Skip to content

Madagascar

Madagascar ƙasa ce da ke cikin tekun Indiya, a gabashin gaɓar Afirka. Ita ce tsibiri mafi girma a Afirka, kuma tana daga cikin manyan tsibiran duniya. Babban birnin ƙasar shi ne Antananarivo. Madagascar ta shahara sosai saboda keɓantaccin halittun dabbobi da tsirrai, wanda mafi yawancin nau’ikan halittun da ake samu a ƙasar ba a samun su a wasu wuraren a duniya, ciki har da nau’ikan lemur da dama, wannan ya sa Madagascar ta kasance ƙasa ta musamman wajen nazarin halittu.

Madagascar tana da albarkatun ƙasa da dama, kuma tattalin arzikinta ya dogara da noma, kamun kifi, ma’adinai da yawon buɗe ido.

Tarihin kafuwar Madagascar

Tarihin Madagascar ya samo asali ne daga zuwan mutane daga kudu maso gabashin Asiya da gabashin Afirka. Daga baya ne kuma Larabawa suka kafa wuraren kasuwanci a gaɓar arewa maso yammacin tsibirin, sannan turawa suka fara zuwa yankin daga ƙarni na 16.

A ƙarni na 18 da na 19, Masarautar Merina ta ƙara faɗaɗa ikonta har ta mamaye babban ɓangare na tsibirin. A ƙarni na 19 ne kuma turawa suka ƙara tasiri a yankin, har Faransa ta kafa kanta a Madagascar a 1885, sannan ta karɓi cikakken iko bayan yaƙe-yaƙe a 1895–1896, inda aka kawo ƙarshen masarautar Merina.

Tutar ƙasar Madagascar
Tutar ƙasar Madagascar.

Madagascar ta kasance ƙarƙashin mulkin Faransa har zuwa lokacin da ta samu ƴancin kai a ranar 26 ga Yuni 1960. Bayan samun ƴancin kai, ƙasar ta shiga wasu lokutan sauye-sauyen siyasa da mulkin soja, tare da sauye-sauyen tsarin tattalin arziki da mulki.

Yanayin ƙasa da muhalli

Kamar yadda ya gabata, Madagascar tana cikin Tekun Indiya, a gabashin gaɓar Afirka. Tana rabuwa da nahiyar Afirka ta hanyar mashigin Mozambique, wanda ke tsakaninta da Mozambique. Tsibirin yana da tsawon da ya kai kilomita 1,600 daga arewa zuwa kudu, kuma yana da faɗin da ya kai kilomita 570 a mafi girman wurinsa. Ƙasar tana da yanayin ƙasa mai banbanci sosai. A tsakiyarta akwai manyan tsaunuka da tuddai, yayin da yankunan bakin teku suke da ƙananan filaye. Gabashin ƙasar kuma yana da gangaren ƙasa mai tsawo zuwa tekun Indiya, yayin da yammacin ƙasar yake da filayen masu faɗi.

Yanayin Madagascar ya bambanta daga yanki zuwa yanki. Yankin gabas ya fi samun zafi da ruwan sama, yayin da yamma basa samun ruwa mai yawa, musamman kudu maso yamma. Yankunan da ke da tsaunuka a tsakiyar ƙasar suna da yanayi mai sanyi fiye da bakin teku. Har ila yau, ƙasar tana fuskantar guguwar teku musamman a lokacin damina, yayin da wasu yankunan kudu ke fuskantar fari.

Al’umma da harshe

Al’ummomi

Al’ummar Madagascar suna da bambancin asali da al’adu, wanda ya samo asali daga haɗuwar mutanen da suka zo daga yankunan kudu maso gabashin Asiya da gabashin Afirka. Akwai ƙabilu da al’ummomi daban-daban a ƙasar, waɗanda kowannen su ke da wasu al’adu da salon rayuwa na musamman.

Harsuna

Harshen Malagasy shi ne babban harshen ƙasar kuma ana amfani da shi sosai a rayuwar yau da kullum. Harshen yana da alaƙa da harsunan Austronesian na yankin kudu maso gabashin Asiya, duk da cewa Malagasy ta tasirantu da wasu harsunan Afirka da na kasuwanci.

Sannan Faransanci ma yana taka muhimmiyar rawa a hukumance, kuma ana amfani da shi sosai a gwamnatance, fannin ilimi, kasuwanci da wasu harkokin ƙasa da ƙasa.

Addini da al’adu

Addinai

Mutanen Madagascar suna da ƴancin yin kowane addini, hakan ne ya haifar da mabiya addinai daban-daban. Sai dai Kiristanci ne addinin da ya fi yawan mabiya, musamman Furotesta da Katolika. Haka kuma akwai Musulmai da kuma mutanen da ke bin addinan gargajiya na Malagasy, waɗanda ke da imani da tsohon tarihin kakanni da al’adun gargajiya. Wasu mutane kuma suna haɗa wasu daga cikin al’adunsu na gargajiya da koyarwar Kiristanci.

