Skip to content

Denmark

Denmark ƙasa ce da ke yankin arewacin turai, sannan tana daga cikin ƙasashen yankin Scandinavia musamman Norway da Sweden. Denmark tana da tsarin mulkin masarautawato constitutional monarchy, inda sarki ko sarauniya ke zama shugaban ƙasa, yayin da gwamnati da majalisar dokoki ke gudanar da harkokin siyasa da mulkin ƙasa. Babban birnin ƙasar shine Copenhagen, wanda kuma shine cibiyar siyasa, tattalin arziki da al’adun Denmark. Masarautar Denmark tana da dangantaka ta musamman da Greenland da Faroe Islands, waɗanda suke da ikon cin gashin kansu a cikin Kingdom of Denmark.

Yanayin ƙasa da muhalli

Kamar yadda ya gabata, Denmark tana cikin Arewacin Turai, kuma tana daga cikin ƙasashen Scandinavia. Ƙasar tana tsakanin tekun Arewa wato North Sea da tekun Baltic. A gefen kudu tana da iyaka da Jamus, yayin da Sweden da Norway suke a arewa da gabas ta hanyar ruwan teku.

Babban yankin ƙasar shi ne Jutland Peninsula, wanda yake shimfiɗe daga kudancin Denmark zuwa arewa, kuma shi ne ɓangaren ƙasar da yake haɗe da nahiyar Turai. Sauran manyan sassan ƙasar kuwa suna kan tsibirai, musamman Zealand, inda babban birnin Copenhagen yake, da Funen. Denmark tana da fiye da tsibirai 400, duk da cewa ba dukkansu ne ake zaune a kansu ba.

Ƙasar tana da fili mai faɗi amma ba ta da manyan duwatsu. Yanayinta ya fi kasancewa ƙasa mai laushi da tuddai ƙanana, filayen noma, ciyayi, dazuzzuka da yankunan bakin teku.

Tutar ƙasar Denmark
Yanayi da tsarin tutar ƙasar Denmark

Denmark tana da tsayin bakin teku sosai, wanda ya kai kusan kilomita 8,750. Saboda kasancewarta ƙasa mai yawan tsibirai da kuma kusanci da teku, ruwa yana da muhimmamci a yanayin ƙasar.

Al’umma da harshe

Al’ummomi

Denmark ƙasa ce mai yawan jama’a kusan miliyan 6.03, a bisa ƙididdigar da aka yi a watan Agusta 2026. Jama’ar ƙasar sun haɗa da ‘yan asalin Denmark da kuma al’ummomin da suka samo asali daga ƙasashe daban-daban, a sassan duniya.

Harsuna

Danish shi ne babban harshen da jama’ar Denmark ke amfani da shi. Sannan yana cikin rukunin harsunan Germanic na dangin harsunan Indo-European, kuma yana da kusanci da Norwegian da Swedish saboda tarihinsu na Nordic guda.

Harshen Danish yana da haruffa guda uku da suka bambanta da haruffan Turanci na yau da kullum wato (Æ, Ø da Å). A cikin ƙasar kuma akwai yaruka daban-daban na Danish, musamman a yankunan karkara da tsibiran ƙasar. Ɗaya daga cikin sanannun yarukan yankin shi ne Sønderjysk, wanda ake magana da shi a kudancin Jutland.

A cikin Kingdom of Denmark, harsunan yankunan masu cin gashin kansu suna da matsayi na musamman. A Greenland, harshen Greenlandic shi ne harshen hukuma, yayin da a Faroe Islands, Faroese shi ne harshen hukuma tare da Danish.

Addini da al’adu

Addinai

Kiristanci, musamman Evangelical Lutheranism, shi ne addinin da ya fi tarihi da alaƙa da al’ummar Denmark. Tsarin mulkin ƙasar ya bayyana Evangelical Lutheran Church a matsayin Danish People’s Church, kuma gwamnati tana tallafa mata. A halin yanzu, kusan kashi 72 na jama’ar Denmark suna cikin wannan cocin.

Har ila yau akwai kuma Musulmai, Katolika, Yahudawa da mabiya wasu addinai a ƙasar, domin Denmark tana da ƴancin yin addini. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya bai wa mutane damar yin ibada bisa imaninsu.

