Ƙasar Comoros, wadda a hukumance ake kira da Union of the Comoros, ƙasa ce ta tsibirai da ke cikin tekun Indiya a arewacin mashigar Mozambique, a tsakanin gabashin nahiyar Afirka da tsibirin Madagascar. Babban birnin ƙasar shi ne Moroni, wanda kuma shi ne cibiyar gudanarwa da kasuwanci ta ƙasar. Comoros ta ƙunshi manyan tsibirai uku masu cin gashin kansu a ƙarƙashin gwamnatin tarayya. Al’ummar ƙasar sun samo asali ne daga mutanen Afirka, Larabawa da Malagasy.
Yanayin ƙasa da muhalli
Kamar yadda ya gabata, ƙasar Comoros tana cikin Tekun Indiya, a arewacin mashigar Mozambique, tsakanin gaɓar gabashin nahiyar Afirka da tsibirin Madagascar. Tana da iyaka ta ruwa da ƙasashen Mozambique, Tanzania da kuma Madagascar. Matsayinta na ƙasa ya sanya ta kasance babbar mahaɗar zirga-zirga da kasuwanci a yankin tekun Indiya. Comoros ta ƙunshi manyan tsibirai uku da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, wato Grande Comore, Anjouan da Mohéli. Akwai kuma tsibirin Mayotte, wanda ke cikin jerin tsibiran Comoros mai cike da tarihi da al’ada, amma a halin yanzu yana ƙarƙashin ikon Faransa. Babban birnin ƙasar, Moroni, yana kan tsibirin Grande Comore.
Faɗin ƙasar Comoros ya kai kilomita 1,861, lamarin da ya sanya ta zama ɗaya daga cikin ƙananan ƙasashe a nahiyar Afirka ta fuskar yawan fili. Duk da ƙanƙantar filinta, ƙasar tana da tsaunuka, gandun daji, kwazazzabai da kuma kyawawan rairayin bakin teku. Yawancin tsibiran Comoros sun samo asali ne daga aman wuta wato volcanic activity. Mafi girman tsaunin ƙasar shi ne Mount Karthala, wanda ke kan tsibirin Grande Comore. Tsaunin na daga cikin manyan duwatsu masu aman wuta, kuma tsayinsa ya kai kusan mita 2,361 daga matakin teku. Yanayin ƙasar na tropikal ne, wato mai zafi da danshi a mafi yawan lokutan shekara. Akwai lokutan damina da na rani, inda damina ke farawa daga watan Nuwamba zuwa Afrilu, yayin da lokacin rani mai ɗan sanyi ke kasancewa daga Mayu zuwa Oktoba. Wannan yanayi yana taimakawa wajen bunƙasar noma da samar da tsirrai masu ƙamshi irin su vanilla, cloves da ylang-ylang. Kasancewar ƙasar tsibirai ce a tsakiyar teku, Comoros tana da yalwar albarkatun ruwa da halittu masu rai, ciki har da kifaye, murjani, da wasu nau’o’in dabbobi da tsirrai da ba a samun su a sauran sassan duniya.
Al’umma da harshe
Al’ummomi
Al’ummar Comoros sun samo asali ne daga haɗuwar ƙabilu da al’adu daban-daban da suka yi ƙaura zuwa tsibiran tun ƙarni da dama da suka gabata. Mafi yawan jama’ar ƙasar sun fito ne daga asalin Afirka ta Gabas, Larabawa da Malagasy, lamarin da ya haifar da wata al’ada ta musamman mai haɗe da al’adun Afirka da na Larabawa. Wannan haɗuwar al’adu ta bayyana a cikin harshe, addini, tufafi, gine-gine da tsarin rayuwar yau da kullum. Yawan jama’ar Comoros ya haura mutum miliyan ɗaya a shekarun baya-bayan nan, inda mafi yawan jama’a ke zaune a tsibiran Grande Comore, Anjouan da Mohéli. Birnin Moroni, wanda shi ne babban birnin ƙasar, yana daga cikin wuraren da suka fi yawan jama’a da bunƙasar tattalin arziki.
Harsuna
Comoros tana da harsuna uku na hukuma, wato Shikomori (Comorian), sai Larabci da Faransanci. Shikomori shi ne harshen da mafi yawan jama’a ke amfani da shi a rayuwar yau da kullum, kuma yana da alaƙa da harsunan Swahili tare da Larabci. Akwai bambance-bambancen karin harshe daga tsibiri zuwa tsibiri, amma dukansu suna ƙarƙashin harshen Shikomori.
