Norway ƙasa ce da ke arewacin Turai, wadda ke cikin yankin Scandinavia. Tana da iyaka mai tsawo da bakin teku a arewacin tekun Atlantika da tekun Arctic. Babban birnin Norway shi ne Oslo, inda tushen ƙasar ya samu asali tun a ƙarni na tara, yayin da kuma ta samu cikakken ƴancin kanta daga Sweden a shekara ta 1905.
A fagen shugabanci kuwa, ƙasar tana da tsarin mulkin masarauta, wato constitutional monarchy da tsarin dimokuraɗiyya na majalisa. Kundin tsarin mulkinta na 1814 na daga cikin tsofaffin rubutattun kundin tsarin mulki da har yanzu ake amfani da su a duniya. Norway na daga cikin ƙasashen da suka samu babban ci gaban tattalin arziki da walwalar jama’a, gami da albarkatun man fetur da iskar gas, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikinta, har ila yau, kiwon kifaye, jigilar kayayyaki ta ruwa ma taka rawa wajen cigaban tattalin arzikinta. Sannan ƙasar tana da wani babban asusun dukiyar ƙasa da ake amfani da shi wajen adana wani kaso daga kuɗaɗen albarkatun man fetur da zuba su a harkokin saka jari.
Tarihin kafuwar Norway
Tarihin Norway ya samo asali tun ƙarni na farko, amma ƙarshen ƙarni na 9 ya kasance lokaci na musamman wajen samuwar masarautar Norway, lokacin da Harald Fairhair ya haɗa ƙananan masarautun yankin ƙarƙashin mulki guda. Wannan zamani ya kuma kasance farkon zamanin Vikings, waɗanda suka yi suna wajen tafiye-tafiye, kasuwanci da yaƙe-yaƙe a sassan Turai. Daga baya Norway ta shiga ƙungiyoyin mulki da Denmark da Sweden.
Daga 1536 zuwa 1814, tana ƙarƙashin mulkin Denmark. A shekarar 1814, bayan yaƙe-yaƙen Napoleon, Norway ta rabu da Denmark, inda ta samar da kundin tsarin mulkinta a ranar 17 ga Mayu 1814, sannan ta shiga ƙungiyar sarauta da Sweden.

Wannan haɗin kai da Sweden ya ci gaba har zuwa 1905, lokacin da Norway ta yanke shawarar kawo ƙarshen sa. A ranar 7 ga Yuni 1905, majalisar Norway ta ayyana cewa sarkin Sweden ya daina zama sarkin Norway, kuma daga baya aka tabbatar da rabuwa da Sweden cikin lumana. An zaɓi Haakon VII a matsayin sabon sarkin Norway.
A ƙarni na 20, Norway ta gamu da manyan sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki. Ta fuskanci mamayar Jamus a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu a 1940–1945, sannan bayan yaƙin ta shiga wani sabon zamani na ci gaba da gina ƙasa. Daga baya ganowa tare da bunƙasar albarkatun man fetur da iskar gas a Tekun Arewa ya ƙara sauya tattalin arzikinta.
Yanayin ƙasa da muhalli
Kamar yadda ya gabata, ƙasar Norway tana a cikin arewacin Turai, a yammaci da arewacin yankin Scandinavian Peninsula. Tana da iyaka da Sweden a gabas, Finland a arewa maso gabas, da Rasha a arewa maso gabas. A sauran bangarorinta kuma tana fuskantar ruwan Tekun Barents, Tekun Norway, Tekun arewa da Skagerrak.
Siffar ƙasar tana da tsawo kuma siririya ce, tana da shimfiɗa kusan kilomita 1,752 daga kudu zuwa arewa. Yankin babban ɓangaren ƙasar ya kai kusan kilomita 323,781. Sannan Norway na da tsibiran Arctic, musamman Svalbard, wanda ke ƙarƙashin mulkin Norway.