Al’adu

Al’adun Denmark suna da alaƙa sosai da tarihin Nordic, rayuwar bakin teku, aikin noma, Kiristanci da kuma tsarin rayuwar al’umma. Ɗaya daga cikin kalmomin da suka shahara wajen bayyana salon rayuwar Danish ita ce hygge, wadda ke nuni da jin daɗin zama cikin yanayi mai nutsuwa, kusanci da iyali ko abokai, da jin daɗin ƙananan abubuwa na rayuwa.

Bikin Kirsimeti na daga cikin manyan bukukuwan da ake yi a Denmark. Haka kuma ana bikin wasu ranaku da bukukuwan gargajiya waɗanda suka samo asali daga tarihin Kiristanci da al’adun Nordic.

Denmark ta kuma shahara da ƙirar kayan ɗaki da gine-gine na zamani, musamman salon Danish design, wanda ya fi karkata ga sauƙi, amfani da abu yadda ya kamata da kyakkyawan tsari.

Tarihin kafuwar Denmark

Tarihin Denmark ya samo asali tun daga zamanin da mutanen farko suka fara zama a yankin bayan ƙarshen Ice Age, wato kimanin shekaru 10,000 kafin haihuwar Annabi Isa. Daga baya noma da kiwo suka bazu, sannan al’ummar yankin suka shiga zamanin ƙarfe da kasuwanci da sauran sassan Turai.

A lokacin Viking Age, musamman daga ƙarni na 8 zuwa na 11, Denmark ta zama wata muhimmiyar cibiyar ikon Vikings a Arewacin Turai. Sarakuna irin su Gorm the Old da ɗansa Harald Bluetooth sun taka muhimmiyar rawa wajen haɗa yankunan Denmark ƙarƙashin mulkin sarauta. Jelling Stone, wanda Harald Bluetooth ya kafa a ƙarni na 10, yana daga cikin muhimman alamomin tarihin ƙasar, kuma ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin farkon rubuce-rubucen da suka ambaci Denmark.

A kusan 965 AD, Harald Bluetooth ya karɓi Kiristanci, wanda ya taimaka wajen sauya tsarin addini da zamantakewar Denmark. A ƙarni na gaba ne, masarautar Denmark ta ƙara ƙarfafa ikonta, kuma ta shiga manyan sauye-sauyen siyasa na Scandinavia. A 1397, Denmark, Norway da Sweden suka shiga Kalmar Union, wadda Sarauniya Margrethe I ke jagoranta. Wannan haɗin kai ya ci gaba har Sweden ta fice a 1523.

A shekarar 1660, Denmark ta koma tsarin masarautar kama karya wato absolute monarchy, inda ikon siyasa ya fi karkata ga sarki. Wannan tsarin ya ɗauki kusan ƙarni biyu, har zuwa sauye-sauyen siyasa na ƙarni na 19. A ranar 5 Yuni 1849, Sarki Frederik VII ya rattaba hannu kan kundin tsarin mulkin farko na Denmark, wanda ya kawo ƙarshen mulkin kama-karya tare da kafa tsarin mulkin dimokuraɗiyya da majalisa.

A ƙarni na 19 da na 20, Denmark ta ci gaba da sauya tsarin mulkinta da zamantakewarta. A 1915, an ba mata cikakken ƴancin zaɓe, sannan a 1920 wani ɓangare na kudancin Jutland ya koma ƙarƙashin Denmark bayan zaɓen jama’a.

Tsarin mulki

Denmark tana da tsarin mulkin dimokuraɗiyya na majalisa wato parliamentary democracy, tare da masarautar tsarin mulki wato constitutional monarchy. Wannan yana nuna cewa akwai Sarki a matsayin shugaban ƙasa, amma ikon mulkin ƙasar yana aiki ne bisa kundin tsarin mulki da tsarin majalisa. Kundin tsarin mulkin Denmark na yanzu ya samo asali daga 5 Yuni 1849, lokacin da aka kawo ƙarshen mulkin kama-karya aka kafa tsarin mulkin kundin tsarin mulki.

Masarautar Denmark

Sarautar Denmark tana bin tsarin gado, tun bayan sauyin dokar gadon sarauta da aka amince da ita a 2009, ɗan fari ko ƴa mace ta farko ce ke da fifiko wajen gadon sarauta ba tare da la’akari da jinsi ba.

