Skip to content

Burundi

Burundi ƙasa ce mai cin gashin kanta, wadda ke yankin da ake kira Great Lakes Region na gabashin Afirka. Wannan yanki ya shahara ne da manyan tafkuna, tsaunuka. Burundi tana daga cikin ƙasashe masu ƙarancin girma a Afirka, sai dai tana da yawan jama’a idan aka kwatanta da girman ƙasarta. Wannan ne ya sa take cikin ƙasashe mafi cunkoson jama’a a nahiyar Afrika. Ƙasar tana da muhimmiyar rawar takawa a yankinta, saboda tana a tsakanin ƙasashen da suka haɗa da Rwanda, Tanzania, da jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango. Wannan matsayi yana da tasiri sosai wajen kasuwanci, hulɗar ƙasa da ƙasa, da kuma harkokin tsaro.

Babban birnin ƙasar shi ne Gitega. An kuma mayar da shi babban birni a hukumance ne a shekarar 2019, yayin da Bujumbura ke ci gaba da zama cibiyar kasuwanci da tattalin arziki. Burundi na fuskantar ƙalubale masu yawa da suka haɗa da talauci, ƙarancin ababen more rayuwa, da kuma tasirin sauyin yanayi. Amma duk da haka, ƙasar na da albarkatun noma da kuma al’umma masu ƙoƙarin bunƙasa rayuwarsu, wanda ke nuna akwai damar ci gaba a nan gaba.

Matsayin ƙasa da iyakoki

Burundi tana a yankin gabashin Afirka, wurin da ake kira Great Lakes Region. Wannan yanki ya ƙunshi ƙasashen da ke kewaye da manyan tafkuna da tsaunuka, wanda ke ba su yanayi na musamman. Burundi ba ta da hanyar kai tsaye zuwa teku. Wannan kuma yana shafar kasuwancinta da sufuri, domin dole ne ta bi ta wasu ƙasashe wajen fitar da kaya ko shigo da su.

Tutar ƙasar Burundi
Tutar ƙasar Burundi na launuka uku: kore, ja da kuma fari. Sannan akwai taurari uku a tsakiya.

Burundi tana da iyaka da ƙasashe uku da suka haɗa da Rwanda, wadda take a arewacin ƙasar sai Tanzania a gabas da kudu. Democratic Republic of the Congo kuma a yamma. Har ila yau a ɓangaren yamma kuma, Burundi tana kusa da tafkin Lake Tanganyika, wanda yake ɗaya daga cikin manyan tafkuna mafi zurfi a duniya. Wannan tafki yana taka rawa wajen sufuri, kamun kifi, da kuma tattalin arzikin ƙasar.

Yanayin ƙasa

Yawancin yankin ƙasar Burundi tsaunuka ne da tuddai, sannan akwai filayen ƙasa a kusa da tafkin Tanganyika. Tsayin ƙasar yana sa yanayinta ya fi sanyi fiye da wasu ƙasashen yankin. Haka kuma, ƙasar tana da ƙasa mai amfani ga noma, amma tana fuskantar matsalolin zaizayar ƙasa da ke rage ƙarfinta.

Burundi kafin mulkin mallaka

Kafin zuwan Turawa, ƙasar Burundi ta kasance ƙasa mai cikakken tsarin sarauta da ya daɗe yana gudana tun shekaru aru-aru. Wannan tsarin sarauta ana kiran shi Masarautar Burundi, kuma sarkin ƙasar wanda ake kira Mwami shi ne ke da cikakken iko a kan harkokin mulki da shugabanci. Mwami yana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, warware rikice-rikice, da kuma kula da haɗin kan al’ummar ƙasar.

A wannan lokaci, al’ummar Burundi sun kasu zuwa manyan rukuni uku, wato Hutu, Tutsi, da Twa. Waɗannan rukuni suna rayuwa tare a ƙarƙashin wannan tsarin sarauta, kuma kowane rukuni yana da irin rawar da yake takawa a cikin al’umma. Duk da kasancewar akwai bambance-bambance a tsakaninsu, al’ummar ƙasar sun kasance cikin tsari da haɗin kai a ƙarƙashin jagorancin sarki.