Al’adu

Al’adun Madagascar sun samo asali ne daga haɗuwar mutanen Afirka da kudu maso gabashin Asiya, kuma waɗannan al’adu suna bayyana ne a cikin kiɗa, rawa, tufafi, abinci da bukukuwa. Girmama kakanni yana da muhimmiyar rawa a wasu al’ummomi, kuma akwai bukukuwa da al’adu na musamman da ake gudanarwa domin tunawa da su.

Tambarin ƙasar Madagascar
Tambarin coat of arms na ƙasar Madagascar.

Daga cikin sanannun al’adun ƙasar akwai Famadihana, wata al’ada ce da wasu al’ummomin Malagasy ke gudanarwa domin girmama kakanni. Sai kuma Hira Gasy, wato wasan kwaikwayo da kiɗan gargajiya, duk suna cikin abubuwan da suka shahara a al’adun ƙasar.

Tsarin mulki

Madagascar tana da tsarin jamhuriya mai tsarin shugaban ƙasa wato semi-presidential republic. Shugaban ƙasa shi ne shugaba mai cikakken iko, kuma ana zaɓensa ta hanyar kuri’ar jama’a. Yana da babban matsayi wajen tsara manufofin ƙasa da kuma kula da harkokin tsaro da siyasar ƙasar.

Firayim Minista kuma shi ne shugaban gwamnati, kuma shugaban ƙasa ne ke naɗa shi daga cikin jam’iyyar ko ƙungiyar siyasa da ke da rinjaye a majalisar dokoki. Inda gwamnati ke gudanar da harkokin yau da kullum na ƙasar.

Majalisar dokokin Madagascar tana da majalisu biyu da suka haɗa da National Assembly da kuma Senate. Ayyukansu sun haɗa da tsara dokoki, amincewa da wasu manufofin gwamnati da kuma sa ido kan harkokin mulki.

Sai ɓangaren shari’a da shima yana da nasa tsarin kotuna, kuma High Constitutional Court na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa dokoki da wasu matakan gwamnati sun dace da kundin tsarin mulkin ƙasar.

Dan haka, tsarin mulkin Madagascar ya dogara ne kan rarraba iko tsakanin Shugaban Ƙasa, Gwamnati, Majalisar Dokoki da Shari’a, tare da kundin tsarin Mulkin ƙasar a matsayin babban tushen dokokin gwamnati.

Tattalin arziki

Tattalin arzikin Madagascar ya fi dogaro ne da noma, wanda yake samar da aikin yi da kuma abin dogaro ga yawancin al’ummar ƙasar. Daga cikin muhimman amfanin gonar da suke nomawa akwai shinkafa, vanilla, kofi, cloves da lychee. Madagascar tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da vanilla a duniya. Sannan kamun kifi da kiwon kifaye, masana’antu da ma’adinai ma suna da muhimmiyar rawar takawa. Har ila yau, ƙasar tana da albarkatun ma’adinai kamar nickel, cobalt, graphite da ilmenite, waɗanda ake fitarwa zuwa kasuwannin duniya.

Yawon buɗe ido ma na bada gudummawa ga tattalin arzikin ƙasar, saboda keɓantattun namun dajin da suke da su, gami da dazuzzuka, rairayin bakin teku da wuraren tarihi.

Muhimmancin Madagascar a duniya

Madagascar tana da matsayi na musamman a duniya, saboda halittun dajin da suke da su. Kimanin kashi 90 na nau’ikan halittun daji da ake samu a ƙasar ba a samun su a wani wuri a duniya, lamarin da ya sa Madagascar ta zama muhimmiyar cibiyar binciken kimiyyar halittu da kare muhalli. Ƙasar tana da matsayi a kasuwancin duniya, musamman ta hanyar fitar da vanilla, nickel, cobalt, graphite da wasu kayayyakin noma.

Kuɗin ƙasar Madagascar
Wasu daga cikin nau’ikan takardun kuɗin ƙasar Madagascar.

Sannan Madagascar tana da muhimmanci a Tekun Indiya, saboda matsayinta na kusa da hanyoyin safara a cikin teku tsakanin Afirka da Asiya. Haka kuma.

Shugaban ƙasar Madagascar, Michael Randrianirina.
Michael Randrianirina, shi ne shugaban ƙasar Madagascar mai ci.

Bugu da ƙari, yawon buɗe ido ya sa Madagascar ta zama sananniya a duniya saboda lemurs, baobab, dazuzzuka da wurare masu zafi da sauran halittun da ba a samun irinsu a ko’ina.