Harshen Larabci yana da muhimmanci sosai saboda alaƙarsa da addinin Musulunci da ilimin addini. Ana koyar da shi a makarantu da cibiyoyin addini, kuma ana amfani da shi wajen karatun Alƙur’ani da sauran ayyukan ibada. Harshen Faransanci kuwa shi ne babban harshen gwamnati, ilimi da harkokin gudanarwa, sakamakon mulkin mallakar Faransa
Addini da al’adu
Addini
Addinin Musulunci shi ne ginshiƙin rayuwar al’ummar Comoros kuma addinin da mafi rinjayen jama’ar ƙasar ke bi. Mafi yawan Musulman ƙasar mabiya Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah ne, kuma koyarwar Musulunci tana da tasiri sosai a harkokin zamantakewa, ilimi, al’adu da tsarin rayuwar yau da kullum. Masallatai suna da yawa a sassan ƙasar, kuma ana ba ilimin addini muhimmanci tun daga ƙuruciya. Bukukuwan Musulunci kamar Ƙaramar Sallah, Babbar Sallah, da Maulidin Annabi Muhammad (SAW) suna daga cikin manyan bukukuwan da ake gudanarwa a ƙasar. A irin waɗannan lokuta, al’umma kan taru domin gudanar da ibada, ziyartar dangi da abokai da kuma raba abinci da kyaututtuka.
Al’adu
Al’adun Comoros sun samo asali ne daga haɗuwar al’adun mutanen Afirka ta Gabas, Larabawa da Malagasy. Wannan haɗin ya bayyana a cikin salon sutura, abinci, kiɗa, raye-raye da kuma gine-ginen gargajiya. Maza da mata suna sanya tufafin gargajiya da na Musulunci, musamman a lokutan bukukuwa da tarurruka na musamman. Ɗaya daga cikin fitattun al’adun ƙasar shi ne bikin aure na gargajiya wanda ake kira Grand Marriage . Wannan bikin kan haɗa da tarurruka, liyafa da wasu al’adun gargajiya da kan ɗauki lokaci mai tsawo kafin kammalawa.
Abinci
Abincin gargajiya na Comoros ya haɗa da shinkafa, kifi, kwakwa, ayaba da kayan ƙamshi irin su cloves, vanilla da ylang-ylang waɗanda ƙasar ke samarwa.
Kiɗa
A fannin kiɗa da raye-raye, al’ummar Comoros suna da nau’o’in waƙoƙi da raye-raye na gargajiya waɗanda ake gudanarwa a bukukuwa da lokutan farin ciki. Waɗannan al’adu suna taimakawa wajen adana tarihin ƙasar da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin jama’a. Sai dai duk da tasirin zamani da al’adun ƙasashen waje, al’ummar Comoros suna ci gaba da kiyaye al’adunsu na gargajiya tare da bin koyarwar addinin Musulunci, lamarin da ya ba ƙasar wata fitacciyar al’ada mai cike da haɗin kai tsakanin addini da rayuwar al’umma.
Tarihin kafuwar Comoros
Tarihin Comoros ta samo asali tun ƙarni da dama da suka gabata lokacin da masu ƙaura daga gabashin Afirka, Larabawa da yankin Madagascar suka fara zama a tsibiran. Saboda matsayinta a tsakiyar hanyoyin kasuwancin Tekun Indiya, Comoros ta zama muhimmiyar cibiyar kasuwanci tsakanin Afirka, Larabawa da Asiya. A wannan lokaci ne Musulunci ya shiga ƙasar ta hannun ƴan kasuwa da malamai Larabawa, inda daga baya ya zama addinin mafi rinjaye.
Daga ƙarni na sha biyar zuwa na sha tara, tsibiran Comoros sun kasance ƙarƙashin ƙananan masarautu da sarakuna daban-daban. A wannan lokaci, hulɗar kasuwanci da ƙasashen Larabawa da na gabashin Afirka ta bunƙasa, musamman a fannin kayan ƙamshi da sauran kayayyakin kasuwanci.
A shekarar 1841, Faransa ta fara kafa ikonta a tsibirin Mayotte, sannan daga baya ta mamaye sauran tsibiran Comoros. A shekarar 1912, Comoros ta zama wani ɓangare na mulkin mallakar Faransa a hukumance. A lokacin mulkin mallakar, Faransawa sun gudanar da harkokin siyasa da tattalin arzikin ƙasar tare da inganta noman kayan ƙamshi irin su vanilla, cloves da ylang-ylang.