Burundi a lokacin mulkin mallaka

A ƙarshen ƙarni na goma sha tara ne Turawa suka fara mamaye yankunan Afirka, ciki har da Burundi. Da farko, Jamus ce ta mallaki Burundi, inda ta haɗa ta cikin yankin da ake kira German East Africa. Wannan ya sa Burundi ta shiga ƙarƙashin ikon Turawan Jamus, waɗanda suka kafa tsarin mulki na mallaka domin cin gajiyar albarkatun yankin. Bayan ƙarshen Yaƙin Duniya na Farko, Jamus ta rasa iko a kan wasu yankunanta na mallaka. Daga nan ne Belgium ta karɓi ikon mulkin Burundi tare da Rwanda, ƙarƙashin kulawar League of Nations. Wannan canjin mulki ya kawo sabbin tsare-tsare na mulkin mallaka da suka yi tasiri sosai ga zamantakewar al’ummar Burundi.

A lokacin mulkin Belgium, an samu manyan sauye-sauye a tsarin zamantakewa da siyasar Burundi. Mulkin mallakar Belgium ya ƙarfafa bambance-bambancen ƙabilanci tsakanin Hutu da Tutsi, inda aka fifita wasu rukuni fiye da wasu wajen samun ilimi, mukaman gwamnati, da sauran damammaki. Wannan tsarin fifiko ya jawo rashin daidaito a cikin al’umma, inda wasu rukuni suka fara jin ana ware su daga muhimman fannoni na rayuwa. Wannan shi ne ya haifar da tushen rikice-rikicen ƙabilanci da suka biyo baya, domin ya haifar da rashin jituwa, ƙiyayya, da rashin amincewa tsakanin al’ummomin ƙasar.

Samun ‘yancin kai

Burundi ta samu ‘yancin kai daga Belgium a shekarar 1962, bayan shekaru masu yawa na mulkin mallaka. Wannan lokaci ya kasance abin farinciki ga al’ummar ƙasar, domin sun samu damar gudanar da harkokinsu da kansu ba tare da ikon Turawan mulkin mallaka ba. Bayan samun ‘yancin kai, Burundi ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin tsarin sarauta na wani ɗan lokaci, inda sarki ya ci gaba da mulki. Amma daga baya, aka kifar da tsarin sarautar, aka kafa tsarin jamhuriya, inda aka fara shugabancin gwamnati ta hanyar shugaban ƙasa.

Rikice-rikicen ƙabilanci

Daga shekarun 1960 zuwa 1990, Burundi ta shiga cikin rikice-rikicen ƙabilanci masu tsanani tsakanin Hutu da Tutsi. Waɗannan rikice-rikice sun samo asali ne daga rabuwar kai da wariyar da aka gina tun lokacin mulkin mallaka.

A shekarar 1972, an fuskanci mummunan tashin hankali da kisan kiyashi wanda ya jawo asarar rayuka masu yawa. Bayan haka kuma, rikice-rikicen siyasa da juyin mulki suka ci gaba da faruwa a ƙasar. A shekarar 1993, bayan zaɓen shugaban ƙasa na farko daga ƙabilar Hutu, rikici ya sake ɓarkewa cikin tsanani, wanda daga ƙarshe ya kai ga barkewar yaƙin basasa.

Yaƙin basasa da zaman lafiya

Yaƙin basasar Burundi ya fara ne daga shekarar 1993 har zuwa 2005, kuma ya jawo mummunar asara ga ƙasar. Mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da dubban mutane suka tsere daga gidajensu suka zama ‘yan gudun hijira a cikin ƙasar da ma ƙasashen maƙwabta. Bayan shekaru na rikici, an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tare da taimakon ƙasashen duniya da ƙungiyoyi masu zaman kansu. Wannan yarjejeniya ta taimaka wajen rage tashin hankali da kuma dawo da kwanciyar hankali a hankali.

