Skip to content

Equatorial Guinea

Equatorial Guinea ƙasa ce da ke yankin Afirka ta tsakiya, a gefen tekun Guinea. Ƙasar Equatorial Guinea ta ƙunshi sassa biyu mabanbanta, wato ɓangaren nahiyar da ake kira Río Muni, da kuma yankin tsibirai, inda mafi girma cikinsu ita ce tsibirin Bioko. Babban birnin ƙasar shi ne Malabo, wanda yake a tsibirin Bioko.

A yankin Afirka, Equatorial Guinea ce kaɗai ƙasar da harshen sifaniyanci yake cikin harsunan hukuma, sakamakon tarihin mulkin mallakar Sifaniya. Har ila yau, Faransanci da Fotugis suna cikin harsunan hukuma na ƙasar.

Yanayin ƙasa da muhalli

Kamar yadda ya gabata, Equatorial Guinea tana yankin yammacin Afirka ta tsakiya, a gefen tekun Guinea daga tekun Atlantika. Ƙasar tana da tsarin ƙasa na musamman domin ta ƙunshi ɓangaren nahiyar Afirka da kuma wasu tsibirai, wanda suka hana ta kasancewa ƙasa guda ɗaya a wuri ɗaya.

Babban ɓangaren nahiyar ƙasar ana kiransa Río Muni, garin na da iyaka da Cameroon a arewa da kuma Gabon a gabas da kudu. Baya ga wannan, ƙasar tana da muhimman tsibirai da suka haɗa da Bioko, Annobón, Corisco, Elobey Grande, da Elobey Chico. Tsibirin Bioko shi ne mafi girma, kuma a kansa ne babban birnin ƙasar Malabo yake. Jimillar faɗin ƙasar kusan kilomita murabba’i 28,051 ce, wanda ya sanya ta cikin ƙananan ƙasashen Afirka ta fuskar yanki. Duk da sunanta na da alaƙa da layin Equator, amma yankin ƙasar ba ya kan layin Equator kai tsaye; sai dai tsibirin Annobón yana kusa da shi.

Tutar ƙasar Equatorial Guinea
Tutar ƙasar Equatorial Guinea

Yanayin ƙasar galibi na zafi da danshi ne, sannan suna samun ruwan sama mai yawa a mafi yawan shekara. Yankunan tsibirai suna da tsaunuka masu asalin aman wuta, yayin da yankin nahiyar ke da gandun daji, kwazazzabai da filaye masu tudu. Mafi tsayin wuri a ƙasar shi ne Pico Basile, wanda tsayinsa ya kai kusan mita 3,008.

Al’umma da harshe

Al’ummomi

Al’ummar Equatorial Guinea ta ƙunshi ƙabilu da harsuna daban-daban, waɗanda suka haɗa al’adun yankin nahiyar Afirka da na tsibirai. Mafi rinjayen ƙabila a ƙasar ita ce Fang, wadda ta zama mafi yawan al’umma musamman a yankin Río Muni, sauran manyan ƙabilun sun haɗa da Bubi da ke zaune a tsibirin Bioko, Ndowe, Annobon, da Bujeba.

Harshe

A fannin harshe, Equatorial Guinea tana da matsayi na musamman a Afirka domin ita ce ƙasa mai cin gashin kanta a Afirka da harshen Sifaniyanci yake cikin manyan harsunan hukuma kuma yake yaɗuwa sosai a harkokin gwamnati, ilimi da sadarwa. Sauran harsunan sun haɗa da Faransanci da Fotugis.

Sannan a kwai harsunansu nagargajiya da suke rayuwar yau da kullum da su, inda harshen Fang shi ne mafi yaɗuwa cikin harsunan gida, sannan akwai Bubi, Benga, Ndowe, da wasu harsunan yankin Bantu da ake amfani da su a al’umma daban-daban.

Addini da al’adu

Addinai

A ƙasar Equatorial Guinea, addini da al’adu suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’umma. Inda mafi yawan al’ummar Equatorial Guinea suna bin addinin Kiristanci, musamman Roman Catholic, wanda ya samo asali daga tasirin mulkin mallakar Sifaniya. An yi ƙiyasi cewa, mafi yawancin jama’a suna bin Katolika, yayin da wasu kuma suke bin ɗarikun Furotesta daban-daban.

A gefe guda kuma, akwai ƙananan adadin mutane masu bin addinin Musulunci, musamman daga baƙin haure ko wasu ƙananan ƙabilu. Haka kuma, har yanzu akwai wasu al’ummomi da ke bin addinan gargajiya, inda ake haɗa imani da ruhohi, kakanni, da al’adun gargajiya cikin rayuwar yau da kullum.