Yanayin ƙasar ya fi karkata ga tsaunuka da tuddai, musamman a yammaci da tsakiyar ƙasar. Tsaunukan Scandinavia sun mamaye wani babban ɓangare na ƙasar, yayin da kwaruruka masu zurfi, tafkuna da rafuka suka ratsa tsakanin tsaunukan. Domin kusan kashi ashirin cikin ɗari na yankin ƙasar yana cikin tsaunuka da suka haura mita 900 a matakin teku.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi bambanta ƙasar da wasu ƙasashe shi ne fjords, wato dogayen teku da suka kutsa cikin ƙasa tsakanin manyan tsaunuka. An same su ne sakamakon aikin glaciers na tsawon shekaru, waɗanda suka sassaƙa kwarurruka masu zurfi, sannan ruwa ya mamaye su. Wannan ya sa gaɓar tekun Norway ta kasance a karkace, tare da haifar da fjords, gami da ƙananan tsibirai da manyan teku masu yawa. Gaɓar tekun Norway tana da tsawo sosai; babban yankin ƙasar kaɗai yana da fiye da kilomita 2,500 na gaɓar teku, idan ba a haɗa fjords da bays ba. Idan aka haɗa da su kuwa tsawonta ya fi haka nesa ba kusa ba.

Yanayin Norway yana bambanta daga yanki zuwa yanki. Yankunan bakin teku sun fi samun yanayi mai sauƙi fiye da yadda ake tsammani saboda tasirin North Atlantic Current, yayin da yankunan cikin ƙasa da arewa suka fi fuskantar sanyi mai tsanani. Tsaunuka kuma suna da tasiri sosai ga samuwar ruwan sama, inda yammacin ƙasar ke samun ruwan sama mai yawa, yayin da wasu yankunan gabashin tsaunuka basa samun ruwan sama sosai.
Haka kuma, wasu yankunan Norway suna fuskantar canjin yanayi na musamman kamar Midnight Sun, inda rana kan kasance sama da sararin samaniya na tsawon lokaci a lokacin bazara, da kuma Polar Night, lokacin da rana ba ta fitowa a sararin samaniya na wani lokaci a lokacin hunturu. Yankunan arewacin ƙasar kuma suna daga cikin wuraren da ake iya kallon Northern Lights.
Al’umma da harshe
Norway tana da al’ummomi masu bambancin asali da al’adu. Yawancin mazauna ƙasar ƴan Norway ne, amma akwai kuma al’ummomi baƙi daga ƙasashe daban-daban. A cikin al’ummomin ƙasar akwai Sámi, waɗanda ake ɗauka a matsayin ƴan asalin Norway. Sámi suna da nasu al’adu, tarihi da tsarin rayuwa, kuma suna da kaso mai yawa a cikin al’adun ƙasar.
Harshen Norwegian shi ne babban harshen ƙasar, kuma yana da nau’ikan rubutu guda biyu da suke da matsayi iri ɗaya, wato Bokmål da Nynorsk. Baya ga Norwegian, harsunan Sámi ma suna da daraja ta musamman a ƙarƙashin dokokin ƙasar, musamman a yankunan da al’ummar Sámi ta fi yawa.
Manyan harsunan Sámi da ake amfani da su a Norway a yau sun haɗa da Northern Sámi, Lule Sámi da Southern Sámi. Haka kuma, Norway tana darajta wasu harsunan ƙananan al’umma kamar Kven, Romani da Romanes.
Addini da al’adu
Addinai
A ƙasar Norway Kiristanci shi ne addinin da ya fi daɗewa da tasiri a tarihinsu, musamman ta hanyar Church of Norway, wadda ke da alaƙa da al’adar Lutheran. Har ila yau, Norway na da ƴancin addini, kuma akwai mabiya addinai daban-daban da kuma mutanen da ba sa bin wani addini. A shekarar 2025, kusan kashi 60.9% na mazauna Norway suna bin Church of Norway. Haka kuma akwai al’ummomin Musulmi, Hindu, Buddha, Yahudawa da sauran kungiyoyin addini daban-daban.