Bayan shekaru da dama na fafutukar neman ƴanci, Comoros ta ayyana samun ƴancin kai daga Faransa a ranar 6 ga Yulin 1975. Sai dai tsibirin Mayotte ya ci gaba da kasancewa ƙarƙashin Faransa, lamarin da ya haifar da saɓani tsakanin Comoros da Faransa wanda har yanzu yake ci gaba a matakin diflomasiyya.
Bayan samun ƴancin kai, Comoros ta fuskanci sauye-sauyen gwamnati da juyin mulki da dama, wanda ya sa siyasar ƙasar ta kasance cike da ƙalubale. Duk da haka, a farkon ƙarni na ashirin da ɗaya an aiwatar da wasu gyare-gyaren tsarin mulki domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin tsibiran ƙasar da samar da kwanciyar hankali.
Tsarin mulki
Ƙasar Comoros jamhuriya ce mai tsarin mulkin tarayya, wadda ta ƙunshi manyan tsibirai uku: Grande Comore, Anjouan da Mohéli. Tsarin mulkin ƙasar ya tanadi raba iko tsakanin gwamnatin ƙasa da gwamnatocin tsibiran domin tabbatar da wakilci da haɗin kai a tsakanin al’ummomin tsibiran.
Shugaban ƙasa shi ne shugaban gwamnati kuma shugaban ƙasa baki ɗaya. Ana zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen jama’a na dimokuraɗiyya na wani wa’adi da tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Shugaban ƙasa ne ke jagorantar harkokin gudanarwa, tsaro, manufofin ƙasa da kuma hulɗar ƙasar da sauran ƙasashe. Majalisar dokoki ta Comoros tana da alhakin tsara dokoki, amincewa da kasafin kuɗi da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati. Mambobin majalisar ana zaɓensu ne ta hanyar zaɓe domin wakiltar jama’ar ƙasar. Tsarin dimokuraɗiyya yana bai wa jama’a damar shiga cikin harkokin siyasa ta hanyar zaɓe da sauran hanyoyin da doka ta tanada.
Bangaren shari’a kuwa yana aiki ne a matsayin hukuma mai zaman kanta wadda ke fassara dokoki da tabbatar da adalci. Kotuna suna kula da warware rikice-rikice tare da tabbatar da cewa gwamnati da jama’a suna bin kundin tsarin mulkin ƙasar.
Tun bayan samun ancin kai a shekarar 1975, Comoros ta fuskanci sauye-sauyen siyasa da dama, ciki har da juyin mulki da gyare-gyaren kundin tsarin mulki.
A yanzu, Comoros memba ce ta ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama, ciki har da Majalisar ɗinkin duniya, da kungiyoyin Tarayyar Afirka, Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci da kuma Arab League. Kasancewarta mamba a waɗannan ƙungiyoyi yana taimaka mata wajen bunƙasa dangantakar diflomasiyya, tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
Tattalin arziki
Tattalin arzikin Comoros ya ta’allaka ne musamman a kan noma, kamun kifi, yawon buɗe ido da kuma kuɗaɗen da ‘yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje ke aikowa ga iyalansu. Duk da kasancewarta ƙasa mai ƙaramin fili da ƙarancin albarkatun masana’antu, noma yana ci gaba da kasancewa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar tare da samar da ayyukan yi ga yawancin jama’a.
Comoros ta shahara wajen samar da kayan ƙamshi da amfanin gona na kasuwanci. Daga cikin manyan kayayyakin da ƙasar ke fitarwa akwai vanilla, kanumfari da ylang-ylang, wani tsiro da ake amfani da shi wajen samar da turare da sauran kayayyakin ƙamshi. Comoros na daga cikin manyan ƙasashen duniya masu samar da ylang-ylang, wanda ke ba ta muhimmiyar matsayi a kasuwar turare ta duniya.
Kamun kifi
Kamun kifi ma na da muhimmiyar rawa a tattalin arzikin ƙasar saboda kasancewarta tsibirai a cikin Tekun Indiya. Jama’a da dama suna samun abin dogaro daga kamun kifi da kuma kasuwancin kayan teku. Haka kuma, kifaye da sauran abincin teku suna daga cikin muhimman abubuwan da ake ci a ƙasar.