Tun daga wannan lokaci, Burundi ta fara ƙoƙarin sake gina ƙasa da samar da haɗin kai tsakanin al’umma. Duk da cewa har yanzu ƙasar tana fuskantar ƙalubalen siyasa da tattalin arziki, ana ci gaba da ƙoƙarin gina zaman lafiya mai ɗorewa da inganta rayuwar jama’a.

Yawan ama’ar Burundi

Burundi na da yawan jama’a da ya haura miliyan 12, duk da cewa ƙasa ce mai ƙaramin faɗi. Wannan ya sa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi cunkoson jama’a a nahiyar Afirka. Mafi yawan jama’ar ƙasar suna rayuwa ne a yankunan karkara, inda rayuwarsu ta dogara da noma da sana’o’in gargajiya. Haka kuma, sama da kashi 40 cikin 100 na jama’ar ƙasar yara ne masu ƙasa da shekaru 15, wanda hakan ke nuna cewa Burundi na da yawan matasa masu yawa.

Addinai

Yawancin al’ummar Burundi masu bin addini ne, kuma addinin Kiristanci shi ne ya fi rinjaye a ƙasar, musamman Katolika da Furotesta. Haka kuma akwai mabiya Musulunci, da kuma wasu da ke bin addinan gargajiya. Addini yana da muhimmiyar rawa a rayuwar al’ummar Burundi, domin yana tasiri wajen zamantakewa, tarbiyya, da gudanar da wasu al’adu na gargajiya.

Al’adu

Al’adun mutanen Burundi suna da alaƙa sosai da rayuwar karkara da kuma tarihinsu na gargajiya. Daya daga cikin fitattun al’adunsu shi ne kiɗa da rawa, musamman rawar gargajiya da ake yi tare da bugun ganguna. Wannan rawa tana da muhimmanci a bukukuwa da lokutan murna. Haka kuma, al’ummar Burundi suna daraja iyali da haɗin kai, musamman ta hanyar al’adun aure na gargajiya. Suna kuma girmama manya, wanda hakan ya zama ginshiƙi a zamantakewar al’umma.

Tambarin coat of arms na ƙasar Burundi
Wannan shi ne tambarin coat of na ƙasar Burundi, da hukumomin ƙasar suke amfani da shi.

Yawancin mutane a ƙasar suna rayuwa cikin sauƙi, suna noma da kiwon dabbobi domin ciyar da iyalansu. Wannan rayuwa ta karkara ta taimaka wajen kare al’adunsu na gargajiya har zuwa yau.

Siyasar Burundi

Burundi na amfani da tsarin jamhuriya, inda shugaban ƙasa ke jagorantar gwamnati da ƙasa baki ɗaya. Haka kuma akwai majalisar dokoki da kuma jam’iyyun siyasa da ke taka rawa wajen tafiyar da gwamnati. Sai dai siyasar Burundi ta daɗe tana fama da rikice-rikice na ƙabilanci tsakanin Hutu da Tutsi, da juyin mulki da matsalolin rashin daidaito a mulki. Duk da haka, bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka samu a farkon shekarun 2000, ƙasar ta fara tafiya a kan tsarin dimokuraɗiyya.

Tattalin arzikin Burundi

Burundi na daga cikin ƙasashe mafi ƙarancin tattalin arziki a duniya, amma tattalin arzikinta ya fi karkata ne a kan noma da ƙananan sana’o’i.

Noma

Noma shi ne babban ginshiƙin tattalin arzikin Burundi, domin kusan kashi 80 cikin 100 na jama’ar ƙasar suna dogaro da shi. Haka kuma noma yana bayar da fiye da kashi 40 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na ƙasar.