Al’adu
Al’adun Norway sun samo asali ne daga haɗuwar tarihin mutanen ƙasar da suka haɗa da rayuwar karkara, al’adun mazauna yankin teku da kuma Viking. Ana kuma daraja ayyukan waje kamar yawo a tsaunuka, ski da sauran wasanni a lokacin hunturu. Kayan gargajiya na Bunad suna daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen nuna al’adun yankuna daban-daban, musamman a lokacin bukukuwa.

Daga cikin manyan bukukuwan ƙasar akwai ranar kundin tsarin mulki ta 17 ga Mayu, wadda ake gudanar da ita cikin fareti da shagulgula. Haka kuma bukukuwan Kirsimeti na da muhimmiyar rawa ga mabiya addinin kiristanci. Sannan al’adun ƙabilar Sámi ma na daga cikin muhimman ɓangarori da ke nuna al’adun Norway, musamman a arewacin ƙasar.
Tsarin mulki
Kamar yadda ya gabata, Norway tana da masarautar tsarin mulki wato constitutional monarchy da tsarin dimokuraɗiyyar majalisa. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya samo asali ne daga 17 ga Mayu 1814, kuma shi ne ginshiƙin tsarin mulki da rarraba ikon gwamnati.
Sarki shi ne shugaban ƙasa, amma ikon siyasa na yau da kullum yana hannun zaɓaɓɓun wakilan jama’a da gwamnati. Gwamnatin ƙasar tana ƙarƙashin jagorancin Firayim Minista.
Storting ita ce majalisar dokokin Norway. Tana da wakilai 169, waɗanda jama’a ke zaɓa, kuma aikinta ya haɗa da yin dokoki, amincewa da kasafin kuɗi da sa ido kan ayyukan gwamnati.
Ikon gwamnati ya kasu zuwa manyan sassa uku: majalisar dokoki (Storting), bangaren zartarwa (Gwamnati), da bangaren shari’a (Kotuna). Kotuna suna da ƴancin yanke hukunci, kuma suna da ikon duba ko dokoki sun yi daidai da Kundin Tsarin Mulki.
Tattalin arziki
Norway tana da tattalin arziki mai ƙarfi da ya dogara da fannoni daban-daban. Man fetur da iskar gas suna daga cikin manyan ginshiƙan tattalin arzikinta, musamman wajen samar da kuɗin shiga da kuma fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje. A shekarar 2024, ɓangaren man fetur ya samar da kusan 22% na darajar kayayyakin da ƙasar ta samar, sannan ya kai kusan 48% na darajar kayayyakin da Norway ta fitar.
Baya ga man fetur, Norway tana da babbar harkar kamun kifi da kiwon kifaye, masana’antu, safara ta cikin ruwa, da ayyukan sabis. Kasancewar ƙasar tana da dogayen bakin teku, hakan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin da ya shafi teku.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta tsarin tattalin arzikin Norway shi ne Government Pension Fund Global, wanda aka kafa domin zuba wani kaso na kuɗaɗen albarkatun man fetur a kasuwannin duniya da adana arzikin ƙasar domin amfanin jama’a na tsawon lokaci. Gwamnati tana amfani da wani kaso daga asusun wajen tallafa wa kasafin kuɗin ƙasa, bisa ƙa’idojin da aka tsara domin kare arzikin a nan gaba.
Muhimmancin Norway a idon duniya
Duk da kasancewar Norway ƙasa ce mai ƙarancin yawan jama’a idan aka kwatanta da manyan ƙasashen duniya, amma tana da muhimmiyar rawar takawa a harkokin ƙasa da ƙasa. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba ta suna shi ne diplomasiyyar zaman lafiya, inda take taimakawa wajen tattaunawa da sasanta rikice-rikice tsakanin ɓangarori masu gaba da juna.