Al’adu

Ta ɓangaren al’adu kuwa, mutanen Equatorial Guinea sun bambanta bisa ƙabilu. Kowane rukuni yana da salon rayuwa, kiɗa, rawa da bukukuwa na musamman. A cikin ƙabilar Fang, ana amfani da kiɗa da ganguna wajen bukukuwa da tarurrukan gargajiya, kuma ana ba da muhimmanci ga labaran baka. Ƙabilar Bubi kuma tana da al’adu da suka shafi noma, bukukuwa na addini na gargajiya, da kuma raye-raye na musamman.

A tsibirin Annobón, al’adunsu na da alaƙa da al’adu daga Portugal da kuma Afirka, wanda ya ba su salo na musamman a kiɗa da harshe. Haka kuma, mutanen ƙasar suna amfani da kayan gargajiya da tufafi na musamman a lokutan bukukuwa.

Tarihin kafuwar Equatorial Guinea

Kafin zuwan Turawa, yankin Equatorial Guinea ya kasance gida ga ƙabilu daban-daban, musamman Fang a yankin nahiyar Río Muni da Bubi a tsibirin Bioko. Waɗannan al’ummomi sun rayu ne ta hanyar noma, farauta, kamun kifi da kuma tsarin shugabancin gargajiya. A ƙarni na 15, Turawan Fotigal suka fara isa yankin tsibirai, inda suka kafa kansu, musamman a tsibirin Bioko da Annobón. Daga baya, a ƙarshen ƙarni na 18, yankin ya shiga ƙarƙashin ikon Sifaniya, wadda ta ƙarfafa mulkin mallaka a ƙasar na tsawon lokaci.

Tambarin ƙasar Equatorial Guinea
Tambarin coat of arms na ƙasar Equatorial Guinea.

A lokacin mulkin mallakar Sifaniya, an kafa gonaki na Cocoa da coffee, kuma an shigo da ma’aikata daga wasu yankuna na Afirka domin aiki a gonakin. A wannan lokaci, an samu sauye-sauyen zamantakewa, addini da kuma harshe.

Equatorial Guinea ta samu ƴancin kai daga Sifaniya a ranar 12 ga Oktoba, 1968, inda aka kafa ta a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Bayan samun ƴancin kai, ƙasar ta shiga wasu matsaloli na siyasa, ciki har da sauye-sauyen gwamnati da rikice-rikice na cikin gida a wasu lokuta.

Daga ƙarshen shekarun 1990 zuwa gaba, gano man fetur da iskar gas ya canza tattalin arzikin ƙasar sosai, wanda ya sa ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka masu arzikin makamashi.

Tsarin mulki

Equatorial Guinea ƙasa ce mai tsarin mulki na jamhuriya, inda shugaban ƙasa shi ne babban mai iko a ƙasa. Duk da cewa akwai tsarin gwamnati da aka tsara a kundin tsarin mulki.

Sannan shugaban ƙasa shi ne shugaban gwamnati kuma shi ne ke da iko mafi girma a fagen zartarwa. Shugaban ƙasa yana jagorantar harkokin siyasa, tsaro, da manufofin ƙasa gaba ɗaya. A tarihi, ƙasar ta kasance ƙarƙashin shugabanci mai dogon zango na Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, wanda ya hau mulki tun a shekarar 1979 bayan juyin mulki.

Har ila yau a ƙasar akwai tsarin majalisa mai sassa biyu wato Senate, da majalisar wakilai. Waɗannan majalisu suna da alhakin tsara dokoki da tattaunawa kan al’amuran ƙasa.

Babbar jam’iyyar siyasa a ƙasar ita ce Democratic Party of Equatorial Guinea (PDGE), wadda ke da rinjaye sosai a siyasar ƙasar. Akwai wasu ƙananan jam’iyyun adawa, amma tasirinsu yana da iyaka a tsarin siyasa.

Tattalin arziki

Tattalin arzikin Equatorial Guinea ya samu sauyi mai girma daga kasancewarsa mai dogaro da noma zuwa mai dogaro da albarkatun man fetur da iskar gas.

Tun daga ƙarshen shekarun 1990, gano manyan albarkatun man fetur da gas ya zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar. Wannan ya sa ƙasar ta shiga cikin jerin ƙasashen Afirka masu samun kuɗaɗen shiga masu yawa daga fannin makamashi. Man fetur yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje, kuma shi ne ke kawo mafi yawan kuɗin gwamnati.

Sai dai kafin samuwar man fetur ɗin, noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikinsu. Kuma har yanzu, noma yana da muhimmanci musamman a yankunan karkara, inda suke shuka kayayyakin da suka haɗa da cocoa, coffee, ayaba, rogo da sauran amfanin gona

Har ila yau, gandun daji na ƙasar na da muhimmanci wajen samar da itace da kayayyakin gandun daji.

Kuɗin ƙasar Equatorial Guinea
Wasu daga cikin nau’ikan takardun kuɗin ƙasar Equatorial Guinea.