Burundi tana samar da muhimman amfanin gona kamar kofi da shayi, waɗanda su ne manyan kayayyakin fitarwa zuwa ƙasashen waje. Baya ga haka, ana noma masara, wake, da sauran amfanin gona domin amfanin cikin gida.

Bayan noma, akwai wasu ƙananan hanyoyin tattalin arziki kamar kasuwanci na cikin gida, ƙananan masana’antu, da kamun kifi a tafkin Tanganyika, amma har yanzu noma ne ke jagorantar tattalin arzikin ƙasar.

Ƙalubale da matsalolin Burundi

Duk da irin ƙoƙarin da ƙasar Burundi take yi na bunƙasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya, har yanzu tana fuskantar manyan ƙalubale da matsaloli a fannoni daban-daban. Waɗannan matsaloli suna tasiri sosai ga rayuwar jama’a da kuma cigaban ƙasar baki ɗaya.

Talauci

Ɗaya daga cikin manyan matsalolin Burundi shi ne talauci. Burundi na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci a duniya, inda yawancin jama’arta ke rayuwa cikin ƙarancin kuɗin shiga. Wannan talauci yana shafar samun abinci, lafiya, ilimi, da sauran muhimman abubuwan rayuwa, musamman a yankunan karkara inda mafi yawan jama’a ke rayuwa.

Karancin abinci

Wata babbar matsala ita ce rashin wadataccen abinci. Saboda yawan dogaro da noma na gargajiya, sauyin yanayi, da ƙarancin kayan aikin noma, ana yawan fuskantar ƙarancin abinci a wasu lokuta. Wannan yana haifar da yunwa da rashin ingantaccen abinci mai gina jiki ga jama’a da dama.

Takardun kuɗin ƙasar Burundi
Wasu daga cikin nau’ikan kuɗaɗen ƙasar Burundi.

Karancin aikin yi

Har ila yau, Burundi na fuskantar matsalar ƙarancin ayyukan yi, musamman ga matasa. Duk da cewa matasa a ƙasar suna da yawa, amma ba a samar da isassun guraben ayyukan yi da za su wadatar da su ba. Wannan na janyo ƙarancin kuɗaɗen shiga da kuma ƙara yawan talauci a cikin al’umma.

Rikice-rikicen siyasa

A ɓangaren siyasa kuwa, har yanzu akwai rashin kwanciyar hankali a siyasa, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cim ma bayan yaƙin basasa. Rikice-rikicen siyasa, rashin amincewa tsakanin jam’iyyun siyasa, da tasirin bambance-bambancen ƙabilanci suna ci gaba da kawo cikas ga cigaban ƙasar.

Matsalolin kiwon lafiya

Haka kuma, Burundi tana fama da raunin tsarin kiwon lafiya. Asibitoci da cibiyoyin lafiya ba su wadata ba, musamman a yankunan karkara. Rashin kayan aiki, ƙarancin ma’aikatan lafiya, da yawaitar cututtuka suna hana jama’a samun ingantaccen kulawar lafiya.

Matsalolin ilimi

Matsalolin ilimi ma suna cikin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta. Duk da ƙoƙarin inganta ilimi, har yanzu akwai ƙarancin makarantu, malamai, da kayan koyo. Wannan yana sa yara da dama, musamman a yankunan karkara, ba sa samun damar yin karatu yadda ya kamata.

Cunkoson jama’a

Wani ƙalubale kuma shi ne yawaitar jama’a. Burundi ƙasa ce mai ƙarancin faɗi amma tana da yawan jama’a sosai, wanda hakan ke haddasa matsin lamba a kan albarkatun ƙasa kamar filayen noma, ruwa, da matsuguni. Wannan matsin lamba yana haifar da rikice-rikice a wasu lokuta, musamman a tsakanin manoma.