Majalisar dokoki

Folketing ita ce majalisar dokokin Denmark. Tana da mambobi 179, waɗanda jama’a ke zaɓa ta hanyar zaɓe kai tsaye da na sirri. Zaɓen majalisa dole ne ya gudana aƙalla sau ɗaya cikin shekaru huɗu, kodayake ana iya gudanar da zaɓe kafin wannan lokacin.

Tsarin siyasar Denmark yana da jam’iyyu da dama. Saboda haka, sau da yawa gwamnati tana samuwa ne ta hanyar haɗin gwiwar jam’iyyu.

Gwamnati da firayim minista

Firayim Minista shi ne shugaban gwamnati kuma yana jagorantar majalisar ministoci. Gwamnatin ba za ta iya ci gaba da mulki ba idan Folketing ta bayyana rashin amincewa da ita da rinjaye. Wannan shi ake kira negative parliamentarism, kuma yana daga cikin muhimman ginshiƙan tsarin siyasar Denmark.

Tattalin arziki

Denmark tana da tattalin arziki mai ƙarfi da bunƙasa, wanda ya dogara kan masana’antu, ayyukan kasuwanci, fasaha, noma, sufuri da kasuwancin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2025, GDP ɗin Denmark ya kai kusan dala biliyan 462.5, yayin da GDP a kan kowane mutum ya kai kusan $76,970. Tattalin arzikin ya samu ci gaban kusan 2.9% a wannan shekarar.

Masana’antu

Masana’antu da magunguna suna daga cikin muhimman ginshiƙan tattalin arzikin Denmark. Ƙasar tana da manyan kamfanoni a fannonin pharmaceuticals, biotechnology da life sciences, tare da zuba jari mai yawa a bincike da fasaha.

Noma

Noma da masana’antar abinci ma suna da muhimmiyar rawar takawa. Denmark tana samar da kayan gona da dabbobi, musamman naman alade, madara, hatsi da sauran kayan abinci. Ana kuma fitar da yawancin kayayyakin abincin zuwa kasuwannin ƙasashen waje.

Sufuri da harkokin teku suna da muhimmanci saboda matsayinta a tsakanin Tekun Arewa da Baltic Sea.

Makamashi

Denmark tana daga cikin ƙasashen da suka yi fice wajen amfani da makamashin wind energy. A cewar gwamnatin Denmark, iska tana samar da wani babban ɓangare na makamashin ƙasar, kuma Denmark tana da ƙwarewa sosai wajen fasahar turbines da makamashin iska.

Kasuwancin ƙasa da ƙasa

Denmark tattalin arzikinta yana da matuƙar alaƙa da kasuwancin duniya. Ƙasar tana fitar da kayayyaki da ayyuka zuwa kasuwannin ƙasashen Turai da sauran duniya. Daga cikin muhimman abubuwan da take fitarwa akwai magunguna da kayayyakin sinadarai, injuna da kayan fasaha, kayan abinci, kayayyakin sufuri da ayyukan kasuwanci.

Haraji

Denmark tana da tsarin welfare state, inda gwamnati ke karɓar haraji sannan ta yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen wajen samar da ayyukan jama’a kamar ilimi, kiwon lafiya, tallafin zamantakewa da kula da yara.

Fasaha

Fasahar zamani da digitalisation suna da muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Denmark. Gwamnati da kamfanoni suna amfani da tsarin dijital wajen gudanar da ayyuka, kasuwanci da hulɗa da jama’a. Denmark ta kuma haɓaka fannonin fintech, information technology, biotechnology da fasahar muhalli.

Muhimmancin Denmark a duniya

Duk da cewa Denmark ƙaramar ƙasa ce idan aka kwatanta da manyan ƙasashen duniya, tana da muhimmiyar rawar takawa a harkokin Turai, tsaro, tattalin arziki, ci gaban ƙasa da ƙasa da kuma harkokin Arctic. Matsayinta na ƙasa mai haɗa Tekun Arewa da Baltic, tare da kasancewar Greenland da Faroe Islands cikin Masarautar Denmark, yana ƙara mata muhimmancin dabarun siyasa da tsaro.

Matsayinta a Tarayyar Turai

Denmark ta shiga Tarayyar Turai (EU) tun daga 1973. Tana shiga cikin ayyukan majalisar EU da sauran hukumomin Tarayyar, kuma tana amfani da Danish krone maimakon euro saboda tana da yarjejeniyar keɓewa daga amfani da euro.

