai wa tsibiran hari kai tsaye ba ta da yawa idan aka kwatanta da wasu yankunan Tekun Pacific.

Manyan duwatsu masu aman wuta

A tsibirin Hawaiʻi Big Island ne ake samun mafi yawan manyan duwatsu masu aman wuta. daga cikinsu sun haɗa da:

  • Mauna Loa: Mauna Loa shi ne ɗaya daga cikin manyan duwatsu masu aman wuta a duniya idan aka auna girmansa da yawan dutsen da ya ƙunsa.
  • Kīlauea: Kīlauea na ɗaya daga cikin duwatsu masu aman wuta a duniya. Tun daga ƙarni na ashirin, ya yi aman wuta akai-akai, yana fitar da narkakken dutse wanda ke ƙara faɗaɗa gaɓar tsibirin Hawaii.
  • Mauna Kea: Mauna Kea shi ne mafi tsayin dutse a Hawaii daga matakin teku, inda tsayinsa ya kai mita 4,207. Duk da cewa ba ya cikin duwatsu masu aiki a halin yanzu, ana ɗaukarsa a matsayin dutse mai yiwuwar sake yin aman wuta nan gaba.
  • Hualālai: Hualālai dutse ne mai aiki, amma bai cika yin aman wuta ba. Aman wutarsa ta ƙarshe ta faru a farkon ƙarni na 19. Masana suna ci gaba da sa ido a kansa saboda yana iya sake yin aman wuta a nan gaba.
  • Kohala: Kohala shi ne mafi tsufa daga cikin manyan duwatsu biyar na Big Island. Masana sun yi imanin cewa ya daina yin aman wuta tun dubban shekaru da suka wuce, saboda haka ana ɗaukarsa a matsayin dutsen da ya mutu

Hawaii volcanoes national park

Domin kare waɗannan muhimman wurare na halitta, an kafa Hawaii Volcanoes National Park a tsibirin Hawaiʻi. Gandun dajin yana haɗe da Kīlauea da Mauna Loa, kuma yana daga cikin wuraren tarihin duniya da UNESCO ta amince da su.

Ƙabilu da harsuna

Jihar Hawaiʻi tana da al’umma mai mabanbantan ƙabilu da al’adu. Kasancewarta a tsakiyar Tekun Pacific mai tarihin ƙaura daga sassa daban-daban na duniya, Hawaii ta zama ɗaya daga cikin wuraren da ke da haɗuwar mutane mafi yawa a Amurka.

A ƙididdigar yawan jama’a ta baya-bayan nan, Hawaii na da kusan mutane miliyan 1.4 zuwa 1.5, kuma mafi yawansu suna zaune ne a tsibirin Oʻahu, musamman a birnin Honolulu, wanda shi ne babban birni kuma cibiyar gwamnati da kasuwanci.

Ƙabilu

Al’ummar Hawaii sun ƙunshi mutane daga ƙabilu da asali iri-iri. Manyan rukunan sun haɗa da mutanen Hawaiʻi na asali, Sai mutanen Asiya, ciki har da waɗanda asalinsu daga Japan, Philippines, China, Korea da sauransu. Yawancinsu sun zo Hawaii ne a ƙarni na 19 da na 20 domin yin aiki a gonakin rake da abarba.

Sai fararen fata da galibi zuriyar turawa ne da Amurkawa da suka zauna a Hawaii tun bayan hulɗarta da ƙasashen yamma. Akwai kuma mutanen Pacific Islands, Kamar Samoans, Tongans da Guamanians. Sai baƙaƙen fata wato African Americans da sauran ƙabilu daga sassa daban-daban na duniya.

Harsuna

Hawaii tana da harsuna biyu na hukuma, wato turanci, shi ne harshen da aka fi amfani da shi a gwamnati, makarantu, kasuwanci da kafofin watsa labarai. Sai kuma Harshen Hawaiʻi, wanda shi ne harshen gargajiyar mutanen Hawaiʻi na asali. Duk da cewa ya taɓa fuskantar barazanar ɓacewa, yanzu ana koyar da shi a makarantu da jami’o’i, kuma gwamnati da ƙungiyoyi da dama suna aiki wajen farfaɗo da shi.

Addinai

Hawaii na da ƴancin addini, kuma mutane suna bin addinai daban-daban. Daga cikin manyan addinan akwai Musulunci, Kiristanci, Buddha, Hindu, Yahudanci, da kuma wasu da ke ci gaba da bin al’adun gargajiyar mutanen Hawaiʻi.