Matsaloli da ƙalubale

Talauci

Madagascar tana fuskantar manyan ƙalubale da suka shafi talauci da rashin daidaiton tattalin arziki. Wani babban kaso na al’ummar ƙasar yana rayuwa cikin matsanancin talauci, musamman a yankunan karkara, inda damar samun ingantaccen ilimi, lafiya da ababen more rayuwa ke wahala.

Sauyin yanayi

Sauyin yanayi ma yana ƙara matsalolin ƙasar. Guguwar cyclone, ambaliyar ruwa da fari kan lalata amfanin gona da gidaje, musamman a yankunan da suka fi dogaro da noma. Wata babbar matsala ita ce sare dazuzzuka da lalacewar muhalli. Ana rasa wasu wuraren zama na namun daji saboda sare bishiyoyi. Wannan na barazana ga nau’ikan halittu na musamman da Madagascar ta shahara da su.

Ƙarancin ababen more rayuwa

Haka kuma, ƙasar tana fuskantar raunin ababen more rayuwa da ƙarancin makamashi, wanda ke kawo cikas ga sufuri, kasuwanci da bunƙasar masana’antu.

Shugabannin Madagascar tun daga farko

Kamar sauran ƙasashe, Madagascar na da jerin shuwagabannin da suka mulke ta shekaru da dama, waɗanda suka haɗa da:

  • Philibert Tsiranana: Ya fara mulkinsa a shekarar 1959 zuwa 1972.
  • Gabriel Ramanantsoa: Ya kafa gwamnatin sa a 1972 zuwa 1975.
  • Richard Ratsimandrava: Ya fara tare da gama mulkinsa a 1975.
  • Gilles Andriamahazo: Shima a 1975 yayi mulkinsa ya gama.
  • Didier Ratsiraka: Ya fara mulkinsa 1975, inda ya gama 1993.
  • Albert Zafy: Ya yi mulki a 1993 zuwa1996.
  • Norbert Ratsirahonana: Ya yi mulkin riƙon ƙwarya a 1996 zuwa 1997.
  • Didier Ratsiraka: A karo na biyu ya dasa mulkinsa 1997 zuwa 2002.
  • Marc Ravalomanana: Ya fara mulki a 2002 zuwa 2009.
  • Hippolyte Ramaroson: Ya yi mulkin riƙon ƙwarya na ɗan lokaci a 2009.
  • Andry Rajoelina: shima ya shugabanci Madagascar na riƙon ƙwarya daga 2009 zuwa 2014.
  • Hery Rajaonarimampianina: Ya yi mulkinsa a 2014 zuwa 2018
  • Rivo Rakotovao: Shima mulkin riƙon ƙwarya ne a 2018 zuwa 2019.
  • Andry Rajoelina: An sake zaɓar sa a 2019 zuwa 2025.
  • Michael Randrianirina: Shi ne  shugaban Madagascar a yanzu, ya kuma fara mulkinsa ne a shekarar 2025 bayan rikicin siyasa da juyin mulkin soja na Oktoba a shekarar. Hukumar CIA kuma ta nuna shi a matsayin shugaban Madagascar a sabuntawar da aka yi a watan Yuli 2026.

Madagascar ƙasa ce mai dimbin tarihi da al’adu a tekun Indiya, wadda ta samu sauye-sauye masu yawa tun daga zamanin tsoffin al’ummominta. A fannin siyasa, Madagascar ta fuskanci lokuta daban-daban na mulkin farar hula, mulkin soja, rikice-rikice da sauye-sauyen tsarin mulki. Duk da waɗannan ƙalubale, ƙasar ta ci gaba da gina cibiyoyin gwamnati da tsarin siyasa da nufin tabbatar da zaman lafiya, dimokuradiyya da ci gaba.

A yau, Madagascar na da muhimmiyar rawar takawa a yankin tekun Indiya da gabashin Afirka. Arzikinta na ƙasa, musamman albarkatun noma, ma’adinai, gandun daji da yawon buɗe ido, na ba ta babbar damar bunƙasa tattalin arzikinta. Haka kuma, kasancewar ƙasar gida ga nau’o’in halittu masu yawa da ba a samunsu a wasu sassan duniya ya sanya kiyaye muhalli ya zama muhimmin ɓangare na makomarta.

Manazarta

EBSCO Research. (n.d.) Madagascar | Geography and Cartography | Research Starters. EBSCO.

Planeta Africa Travel. (2021, January 13). Madagascar, Complete Guide: Climate, Currency, Tourism –  Planeta Africa Travel.

Experience Nat Hab’s Wild Madagascar Adventures. (n.d.). [Video]. Natural Habitat Adventures.

 

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×