Kasantuwar ƙasar a bakin teku kuma, kamun kifi ma na taka rawa ga arzikin ƙasar, musamman ga al’ummomin da ke tsibiri da na bakin teku. Sannan Gwamnati na ƙoƙari wajen jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje, musamman a fannin makamashi da gine-gine.

Muhimmancin Equatorial Guinea a duniya

Equatorial Guinea tana da muhimmanci a idon duniya ta fannoni daban-daban. Tun bayan gano manyan albarkatun mai, ƙasar ta shiga cikin jerin ƙasashen da ke samar da makamashi ga kasuwannin duniya. Wannan ya sa ta zama babbar abokiyar hulɗa ga kamfanonin makamashi na ƙasashen waje.

A yankin Afirka kuwa, Equatorial Guinea tana cikin ƙungiyoyin yankin da suka haɗa da Economic Community of Central African States (ECCAS), inda take taka rawa wajen tattaunawa kan zaman lafiya da haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen yankin.

Ta fuskar diflomasiyya, Ƙasar tana da alaƙa da ƙasashe da dama a duniya, ciki har da ƙasashen Turai, Asiya da Amurka. Wannan alaƙa tana taimakawa wajen zuba jari, musamman a fannin makamashi da gine-gine. Sannan ƙasar tana da muhimmanci a fannin tsaron yankin teku (maritime security), musamman wajen yaƙi da fashin teku da kare hanyoyin kasuwanci a Tekun Atlantika.

Matsaloli da ƙalubale

Duk da cewa Equatorial Guinea tana daga cikin ƙasashen Afirka masu albarkatun man fetur da iskar gas, itama tana fuskantar wasu muhimman matsaloli da ƙalubale a fannoni daban-daban na rayuwar ƙasa da suka haɗa da

  • Rashin daidaiton rabon arziki: ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen ƙasar shi ne rashin daidaiton rabon arziki. Duk da yawan kuɗaɗen shigar ƙasar daga man fetur ne, yawancin jama’a ba sa tasirantuwa da wannan arziki kai tsaye, musamman a yankunan karkara.
  • Talauci da rashin aikin yi: Akwai talauci da rashin aikin yi a tsakanin jama’a, musamman matasa, duk da cewa ƙasar tana da albarkatun masu kawo kuɗi, amma damar aiki ba ta isa ga kowa ba.
  • Batutuwan siyasa da mulki: Tsarin siyasar ƙasar yana fuskantar suka daga ƙasashen duniya dangane da ƙarancin gasa ta siyasa, ƙarfin iko a hannun ɗan tsirarun shugabanni da kuma ƙalubalen inganta dimokiraɗiyya
  • Rashin ababen more rayuwa: Duk da cigaban da aka samu a manyan birane, har yanzu akwai ƙalubalen ababen more rayuwa a wasu yankunan karkara, kamar hanyoyi, ruwa mai tsafta, da wutar lantarki.
  • Lafiya da ilimi: Fannonin ilimi da kiwon lafiya suna ci gaba, amma har yanzu akwai buƙatar ƙarin ƙoƙarin gwamnati don inganta makarantu, asibitoci da ma’aikata a waɗannan fannoni.
  • Dogaro da man fetur: Ƙasar tana fuskantar haɗarin dogaro sosai da man fetur, wanda ke sa tattalin arzikinta ya kasance mai rauni idan farashin mai ya ragu a kasuwannin duniya.
Teodoro Obiang Nguema Mbasogo
Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shi ne shugaban ƙasar Equatorial Guinea mai ci kuma ya shafe sama da shekaru 57 yana ci gaba da mulkin ƙasar.

Jerin shugabannin Equatorial Guinea yun daga samun ‘yancin kai

Tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 1968, Equatorial Guinea ta samu shugabanni kaɗan, saboda tsawon lokacin mulki na wasu shugabanni. Daga cikin shugabannin akwai:

  • Francisco Macías Nguema (1968 – 1979): Shi ne shugaban ƙasa na farko da ya fara mulkin ƙasar tun daga samun ƴancin kai a hannun Sifaniya, sannan daga baya ya zama shugaban ƙasa mai cikakken iko. An hambarar da shi a juyin mulkin da ya faru a shekarar 1979.
  • Teodoro Obiang Nguema Mbasogo (1979 – zuwa yanzu): Ya hau mulki bayan juyin mulki a 1979. Shi ne kuma shugaban ƙasa mafi daɗewa a Afirka a halin yanzu. Ya kafa gwamnati bayan hambarar da Macías Nguema, sannan ya ci gaba da mulki har zuwa yanzu.

Manazarta

Grokipedia (2026, January 14). List of presidents of Equatorial Guinea. Grokipedia.

Equatorial Guinea. (n.d.). History and culture. Equatorial Guinea.

Global Tenders. (2025, April 21). Economy and business opportunities in Equatorial Guinea, Equatorial Guinean Equatoguinean economy. Global Tenders.

Office of the Historian. (n.d.). Equatorial Guinea – Countries – Office of the Historian.

 

 

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×