Norway kuma tana taka muhimmiyar rawa a majalisar ɗinkin duniya (UN), musamman wajen tallafa wa zaman lafiya, dokokin ƙasa da ƙasa, kare fararen hula da ayyukan jin kai. Haka kuma tana cikin NATO, wanda yake daga cikin muhimman ginshiƙan manufofinta na tsaro da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
Ƙasar tana ba da gudummawa ga ayyukan agaji da ci gaban ƙasashe, tare da tallafa wa shirye-shiryen da suka shafi zaman lafiya, rage rikice-rikice da bunƙasa rayuwar al’umma.
Matsaloli da ƙalubale
Duk da ci gaban da Norway ta samu a duniya, ƙasar tana fuskantar wasu ƙalubale da za su iya shafar rayuwar jama’a da tattalin arzikinta a nan gaba.
Sauyin yanayi na daga cikin manyan ƙalubalen. Ƙaruwar zafi na haifar da yawaitar ambaliyar ruwa, zaizayar ƙasa, dusar ƙanƙara mai haɗari da hauhawar matakin teku, lamarin da ke barazana ga wasu hanyoyi, gine-gine da muhallin halittu.

Har ila yau, tsufa da raguwar haihuwa ma na ƙara zama babban kalubale. Domin kuwa yawan tsofaffi na ƙaruwa a yankin, yayin da yawan mutanen da ke da ƙananan shekaru ba ya ƙaruwa akai-akai
Haka kuma, akwai bambancin ci gaba tsakanin birane da yankunan karkara. Wasu ƙananan garuruwa suna rasa jama’a, musamman matasa, yayin da wasu yankuna ke fuskantar ƙarancin ma’aikata da wahalar samar da wasu ayyukan jama’a.
A fannin tattalin arziki, Norway tana buƙatar shirin rage dogaro da kuɗaɗen man fetur a hankali, domin ana sa ran kuɗaɗen da ake samu daga man fetur za su ragu a nan gaba. Hakan yana buƙatar ƙara samar da sabbin hanyoyin ci gaban tattalin arziki.
Jerin sarakunan ƙasar Norway tun daga 1814
Norway ta kasance masarauta tun zamanin da. Harald Fairhair ne wanda aka fi ɗauka a matsayin sarkin farko da ya haɗa ƙananan masarautun Norway zuwa mulki guda kusan shekara ta 890.
Bayan ƙarni da dama na sauye-sauyen sarauta da kuma haɗin Norway da Denmark da Sweden, Norway ta sake samun cikakkiyar masarauta mai cin gashin kanta a 1905. Tun daga wannan lokacin, sarakunan Norway suka kasance kamar haka
- Christian Frederik: ya yi mulkinsa a 1814.
- Charles II: ya fara mulki a 1814 zuwa 1818.
- Charles III John (Karl Johan): ya karɓi mulki a shekarar 1818 zuwa 1844
- Oscar I: Mulkinsa ya fara ne daga 1844 zuwa 1859.
- Charles IV: ya fara mulki daga 1859 zuwa 1872.
- Oscar II: ya fara mulkin sa a shekarar 1872–1905.
- Haakon VII: ya yi mulki a shekarar 1905 zuwa 1957.
- Olav V: mulkin sa ya fara a shekarar 1957 zuwa 1991.
- Harald V: shi ne sarkin Norway na yanzu, kuma ya hau gadon sarauta a ranar 17 ga Janairu 1991 bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Olav V.
Norway ƙasa ce da ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar haɗa tarihi mai zurfi, tsarin dimokuraɗiyya, kyakkyawan tsarin jin daɗin jama’a da kuma sarrafa albarkatun ƙasa cikin tsari. Ta kuma gina matsayi na musamman a duniya ta hanyar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, diflomasiyya da ƙoƙarin samar da zaman lafiya. Duk da ƙalubalen da take fuskanta, Norway na ci gaba da neman hanyoyin kare muhalli, bunƙasa tattalin arziki da kuma tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummarta. Matsayinta a harkokin duniya, da kuma yadda take amfani da albarkatunta wajen tsara makomar ƙasa, sun sa ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka cancanci a yi nazari a kansu.
Manazarta
Nikel, D. (2025, July 2). A brief history of Norway. Life in Norway.
Office of the Historian. (n.d.) Norway
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.