Yawon buɗe ido
Fannin yawon buɗe ido yana bunƙasa sosai saboda kyawawan rairayin bakin teku, tsaunuka masu aman wuta, gandun daji da kuma yalwar halittun ruwa.
Wata muhimmiyar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga tattalin arzikin Comoros ita ce kuɗaɗen da ƴan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje ke aikowa gida. Waɗannan kuɗaɗe suna taimakawa iyalai da dama wajen biyan buƙatun rayuwa da kuma tallafawa tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya.
Muhimmancin Comoros a idon Duniya
Duk da cewa Comoros ƙasa ce ƙarama mai tsibirai a Tekun Indiya, tana da babban matsayi a idon duniya saboda yanayin wurinta, tarihinta da kuma rawar da take takawa a yankin gabashin Afirka. Matsayin ƙasar a tsakanin nahiyar Afirka da hanyoyin ruwa na Tekun Indiya ya sanya ta zama muhimmiyar mahaɗa ta zirga-zirga da kasuwanci tun ƙarni da dama da suka gabata.
Comoros tana da muhimmanci a fannin tsaro da harkokin teku saboda kasancewarta kusa da mashigar Mozambique, ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa da jiragen ruwa na duniya ke bi wajen jigilar kayayyaki. Wannan matsayi ya sa ƙasashe da ƙungiyoyin duniya ke nuna sha’awa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
A fannin addini da al’adu, Comoros tana daga cikin ƙasashen Afirka da al’ummarta kusan gaba ɗaya Musulmai ne. Wannan ya ba ta matsayi na musamman a cikin duniyar Musulunci, musamman ta hanyar kasancewarta mamba a ƙungiyoyin Musulunci na ƙasa da ƙasa da kuma gudummawar da take bayarwa wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmi.
Ƙasar tana da suna a duniya wajen samar da wasu daga cikin muhimman kayan ƙamshi da ake amfani da su a masana’antar turare. Vanilla, kanumfari da ylang-ylang da ake samarwa a Comoros suna isa kasuwannin duniya, lamarin da ya sa ƙasar ke da muhimmiyar rawa a wannan fanni na tattalin arziki.
Kamar yadda ya gabata, Comoros na taka rawa a ƙungiyoyin duniya da na yanki kamar majalisar dinkin duniya, Kungiyoyin Tarayyar Afrika, ƙungiyar haɗa kan Musulmai da Arab League. Ta hanyar waɗannan ƙungiyoyi, ƙasar tana shiga tattaunawa da shirye-shiryen da suka shafi zaman lafiya, ci gaba, tattalin arziki da kare muradun ƙasashe masu tasowa.
Bugu da ƙari, Comoros tana da muhimmanci a fannin kare muhalli da halittu masu rai. Tsibiranta suna ɗauke da nau’o’in tsirrai da dabbobi masu yawa, wasu daga cikinsu ba a samun su a sauran sassan duniya. Wannan ya sa ƙungiyoyin kare muhalli da cibiyoyin bincike na duniya ke ba da muhimmanci ga ƙasar wajen kare halittu da rage tasirin sauyin yanayi.
Matsaloli da ƙalubale
Kamar sauran ƙasashe masu tasowa, Comoros na fuskantar matsaloli da ƙalubale da dama waɗanda ke da tasiri ga ci gabanta na tattalin arziki, siyasa da zamantakewa. Duk da irin ci gaban da ƙasar ta samu a wasu fannoni, har yanzu akwai batutuwa da ke buƙatar kulawa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Ƙarancin tattalin arziki
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen ƙasar shi ne ƙarancin tattalin arziki da yawaitar talauci. Yawancin jama’a suna dogaro ne da noma da kamun kifi na gargajiya, yayin da damar samun ayyukan yi a masana’antu da sauran fannoni ke da iyaka. Wannan yanayi yana hana tattalin arzikin ƙasar bunƙasa cikin sauri.
Ƙarancin ababen more rayuwa
Comoros tana kuma fuskantar matsalar rashin wadatattun ababen more rayuwa kamar hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa, samar da wutar lantarki da wasu muhimman ayyukan gwamnati. Wannan ya rage damar zuba jari da bunƙasar kasuwanci a cikin ƙasar.
Matsalolin siyasa
A fannin siyasa, Comoros ta sha fama da rashin kwanciyar hankali a wasu lokuta tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 1975. Juyin mulki da rikice-rikicen siyasa da suka faru a tarihi sun yi tasiri ga tsarin mulki da ci gaban ƙasar, ko da yake an samu ingantuwar zaman lafiya a shekarun baya-bayan nan.