Tsaro da NATO

Denmark tana daga cikin ƙasashen da suka kafa NATO a shekarar 1949. Saboda matsayinta tsakanin Arewacin Turai, Tekun Baltic da Tekun Atlantika, ƙasar tana da muhimmiyar rawar takawa wajen tsaron yankin. Denmark kuma tana ba da gudummawa ga ayyukan NATO da wasu ayyukan tsaro na ƙasa da ƙasa.

Muhimmancin Arctic da Greenland

Greenland yana ƙara muhimmancin Denmark a harkokin Arctic. Masarautar Denmark tana da matsayi na musamman a yankin Arctic, kuma tun Mayu 2025 Kingdom of Denmark ke riƙe da shugabancin Arctic Council na shekarun 2025–2027. Wannan ya ba Denmark ƙarin dama wajen shiga tattaunawar da ta shafi tsaron Arctic, muhalli, sauyin yanayi, bincike da harkokin tattalin arziki.

Mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya

Denmark tana daga cikin ƙasashen da suka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), kuma ta dade tana shiga ayyukan da suka shafi kare haƙƙin ɗan Adam, rage talauci, taimakon jin kai da samar da ci gaba. A shekarun 2025–2026, Denmark tana cikin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Security Council).

Al’adu da sanannun abubuwa

A fannin al’adu, Denmark ta yi fice a duniya ta hanyar adabi, ƙira, gine-gine, kayan daki, fasahar zamani da kamfanonin da suka samo asali daga ƙasar. Sunayen tarihi kamar marubucin tatsuniyoyi Hans Christian Andersen, da kuma al’adun Nordic na Denmark, sun taimaka wajen yaɗa sunan ƙasar a duniya.

Matsaloli da ƙalubale

Duk da ƙarfin tattalin arzikin Denmark da ingantaccen tsarin jin daɗin jama’a, ƙasar tana fuskantar wasu ƙalubale na tsawon lokaci. Daga cikin su akwai tsufar al’umma, wanda ke buƙatar ƙara inganta kiwon lafiya, kula da tsofaffi da ma’aikata; da kuma tsadar gidaje, musamman a manyan birane.

Haka kuma, sauyin yanayi yana ƙara haɗarin ambaliya da zaizayar bakin teku, yayin da wasu fannoni kamar kiwon lafiya da kula da tsofaffi ke fuskantar ƙarancin ma’aikata. Tattalin arzikin ƙasar kuma yana da alaƙa sosai da kasuwancin duniya, don haka sauyin tattalin arziki ko rikice-rikicen ƙasa da ƙasa na iya yin tasiri a kanta.

Jerin shuwagabannin Denmark tun daga farko

A nan akwai ɗan muhimmin bayani da ke nuna Denmark masarauta ce ta tsarin mulki, don haka akwai bambanci tsakanin Shugaban Ƙasa wato Sarki da Shugaban Gwamnati. Sarki ne shugaban ƙasa, yayin da Firayim Minista ke jagorantar gwamnati.

Sarakunan Denmark

Masarautar Denmark tana da tarihi sama da shekaru 1,000, kuma ana danganta jerin sarakunanta tun daga Gorm the Old. Daga cikin manyan sarakunan zamanin ƙarshe akwai:

  • Christian VII 1766–1808
  • Frederik VI 1808–1839
  • Christian VIII 1839–1848
  • Frederik VII 1848–1863
  • Christian IX 1863–1906
  • Frederik VIII 1906–1912
  • Christian X 1912–1947
  • Frederik IX 1947–1972
  • Margrethe II 1972–2024
  • Frederik X 2024–yanzu

Wannan jerin ya nuna yadda masarautar ta ci gaba daga zamanin mulkin sarauta zuwa tsarin constitutional monarchy bayan Kundin Tsarin Mulki na 1849.

Firayim ministocin Denmark

Tun bayan kafa tsarin gwamnati na zamani, Denmark ta samu Firayim Minista da dama. Wasu daga cikin na baya-bayan nan sun haɗa da:

  • Anders Fogh Rasmussen — 2001–2009
  • Lars Løkke Rasmussen — 2009–2011
  • Helle Thorning-Schmidt — 2011–2015
  • Lars Løkke Rasmussen — 2015–2019
  • Mette Frederiksen — 2019–yanzu.

Manazarta

Geography. (2021, February 10). Denmark. Geography.

GlobalEDGE. (n.d.). Denmark: Introduction.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×