Raunin tattalin arziki

Bugu da ƙari, Burundi na fuskantar raunin tattalin arziki, domin tattalin arzikinta ya fi dogaro da noma, wanda ke da rauni ga sauyin yanayi da ƙarancin fasaha. Rashin bunƙasar masana’antu da ƙarancin zuba jari suna rage damar haɓakar tattalin arzikin ƙasar.

Évariste Ndayishimiye
Shugaban Burundi mai ci, Évariste Ndayishimiye.

Jerin sunayen shugabannin Burundi

Tun bayan samun ‘yancin kai daga ƙasar Belgium a shekarar 1962, Burundi ta sami shugabanni da dama, tun daga sarakuna har zuwa shugabannin ƙasa a tsarin jamhuriya. Ga jerin sunayen shugabannin Burundi daga lokacin samun ‘yanci zuwa yau:

  • Mwambutsa IV Bangiricenge (1962–1966): Shi ne sarkin Burundi a lokacin da ƙasar ta samu ‘yancin kai. Ya ci gaba da mulki a matsayin Mwami, amma daga baya rikice-rikicen siyasa suka raunana mulkinsa.
  • Ntare V Ndizeye (1966): Ya gaji mahaifinsa Mwambutsa IV a matsayin sarki, amma mulkinsa bai daɗe ba domin an kifar da shi a shekarar 1966 lokacin da aka soke tsarin sarauta.
  • Michel Micombero (1966–1976): Shi ne shugaban ƙasa na farko bayan kafa jamhuriya a Burundi. Ya hau mulki bayan juyin mulki, kuma mulkinsa ya kasance ƙarƙashin tsarin soja.
  • Jean-Baptiste Bagaza (1976–1987): Ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki. Ya yi ƙoƙarin kawo wasu sauye-sauye, amma mulkinsa ya kasance ƙarƙashin iko mai tsauri.
  • Pierre Buyoya (1987–1993): Ya hau mulki ta hanyar juyin mulki. A zamaninsa ne aka fara ƙoƙarin buɗe ƙofa ga dimokuraɗiyya.
  • Melchior Ndadaye (1993): Shi ne shugaban ƙasa na farko da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya, kuma shugaban farko daga ƙabilar Hutu. An kashe shi bayan ɗan lokaci kaɗan da hawa mulki, wanda ya haddasa rikicin basasa.
  • Sylvie Kinigi (1993–1994): Ta riƙe mulki na riƙon ƙwarya bayan kisan Ndadaye. Ta kasance ɗaya daga cikin shugabannin riƙo na Burundi.
  • Cyprien Ntaryamira (1994): Ya zama shugaban ƙasa bayan Ndadaye, amma shi ma ya mutu a hatsarin jirgin sama bayan ɗan gajeren lokaci.
  • Sylvestre Ntibantunganya (1994–1996): Ya jagoranci ƙasar a lokacin tsananin rikicin siyasa da yaƙin basasa.
  • Pierre Buyoya (1996–2003): Ya sake komawa mulki bayan juyin mulki. Daga baya ya shiga yarjejeniyar raba mulki domin kawo ƙarshen yaƙin basasa.
  • Domitien Ndayizeye (2003–2005): Ya hau mulki a ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya, a wani mataki na raba mulki tsakanin ɓangarori masu rikici.
  • Pierre Nkurunziza (2005–2020): Ya yi mulki na tsawon shekaru 15. Mulkinsa ya kawo wasu sauye-sauye, amma ya kuma fuskanci rikice-rikicen siyasa musamman bayan ya nemi wa’adi na uku.
  • Évariste Ndayishimiye (2020–zuwa yau): Shi ne shugaban ƙasa na yanzu. Ya hau mulki bayan mutuwar Pierre Nkurunziza, kuma yana ci gaba da jagorantar ƙasar.

Manazarta

Rush, C. (2025, May 10). Exploring the Burundi Franc (BIF): A closer look at the currency of Burundi. Beyond Borders. .

globalEDGE. (n.d.). Burundi: Economy. .

The country – Burundi Embassy in Germany. (n.d.).

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×