Al’adu

Al’adun Hawaiʻi suna daga cikin mafiya shahara kuma mafiya bambanci a duniya. Sun samo asali ne daga al’adun mutanen Polynesia da suka fara zama a tsibiran, sannan daga baya suka haɗu da al’adun Turawa, Asiyawa da sauran al’ummomin da suka yi ƙaura zuwa Hawaii. Wannan haɗuwar ta samar da wata al’ada ta musamman wadda ke bambanta Hawaii da sauran jihohin Amurka.

Tufafin gargajiya

Mutanen Hawaii suna da tufafi na gargajiya da ake sanyawa musamman a bukukuwa da lokutan al’adu. Daga cikinsu akwai Aloha shirt, riga mai zane-zane da launuka masu ƙayatarwa, wadda ta zama sananniyar alamar Hawaii. Sai Muʻumuʻu, wato doguwar rigar mata mai faɗi, wadda ake sanyawa a bukukuwa da taruka.

Bukukuwa

Ana gudanar da bukukuwa da dama a Hawaii domin nuna al’adu da tarihin tsibiran. Daga cikin shahararrun bukukuwa akwai: Merrie Monarch Festival, babban bikin rawar Hula da ake yi duk shekara a tsibirin Hawaiʻi. Da Lei Day, bikin da ake yi a ranar 1 ga Mayu domin nuna muhimmancin Lei da al’adun Hawaii.

Abinci

Abincin Hawaii ya samo asali daga haɗuwar al’adun Polynesia, Asiya da Turai. Daga cikin fitattun abinci akwai Poi, wanda abinci ne da ake yi daga tushen shukar taro. Sai Kalua Pig, Naman alade da ake dafa wa a cikin rami mai zafi a ƙarƙashin ƙasa. Da Lomi Lomi Salmon, shi ma abinci ne da ake yi da kifin salmon da kayan lambu. Da Kuma Poke, wato Kifi ɗanye da aka yanka ƙanana tare da kayan haɗi, wanda ya shahara a duniya.

Tattalin arziki

Tattalin arzikin Hawaiʻi ya ta’allaka ne kan haɗuwar harkokin yawon buɗe ido, ayyukan gwamnati, tsaro, noma, binciken kimiyya, da kasuwanci.

Tattalin arzikin Hawaii yana fuskantar wasu ƙalubale, ciki har da Tsadar rayuwa, wadda take daga cikin mafi girma a Amurka. Sai Tsadar gidaje da haya. Dogaro sosai da yawon buɗe ido, wanda kan sa tattalin arzikin ya yi rauni idan aka samu annoba, bala’in ƙasa ko koma bayan tattalin arziki. Yawan shigo da kayayyaki daga nahiyar Amurka da sauran ƙasashe, saboda ƙarancin masana’antu a cikin jihar.

A takaice, Hawaiʻi wata jiha ce mai matsayi na musamman a cikin Tarayyar Amurka da ma duniya baki ɗaya. Tsibiran Hawaii sun samo asali ne daga duwatsu masu aman wuta da suka gudana tsawon miliyoyin shekaru, lamarin da ya haifar da tsaunuka, kwaruruka, gandun daji, da rairayin bakin teku masu ƙayatarwa. Baya ga haka, jihar tana da nau’o’in tsirrai da dabbobi da dama waɗanda ba a samun su a wani wuri na duniya sai a cikinta.

Al’ummar Hawaii sun haɗa mutane daga ƙabilu da al’adu daban-daban, amma har yanzu ana ci gaba da kiyaye al’adun mutanen Hawaiʻi na asali, musamman harshensu, al’adunsu da gadonsu na tarihi.

A fannin tattalin arziki kuwa, yawon buɗe ido, noma, binciken kimiyya, da harkokin tsaro suna daga cikin manyan ginshiƙan ci gabanta. Duk da ƙalubalen da take fuskanta, kamar sauyin yanayi da tsadar rayuwa, Hawaii na ci gaba da zama ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin baƙi da masana daga sassa daban-daban na duniya.

Manazarta

USGS. (n.d.). Evolution of Hawaiian volcanoes. USGS.

EcoTours, H. (2023, July 1). A brief history of the Luau – Haleakala Ecotours. Haleakala Ecotours.

AvD_BwE. Skyline_Admin. (2025, March 12). How many Hawaiian islands do you know? | Skyline Hawaii. Skyline Hawaii.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×