Sauyin yanayi
Sauyin yanayi na daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta. Kasancewar Comoros ƙasa ce ta tsibirai, tana cikin haɗarin fuskantar hauhawar ruwa a teku, ambaliyar ruwa, guguwa da sauran matsalolin muhalli. Waɗannan matsaloli suna iya yin illa ga noma, kamun kifi da rayuwar jama’a gaba ɗaya.
Koma bayan limi da kiwon lafiya
Har ila yau, ƙasar na fuskantar ƙalubale a fannin lafiya da ilimi. A wasu yankuna, samun ingantattun cibiyoyin lafiya da makarantu yana kasancewa da wahala, musamman a wuraren karkara. Wannan na iya shafar ci gaban albarkatun ɗan Adam da ingancin rayuwar jama’a.
Ƙaura
Wani ƙalubale kuma shi ne ƙaura da yawan dogaro da kuɗaɗen da ƴan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje ke aikowa gida. Duk da cewa waɗannan kuɗaɗe suna taimakawa tattalin arziki, dogaro da su sosai na iya nuna raunin wasu fannoni na tattalin arzikin cikin gida.
Jerin Shugabannin Comoros tun daga farko
Tun bayan samun ƴancin kai daga Faransa a ranar 6 ga Yuli, 1975, ƙasar Comoros ta samu shugabanni da dama. Wasu sun hau mulki ta hanyar zaɓe, yayin da wasu kuma suka hau ta hanyar juyin mulki. Ga jerin sunayensu
Ahmed Abdallah (1975): Shi ne shugaban ƙasar na farko bayan samun ‘yancin kai. Ya ayyana Comoros a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta daga Faransa. Sai dai bai daɗe a mulki ba aka yi masa juyin mulki.
- Said Mohamed Jaffar (1975-1976): Ya karɓi mulki bayan kifar da gwamnatin Ahmed Abdallah. Mulkinsa ya kasance na wucin gadi kuma ya fuskanci matsalolin siyasa.
- Ali Soilih (1976-1978): Ya yi ƙoƙarin kawo sauye-sauye a harkokin siyasa da tattalin arziki. Ya yi wasu gyare-gyare masu yawa, duk da wasu daga cikinsu sun haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma.
- Said Atthoumani (1978): Ya shugabanci ƙasar na ɗan lokaci bayan juyin mulki da ya kifar da Ali Soilih.
- Ahmed Abdallah (1978-1989): Ya sake komawa kan mulki kuma ya yi shugabanci na tsawon shekaru goma sha ɗaya. A lokacin mulkinsa ne aka samu ɗan kwanciyar hankali idan aka kwatanta da shekarun baya.
- Said Mohamed Djohar (1989-1995): Ya gaji Ahmed Abdallah bayan rasuwarsa. Mulkinsa ya fuskanci ƙalubale da dama ciki har da yunkurin juyin mulki.
- Mohamed Taki Abdoulkarim (1996-1998): An zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Ya yi ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan tsibiran Comoros, amma ya rasu yana kan mulki.
- Tadjidine Ben Saïd Massounde (1998-1999): Ya zama shugaban riƙon ƙwarya bayan rasuwar Mohamed Taki Abdoulkarim.
- Azali Assoumani (1999-2006): Ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki. Daga baya ya jagoranci sauye-sauyen kundin tsarin mulki da suka taimaka wajen rage rikice-rikicen siyasa tsakanin tsibiran ƙasar.
- Ahmed Abdallah Mohamed Sambi(2006-2011): An fi saninsa da Ayatollah na Comoros saboda karatunsa na addini. Ya mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki da haɗin kan ƙasa.
- Ikililou Dhoinine (2011-2016): Ya ci gaba da manufofin zaman lafiya da ci gaba. A lokacin mulkinsa an yi ƙoƙarin bunƙasa harkokin kiwon lafiya da ilimi.
- Azali Assoumani (2016–Yanzu): Ya sake komawa mulki bayan lashe zaɓe. Ya aiwatar da wasu gyare-gyaren tsarin mulki da tattalin arziki. Har yanzu shi ne shugaban ƙasar Comoros a lokacin rubuta wannan bayani.
Manazarta
Comoros — history and culture. (n.d.).
Grokipedia (n.d.). List of heads of state of the Comoros. Grokipedia
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.